1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Adawa na zargin kotu da mara wa APC baya

Ubale Musa Mouhamadou Awal
February 6, 2026

A yayin da ake kara kusantar zabe, 'yan adawa na korafi game da kokarin alkalai na rushe daukacin tsarinsu ta hanyar hukunci da umurni a Najeriya, a yayin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi nisa a shirin tinkarar zabe.

https://p.dw.com/p/58Doa
Rahoto kan zargin da 'yan adawa ke yi wa kotu da mara wa APC baya
Rahoto kan zargin da 'yan adawa ke yi wa kotu da mara wa APC bayaHoto: Olamikan Gbemiga/AP Photo/picture alliance

Daukacin jam'iyyun adawa Kama daga NNPP ya zuwa PDP da Labour Party da ADC na cikin babban rudu, sakamakon jerin hukunci da umurnin da ke fitowa daga zauren shari'a na Najeriya. Sannun a hankali, kotu na barazanar komawa makabarta ga adawa da ke fuskantar rigingimu iri-iri a daidai lokacin da ya rage shekara guda a gudanar da babban zabe na kasa.

Karin bayani: Me ke faruwa da jam'iyyar adawar Najeriya PDP?

Rawar da alkalan ke takawa ta fara ta da hankali a fagen siyasa da ke dada nuna alamun sake dora Najeriya bisa turbar jam'iyya daya tilo ta APC. Amma Buba Galadima, jigo a bangaren adawa ya ce da kamar wuya bangaren adawa ta yi tasiri a yanayi da alkalai ke murde wuyar siyasa a kasar.

Bangaren Peter Obi da Atiku Abubakar na ganin cewa Bola Tinubu na samun goyon bayan kotu
Bangaren Peter Obi da Atiku Abubakar na ganin cewa Bola Tinubu na samun goyon bayan kotuHoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

A cikin tarihi, alamun tsoma bakin alkalai a fannin harkokin siyasa ya dada kamari ne a shekarar 1992 a lokacin da wani hukunci ya kare fatan Chief Mashood Abiola na shugabanci a kasar.

Ta ya ya APC ke amfana da kotu?

Sai dai a yayin da daukacin jam'iyyun adawa ke kokarin tsallake siradin kotu, jam'iyyar APC mai mulki na dada nisa a shirinta na dorawa bisa mulki na kasar. Sai dai Jamilu Jega, da ke zaman tsohon alkali a Najeriya, ya ce abin da ke faruwa a cikin gidan shari'a na da alamun neman bin kowa.

Karin bayani: Shin jam'iyyu adawa a Najeriya suna iya katabus?

A yanayi na rudani a cikin gidan adawa, akwai tsoron murde wuyan 'yan adawa na iya shafar ita kanta jam'iyyar APC mai mulki. Babban aikin da ke gaban masu tsintsiya na zaman shawo kan buri da kila mantawa da gidan alkalan a kokarin neman nasara a zabukan da ke tafe.

Jam'iyyar APC mai mulki ta yi nisa a shirinta na tinkarar zaben 2027
Jam'iyyar APC mai mulki ta yi nisa a shirinta na tinkarar zaben 2027Hoto: SAMUEL ALABI/AFP

Faruk BB Faruk, da ke sharhin kan batun siyasa, ya ce da akwai alamu na fahimta a tsakanin 'yan APC da shugabancin cikin gidan alkalai kan hanyar nasarar jam‘iyyar.

Karin bayani: Kururuwar neman sauya tsarin zaben Najeriya

A cikin watan Maris 2026 ne APC mai mulki a Najeriya ke shirin gudanar da babban zaben zama zakaran gwajin dafi cikin danyen ganyenta da alkalai na kasar.