IMARA - by Nanameera
IMARA - by Nanameera
© AMINA I IBRAHIM
*Nanameera*
*SADAUKARWA*
*This book na Dedicated to yhu SALMA AHMAD ISAH, Tabbas ke ta dabance a wajena ina
matuƙar jin daɗin kasancewar mu tare, Ubangiji ya saka maki da mafificin Alkhairi
ya ɗaukaka min ke my graphics designer😍 yasa kifi haka rabbi ya wadataki da farin
ciki mara yankewa 😍Really appreciate 🍬 tarh 🥺😍 ur stubborn friend Nanameera 🥰.*
*BOOK 1*
*Page 1*
*DOHA (QATAR)*
*Al-Udaid Kingdom*
*7:30 pm*
A nutse yake taka ƙasa, duk inda ya taka sai wajen ya amsa dalilin takalmin dake
ƙafafunsa, hannayensa zube cikin aljihun wandon dake jikinsa yanayin yanda yake
tafiyar zai tabbatar maka da ba ƙaramin mutum bane domin tafiya yake cikin isa da
taƙama. Yanda yake ɗaga ƙafartasa zuwa gaba haka itama take janye tata ƙafar zuwa
baya, yayin da mabayyanin tashin hankali ya wanzu akan fuskarta, ɗaga ƙafarta tayi
da niyyar yin baya taji ta maƙale jikin bango wanda hakan ke nuni da tazo ƙarshen
bathroom ɗin, fararen hannayenta ta sanya ta rufe fuskarta har sannan jikinta rawa
yake na tsananin tsoron da take ciki a hankali ya furzar da wani zazzafan numfashi
yana zare glasses ɗin dake maƙale kan farar fuskarsa ya zuba mata kyawawan idanunsa
yana kallonta frm head to toe wani irin yar-yar haka taji abu na bin jikinta wanda
ya samo asali dalilin kallon da yake mata kokari take tasamu zarafin ɗago fuskarta
amma ta gagara sai sauke numfashi take da sauri da sauri. Hannunsa ya sanya ya
shafi fuskarta dashi da sauri ta janye fuskar daga kallonsa wasu zafafan hawaye
suka shiga sintiri akan kuncinta girgiza kansa ya yi cikin wata kamilalliyar murya
yake furta
"My Baby girl meyasa kike son wahalar da zuciyar wanda yake sonki da gaskiya?,
Meyasa baki sona? kinsan irin yanda nakejin sonki cikin raina kuwa? Haba Imara ya
kamata ace kina tausayawa wannan zuciyar ki soni nikuma zan fitar dake daga cikin
wannan halin ƙuncin da kike ciki"
Wani raunataccen kuka ne ya kwace mata tana girgiza kanta ta haɗe hannayenta waje
ɗaya alamar roƙo tana kallonsa da idanunta wanda suka rine cikin wata iriyar murya
mai matuƙar rauni ta shiga furta
"Dan Allah dan Annabi ka rufamin asiri Ameer kaifa tamkar uba haka kake a gareni ko
ka manta matsayina ne? Ni ce fa Imara matar ɗanka Maheer dan Allah yallaɓai kadaina
furta wannan maganar wlh zan iya mutuwa dan Allah..." Ta ƙarashe maganar tana
fashewa da wani sabon kukan, ɗan murmushi Ameer ya yi ya juya yana takawa a hankali
har yaje gaban mirror ɗin dake maƙale jikin sink ya ƙurawa fuskarsa idanu babban
mutum ne dan aƙalla zai iya kaiwa 60-65yrs da haihuwa kana ganinsa kaga mutum mai
tarin kamala da haiba gameda kwarjini above 30s sannan ya juyo ya zuba mata idanu
ganin yanda take kuka idanunta a rufe kamar wacce aka ce an yiwa mutuwa kallon
shigar jikinta ya shiga yi wata doguwar riga ce Abaya black colour a jikinta kanta
babu ɗankwali gashinta duk ya barbare a fuskarta yarinya ce qarama dan bazata shige
18-19yrs ba sai rawar jiki take har sannan tana sake ɗauke fuskarta daga inda
takejin alamun yana kallonta. Gabanta ya ƙaraso ya kama hannunta tayi saurin
janyewa tana girgiza kanta murmushinsa mai kyau ya yi ya ce"shikenan Imara amma ki
sani ni Sheykh Fahad bin saleem al-kuwari bazan taɓa daina sonki ba kuma nayi miki
alƙawarin saina mallakeki ta kowace hanya Ma'assalama(Sai anjima)" yana gama faɗin
hakan ya fice daga bathroom ɗin, a hankali ta sulale ƙasa kan tiles ta fashe da
wani irin matsanancin kuka inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun shine kawai abinda
bakinta ke iya furtawa wace irin masifa ce wannan ke neman shigowa rayuwarta bayan
wacce take ciki? Meyasa Ameer ke neman tarwatsa mata ragowar rayuwar data rage mata
rashin sanin wanda zai bata amsa ya sanya ta haɗe kanta tsakanin cinyoyinta tana
cigaba da kukanta wanda batasan ranar dainawarsa ba.
Turus ya yi bakin bathroom ɗin yana kallonta ganin yanda ta cure waje ɗaya tana
kuka wani tsaki yaja sannan ya ƙarasa cikin zafin nama yana zuwa ya jawo kanta
wanda hakan ya sanya ta fashe da wani sabon kukan tana riƙe hannunsa fincikota ya
yi yana janta a ƙasa har suka baro bathroom ɗin yana tafe da ita tana kuka ya buɗe
wani babban ɗaki ya jefata ciki rufe ɗakin ya yi ya juyo yana kallonta da idanunsa
wanda suka rine saboda ɓacin rai sai huci yake ya gaza furta komai Ita kuwa maƙale
jikinta tayi tana cigaba da rera kukanta
"Wai ke me kika ɗauki kanki a gidan nan? Gani kike kamar ke wata abar damuwa ce? Ko
kuma kina tunanin yanda ake cemiki Gimbiya haka abun yake? To bari kiji ke bakomai
bace face Dolly wacce za'a yi amfani dake wajen cimma burin wannan masarautar
saboda haka ki wani daina ɗaukan kanki wata ki dinga tunawa dake ƴar matsiyata ce
wacce aka ɗauko ki cikin wahala kuma zaki ƙare cikinta!"
"Keeeeee!"
Da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa ganin yanda ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan table ɗin
dake gefenta yana kallonta sai kuma ya yatsine fuska ya ce"kidaina wannan koke-
koken da babu inda zai kaiki ki maida hankali kan abubuwan dana faɗa miki idan har
baki maida hankalinki kin koyi komai ba zakisha baƙar wahala cikin Al-Udaid" goge
idanunta tayi tana kallonsa sai kuma ta ce"me kuma kakeson nayi? nagaji yallaɓai
kawai ka mayar dani gida inda ka ɗaukoni na huta da wannan masifar wacce kuke neman
jefani ciki ni bansan komai gameda rayuwarku ba kuma wlh bana fatan na sani dan
girman Allah kamayar dani gida dan Allah..." Ta ƙarashe maganar tana kuka taɓe
bakinsa ya yi ya miƙe tsaye ya dafa table ɗin gabansa yana mata wani shegen kallo
ya ce" ya sunanki?"
"IMARA!"
Ta bashi amsa itama tana kallonsa, da wani irin ƙarfi ya daki table ɗin gabansa nan
take ya tsage ya ɗago idanunsa yana kallonta sauke nata idanun tayi ganin yanda ya
haɗe fuska kamar hadari cikeda masifa yake faɗin
"Koda wasa idan na sake jin kin ambaci wannan sunan saina yi miki abinda zaki daɗe
baki manta ba a rayuwarki KATALINA shine sunan dana zaɓa miki kuma da haka nakeson
a kiraki daga rana mai irinta yau ki manta da sunanki IMARA ki sanya a ranki ke
KATALINA ce idan ba haka ba..." Ya cije lips ɗinsa wanda suka jiƙe saboda masifar
da yake
Cakk ya tsaya a bakin ƙofar hannayensa zube cikin aljihu amma bai juyo ba tasowa
tayi tazo har gabansa tana kallon bayansa ta cigaba da faɗin "Zaka kasheni ne? Koko
zaka mayar dani wajen iyayena? Ko kuma sakina zakayi? Ni ba Katalina ba ce kuma
bazan amsa sunan da banawa ba koda kuwa a ce hakan na nufin rasa rayuwata ni IMARA
shine sunana!".
Zaune ya samesu suna magana ƙasa-ƙasa yana zuwa ya kara kunnensa a bayansu juyowa
sukayi duka ta dungure masa kai
"Ochh! Shamma akwai zafi fa" ya faɗa yana kwaɓe fuska harararsa Shamma tayi ta
ce"gulma babu kyau Maheer" "shuu Ummi" ya faɗa yana zama gefenta kansa ya ɗora bisa
cinyarta tashiga shafa masa cikeda so da ƙauna take faɗin" ka dinga rufe kanka kaga
akwai sanyi" gyaɗa mata kai ya yi yana lumshe idanunsa saboda daɗin shafar kan da
yakeji gan haka yasa Ameer wanda tun ɗazu ke binsu da idanu ya ce a nutse
"Ya maganar Companyn Udaid Maheer?" Tashi zaune ya yi yana fuskantar mahaifin nasa
cikin girmamawa ya ce"muna iya bakin ƙoƙari Ameer komai yana tafiya yanda ya kamata
da yardar Allah" jinjina kai ya yi ya miƙe yana gyara zaman alkyabbar jikinsa ya
ce"Allah ya taimaka" Ameen Maheer ya ce shi kuma Ameer ya yi waje yana tafiya
cikeda nutsuwa wacce tagama ratsa shi.
A hankali take buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi da mamaki ta ƙarasa buɗesu
tana murza idanun ganin inda tayi baccin jiki babu kwari Imara ta tashi kai tsaye
kuma wankan daya kawota ta fara tana gamawa ta fito cikin towel tana tsane jikinta
jikin mirror ɗin wajen ta tsaya tana kallon fuskarta gaba ɗaya ta sake ramewa kamar
ba ita ba fuska ta sakeyi ƴar ƙarama da ita kyakkyawar saƙar dake maƙale a wuyanta
ta zubawa idanu
Yammacin Alhamis ne yanayin garin lokacin sanyi ne hakan yasa ko'ina na ɗan ƙaramin
ƙauyen ya ɗauki sanyi irin mai shiga jikin nan, a hankali ta kamo hannunta ta riƙe
cikin nata bakinta na rawa take furta
"IMARA ki kula da rayuwa ki yarda da duk ƙaddarar data zo miki ba lallai yanzu ki
fahimci abinda yake akwai ba amma tabbas watarana zaki gane abinda nake yawan gaya
miki idan kinada rabo zaki iya haɗuwa da iyayenki idan kuma ubangiji bai ƙadarta ba
to shikenan ke dasu har abada, hannunta ta sanya cikin samirar dake gefenta ta xaro
wata kyakkyawar sarƙa sai kyalli take cikin kakkarwar hannu ta danƙa mata cikin
nata siririn hannun tana kallonta da idanunta wanda suka fara rufewa ta ce"wannan
ita kaɗai ce ragowar abinda yake mallakinki ki kula da ita karki bari tabar wuyanki
IMARA domin ita ɗin ƙaddararki ce ki kul..." Tsit ɗan ƙaramin ɗakin ya ɗauki shiru
na wasu sakwanni kafin Imara ta mayar da idanunta kan mahaifiyar tata ta kalleta da
son sanin abinda ya sanya tayi shiru saidai yanda taga idanunta sun ƙafe ya sanya
ta saki wani razanannen ihu
"Ummaaaaaaaa!"
Da sauri ta dafe ƙirjinta tana sake taɓa wuyanta har sannan sarƙar tana nan wasu
hawaye Masu kamada na kewa suka shiga zirarowa kan kyakkyawar fuskanta a hankali ta
sanya hannayenta ta share hawayen sannan ta ɗauki rigar dake maƙale jikin ƙarfen ta
dinga binta da kallo yama za'a yi ta sanya irin wadannan kayan? akanme za'a mayar
da ita wata can daban wacce ba ita ba? menene dalilin daya sanyama take kamada
Katalinan tasu? Wace ma KATALINAN?, Taɓe bakinta ta yi rashin sanin amsar
tambayoyin nata ta ɗaga rigar tana sake juyata kamar zatayi kuka haka ta sanya
rigar.
A babban kitchen ɗin masarautar suke tsaye kowa da abinda yake yi ganin sunyi sauri
sun kammala abinda za'a ci da daddare, shigowa tayi tana sanye da wata riga t-shirt
fara sai wani jeans trouser wanda ya matseta sosai gashin kanta wanda yasha gyara
ya zubo har gadon bayanta cikeda ladabi suka sunkuya dukansu suka gaisheta da idanu
ta bisu sai kuma ta nufi wajen carbinet ta ɗauko wani glass cup da idanu suka shiga
binta sanin halinta kuma yasa babu wanda ya yi yunƙurin karɓar aikin da take
"A'a mene haka nake gani?" Da sauri Joda da ɗago manyan idanunta tana kallon Immi
da tashi kitchen ɗin cikin faɗa take kallon maids ɗin tana cewa" mene amfaninku
kuna ganinta babu wanda zai yi tunanin karɓar aikin da take ko kun manta matsayinta
ne cikin wannan fadar? naga..."
"Hyyyy Immi ni ce ban saka su kinsan banason ƙazanta so ban yarda da tsaftarsu ba
kwata-kwata calm down" kallonta Immi tayi sai kuma ta jinjina kai ta ce"nayi zaton
wani abun suke son fitowa dashi a cikin fadar nan, na fuskanci ba ƙaunarmu ake a
gidan nan ba kawai dan babu yanda aka iya damu ne kuma nan bada jimawa ba fadar
zata dawo hannunmu" taɓe baki Joda tayi bata sake cewa komai ba ta juya ta fice
daga kitchen ɗin dan ba kasafai ta fiye son hayaniya ba saida Immi ta gama
sababinta sannan ta fice daga kitchen ɗin tana tafiya cikeda izza da ƙasaita.
A hankali take tafiya tana jan rigar jikinta a ƙoƙarinta naganin rigar ta saukar
mata ƙasa wata irin riga ce wacce ta tsaya iya gwuiwarta fararen ƙafafunta sun
bayyana daga saman riga mai irin half shoulder ɗin nan ce hakan yasa har saida
tudun breast ɗinta ya fito ta cikin rigar, sosai necklace ɗin wuyanta ta ƙarawa
kwalliyar tata kyau tayi kamar wata ƴar tsana gwanin ban sha'awa saidai gaba ɗaya
ba daɗin jikinta take jiba dan bata saba irin wannan sheɗancin shigar ba a hankali
take taka ƙasa saboda hills ɗin takalman dake ƙafarta wanda suke neman kayar da
ita, tunda ta tawo yake zuba mata lulu eyes ɗinsa yana kallonta frm head to toe
ganin yanda take tafiya tana wani cure jikinta ya sanya ya taɓe baki cikin takunsa
na isa ya ƙaraso gabanta sunkuyar da kanta tayi tana wasada fingers ɗinta hannun
nata ya kalla ganinsu zara-zara sai kuma ya mayar da idanunsa fuskarta wacce ta
faɗa sosai hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta ɗauke kanta tayi tana kallon gefe ya
riko fuskar tata ya yi copping face ɗinsu suna shaƙar ƙamshin juna ya ce"...*
*****Tunda suka fara taka stairs ɗin haɗɗaɗen benen fadar ake binsu da kallo
yanayin yanda suke tafiya a hankali kuma cikin nutsuwa ba ƙaramin kyau ya yi musu
ba, kowa na parlon akwai abinda yake saƙawa acikin ransa ganin irin kallon da ake
musu ya sanya Maheer sake matse hannunta cikin nasa fuskarsa a haɗe babu alamar
fara'a suka ƙarasa sakkowa, wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Dameer ya sauke sai kuma
ya ɗauke kansa murmushi Shamma tayi tana kallon Imara ta ce" wow dear kinyi kyau
Masha Allah, allahumma bareek" ɗan murmushi Imara ta saki tana kallon Shamma sai
kuma ta juyar da kanta wanda kai tsaye ya faɗa cikin idanun Ameer, wata irin bugawa
zuciyoyinsu sukayi a tare kowa da kalar nasa tashin hankali a nutse yake bin shigar
jikinta da kallo sai kuma yaja idanunsa ya lumshe jin yanda kansa ke barazanar
tsagewa bai ce komai ba ya miƙe yana dogara sandarsa da mamaki Shamma ta ce" a'a
Ameer ina zaka kuma bayan bakaci abinci ba?" Batareda ya juyo ba ya ce"
Alhamdulillah" da idanu kawai mutanen wajen suka bi shi har ya haye saman fadar kai
tsaye kuma apartment ɗinsa ya nufa.
Yana shiga ya zare alkyabbar jikinsa ya rage daga shi sai Jallabiya ya shige
toilet, a jikin sink ya tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarsa a mudubi kafin a
hankali kuma wani gudan jini ya fito daga bakinsa hancinsa ya fara zubar da jini
yana cikin wannan yanayin na wasu mintuna kafin ya buɗe idanunsa wanda suke rine na
tsananin azaba famfo ya kunna ya tari ruwa ya wanke bakinsa da fuskarsa gemunsa na
ɗigar ruwa ya sanya tafin hannunsa ya goge fuskar tasa sannan ya juya ya fita.
Cikin dare tana kwance ya shigo yana sanye cikin wasu pyjamas white colour ya ɗora
hula akansa tsayawa ya yi jikin ƙarfen gadon ya zuba mata idanu ganin yanda take
baccinta a hankali lumshe idanunsa ya yi ganin yanda tayi masa wani irin kyau kamar
ya ɗauketa ya mayar da ita nasa ɗakin ya kwantar da ita gefensa yana shafa kanta
haka yaji, wata iskace ta kaɗa wacce ta sanyata juyawa da niyyar sauya ɓari
idanunta ya sauka cikin nasa da sauri ta miƙe zaune tana ja baya cikin tashin
hankali murya can ƙasa take faɗin
"Nashiga uku Ameer dan Allah dan Annabi ka koma ɗaki kar wani yazo ya ganka wlh
nashiga uku, kaifa sirikina ne matsayin mahaifi nake kallonka Ameer dan Allah karka
karyamin zuciya kaji tausayina wlh idan Maheer ya gano wannan alaƙar bazai yafe
mana ba dagani har kai Ameer ni ƴarka ce wacce zaka yiwa faɗa idan kaga ina shirin
aikata ba daidai ba bai kamata ace kaine wanda zaka nemi aikata irin wannan
mummunan abun gareni ba" ta ƙarashe maganar tana sakin wani marayan kuka, murmushi
ya yi ya tako har inda take ya zauna gefen gadon ya kama hannunta yana murzawa a
hankali cikin nutsuwa yake cewa
"Babyn Ameer ya kamata ki tausayawa Ameer ɗinki ina cikin matsala zuciyata zafi
takemin a duk sanda na ganki da Maheer inajin kamar na kwaceki daga hannunsa ki
yarda da Ameer zai baki farin ciki mara yankewa zan zame miki garkuwa zan mayar
dake Sarauniyar Udaid kinji Lolona"
*©AMEENA I IBRAHIM*
*Nanameera#*
*Fashion gurl#*
*IMARA💋#*. *IMARA 💋💋*
*© AMEENA I IBRAHIM*
*Nanameera ✍️*
*Page 2*
"A'a Ameer dan Allah ka rufamin asiri wlh zuciyata zata iya tarwatsewa idan har ka
cigaba da yimin irin wadannan abubuwa..." Cak maganar tata ta tsaya ganin hawaye na
sintiri kan fuskarsa baki buɗe Imara tashiga kallonsa sai kuma tashiga girgiza
kanta hawaye na bin kuncinta, Ameer bai sake cewa komai ba ya miƙe tsaye yana riƙe
da sandarsa ya fice daga ɗakin hannayenta biyu ta ɗora aka ta fashe da wani irin
kuka mai ban tausayi wace irin masifa ce haka?. A hankali ta tashi daga kan gadon
tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a jiki ta fice daga bedroom ɗin nata,
tafiya take tana leƙe-leƙe amma babu wanda taci karo dashi har ta ƙaraso wajen
swimming pool ɗin haskene a wajen tamkar rana a hankali ta ƙarasa wajen kujerar
daya saba zama saidai kuma babu shi babu alamunsa ba ƙaramin mamaki hakan ya bawa
Imara ba above 5mins tana tsaye gaban kujerar kafin tabar wajen cikeda zulumi kai
tsaye kuma bedroom ɗinsa ta nufa tana zuwa ta tura ƙofar a hankali gabanta na
faɗuwa saidai ga mamakinta nanma baya nan da alama ma kwata-kwata bai shigo ɗakin
ba, jingina tayi da jikin ƙofar tana tunanin inda Maheer ya tafi da wannan tsohon
daren ganin lokaci na shigewa yasa tabar ɗakin ta koma nata kwanciya tayi ta
lullaɓa da duvet saidai bacci ya gagari idanunta tana nan kwance har ta jiyo
kamilalliyar muryarsa yana kiran sallar farko hakan yasa kawai ta tashi ta shiga
toilet dan ɗauro alwala.
*6:45am*
A harabar fadar motarsa tayi parking ya fito yana sanye da wasu English wears ya
ɗora p-cap akansa yana tafe ana gaisheshi wani ya amsa wani kuma ya ɗaga musu hannu
har ya shigo cikin fadar zaune ya sameta tana sanye da wata t-shirt milk colour sai
wani mini skirt data sanya irin mai kama jikin nan tana operating system ɗin dake
gabanta kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai
"Barka Akii"
Sautin muryarta ta daki kunnensa lokacin da yake shirin hayewa sama ɗan juyowa ya
yi ya kalleta sai kuma ya saki fuskarsa ya ce" saukar yaushe Joda?" rufe system ɗin
tayi ta tashi tana tafiya cikin isa ta ƙaraso gabansa a jikin handle ɗin benen ta
ɗora kanta tana kallonsa ta ce" jiya nazo nd kuma ban ganka ba sai yanzu fatan kana
lpy" jinjina kansa ya yi ya ce" ina klao y mutanen Turkey ɗin" murmushi tayi wanda
ya fito da zallar kyanta ta ce" suna jiran ranar komawarka" samun kansa ya yi da
yin dariya ya shafa kansa ya ce" yep lemme take shower zamu yi magana" okay ta ce
sannan ya juya yabar wajen, da idanu Joda ta bisa har ya kammala hawa stairs ɗin
sannan tabar wajen tana zuwa ta ɗauki system ɗinta zata bar wajen
"Joda!"
Batareda ta juyo ba ta tsaya ya ƙaraso inda take yana murmushi ya ce" ni Meyasa
baki kulani" ɗago daradaran idanunta tayi ta watsa masa sai kuma ta ce"kana lpy"
bata jira amsar dazai bata ba tabar wajen, kwafa Dameer ya yi ya zauna kan kujera
ya yi crossing legs ɗinsa cikeda annashuwa yake faɗin
"Karki damu yarinya soon zanyi gyara komai zan tabbatar da cewa Udaid ta dawo
ƙarƙashin ikona!".
Tura ƙofar bedroom ɗin ya yi ya hangota zaune kan stool tana ƙoƙarin gyara gashin
kanta taɓe baki ya yi sannan ƙaraso gabanta yana kallon fuskarta ta jikin mirror
ɗin gabanta ya ce"idan kin gama akwai kaya a bedroom an ajiye miki kije ki ɗauka su
zaki saka" yana faɗin hakan ya juya zai tafi
"Wait!"
Cak ya tsaya ya juyo yana kallonta ya ce"akwai wani abun ne?" Tasowa tayi tana
kallonsa ta ce"inada kayan da zan saka anan beside ma kuma ina kaje da daddare
banganka ba" wani banzan kallo Maheer ya watsa mata baice komai ba kuma ya yi
ficewarsa. Da idanu Imara ta bishi sai kuma takoma ta cigaba da abinda take, fitowa
tayi cikin wata doguwar riga milk colour ga gyara gashinta rabi ya sauka gadon
bayanta rabi kuma yana ta gefen kafaɗarta a main parlor na fadar tasamu duk family
ɗin kowa yana harkar gabansa cikin sanyin jiki ta ƙaraso tana zuwa ta tsuguna gaban
Shamma
"Barka da safiya"
Shafa kanta Shamma tayi tana murmushi ta ce"how was ur night?" kanta a ƙasa tana
wasada fingers ɗinta ta ce"Alhamdulillah" jinjina kai Shamma tayi sannan ta ɗaga
idanunta tana kallonsa sanye yake da wasu suit black colour gashin kansa ya sha
gyara ya yi wani irin sihirtaccen kyau da hannu tayi masa alama da yazo ya ƙaraso
yana zuwa ya zauna gefenta ya ɗora kansa gefen kafaɗarta tana sauke ajiyar zuciya
shafa kansa tayi cikin taushin murya ta ce" Maheer what's wrong with you?" shiru ya
yi bai ce komai ba sai ajiyar zuciya da yake saukewa a jere a jere, fitowa ya yi
cikin hanzari yana gyara maɓallin hannunsa murmushi Immi tayi ta ce"magaji ka
fito?" gyaɗa mata kai ya yi ya ce"Eh Immi zani Company ne, Sabahul khair Shamma" ya
faɗa yana kallonta jinjina masa kai tayi fuskarta ɗauke da murmushi kamar koda
yaushe ta ce"ka tashi lpy Dameer?" "Alhamdulillah" ya bata amsa yana ƙoƙarin fita
daga fadar, da idanu Immi ta bishi sai kuma ta tashi tabi bayansa.
*** Tsaye yake gaban motarsa hannayensa naɗe cikin aljihu ya zuba mata ido yana
kallonta, "baka jina ne Dameer?" ɗan mirmushin gefen baki yayi sai kuma ya
ce"nafaɗa miki ki bar komai a hannuna Immi zan kula da komai amma sai kina neman
dagulan lissafi" ɗan juyawa tayi tana kallon ma'aikatan da suke ta kai komo a
compound ɗin sai kuma ta jawo gefen rigarsa tana kallonsa cikin ido ta ce"kai baka
gane abinda nake nuna maka idan har bamuyi komai a yanzu ba zamu faɗa cikin
danasani Udaid zata kwace daga hannunmu" hannunsa ya sanya ya hargitsa gashin kansa
wanda yake a gyara sai kuma ya furzar da wani zazzafan numfashi ya ce"shikenan naji
na kuma san abinda zanyi da fari dole mu janye wannan yarinyar dan ita ce babbar
matsalarmu a halin yanzu" "nasani kuma ina goyan bayanka duk abinda zaka aikata dan
ganin ka kwaci abinda yake mallakinka" jinjina mata kai ya yi sannan ya juya ya
shige mota yayi mata key not too long ya bar fadar. Tunda ta shiga kitchen ɗin take
kai komo tama rasa abinda zatayi jingina tayi da jikin carbinet tana sanya ɗan
yatsanta ɗaya a baki tana tsotsa kamar yanda tasaba, shigowa yayi yana kallonta bai
ce mata komai ba ya kama hannunta suka bar kitchen ɗin ɗan taɓe baki Joda tayi tana
gyara zaman Bluetooth ɗin dake kunneta a hankali ta ajiye cup ɗin hannunta ta fita,
kai tsaye ɗakinta tashiga tana zuwa ta zauna gefen royal bed ɗinta ta jawo wayarta
ta shiga danna wasu nambobi tana jin wayar ta fara ringing ta tashi ta shige toilet
ta rufe ƙofar
"Akwai buƙatar ka dawo Al-Udaid Damisa abubuwa na gab da lalacewa a tanan Al-Udaid
na buƙatar magaji!" Joda ta faɗa cikin tsantsar nutsuwa da kwantar da murya shiru
taji yayi kuma daman tanada tabbacin bazai magana ba tana ji ya katse kiran.
Jingina tayi da jikin bango tana sauke ajiyar zuciya.
*** Kallonsa take da manyan idanunta wanda sukayi jajur dasu sun kumbura ganin
yanda ta zuba masa idanu ya sanya ya matso kusada ita hannunsa ya sanya ya dungure
mata kai tayi saurin dafe kanta hawaye na biyo kuncinta hannunsa ya sanya ya kama
haɓarta yana kallon fuskarta ya ce"idan ina miki magana kina kafeni da idanu ranki
zai dinga ɓaci" turo baki tayi tana ƙoƙarin kwace fuskarta ta ce" daman akwai
watarana wacce raina yake ba a ɓace ba a gidan nan?" Baki buɗe Maheer ke kallonta
sai kuma ya yi kwafa ya janyo rigar dake maƙale jikin hanger ya wulla mata ya
ce"yanzu ba sai anjima ba ki sanyata ki fito karki bari nadawo kiranki"
"Amma..." Maganar ta tsaya cak ganin ya rufo mata ƙofar bathroom ɗin wasu zazzafan
hawaye suka fara sintiri kan fuskarta a hankali ta sulale a ƙasa gefen sink ta haɗe
gwuiwarta tana rushewa da wani kuka mai cin rai kwata-kwata lamarin Maheer ya fara
ɗaga mata hankali nema yake ya tarwatsa zuciyarta kullum tunaninta ɗaya wacece
KATALINA? Meyasa Maheer ya zaɓi ya mayar da ita KATALINA?!.
Tana fitowa ta ganshi tsaye hannayensa zube cikin aljihu da alama waya yake hakan
yasa taja ta tsaya a wajen saida ya kammala sannan ya kalleta ya ɗan taɓe baki ya
ce" ki saki jikinki ki daina wannan abun da kike ki sani ke yanzu matsayin Gimbiyar
Udaid kike dole ki koyi komai kuma ki ganeshi kamar yanda nafaɗa miki zan mayar
dake Katalina to bazan sare ba har sai naga kin zama kamar tan saboda haka ki
shirya!" Da idanu kawai Imara ke binsa sai kuma ta buɗe bakinta wanda takejin ya yi
mata nauyi ta ce"dan Allah zan iya tambayarka abu guda ɗaya?" yana kallon wani
wajen daban ya ce"tambayi" "Meyasa ka aureni? Kuma wacece KATALINA?" Kallonta ya yi
sai kuma ya yi murmushi ya ce" idan lokacin ki sani ya yi xaki sani" kafin tayi
magana taga ya juya ya bar wajen hakan yasa ta bisa da kallo sai kuma ta juya da
niyyar tafiya.
Cak! Imara ta tsaya tana tunanin muryar dan bata taɓa jin mai irinta cikin fadar ba
cikin takunta na isa ta ƙaraso gabanta tana sanye da riga da wando as usual ta raba
gashinta gida biyu rabi ya zuba bayanta rabi kuma gefen kafaɗarta da idanu Imara ta
bita kallo irin na mamaki kyakkyawace irin ajin farko ɗin nan tanada manyan idanu
masu ɗaukan hankali, cikin sanyin murya Imara ta ce"Eh inaso nasani inason sanin
dalilin daya sanya Maheer ya aureni meyasa kuma yakeson mayar dani wata daban
kuma..."
"Hyyyy what's wrong with you?, Kina ta magana baki gajiya I'm just asked u a single
question amma kina neman fasamin kai da hayaniya kinsan matsayinki a gidan nan
kuwa? kinsan me zama matar Maheer yake nufi? Stupid!" Da idanu Imara tashiga bin
Joda har ta ɓacewa ganinta
"Ko wace ita take yiwa mutane masifa ohho!" Imara ta faɗa tana yin gaba abinta.
*** Tunda ya shiga yake zagaye office ɗin yana girgiza kai tamkar wani mahaukaci
kallonsa Ahlan ya yi sai kuma ya ce" wannan fa duk ba mafita bace Dameer idan har
kanason ganin ka kwaci Udaid dolene ka saita zuciyarka ka rage fushinka" kallonsa
Dameer ya yi da idanunsa wanda suka sauya launi sai ya ce"me zanyi Ahlan? Akanme
za'a dinga bawa Maheer abu ni ana banza dani? Maheer ya yimin abubuwa dayawa yasha
hanani samun abu shiyasa this time around billah sai naga bayansa yanda ko babu ran
Ameer ni ne Magaji!" Dafashi Ahlan ya yi ya ce"kayi komai abokina ka tsaya tsayin
daka ka kwatarwa kanka yanci kaima ɗan Ameer ne saboda haka kanada kowace dama
tazama shugaban Udaid".
Shamma na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da fadar ta ɗora ƙafa ɗaya
kan ɗaya wanda ke nuni da irin tata isar fitowa Immi tayi tana kallonta kamar zata
shige sai kuma ta ce"Barka da hutawa Shamma" jingina mata kai tayi ta ce" ykk?"
Yanda ta bata amsa ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba amma kawai ta dake ta juya ta
fice daga fadar taɓe baki Shamma tayi tana cigaba da kallonta, da gudu Joda ta fito
tana zuwa ta zauna gefen Ameer tana dariya ta ce"Ameer dan Allah kalli kaga" karɓar
system ɗin tata ya yi sai kuma ya kalleta ya yi murmushi ya ce"yanzu kinyi farin
ciki?" gyaɗa masa kai tayi tana murmushinta mai kyau dafa kanta ya yi ya ce"Allah
ya sanya albarka" "Ameen ya rabbi Shukran Ameer" jan kumatunta ya yi ya ce"haza
wajib" tashi tayi ta shige ciki da idanu Shamma ta bita sai kuma ta girgiza kai shi
kansa Ameer bai ji daɗi yanda ta rasheta ba amma ya ya zai yi haka ƙaddara ta zaɓar
musu.
Zaune take gefen swimming pool ɗin ta zubawa ruwan idanu yanayin yana tuna mata da
wasu shekaru da suka shuɗe cikin rayuwarta lokuta wanda bazata manta dasu ba duk da
batada wayo amma hakan bai hanata kasa tuna wani abu daga ciki ba duk da bata ganin
fuskarsa amma tana jin bugun zuciyarta na sauyawa a duk Lokacin da taga surarsa.
Tsugune take bakin Kogin tana ƙoƙarin ɗiban ruwa tanajin sanda yazo ya tsaya a
bayanta hakan yasa ta miƙe tana kallon fuskarsa da take a rufe ta ce" yauma ka sake
zuwa ko?, wai ya sunanka?" da idanu kawai taga yana binta hakan yasa ta tura baki
gaba tana harararsa ta ce"wannan kaman kurma baya magana, kai kana jina? Yayane
sunanka?" Shiru nan ma taji ya yi mata ta galla masa harara ta ɗora tulunta aka
tashige ta gefensa saida tayi nisa sannan ta tsaya ita kaɗai take cewa" to kodai
nayi masa turanci inaga baya jin Hausa" da wannan tunanin ta koma inda yake tsaye
har sannan tana kallonsa ta ce" kai what's ur name? Kanajin turanci? Ni sunana
Imara gurin granny na nazo wannan ƙauyen kai ya sunanka? ko kai bature ne? nima
mama ta ce inada kyau kai kaga kyan?" Ganin har sannan bai ce mata komai ba kuma
bai buɗe fuskarsa ba ya sanya ta haɗe rai tana ƙoƙarin fashewa da kuka ta sanya
hannunta a baki cikeda shagwaɓa take cewa"sai kai ta tsaiwa nonse kawai ni babu
ruwana ma dakai aljani kawai".
"Keeee!"
A ɗan firgice ta ɗago idanunta sai kuma ta sunkuyar da kanta "what are you
thinking?" Girgiza masa kai tayi tana ƙoƙarin tashi tsaye cikin rawar murya ta
ce"bab.bb.bakomai" taɓe baki ya yi ya ce"koma mene bai dameni ba kije Ameer na
kiranki" dafe ƙirjinta tayi tana gwalalo ido ta ce" Ameer kuma ni?" Da mamaki yake
kallonta ya ce"akwai matsala ne? ya ce kin masa laifi to kije yanzu ba sai anjima
ba ki kuma shirya gobe zaki fara zuwa school karki manta da sunanki KATALINA!"
Cikeda tsiwa ta ce" nifa wlh sunana IMARA!" haɓarta ya kama yana mata wani banzan
kallo ya ce" ba roƙonki nake ba idan har kinajin zaki iya to gobe idan kin fita
daga Udaid kice sunanki IMARA a sannan zaki gane kuskurenki sannan zan nuna miki
wane Maheer!" yana gama faɗin hakan ya juya ya bar wajen yana wuci. Dafe kanta tayi
tana sakin kuka ta ce"nashiga ukuna Allah ka taimakeni bazan iya ba" tafaɗa tana
fashewa da wani sabon kukan.
*** Around 10pm tana tsaye jikin mirror tana gyara kanta ya turo kofar ya shigo
batasan sanda ta saki comb ɗin hannunta ba tana girgiza kanta a hankali yake tafe
cikin nutsuwa ya ƙaraso gabanta ja da baya tafara bakinta na rawa ta kasa magana
"Lolo narh"
Ameer ya furta cikin wani iriyar murya mai rauni gaba ɗaya ya rame kamar bashi ba
manya-manyan idanunsa sun janye kaɗan kuma sun sauya launi daga farare zuwa ja
damuwa tagama bayyana akan fuskarsa, tsayawa yayi ya zuba mata idanu yana kallonta
ƙasa tayi da nata idanun wanda hawaye ya gama cikashi cikin sanyin murya take cewa"
dan darajar Annabi Ameer kayi haƙuri kabar wannan tunanin a cikin ranka wlh nasan
shaiɗan ne kayi yaƙi dashi kamar yanda kake faɗa a masallaci ka taimaki rayuwata
kada ka jefani halin da bazan iya ba ka taimaka Ameer" tafaɗa tana haɗe hannayenta
waje ɗaya alamar roƙo, numfasawa ya yi cikin taushin murya yake cewa"Lolo nafi kowa
son na ganki cikin farin ciki nafi kowa damuwa dake a cikin fadar nan wlh nafi kowa
sonki nine na dace dake ba Maheer ba ki taimaka ki fahimci Ameer ɗinki zan shiga
wani hali idan har kika cigaba da watsar da buƙatata koda yaushe zuciyata zafi
takemin inaji kamar zan mutu dan Allah Lolo ki taimaki Ameer" girgiza kanta tayi
tana ƙunshe bakinta gudun kada kukanta ya fito ta ce" inna'lil lahi wa ina ilayhi
raji'uun Auzubillahi minna shaiɗanin rajeem astgfirullah ya Allah dan Allah Ameer
kadaina faɗar wannan maganar wlh zuciyata zata buga nashiga uku ni IMARA!" Shiru
Ameer ya yi ya zuba mata ido yana kallon yanda take kuka kamar ranta zai fita above
5mins sannan ya yi murmushi yana kallonta ya ce"kina iya kirana da duk sunan da
kikaso Lolo naji nine shaiɗani amma inason ki sani bazan taɓa iya daina sonki ba
IMARA koda kuwa a ce soyayyarki zatayi ajalina Ni Fahad ke nakeso kuma zan cigaba
da sonki har zuwa ƙarshen numfashina a duniya nasan koda bana raye watarana zaki so
ni" banda kuka babu abinda IMARA keyi gaba ɗaya ta birkita kanta tashi ya yi yana
dogara sandarsa ya yi waje daidai nan Maheer ya shigo ɗakin da sauri ta juya masa
baya ta goge hawayen fuskarta sannan ta juyo tana cigaba da taje kanta
"Lafiyarki?"
Girgiza masa kai tayi tana ƙoƙarin ɓoye hawayen dake shirin sauka kan fuskarta ɗaga
kafaɗarsa ya yi irin i don't care ɗin nan ya ce" anyway ga kayana an kawo maki ki
tabbata gobe kin shirya kamar yanda na nuna miki kafin ki fito" yana gama faɗin
hakan ya bar ɗakin da idanu Imara ta bishi zuciyarta na mata suya wane irin miji ne
Maheer????.
Tana gama gyara kanta ta ɗauki wata sleeping dress ma ɗan kauri ta sanya a jikinta
ta haɗe gashinta waje guda ta ɗaure gudun kar ya dameta ta shafa turare sannan ta
ɗauki wata hula ta rufe gashin kanta, agogon gefenta ta kalla taga kusan 11pm hakan
yasa kawai ta fice daga ɗakin kai tsaye kuma apartment ɗin Maheer ta nufa tana zuwa
without knocking ta tura ƙofar ɗakin turus tayi tana kallonsu ganin yanda take
zaune ta ɗora kanta akan cinyarsa tana masa hira sai dariya yake yana ganinta ya
haɗe rai Joda ta miƙe tsaye tana kallonta sai kuma ta taɓe baki ta kalleshi ta
ce"saida safe Akii" miƙewa tsaye ya yi shima ya sumbaci goshinta ya ce"laylatan
sa'eedan" murmushi tayi sannan ta ratsa ta gefen Imara ta fita, Maheer bai sake
kallon inda take ba ya shige toilet jiki a sanyaye ta ƙarasa gefen gadon ta zauna
lokaci ɗaya hawaye ya kawo kan fuskarta. Kusan 30mins kafin ya fito sanye da
bathrobe sai ɗan ƙaramin towel yana goge gashin kansa tana kallonsa har ya kammala
duk abinda yake ya shirya cikin pyjamas maroon colour wanda sukayi masa kyau cikin
takunsa na isa ya ƙaraso gefen gadon ya zauna yana kallonta ya ce" keeee!" ɗago
idanunta tayi ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana wasada fingers ɗinta.
"Me kike anan?" Cikin sanyin jiki ta ce" ni tsoro nakeji bazan iya kwana ni kaɗai
ba anan zan kwana" a fusace ya juyo yana kallonta ya ce".
*Nanameera#*
*Fashion gurl 🥰#*
*IMARA 💋#*
*LOLO#*
*Writer ✍️#**Chapter 3:*
"Get out!" Abinda kawai ya furta kenan yana kafeta da manyan idanunsa ɗan turo baki
tayi sai kuma ta ce"ni bazan iya kwana ni kaɗai ba wlh saidai na kwanta a nan a
ƙasa" buɗe idanunsa ya yi a kanta yana yi mata wani mugun kallo cikin kakkausar
murya ya ce"idan nayi kamada abokin wasanki to ki cigaba da zama anan" da haka ya
juya mata baya yana rufe gaba ɗaya jikinsa da duvet, bayansa Imara tabi da kallo
hawaye na zubowa kan fuskarta me Maheer yake nufi da ita?, Wane irin mutum ne shi?.
***A nutse ya turo kofar ɗakin yana sanye cikin wasu suit black colour as usual
idanunsa maƙale da glasses, lumshe idanunsa ya yi saboda ƙamshin turaren daya daki
hancinsa kusan 2mins kafin ya buɗe idanunsa akanta sanye take cikin wata Abaya
black colour ta yi rolling veil ɗin abayar a fuskarta ƴar ƙaramar round face ɗinta
ta fito sosai gwanin sha'awa ɗauke idanunta tayi daga kallonsa fuskanta a haɗe babu
walwala bai ce mata komai ba ya kamo hannunta ya matse cikin nasa ya tallafi
fuskarta akan tafin hannunsa yana bin ta da kallo hannunsa ya sanya ya gyara mata
gashinta wanda yake kwance gefen fuskarta ta yi saurin lumshe idanunta tana ƙamƙame
jikinta waje guda batayi aune ba taji dungure mata kai tayi baya zata fadi ya sanya
ƙafa ya tareta yana yi mata wani irin kallo ya ce"ke har abada bazaki ji magana ba
ko?" Ɗago idanunta wanda suka sauya kala tayi tana kallonsa da rashin fahimta ta
ce"me kuma nayi maka?" Ta faɗa tana dafe goshinta, harararta ya yi bai sake ce mata
komai ba ya juya ya bar ɗakin. A dinning area ya samesu duka kowa na cin abincinsa
cikeda nutsuwa wajen Shamma ya ƙarasa ya rungumeta yana murmushi ya ce" Barka da
safiya Shamma" murmushi ta yi ta ce" ka tashi lpy?" "Alhamdulillah" ya ƙarasa wajen
Ameer sunkuyawa ya yi a gabansa ya ɗora kansa bisa cinyarsa yana sakin wata ajiyar
zuciya wani yalwataccen murmushi Ameer ya yi yana shafa sumar wacce tasha gyara ya
ce"Ka tashi lpy?" ɗago kansa ya yi yana murmushi ya ce"Alhamdulillah Ameer" jinjina
kai Ameer ya yi yana zamesa daga jikinsa ya mike tsaye dai-dai lokacin da ta shigo
dinning area ɗin kallo ɗaya Ameer ya yi mata ya ɗauke kansa yabar parlon zuciyarsa
na ayyana masa abubuwa dayawa da idanu kawai Imara ta bisa sai kuma ta sunkuyar da
kanta ta ƙaraso wajensu Shamma ta gaishesu kamar yanda ta saba. Kujerar gefensa ta
zauna sai juya abincin gabanta take ta gagara kai shi bakinta kallonta Shamma ta yi
ta ce" ki ci abinci mana daughter ko bakison school ɗin?" ɗan murmushi ta yi tana
girgiza kanta ta kai abincin bakinta,
"Maybe bata saba irin wannan rayuwar ba shiyasa ta fito daga ƙabilar matsiyata dole
ta dinga kasa cin abinci"
Cak! Imara ta tsaya da tauna abincin da takeyi ta zubawa Immi idanu wanda suka gama
sauya kala ba ita kaɗai ba kowa ma na wajen kallon Immi yake, ajiye spoon ɗin
hannunsa ya yi ya miƙe tsaye bai kalli kowa ba ya kama hannunta suka bar wajen da
idanu Joda ta bisu sai kuma ta taɓe baki.
Fitowa ya yi daga office ɗin yana kallonta ya ce"idan har kika aikata wani abu
wanda za'a gane ke ba Katalina ba ce wlh sai na saki dana sani" kallonsa kawai tayi
sai kuma ta taɓe baki tana kallon wani wajen bai sake ce mata komai ba ya fice daga
wajen ita kuma tabi wanda zai nuna mata class ɗin nasu. Babban class mai matukar
kyau da ɗaukan hankali komai na amfanin student an tanada a cikinsa a hankali take
wara idanunta tana kallon tsirarun mutanen dake cikinsa wanda basu fi 20 ba suna
ganinta suka tashi suna ihu sai murna suke
"Welcome back friend kin dawo?" juyawa Imara tayi tana kallon wacce take mata
magana ganin yanda take dariya yasa ta yi murmushi itama wanda yake iya laɓɓanta ta
gyaɗa mata kai dukda bata gane inda ta dosa ba hannunta taji an kama ta juya tana
kallonta bata ce komai ta zaunar da ita gefenta tana kallonta ta ce"munyi kewarki
sosai Katalina yanzu kin ji sauƙi?" da idanu kawai Imara ke bin ta tama rasa abin
da zata ce gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta gaza gane abin da suke nufi shin wa ce
Katalina? Meyasa suke zaton ita Katalina ce? kuma ina Katalinan?, Jijjigatan da
akayi ya sanya ta ɗago manyan idanunta tana kallonta ta ce"Eh I'm fine" murmushi
tayi ta ce"Allah ya ƙara lafiya Ina Maheer?" " Ya tafi" Imara ta ce da sauri tana
sunkuyar da kanta, da gudu ta ƙaraso zata ta ɓata tayi saurin riketa ganin yanda ta
ɗora kanta kan desk idanunta a rufe ta ce"bari Nora inaga bata jin daɗi na ganta
wani iri" kwaɓe fuska ta yi ta ce"Rania na ƙagu nayi magana da Katalina wlh nayi
kewarta ki barni ko sau ɗaya ne nayi mata magana" girgiza kai Rania tayi tana gyara
gashinta da ya rufe mata fuska ta ce" ki bari sai anjima please" numfasawa tayi ta
ce"shikenan Allah ya kaimu" "Ameen".
*** Tunda ta shigo gidan take zaune a fadar tayi shiru tunani ne kala-kala cikin
zuciyarta jira take Maheer ya dawo ta tambayeshi amma har yanzu shiru bai shigo
fadar ba, fitowa tayi tana sanya da wata riga iya gwuiwa ta gyara gashin kanta sai
sheƙi yake hannunta riƙe da wayarta tana dannawa hankali kwance tana zuwa ta nemi
waje ta zauna a kujera ta ɗora ƙafarta saman kujerar tana cigaba da danna wayarta
da kallo Imara ta bita sai kuma tayi tunanin ta tambayeta tunda taji rannan ta fara
maganar da wannan tunanin ta daga ta kalleta sai kuma ta ce"daman kince za ki
faɗamin wace Katalina to ki faɗamin yanzu" tayi maganar tana langwaɓar da kanta
gefe ɗaya, tamkar tana magana da kujerar gabanta haka Joda tayi mata bazaka taɓa
cewa da ita take maganar ba ganin tayi mata banza ya sanya Imara ta harareta tana
ala wadan hali irin nata. Tana ƙoƙarin tashi ya shigo hannunsa riƙe da wata kwalba
ƴar ƙarama sai tangaɗi yake a matuƙar tsorace Imara ke kallonsa ganin yanda ya yo
kanta tashi Joda tayi tana kallonsa sai kuma ta girgiza kanta da gudu Imara ta nufi
stairs ganin yanda yake ƙoƙarin cimmata da sauri shima ya hau saman duk inda tayi
yana bin ta, karo tayi da Ameer da yake ƙoƙarin shiga nasa apartment ɗin yana
dogara sandarsa cikeda nutsuwa bayansa tashige tana kuka cikin tashin hankali take
faɗin
"Dan Allah Ameer ka taimaka mini wayyo Ummana zai kasheni dan Allah Ameer!" Cikin
wata murya irinta bugaggu Dameer ya ce" babu wanda ya isa ya hanani gamawa dake a
wannan daren dole sai kin mutu ni ne zanyi ajalinki..." Ya ƙarasa maganar yana
ƙoƙarin yin inda take. Ƙara ta saki tana riƙe alkyabbar jikin Ameer ba tareda tasan
tayi hakan ba, wata irin ajiyar zuciya Ameer ya sauke jin yanda jikinta ya haɗu da
nasa ya runtse idanunsa yana jin wani abu na taso masa tun daga ƙafafunsa, baisan
sanda Dameer ya fincikota daga jikinsa ba ya haɗata da jikin bango ya shaƙe mata
wuya tuni idanun Imara suka firfito waje sai miƙa hannunta take hawaye na zuba daga
idanun da gudu Joda tazo ta dinga dukansa amma hakan bai sa ya saketa ba saima sake
shaƙeta da yayi yana wani irin cije leɓe ihun da Joda keyi ne ya sanya mutanen
fadar suka jiyo da gudu kuma suka ƙaraso wajen ana masa magana amma kamar ma ba
dashi ake ba.
Hannu ɗaya ya sanya ya fincikeshi daga jikinta ta faɗi ƙasa nan sumammiya ya juyo
da fuskarsa ya wanke shi da mari har biyu bai gama buɗe idanun ba ya sake masa wani
ya shaƙe masa wuya yana kallonsa da idanunsa wanda sukayi jajur dasu ganin yana
ƙaƙarin mutuwa ya sanya Immi ta ƙaraso gabansu tana kallonsa cikin kwantar da murya
ta ce"yi haƙuri magaji ka rabu dashi kaga ƙaninka ne sake shi" tamkar tana magana
da dutse haka Maheer ya yi mata madadin ya sake shi sai ma sake shaƙesa da ya yi
above 5mins kafin Ameer ya ƙaraso gabansa ya kama hannunsa bai ce masa komai ba
suka bar wajen.
***A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi kallon inda take a
kwance tayi sai kuma ta miƙe zaune tana shafa wuyanta saboda wani raɗaɗi da taji
yana yi mata ɗan turo bakinta tayi tana tuno yanda ya shaƙe mata wuya kwaɓe fuska
ta yi ta ce"mugu kawai" ta faɗa tana tura baki gaba, shigowa ya yi hannayensa zube
a aljihun trouser ɗin jikinsa ya tsaya a kanta yana kallonta kwaɓe fuska ta yi ta
"kaga abinda ya yimin ko?" jin ya yi shiru yasa ta sake cewa "kuma da zafi sosai
kamar zan mutu wayyo Allahna..." sakar baki Maheer ya yi yana kallonta ganin yanda
take abu kamar ƙaramar yarinya girgiza kansa ya yi bai ce komai ba ya juya zai
fita. Da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce
"Yawwa daman ina ta jiranka xan tambayeka" tsayawa ya yi ba tareda ya juyo ba tana
wasada fingers ɗinta ta ce"daman yau a school ne aka dinga cemin Katalina kuma wai
ya jikina? Daman ita Katalina kamar mu ɗaya? kuma itama fara ce? Tana ina yanzu?
Wai batada lafiya nag..."
"Hyyyyy yimin shiru aku kawai kin fiye surutu karki sake tambayata wani abu kawai
duk wanda ya ce miki Katalina ki amsa sannan koda wasa idan kika ce ba sunanki bane
sai ranki ya ɓaci!" Ya fice daga ɗakin cikin tafiyarsa ta isa, buga ƙafarta tayi a
ƙasa kamar za tayi kuka ta ce" kullum baya bani amsa wai ni ce aku?" Sai kuma tayi
murmushi tana gyada kanta tuna wasu lokuta da suka shuɗe, komawa tayi ta kwanta kan
gadon idanunta a buɗe tayi nisa cikin tunanin da take taga mutum tsaye a kanta
cikin sauri ta tashi tana ja da baya akan gadon fuskarta a kwaɓe kamar zatayi kuka
tana kallonsa zama ya yi gefen gadon har sannan idanunsa na kanta kusan 2mins kafin
ya numfasa cikeda nutsuwa ya fara magana"Lolo narh! Ya jikin naki?" cikin rawar
murya ta ce"naji sauƙi Ameer" jinjina kansa ya yi yana ƙoƙarin ɓoye abin da yake
cikin ransa ya ce" har yanzu ina nan akan bakata ki yarda da Ameer bazai cutar dake
ba, ba sai kin faɗa min ba nasan ba daɗin zama da Maheer kike ba saboda haka ki
bani dama zan fitar dake daga cikin halin da kika shiga..." Ya ƙarashe maganar yana
kallon fuskarta to see her reaction. Ɗan turo baki Imara tayi tana langwaɓar da
kanta gefe ta ce"ka rufamin asiri Ameer wannan maganar ka daina yin ta dan
Allah..."
"Wace magana?", Maheer ya faɗa yana shigowa ɗakin hannunsa riƙe da system, a ɗan
razane Imara ta ce"bab...ba komai kawai akan abin da Dameer ya yimin ne" ajiye
system ɗin hannunsa ya yi a kan wani table ya zauna gefen Ameer yana murmushi ya
ce" karka damu Ameer babu abinda ya sameta ai" murmushinsa mai kyau ya yi yana
kallonta ya ce"haka tace min ai" sunkuyar da kanta tayi jin zuciyarta tayi wata
kyakkyawar bugawa bai sake cewa komai ba ya miƙe tsaye yana dogara sandarsa ya yi
hanyar waje.
"Maheer ka bata shawara taso wanda ya ke sonta a rayuwa karta wulaƙantashi yin
hakan babban zunubi ne" Ameer ya faɗa yana ƙoƙarin barin ɗakin, murmushi Maheer ya
yi ya ce"In sha Allah Ameer".
***Tana danna masa kansa da towel ta ce"koda wasa karka sake yin irin abin da kayi
yau Dameer akan me kasan ka bugu zaka shigo gida? Sannan mene haɗin ka da ita da
har kake neman kasheta? kuma dan rashin hankali a gaban kowa" ture hannunta ya yi
daga kansa yana wuci ya ce"Ni Immi ki daina wani yimin faɗa dole sai ta mutu dan
banason ganinta a cikin fadar nan kuma babu wanda ya isa ya dakatar dani!,
sannan..."
Wasu lafiyayyun maruka Immi ta sauke masa a fuska tana kallonsa fuskarta a haɗe
babu alamar fara'a ta ce"to kasani kanayin wani kuskure Udaid zata kwace maka
shashasha!" Dafe kuncinsa ya yi yana kafeta da idanunsa sai kuma ya yi kwafa ya
tashi ya fice daga bedroom ɗin kamar zai tashi sama.
JODA.
***Tsaye take jikin motarta tana sanye da English wears riga da wando ta tufke
gashinta waje guda tana danna wayarta, tun daga nesa yake kallonta yana murmushi
har ya ƙaraso gabanta kallonsa ta yi bata ce komai ba ta shige motar ganin haka ya
sa shima ya shige ɗaya site ɗin da wani irin speed taja motar suka bar wajen, a
wani restaurant tayi parking suka fito a tare ya kalleta sai kuma ya yi murmushi
harararsa tayi bata ce komai ba tashige ciki hakan yasa shima ya bita sai da ta
zauna sannan ta kalleshi cikin nutsuwa ta ce"ka daina yawan dariya dan Allah haba!"
murmushi ya sake yi yana kallonta ya ce"oh tanan kuma kika ɓullo?" ɗan ƙaramin
tsaki tayi tana kallonsa ta ce"bar wannan maganar akwai abinda yasa na kiraka kuma
yanada amfani saboda haka ka saurara kaji abinda zan ce please" ganin ya bata full
attention nasa ya sa tayi murmushi a karo na farko wanda ya yi matuƙar ƙara mata
kyau cikin siririyar muryarta ta fara magana
".
*Chapter 4*
"Nan da ƴan kwanaki zai dawo ƙasar nan kuma shigarsa Udaid na nufin abubuwa masu
yawa, saboda haka na shirya komai kuma ina buƙatar taimakon ka, Rasheed!" Gyara
zaman glasses ɗin fuskarsa ya yi yana kallonta ya ce"ina tare dake a kowane lokaci
kawai ki sanar dani abin da kika shirya" wani cute smile tayi ta cigaba da magana.
***A hankali take taka stairs din benan dan gaba ɗaya a tsorace take, "Habibty" a
dan firgice ta juyo ta saki wata ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta ta ce"Sabahul
khair Shamma (Barka da safiya Shamma), murmushi Shamma tayi tana kama hannunta ta
ce"why are you scared?" Ta marairaice fuska tana kallon Shamma bata ce komai ba, a
gefenta ta zaunar da ita bayan itama ta zauna tana kallonta ta ce"kar ki saka
damuwa a ranki babu abinda Dameer zai yi miki, ki cire incident din jiya a ranki
kinji baby" jinjina kanta tayi hawaye na kawo idanun nata ta ce" in sha Allah
Shamma" shafa kanta tayi tana murmushi ta ce"good girl" murmushin Imara ta mayar
mata sannan ta tashi tsaye tana kallonta ta ce"zan tafi school" "Allah ya kiyaye"
Ameen ta ce tana gyara zaman veil ɗin ta. Sound ɗin takalminsa ya sanya ta ɗago
kanta tana duban inda hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗin jikinsa ya sakko
fuska babu wata walwala yana zuwa ya gaisheda Shamma ta amsa cikeda fara'a bai cewa
Imara komai ba ya yi waje ta bi bayansa tana murguɗa masa baki.
Yana ƙoƙarin shiga motarsa yaga shigowar wata baƙuwar mota hakan yasa ya tsaya yana
kallon motar har tayi parking, waro idanunsa waje yayi ganin wacce ta fito daga
motar sanye take da wata riga irin mai kama jikin nan wacce ta tsaya iya cinyarta
fararen cinyoyinta duk sun fito waje sai gyara gashin kanta wanda ya ke ƙoƙarin
rufe mata fuska take tana ganinsa ta washe baki ta tawo da gudu da niyyar shigewa
jikinsa saurin matsawa ya yi yana kallonta hakan yasa ta dakata tana tsuke fuska ta
ce cikin wata siririyar murya
"Haba Akhii yaushe rabon dana ganka baka missing ɗina?" tabe bakinsa ya yi yana
ƙoƙarin buɗe motarsa ya ce"wane ya baki shawarar ki dawo?" watsa hannayenta tayi
alamar bata sani ba ya kalleta sai kuma ya shige motarsa, Imara tabi da kallo sai
kuma ta juya tabar wajen. Sun yi nisa da gida ta kalleshi ganin yanda yake tuƙinsa
cikeda nutsuwa ta tura baki gaba ta ce" kuma yau idan suka min magana me zan ce?"
Jin bai ce komai ba yasa ta ci-gaba da faɗin"ni wlh zan ce musu ba sunana Katalina
ba kuma ni ba ƴar ƙasar nan ba ce har ƙasarmu kaje ka ce aurena zaka yi ashe kai
mugu n..." Cak taji ya tsayar da motar ya juyo a fusace ya shaƙe wuyanta yana
kallonta da idanunsa wanda suka gama sauya kala ya ce" kina iya aikata duk abin da
kikaso a sanda kikaga dama amma ki sani Maheer bazai taɓa lamuntar tunon asiri ba
dole ki ɓoye sirrin sannan kiyi abin da na ce miki ki manta da cewa ke Imara ce! Ki
manta da cewa ke ba ƴar ƙasar nan ba ce! Ki manta da wata rayuwa ki sanya a ranki
ke Katalina ce!! Idan kuma ba haka ba..." Ya cije laɓɓansa sannan ya hankaɗata
tsananin azaba ya hana Imara furta wata kalma ta riƙe wuyanta wanda takejin kamar
har yanzu hannunsa yana kai wasu zafafan hawaye ne suka shiga sakkowa kan kuncinta
lokaci ɗaya kuma wani irin tari na azaba ya ziyarceta, tsawon lokacin data ɗauka a
haka Maheer bai kalli inda take ba har ya yi parking a compound ɗin makarantar
"Get down!"
Abinda ya furta kenan ba tareda ya kalleta ba, cikin sanyin jiki Imara ta sauka
daga motar ta shiga tafiya toward direction ɗin class ɗin su har sannan bata daina
jin zafin shaƙewar da Maheer ya yi mata ba. Koda ta shiga class ta tarar har
lecturer ɗinsu ya shiga hakan yasa kawai ta zauna tana sauraran abin da yake cewa
duk da rabin zaman nata tunani take har ya kammala lecturen ya fita Rania ce ta
kalleta tana murmushi ta ce"yau kin makara meyasa?" kallonta Imara tayi sai kuma ta
kwabe fuska ta ce"bansan lokaci ya tafi haka ba" jinjina kai Rania ta yi ta
ce"yanzu ya kike jin jikin naki?" lumshe idanunta tayi nan take hawayen da yake
kwance cikin idanun ya zubo kan kyakkyawar fuskarta da mamaki Rania ta ce"ya Ilahi,
meke damunki? ko ciwon ne? Ina ne ke miki zafi?" hannunta ta sanya ta goge hawayen
sai kuma ta kalli Rania tayi murmushi cikin sanyin murya ta ce"ba komai fa I'm fine
kawai wani abu na tuna" girgiza kai Rania tayi ta ce"wannan ba halin ki bane
Katalina, bamu ɓoyewa juna komai dan Allah ki sanar dani abin da yake damunki
kinji" ta ƙarashe maganar cikin rauni shiru Imara tayi tana kallon Rania tabbas
tana buƙatar wanda zata faɗawa damuwarta, tana buƙatar wanda zata kwanta jikinsa
tayi kuka amma ba Rania ba! "Imara think idan kika ce zaki faɗa mata abin da ke
zuciyarki to tabbas zaki fallasa kan ki kuma Maheer ba zai kyale ki ba dole ki
danne abin da kike ji kiyi kamar yanda ya umarce ki" wani ɓangare na zuciyar Imara
ta faɗa mata haka, da sauri ta dafe saitin zuciyar tata jin yanda take bugawa da
ƙarfi.
"Katalina!", Rania ta kirayi sunanta a ɗan firgice ta kalleta sai kuma tayi
murmushi tana kokarin ɓoye damuwarta ta ce"karki damu friend ina lafiya kinji babu
komai" shiru Rania tayi badan ta gamsu da abin da Katalina ta ce ba.
****
*LONDON*
*7:30pm*
Kwance take akan gadon marasa lafiyar, a hankali take jan cazbahar hannunta. Wata
mata farar tsohuwar mata ce kana ganinta kansa ta manyanta amma kuma da gwarinta
yanda take komai a nutse ne zai tabbatar da hakan, turo ƙofar ɗakin akai wanda yasa
ta maida hankalinta ga ƙofar tana ganin wanda zai shigo likita ta gani hakan yasa
ta ɗan tsuke fuska tana ɗauke kai murmushi kawai likitan ya yi sanin halinta ya
ƙaraso gabanta cikin fara'a ya ce" how are you feeling maa?" kallonsa ta yi sai
kuma ta sake ɗauke kanta tana kallon gefe, girgiza kansa ya yi ya ce cikin harshen
turanci" zan miki allurar yanzu" da sauri ta kalleshi sai kuma ta galla masa harara
cikin wata kamilalliyar murya ta fara magana da larabci
"Ya Ilahy, wane ya ce maka bani da lafiya? A'a ni nasamu sauƙi Ana-bikhair Shukran
laak" ta haɗe hannayenta alamar godiya. Daman ya rigada yasan haka zata yi yasa ya
yi murmushi kawai ya ce"I'm sorry maa dole a miki kodan lafiyarki" wangale baki
tayi tana kallonsa sai kuma ta ce" yau naga abin da ya isheni to na ce na warke ai
sai a barni haka ko kuma..." Shiru ta yi da maganar ganin ya buɗe ƙofar ɗakin ya
shigo jin takun tafiyarsa ya sanya doctorn yin murmushi ya juya ya kalleshi, sanye
yake da wata riga t-shirt fara jikinta da stickern hoton Damisa sai wani cargon 3-
quater black colour sai canvas fari a ƙafarsa yanada tsayi sosai haka kuma yanada
faɗi yanayin jikinsa zaka kalla kasan ma'abocin gym ne saboda yanda duk wani ƙashi
na jikinsa yake a murɗe kallo ɗaya ya yi musu ta tsakanin gashin da ya rufe
fuskarsa sai kuma ya ɗauke kai yana gyara zaman Bluetooth ɗin kunnensa ya shiga
takawa har wajen window ɗin ɗakin da alama waya yake da wani. Ganin ya juya musu
baya yasa ta yafito likitan da hannu cikin ƙasa da murya ta ce"kaga wannan
azababben ya zo dan Allah ka tafi idan ya fita zan nemeka da kaina kaji"
Tsit tayi shiru da bakinta tana kallonsa ganin har sannan wayarsa yake yasa ta sake
kallon likitan ta ce"ka ji yaro" jinjina mata kai ya yi sannan ya juya zai fita,
"wait" ya faɗa yana juyowa murmushi doctorn ya yi yana kallonsa ya ce"sir You need
something?" bai ce masa komai ba ya zauna gefen gadon yana ƙarewa hannunta kallo
above 2mins kafin ya buɗe bakinsa cikin cool voice ɗinsa ya ce" zo ka mata
injection ɗin" da sauri ta kalleshi sai kuma ta hade ranta tana huci ganin haka
yasa likitan ya dawo har ya yi mata allurar ba ta ce komai ba sai kallo da ido tana
ganin ya fita ta bisa da harara.
"Da kin daina harararsa Jadda tunda bashi ya sa kansa ba" a fusace ta ce"koma wane
ya saka shi ya je shi da Allah babu wanda zai dinga cutata yana azabtar dani wlh"
jin ya yi mata shiru yasa ta yi kwafa ta ce"tunda ga mahaukaciya na magana dole ayi
min shiru to uwarka Fateymarh ita ka yiwa shiru ba ni ba" tamkar tana magana da
gadon da take kai haka ya yi mata daga ƙarshe ma ya tashi ya fice daga ɗakin,
girgiza kanta ta yi cikin faɗa ta cigaba da magana " yaro sai shegen miskilanci da
jin kai wai shi wani wannan matarsa ta shiga uku a wajensa wai KA SAUYA HALI!"
Jadda ta faɗa tana cigaba da jan cazbahar hannunta.
Kai tsaye office ɗin likitan ya shiga bayan ya zauna doctorn ya kalleshi fuskarsa
ɗauke da fara'a ya ce cikin harshen turanci" she's getting better yanayin jikinta
ya nuna tana samun sauki sosai" shiru ya yi for some second sai kuma ya numfasa
"zuwa yaushe za'a iya discharging nata?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye, "maybe by next
week" jinjina kai ya yi ya juya ya fice daga office ɗin yana wata irin tafiya mai
nuni da isa.
*UDAID*
Murmushi Shamma tayi tana kallonta ta ce"shine kika dawo?" kwaɓe fuska tayi ta
ce"wlh Shamma na gaji akwai wahala sosai acan shiyasa na dawo kuma wai ina Ameer?"
bata rufe bakinta ba ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama, da gudu ta tashi tana
zuwa ta shige jikinsa tana dariya shafa kanta ya yi da murmushi a fuskarsa ya
ce"kaifa-al-hal?(ya ya kike?)" tana sake riƙe shi ta ce" Ana-bikhair Ameer" jinjina
kansa ya yi sannan ya janye ta daga jikinsa, akan royal cushion ɗin dake parlon ya
zauna ya lumshe idanunsa, kallon Shamma tayi sai kuma ta sake kallonsa ta zauna
gefensa da mamaki ta ce"Shamma Ameer bashida lafiya ne?" numfasawa Shamma tayi tana
kallonta ta ce"nima bana ce ba Maha haka kullum yake yanzu kamar akwai abin da yake
damunsa" hannunta na dama ta ɗora akan fuskarsa ya yi saurin sakin ajiyar zuciya
yana buɗe idanu, sosai ta ji zafi a jikinsa hakan yasa ta kwaɓe fuska tana kallonsa
ta ce"Ameer ka je asibiti kuwa?" jin ya yi shiru yana kallonta yasa ta cigaba"ka ji
jikinka akwai zazzaɓi please ka je asibiti ko a kira doctor ya duba ka?" tayi
maganar tana sake kallonsa. Ɗan murmushi ya yi yana jan kumatunta ya ce" ina lafiya
fa" turo baki tayi tana kallonsa ta ce"a'a ni dai ka shirya gobe muje asibiti"
jinjina mata kai ya yi bai sake cewa komai ba ya tashi ya bar parlon. Da kallo ta
bishi har ya shige apartment ɗinsa sannan ta kalli Shamma dake zaune har sannan ta
ce"Shamma wai ina Akhii?" murmushi ta yi ta ce" bai shigo ba har yanzu" taɓe baki
tayi ta ce"wacce na gansu tare ita ce matar tasa?" gyaɗa mata kai Shamma ta yi,
tayi murmushi ta ce"she's beautiful" girgiza kai Shamma ta yi saboda sanin surutun
Maha kawai ta tashi ta bar wajen. Tana tashi Joda ta fito hannunta riƙe da system
ɗin ta as usual kallo ɗaya Maha ta yi mata ta ɗauke kai dan ko kaɗan basa shiri
itama Jodan zamanta tayi wajen kamar batasan da mutum a gurin ba, above 5mins kafin
Maha ta tashi zata bar wajen har tayi gaba sai kuma ta dawo tana kallon Joda ta ce
cikin harshen larabci
"Ina mai baki shawara ki gyara ɗabi'unki tun kafin lokaci ya ƙure miki, akwai
lokuta da dama da bamu gane masoyanmu da kuma maƙiyanmu musamman idan mutum ya
kasance yana rangwamin sanin ya kamata kamar dai ke ɗin nan. Ki sani lokaci na nan
da za kiyi danasanin abubuwan da kika aikata kuma danasani mara amfani, it's better
for you to change your attitude or else..." Ta juya fuu ta haye sama. Sai a sannan
Joda ta ɗago idanunta wanda suka kaɗa sukayi jajur tabi bayanta da kallo wani irin
tafarfasa zuciyarta ke yi tashi tsaye tana sake duban inda Maha ta yi sai kuma ta
daki glass table ɗin dake gabanta nan take ya tawarwatse hannunta ya fashe kallon
fararen hannunta wanda suka jiƙe da jini tayi sai kuma ta fasa wata irin ƙara ta
zube a wajen sumammiya.
***Zaune ta sameshi a gefen gado ya jingina da jikin fuskar gadon idanunsa a rufe
amma ba bacci yake ba, zama tayi gefensa ta kama hannunsa ta riƙe, buɗe runannun
idanun nasa ya yi yana kallonta sosai abun ya bata mamaki dan ta daɗe bata ga Ameer
cikin irin wannan yanayin ba, cikin sanyin murya ta ce"yallaɓai idan da abin da ke
damunka ka sanar damu ko zamu iya maka maganinsa, idan kuma ba zamu iya ba mu
tayaka da addu'a amma wannan damuwar bata dace da mai irin Shekarunka ba" da idanu
kawai Ameer ya bita ganin hawaye na zuba a idanunta, hannunsa ɗaya ya sanya ya
jawota gefensa ya riƙe haɓarta yana kallonta sai kuma ya yi murmushi yana girgiza
mata kai da sauri ta shige jikinsa tana fashewa da kuka, shiru Ameer ya yi mata
yana jin yanda take kukan. Saida tayi shiru dan kanta sannan ya ɗago fuskarta ya
goge mata hawayen cikin kamilalliyar muryarsa ya fara magana
"Zan so a ce kunada damar warwaren matsalata da nafi kowa son na sanar daku, saidai
abin da ke cikin raina ya shige tunanin mai tunani. Saboda haka ku tayani da addu'a
kawai" kallonsa Shamma tayi sai kuma ta girgiza kanta tana kallonsa ta ce".
# *Imara*
# *Lolo*
# *Joda*
# *Nanameera*
# *Fashion gurl**Chapter 5*
"Wace irin matsala ce da har zata gagara sanar da iyalinka?, Ameer kodan lafiyarka
ka daure ka sanar mana, kowa ya damu a fadar nan, ka daina walwala kullum saidai
kana ɗaki why?" Ta ƙarashe maganar cikin rauni. Bai ce komai ba ya sanya hannunsa
ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya fice daga ɗakin hannunsa goye a bayansa, baki
buɗe ta bisa da kallo har ya ɓacewa ganinta a hankali ta miƙe tsaye ta shiga zagaye
ɗakin tana saƙe-saƙen wasu abubuwa a ranta. Library ɗinsa ya nufa dan akwai
muhimman abubuwan da yakeson gabatarwa duk da baya jin daɗin jikinsa. Akan wata
royal cushion dake gefensa ya zauna hannunsa riƙe da Alqur'ani mai girma, a hankali
fuskarta ke yi masa gizo akan idanunsa yana hango ɗan siririn bakinta wanda take
masa tsiwa dashi, saurin runtse idanunsa ya yi a hankali ya ɗora hannunsa bisa
ƙirjinsa yana jin yanda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.
"Astgfirullah!"
Shine abin da ya samu damar furtawa yana sake rufe idanunsa a karo na babu adadi,
above 10mins yana zaune a wajen ba tare da ya samu damar aiwatar da abin da ya kawo
shi ba, kwakwalwarsa gabaɗaya ba a wajen take ba, tunaninsa da zuciyarsa sun
karkarta zuwa gare ta.
****
*9:30pm*
JODA
Tsaye take ta jingina da jikin wani bango, sanye take da wata riga t-shirt milk
colour sai wandon jeans Blue colour gashinta ya zubo ta gefen kafaɗarta, idanunta
maƙale cikin glasses black colour mai ɗan faɗi, yanayin wajen ya taimaka wajen
ƙarawa backyard ɗin kyau. Furzar da iska ya yi daga bakinsa yana kallonta cikin
harshen larabci ya ce" ?Limadha tanẓur ilayya (Meyasa kike kallona?". Finger ɗinta
ta sanya ta ɗan janye glasses ɗin fuskarta ya dawo kan tsinin hancinta tana
kallonsa da sexy eyes ɗinta ta ce cikin harshen turanci" like how? (Kamar yaya
kenan?" ɗan basarwa ya yi sanin halinta ya yi murmushi har saida beauty point ɗinsu
suka loma ya ce" just move on " jin tayi shiru yasa ya ce"yanzu mene ne plan A?"
Kyakkyawan murmushi Joda tayi ta ɗan cije lips ɗinta ta ce"zan tura maka later "
jin jina kansa ya yi yana kallonta ya ce" shikenan ina jiranki " . Juyawa yayi ya
fara tafiya hannayensa zube cikin aljihu.
"Rasheed!"
Juyowa ya yi yaga bashi take kallo ba sai ya zuba mata idanu, "Kun hadhiran (Ka
kula)", ɗan murmushi ya yi wanda ya fito da zallar kyansa ya ce "then you care
about me?" Wani kallo ta watsa masa sai kuma ta juya tabar wajen, girgiza kansa ya
yi yana jinjina hali irin na Joda kafin ya juya ya tafi shima.
*** Zaune take gefen gadon ta zuba uban tagumi, tunani ne kala-kala cikin ranta
gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta nema take ta gaza ɗaukan abubuwan dake tunkaro ta, dole ta
nemawa kanta mafita. Agogon dake maƙale jikin kusurwar ɗakin ta kalla, 9:45 ta gani
a jiki ta sauke idanunta ƙasa tana tunanin wani abu, mene makomar aurenta?, me
Maheer yake nufi da ita?, wacece ita a wajensa?. Rashin sanin amshoshin tambayarta
ya sanya ta fashe da wani raunataccen kuka ta kwanta kan gadon ta ƙanƙame pillow
tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, kuka ne wanda yake fitowa tun daga ƙasan
zuciyarta, kuka ne wanda yake fassara how sad she is, kuka ne irin kukan komai ya
ƙare mata. Meyasa sai ita?, Meyasa ƙaddararta ta zaɓa mata haka? Yaushe zata yi
farin ciki?
"Sanda kika aminta da Ameer matsayin mai sonki, sanda kika yarda da soyayya da kuma
ƙaunar da nake nuna miki, sanda kika buɗe zuciyarki har ta karɓi saƙon da Fahad ke
aiko mata a kowace rana, ki yarda dani Lolo, ki ƙaunaceni kamar yanda nima nake
ƙaunarki na faɗa kuma zan sake faɗa, billahil-azeem nafi Maheer sonki, ni ne na
dace dake ba Maheer ba, ki karbi soyayya ta hannu bibbiyu nayi miki alƙawarin farin
ciki mara yankewa, zan zame miki garkuwa, zan baki farin ciki, zan kula da
lamuranki, zan tsaya miki. Ki karbi ƙaddarar ki yanda take, ni ne ƙaddarar ki
IMARA!"
Ameer ya faɗa yana ƙarasa shigowa ɗakin hannunsa riƙe da sandarsa as usual, a
firgice ta ɗago tana kallonsa da idanunta wanda suka yi jajur, ta miƙe tsaye tana
goge hawayen da suka mata caɓa-caɓa a fuska ta fara magana;
"Eh, tabbas!, tabbas kai ƙaddararta ne, irin ƙaddarar da kowane bawa yake rokon
ubangiji ya kareshi daga gareta, irin ƙaddarar da idan ta gaba to ka take hanaka
bacci, ka zame mini ƙarfen ƙafa Ameer!, wlh zuciyata gab take da bugawa idan har ka
cigaba da furta irin waɗannan kalaman masu muni a gareni, kanada ilimi, sanin ya
kamata, nutsuwa ta zuci data zahiri amma shaiɗan ya rinjayi zuciyarka, ka kasa gane
abun da yake daidai da kuma wanda yake ba daidai ba." Durƙusawa ƙasa tayi ta haɗe
hannayenta waje ɗaya alamar roƙo tana kuka ta cigaba da faɗin;
"Dan girman Allah, dan darajar Annabi, dan alfarmar iyayenka ka manta dani cikin
rayuwarka, ka cire wannan tunanin daga cikin ranka, wlh babu kyau ko kaɗan nifa
matar Maheer ce, sirika nake a gurinka. Ka taimaka Ameer! Ka taimaka min. Ta zube a
ƙasa tana sake rushewa da wani sabon kukan kamar ranta zai fita, tun da ta fara
magana Ameer ke kallonta a hankali kuma yake lumshe idanunsa, gefen gadon ya zauna
ya dafe saitin zuciyarsa jin yanda take bugawa da ƙarfi. Above 5mins babu wanda ya
ce wani abu a cikinsu, a hankali kuma ta fara rage sound ɗin kukan nata sai ajiyar
zuciya da take ta saukewa, miƙewa tsaye ya yi ya fara takawa cikin tafiyarsa ta isa
ya ƙaraso gabanta. Sunkuyawa ya yi yana kallonta for some seconds sai kuma ya sakar
mata kyakkyawan murmushi, saurin ɗauke idanunta tayi tana runtse su saboda yanda
taga ya yi mata wani irin kwarjini. Ya ɗauki mintuna akanta kafin ya tashi ya fice
daga ɗakin ba tare da ta sani ba.
Washegari.
Tana ƙoƙarin sanya takalmin ta ya shigo ɗakin, fuskarsa a ɗaure babu alamar fara'a,
kallo ɗaya Imara tayi masa ta cigaba da abin da take. Saida ta kammala sanya
takalmin wanda yake canvas white colour sannan ta tashi tsaye, hang bag ɗinta ta
ɗauka ta ratsa ta gefensa zata fita taji ya janyota, gabansa ya dawo da ita
fuskarsa dab da tata, kallonta ya shiga yi frm head to toe sai kuma ya wani yatsine
fuska bai ce komai ba ya kama hannunta suka fita daga ɗakin.
***Gaba ɗaya jama'ar gidan sun hallara wajen cin abinci, babu abin da ke tashi sai
ƙarar spoons da knives, "Ayn Jūdā? (Ina Joda?)," Immi ta faɗa tana sake ɗaga kanta,
murmushi Dameer ya yi ya ce" Maybe akwai mutanen da bata son gani yasa bata fito
ba.", duk suka ɗago suka kalleshi, Shamma ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba ta
ture plate ɗin hannunta ta tashi ta bar wajen.
"Dameer!"
" La tuḥāwilu abadan mā faʿaltahu al-ān (Karka sake irin haka)" cewar Ameer yana
tashi tsaye, cikeda ladabi Dameer ya ce " in sha Allah". Bai sake kallon kowa ba ya
bar wajen. Miƙewa Immi tayi tana kallonsa ta ce"ka sameni a ɗaki" okay ya ce sannan
y tashi yabi bayanta. Tsaye ya sameta tana kai kawo cikin ƙaton parlon dake cikin
part ɗinta, da idanu ya bita ganin kamar hankalinta ba a kwance yake ba yasa ya ce
"what's going on Immi?" dafe kanta tayi ta ce"Dameer abubuwa na gab da lalacewa,
UDAID na gab da barin hannun mu, sirrin da na daɗe ina ɓoyewa nason fitowa fili."
Ɗan murmushi ya yi yana girgiza kansa ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa cikin son
kwantar mata da hankali ya fara magana
"Haba Immi, wannan ba abu bane mai yiwuwa, nayi miki alƙawarin yin duk wani abin da
ya kamata wajen ganin na cika burinki, saboda haka ki kwantar da hankalinki". Wata
nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta gyaɗa masa kai ba tareda ta ce komai ba.
*SHAMMA*.
"Ƴaƴana?, Ƴaƴana?, ku ba Yarana bane!, wlh dana riƙe ku matsayin ya'ya gara na mutu
na bar duniyar, koda wasa bana ƙaunarku, tunda har kun zaɓeta matsayin uwa to nima
na haƙura na sallama mata ku, ta raine ku, ta baku kulawa, amma har abada babu ni
babu ku!"
"Shamma dan Allah kar kiyi haka, ke uwace nasan kina son mu, karki bari a rabamu
dake, ki jiƙanmu a matsayin mu na yayanki, dan Allah Shamma, karki ji mata ciwo ki
taimaka Shamma!" A fusace ta riƙo hannun ƙaramar yarinyar da bazata shige 4-5yrs ba
ta hankaɗata, wata razananniyar ƙara yarinyar ta saki dalilin tafasasshen ruwan
heatern data zubo a jikinta, da gudu yaron ya saki hannunta ya ƙarasa wajen
yarinyar ya shiga jijjigata saidai duk inda ya cire hannunsa sai fatarta ta biyo
hannunsa ganin haka yasa ya saki wata irin ƙara, nan take idanunsa suka kaɗa suka
yi jajur tamkar gauta, jijiyoyin kansa suka firfito. Tamkar wanda aka zabura haka
ya miƙe tsaye naman jikinsa na wani irin rawa wacce ke nuni da ɓacin ran da yake
ciki, hannunsa ɗaya ya sanya ya tattare gashin da ya rufe fuskarsa ya maƙaleshi
gefen kunnensa, ya kafeta da manyan idanunsa bakinsa na rawa.
"Shamma! Shamma!", girgiza kai Maha tayi ta ƙaraso gabanta ta dafata, a firgice
Shamma ta ɗago kanta tana kallonta, sai kuma ta ɗauke idanunta tana ƙoƙarin ɓoye
hawayen dake cikin idanun. Zama Maha tayi gefenta cikeda damuwa ta ce "Shamma
something went wrong with you but you couldn't tell anyone why?" Kyakkyawar
fuskarta ta larabawa Shamma ta kalla sai kuma tayi murmushi ta ce cikin harshen
larabci " karki damu baby, ina lafiya" girgiza kai Maha tayi ta ce"shikenan Allah
yasa haka ne" "Ameen ya rabbi" Shamma ta faɗa tana kaƙalo murmushi. Tashi Maha tayi
ta ce"daman fita zanyi shine nazo na faɗa miki saina dawo bye" hannu kawai Shamma
ta ɗaga mata dan batajin zata iya cewa wani abu ta fice daga ɗakin. Tana fita
Shamma ta ɗora kanta gefen pillow ta fashe da wani sabon kukan mai cin rai tana
nadamar abubuwan da suka faru a baya.
3:30pm.
Zaune suke cikin capteria kowa na duba abinda zai yi order, ganin hankalinta gaba
ɗaya baya wajen yasa Rania ta taɓa ta, a ɗan firgice ta kalleta sai kuma ta sakar
mata murmushi tana murza idanunta wanda yayi jajur dashi, ajiye Menu book ɗin Rania
tayi ta juyo tana fuskantar ta ta ce cikin harshen larabci "Katalina meke damunki?,
tunanin me kike?, me yake hanaki bacci naga idanunki sun koma haka?" Rania ta jero
mata tambayar tana kafeta da manyan idanunta, kasa cewa komai Imara tayi kawai sai
ta faɗa jikinta ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Dafa kanta Rania tayi
bata ce komai ba, saida ta barta tayi kukan mai isarta sannan ta fara sakin ajiyar
zuciya a hankali tana shassheƙar kuka, ɗago fuskarta Rania tayi tana kallonta ta
ce"now tell me what wrong with you?" Ɗan murmushi Imara tayi tana goge hawayen
idanunta ta ce"babu komai fa, kawai na tuna wani abu ne shikenan." Baki buɗe Rania
take kallonta sai kuma ta girgiza kai
"Me kika tuna da yake sanya ki kuka?, ko shikenan Allah yasa hakane abinda kika
faɗa"
Jinjina mata kai Imara tayi ta ce"hakane ma" ta faɗa tana lumshe idanunta. Shiru
suka ɗauka na wasu sakkani kafin Imara ta sake kallonta ta ce"can I ask you
friend?" "Why not?" Rania ta bata amsa tana kallonta with full attention. Numfasawa
Imara ta yi sai kuma ta ce cikin harshen larabci" inada wata friend so tana cikin
matsala nikuma na kasa bata shawara shine nake neman taimakon ki ki bani shawara "
jinjina kai Rania ta yi, Imara ta cigaba da faɗin"zan baki ɗan labarin abin da ke
damunta sai ki bani shawara Please".
Tunda Imara ta fara magana Rania ke bin ta da kallo irin na mamaki, da daɗe bataji
abin da ya gigita mata lissafi ba irin wannan, wane irin son zuciya ne wannan?,
wace irin duniya muke ciki ne? Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, shine kawai
abin da take iya furtawa gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Ganin yanda tayi yasa Imara
tayi murmushi tana taɓa ta ta ce " karki damu kanki fa, kawai shawara nakeson ki
bata" numfasawa Rania tayi tana kallonta ta ce
"Imara na daɗe ban ji abin da ya bani tsoro ba irin wannan, kuma da gaske nufi yake
ta rabu da ɗansa?" Jinjina mata kai Imara ta yi ta cigaba da faɗin;
"Shawara anan shine kawai ta cigaba da addu'a even through nasan tanayi but ta
ƙara, na biyu kuma tana iya using wannan opportunity ɗin wajen ganin ta samu amsar
tambayar da take nema, I mean ta tambaye shi wasu abubuwa game da mijinta da kuma
matar da yake magana akai, ta nan ne zata gane abin da mijin ke ɓoye mata da kuma
wanda ya faru a baya. Idan tayi haka zata iya gano bakin zaren daga nan sai ta
yankewa rayuwarta hukunci dan wannan ba ƙaramin al-amari bane!"
Murmushi Imara tayi ta ce"yawwa Friend Nagode sosai in sha Allah nima zan sanar da
ita Allah yasa a dace" Ameen ya rabbi Rania ta ce sannan suka cigaba da duba
abincin.
***Zaune yake gefen gadonsa idanunsa maƙale akan wani Enlargement na hoto ya zuba
mata idanu, fuskar dake jikin hoton sak Imara babu abin da ya raba su. Yanayin
shigar dake jikinta ne kawai ya bambanta domin ita wannan ƙananun kaya ne a jikinta
gashin kanta kuma a buɗe babu veil.
Da gudu ya ƙarasa sauka daga saman yana tafe yana ture mutane, can ya hango su suna
tsaye kana ganinsu kaga ɗalibai, ajiyar zuciya ya sauke sanda ya hangeta fuskanta a
sake sai murmushi take, tana ganinsa ta saki murmushi da gudu ta tawo ta shige
jikinsa, murmushin shima yake ya riƙeta gam, sun jima a haka kafin ta sake shi tana
kallonsa ta ce cikin cool voice ɗinta "you kept me waiting" ta faɗa tana tura baki
gaba, hannunta ya kama ya riƙe cikin nasa yana dariya ya ce "I'm sorry na tsaya
duba patient ne" langwaɓar da kai tayi ta ce" shikenan kaje sai mun haɗu anjima"
"Really?"
Jinjina masa kai tayi ya bata peck a goshi sannan ya juya zai bar wajen.
"Maheer!"
Juyowa ya yi jin tayi kiran sunansa abin da ya daɗe bai ji ba a rayuwarsa, ɗaga
mata gira ya yi ya ce"what?" Murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma ta
ce" don't forget with me, I love you" yanda tayi maganar jiki a sanyaye ya sanya
yayi murmushi ya gyaɗa mata kai
"Har abada Peanut", murmushi ta saki ta ɗaga masa hannu alamar bye shima ya mayar
mata sannan ya juya ya shige motarsa.
"PEANUTTTTT..."
Ya faɗa a fili yana shafa hoton, ɗumin da yaji a fuskarsa ya tabbatar masa da cewa
kuka yake kuma daman ya cancanci ya yi kukan, he missed her, ƙaunar da yakewa
Katalina daban take a cikin zuciyarsa amma ta tafi, she left him without even say
goodbye to him, why? Why???.
"Saboda baka yi deserving rayuwa da ita ba, kanada son kanka, kana fifita buƙatarka
akan ta wani, kana iya salwantar da wani abu matuƙar kai zaka samu biyan buƙata,
you are too selfish Maheer!"
# *Bestnovel
# *Nanameera
# *Imara
# *2025.
*Chapter 4*
"Nan da ƴan kwanaki zai dawo ƙasar nan kuma shigarsa Udaid na nufin abubuwa masu
yawa, saboda haka na shirya komai kuma ina buƙatar taimakon ka, Rasheed!" Gyara
zaman glasses ɗin fuskarsa ya yi yana kallonta ya ce"ina tare dake a kowane lokaci
kawai ki sanar dani abin da kika shirya" wani cute smile tayi ta cigaba da magana.
***A hankali take taka stairs din benan dan gaba ɗaya a tsorace take, "Habibty" a
dan firgice ta juyo ta saki wata ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta ta ce"Sabahul
khair Shamma (Barka da safiya Shamma), murmushi Shamma tayi tana kama hannunta ta
ce"why are you scared?" Ta marairaice fuska tana kallon Shamma bata ce komai ba, a
gefenta ta zaunar da ita bayan itama ta zauna tana kallonta ta ce"kar ki saka
damuwa a ranki babu abinda Dameer zai yi miki, ki cire incident din jiya a ranki
kinji baby" jinjina kanta tayi hawaye na kawo idanun nata ta ce" in sha Allah
Shamma" shafa kanta tayi tana murmushi ta ce"good girl" murmushin Imara ta mayar
mata sannan ta tashi tsaye tana kallonta ta ce"zan tafi school" "Allah ya kiyaye"
Ameen ta ce tana gyara zaman veil ɗin ta. Sound ɗin takalminsa ya sanya ta ɗago
kanta tana duban inda hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗin jikinsa ya sakko
fuska babu wata walwala yana zuwa ya gaisheda Shamma ta amsa cikeda fara'a bai cewa
Imara komai ba ya yi waje ta bi bayansa tana murguɗa masa baki.
Yana ƙoƙarin shiga motarsa yaga shigowar wata baƙuwar mota hakan yasa ya tsaya yana
kallon motar har tayi parking, waro idanunsa waje yayi ganin wacce ta fito daga
motar sanye take da wata riga irin mai kama jikin nan wacce ta tsaya iya cinyarta
fararen cinyoyinta duk sun fito waje sai gyara gashin kanta wanda ya ke ƙoƙarin
rufe mata fuska take tana ganinsa ta washe baki ta tawo da gudu da niyyar shigewa
jikinsa saurin matsawa ya yi yana kallonta hakan yasa ta dakata tana tsuke fuska ta
ce cikin wata siririyar murya
"Haba Akhii yaushe rabon dana ganka baka missing ɗina?" tabe bakinsa ya yi yana
ƙoƙarin buɗe motarsa ya ce"wane ya baki shawarar ki dawo?" watsa hannayenta tayi
alamar bata sani ba ya kalleta sai kuma ya shige motarsa, Imara tabi da kallo sai
kuma ta juya tabar wajen. Sun yi nisa da gida ta kalleshi ganin yanda yake tuƙinsa
cikeda nutsuwa ta tura baki gaba ta ce" kuma yau idan suka min magana me zan ce?"
Jin bai ce komai ba yasa ta ci-gaba da faɗin"ni wlh zan ce musu ba sunana Katalina
ba kuma ni ba ƴar ƙasar nan ba ce har ƙasarmu kaje ka ce aurena zaka yi ashe kai
mugu n..." Cak taji ya tsayar da motar ya juyo a fusace ya shaƙe wuyanta yana
kallonta da idanunsa wanda suka gama sauya kala ya ce" kina iya aikata duk abin da
kikaso a sanda kikaga dama amma ki sani Maheer bazai taɓa lamuntar tunon asiri ba
dole ki ɓoye sirrin sannan kiyi abin da na ce miki ki manta da cewa ke Imara ce! Ki
manta da cewa ke ba ƴar ƙasar nan ba ce! Ki manta da wata rayuwa ki sanya a ranki
ke Katalina ce!! Idan kuma ba haka ba..." Ya cije laɓɓansa sannan ya hankaɗata
tsananin azaba ya hana Imara furta wata kalma ta riƙe wuyanta wanda takejin kamar
har yanzu hannunsa yana kai wasu zafafan hawaye ne suka shiga sakkowa kan kuncinta
lokaci ɗaya kuma wani irin tari na azaba ya ziyarceta, tsawon lokacin data ɗauka a
haka Maheer bai kalli inda take ba har ya yi parking a compound ɗin makarantar
"Get down!"
Abinda ya furta kenan ba tareda ya kalleta ba, cikin sanyin jiki Imara ta sauka
daga motar ta shiga tafiya toward direction ɗin class ɗin su har sannan bata daina
jin zafin shaƙewar da Maheer ya yi mata ba. Koda ta shiga class ta tarar har
lecturer ɗinsu ya shiga hakan yasa kawai ta zauna tana sauraran abin da yake cewa
duk da rabin zaman nata tunani take har ya kammala lecturen ya fita Rania ce ta
kalleta tana murmushi ta ce"yau kin makara meyasa?" kallonta Imara tayi sai kuma ta
kwabe fuska ta ce"bansan lokaci ya tafi haka ba" jinjina kai Rania ta yi ta
ce"yanzu ya kike jin jikin naki?" lumshe idanunta tayi nan take hawayen da yake
kwance cikin idanun ya zubo kan kyakkyawar fuskarta da mamaki Rania ta ce"ya Ilahi,
meke damunki? ko ciwon ne? Ina ne ke miki zafi?" hannunta ta sanya ta goge hawayen
sai kuma ta kalli Rania tayi murmushi cikin sanyin murya ta ce"ba komai fa I'm fine
kawai wani abu na tuna" girgiza kai Rania tayi ta ce"wannan ba halin ki bane
Katalina, bamu ɓoyewa juna komai dan Allah ki sanar dani abin da yake damunki
kinji" ta ƙarashe maganar cikin rauni shiru Imara tayi tana kallon Rania tabbas
tana buƙatar wanda zata faɗawa damuwarta, tana buƙatar wanda zata kwanta jikinsa
tayi kuka amma ba Rania ba! "Imara think idan kika ce zaki faɗa mata abin da ke
zuciyarki to tabbas zaki fallasa kan ki kuma Maheer ba zai kyale ki ba dole ki
danne abin da kike ji kiyi kamar yanda ya umarce ki" wani ɓangare na zuciyar Imara
ta faɗa mata haka, da sauri ta dafe saitin zuciyar tata jin yanda take bugawa da
ƙarfi.
"Katalina!", Rania ta kirayi sunanta a ɗan firgice ta kalleta sai kuma tayi
murmushi tana kokarin ɓoye damuwarta ta ce"karki damu friend ina lafiya kinji babu
komai" shiru Rania tayi badan ta gamsu da abin da Katalina ta ce ba.
****
*LONDON*
*7:30pm*
Kwance take akan gadon marasa lafiyar, a hankali take jan cazbahar hannunta. Wata
mata farar tsohuwar mata ce kana ganinta kansa ta manyanta amma kuma da gwarinta
yanda take komai a nutse ne zai tabbatar da hakan, turo ƙofar ɗakin akai wanda yasa
ta maida hankalinta ga ƙofar tana ganin wanda zai shigo likita ta gani hakan yasa
ta ɗan tsuke fuska tana ɗauke kai murmushi kawai likitan ya yi sanin halinta ya
ƙaraso gabanta cikin fara'a ya ce" how are you feeling maa?" kallonsa ta yi sai
kuma ta sake ɗauke kanta tana kallon gefe, girgiza kansa ya yi ya ce cikin harshen
turanci" zan miki allurar yanzu" da sauri ta kalleshi sai kuma ta galla masa harara
cikin wata kamilalliyar murya ta fara magana da larabci
"Ya Ilahy, wane ya ce maka bani da lafiya? A'a ni nasamu sauƙi Ana-bikhair Shukran
laak" ta haɗe hannayenta alamar godiya. Daman ya rigada yasan haka zata yi yasa ya
yi murmushi kawai ya ce"I'm sorry maa dole a miki kodan lafiyarki" wangale baki
tayi tana kallonsa sai kuma ta ce" yau naga abin da ya isheni to na ce na warke ai
sai a barni haka ko kuma..." Shiru ta yi da maganar ganin ya buɗe ƙofar ɗakin ya
shigo jin takun tafiyarsa ya sanya doctorn yin murmushi ya juya ya kalleshi, sanye
yake da wata riga t-shirt fara jikinta da stickern hoton Damisa sai wani cargon 3-
quater black colour sai canvas fari a ƙafarsa yanada tsayi sosai haka kuma yanada
faɗi yanayin jikinsa zaka kalla kasan ma'abocin gym ne saboda yanda duk wani ƙashi
na jikinsa yake a murɗe kallo ɗaya ya yi musu ta tsakanin gashin da ya rufe
fuskarsa sai kuma ya ɗauke kai yana gyara zaman Bluetooth ɗin kunnensa ya shiga
takawa har wajen window ɗin ɗakin da alama waya yake da wani. Ganin ya juya musu
baya yasa ta yafito likitan da hannu cikin ƙasa da murya ta ce"kaga wannan
azababben ya zo dan Allah ka tafi idan ya fita zan nemeka da kaina kaji"
Tsit tayi shiru da bakinta tana kallonsa ganin har sannan wayarsa yake yasa ta sake
kallon likitan ta ce"ka ji yaro" jinjina mata kai ya yi sannan ya juya zai fita,
"wait" ya faɗa yana juyowa murmushi doctorn ya yi yana kallonsa ya ce"sir You need
something?" bai ce masa komai ba ya zauna gefen gadon yana ƙarewa hannunta kallo
above 2mins kafin ya buɗe bakinsa cikin cool voice ɗinsa ya ce" zo ka mata
injection ɗin" da sauri ta kalleshi sai kuma ta hade ranta tana huci ganin haka
yasa likitan ya dawo har ya yi mata allurar ba ta ce komai ba sai kallo da ido tana
ganin ya fita ta bisa da harara.
"Da kin daina harararsa Jadda tunda bashi ya sa kansa ba" a fusace ta ce"koma wane
ya saka shi ya je shi da Allah babu wanda zai dinga cutata yana azabtar dani wlh"
jin ya yi mata shiru yasa ta yi kwafa ta ce"tunda ga mahaukaciya na magana dole ayi
min shiru to uwarka Fateymarh ita ka yiwa shiru ba ni ba" tamkar tana magana da
gadon da take kai haka ya yi mata daga ƙarshe ma ya tashi ya fice daga ɗakin,
girgiza kanta ta yi cikin faɗa ta cigaba da magana " yaro sai shegen miskilanci da
jin kai wai shi wani wannan matarsa ta shiga uku a wajensa wai KA SAUYA HALI!"
Jadda ta faɗa tana cigaba da jan cazbahar hannunta.
Kai tsaye office ɗin likitan ya shiga bayan ya zauna doctorn ya kalleshi fuskarsa
ɗauke da fara'a ya ce cikin harshen turanci" she's getting better yanayin jikinta
ya nuna tana samun sauki sosai" shiru ya yi for some second sai kuma ya numfasa
"zuwa yaushe za'a iya discharging nata?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye, "maybe by next
week" jinjina kai ya yi ya juya ya fice daga office ɗin yana wata irin tafiya mai
nuni da isa.
*UDAID*
Murmushi Shamma tayi tana kallonta ta ce"shine kika dawo?" kwaɓe fuska tayi ta
ce"wlh Shamma na gaji akwai wahala sosai acan shiyasa na dawo kuma wai ina Ameer?"
bata rufe bakinta ba ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama, da gudu ta tashi tana
zuwa ta shige jikinsa tana dariya shafa kanta ya yi da murmushi a fuskarsa ya
ce"kaifa-al-hal?(ya ya kike?)" tana sake riƙe shi ta ce" Ana-bikhair Ameer" jinjina
kansa ya yi sannan ya janye ta daga jikinsa, akan royal cushion ɗin dake parlon ya
zauna ya lumshe idanunsa, kallon Shamma tayi sai kuma ta sake kallonsa ta zauna
gefensa da mamaki ta ce"Shamma Ameer bashida lafiya ne?" numfasawa Shamma tayi tana
kallonta ta ce"nima bana ce ba Maha haka kullum yake yanzu kamar akwai abin da yake
damunsa" hannunta na dama ta ɗora akan fuskarsa ya yi saurin sakin ajiyar zuciya
yana buɗe idanu, sosai ta ji zafi a jikinsa hakan yasa ta kwaɓe fuska tana kallonsa
ta ce"Ameer ka je asibiti kuwa?" jin ya yi shiru yana kallonta yasa ta cigaba"ka ji
jikinka akwai zazzaɓi please ka je asibiti ko a kira doctor ya duba ka?" tayi
maganar tana sake kallonsa. Ɗan murmushi ya yi yana jan kumatunta ya ce" ina lafiya
fa" turo baki tayi tana kallonsa ta ce"a'a ni dai ka shirya gobe muje asibiti"
jinjina mata kai ya yi bai sake cewa komai ba ya tashi ya bar parlon. Da kallo ta
bishi har ya shige apartment ɗinsa sannan ta kalli Shamma dake zaune har sannan ta
ce"Shamma wai ina Akhii?" murmushi ta yi ta ce" bai shigo ba har yanzu" taɓe baki
tayi ta ce"wacce na gansu tare ita ce matar tasa?" gyaɗa mata kai Shamma ta yi,
tayi murmushi ta ce"she's beautiful" girgiza kai Shamma ta yi saboda sanin surutun
Maha kawai ta tashi ta bar wajen. Tana tashi Joda ta fito hannunta riƙe da system
ɗin ta as usual kallo ɗaya Maha ta yi mata ta ɗauke kai dan ko kaɗan basa shiri
itama Jodan zamanta tayi wajen kamar batasan da mutum a gurin ba, above 5mins kafin
Maha ta tashi zata bar wajen har tayi gaba sai kuma ta dawo tana kallon Joda ta ce
cikin harshen larabci
"Ina mai baki shawara ki gyara ɗabi'unki tun kafin lokaci ya ƙure miki, akwai
lokuta da dama da bamu gane masoyanmu da kuma maƙiyanmu musamman idan mutum ya
kasance yana rangwamin sanin ya kamata kamar dai ke ɗin nan. Ki sani lokaci na nan
da za kiyi danasanin abubuwan da kika aikata kuma danasani mara amfani, it's better
for you to change your attitude or else..." Ta juya fuu ta haye sama. Sai a sannan
Joda ta ɗago idanunta wanda suka kaɗa sukayi jajur tabi bayanta da kallo wani irin
tafarfasa zuciyarta ke yi tashi tsaye tana sake duban inda Maha ta yi sai kuma ta
daki glass table ɗin dake gabanta nan take ya tawarwatse hannunta ya fashe kallon
fararen hannunta wanda suka jiƙe da jini tayi sai kuma ta fasa wata irin ƙara ta
zube a wajen sumammiya.
***Zaune ta sameshi a gefen gado ya jingina da jikin fuskar gadon idanunsa a rufe
amma ba bacci yake ba, zama tayi gefensa ta kama hannunsa ta riƙe, buɗe runannun
idanun nasa ya yi yana kallonta sosai abun ya bata mamaki dan ta daɗe bata ga Ameer
cikin irin wannan yanayin ba, cikin sanyin murya ta ce"yallaɓai idan da abin da ke
damunka ka sanar damu ko zamu iya maka maganinsa, idan kuma ba zamu iya ba mu
tayaka da addu'a amma wannan damuwar bata dace da mai irin Shekarunka ba" da idanu
kawai Ameer ya bita ganin hawaye na zuba a idanunta, hannunsa ɗaya ya sanya ya
jawota gefensa ya riƙe haɓarta yana kallonta sai kuma ya yi murmushi yana girgiza
mata kai da sauri ta shige jikinsa tana fashewa da kuka, shiru Ameer ya yi mata
yana jin yanda take kukan. Saida tayi shiru dan kanta sannan ya ɗago fuskarta ya
goge mata hawayen cikin kamilalliyar muryarsa ya fara magana
"Zan so a ce kunada damar warwaren matsalata da nafi kowa son na sanar daku, saidai
abin da ke cikin raina ya shige tunanin mai tunani. Saboda haka ku tayani da addu'a
kawai" kallonsa Shamma tayi sai kuma ta girgiza kanta tana kallonsa ta ce".
# *Imara*
# *Lolo*
# *Joda*
# *Nanameera*
# *Fashion gurl*
*Chapter 06*
Da mamaki Maheer ke kallonta yayinda take ƙoƙarin shigowa ɗakin, ajiye hoton
hannunsa ya yi ya miƙe tsaye yana nunata da yatsa ya ce"You...!" Gyaɗa masa kai
tayi tana murmushi ta ce " ko nayi ƙarye ne?, ba halin ka bane?," girgiza kanta
tayi jin yayi shiru ta cigaba da faɗin "halinka kenan, kanada son kanka, baka
damuwa da damuwar waɗanda suke kusa da kai, idan kuma har abin da na faɗa ba
gaskiya bane to Inason ka nunamin gaskiyar, ka bani kunya, ka barni na tafi inda na
fito dan girman Allah" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta alamar roƙo. Da
idanu kawai Maheer ya bita sai kuma ya bi ta gefenta ya fice daga ɗakin ba tareda y
ce mata komai ba, zaman daɓaro Imara ta yi akan tiles ɗin ɗakin da fashe da kuka
tana kallon ƙofa, above 5mins kafin ta tashi ta shiga goge idanunta sai kuma ta
koma inda ya ajiye enlargement ɗin hoton ta ɗaukeshi. Daskarewa Imara ta yi ganin
mai kama da ita sak jikin hoton, hannunta na rawa ta taɓa hoton nan take taji wasu
hawaye sun fara sakko mata wanda batasan na menene ba, wacece wannan?,
"KATALINA!"
Wani ɓangare na zuciyarta ya bata amsar, runtse idanunta tayi sai kuma ta sake buɗe
su kan hoton, kenan wannan shine dalilin daya sanya Maheer ya ɗaukota?, meyasa suke
kama?, wace ita?, mene ne ya rabata da Maheer?, ina take yanzu?. Shiru tayi na ɗan
lokaci ƙwaƙwalwarta na ayyana mata abubuwa dayawa, maganar Rania ce ta faɗo mata
hakan yasa ta miƙe tsaye kamar wacce aka tsikara ta fice daga ɗakin da sauri.
***Zaune take kan kujerar dake gefen gadonta hannunta riƙe da wayarta tana danna
cikeda nutsuwa, wata long sleeve ɗin riga ce a jikinta wacce ta ɗan matseta sosai,
ta tukfe gashin kanta waje guda. Wata number ta yi dialing ta zubawa screen ɗin
wayar tata idanu har ta katse ba'a ɗauka ba, kwaɓe fuska ta yi ta sake dialing amma
kamar ɗazu har ta kashe ba'a yi picking ba. Cilli tayi da wayar kan gadonta ta
tashi ta fice daga ɗakin, apartment ɗin Immi ta nufa tana shiga ta isketa zaune
suna magana da Shamma, kallo ɗaya ta yi mata ta kalli Immi cikin cool voice ɗinta
ta ce"idan kin gama zamuyi magana" murmushi Immi ta yi ta ce"Tom daughter" ganin ta
juya zata fita yasa ta kalli Shamma sai kuma ta ce
"Daughter bakiga Shamma ba?" Tana ƙoƙarin fita daga ɗakin ta ce"naganta mana" kafin
Immi tayi magana ta fice daga ɗakin tana buga ƙofar, shiru Shamma tayi tana jin
wani irin zafi can ƙasan zuciyarta.
"Ki ƙara hakuri kinsan har yanzu yarinya ce" Immi ta faɗa tana dafa Shamma,
murmushin yaƙe Shamma ta yi ta miƙe ta ce"anjima ma ƙarasa" jinjina mata kai Immi
tayi Shamma ta gyara zaman rigar jikinta ta fice daga ɗakin, wani murmushi Immi ta
saki tana bin bayanta da kallo sai kuma ta tashi ta fita domin haɗuwa da Joda.
*8:30pm*
Turo ƙofar ɗakin ta yi ta shigo, wani sassanyan ƙamshi ne ya daki hancinta tayi
saurin lumshe idanunta, zaune ta hangesa kan carpet ya tankwashe ƙafafunsa gabansa
wani littafi ne yana rubutu akai, a hankali ta shiga takawa har gabansa, sai a
sannan ya ɗago dara-daran idanunsa, kai tsaye kuma suka shige cikin nata. Sunkuyar
da kanta tayi tana wasada fingers ɗinta, rufe littafin hannunsa ya yi ya ajiye shi
gefe yana kallonta ya ce" Marhaban biki" jinjina masa kai ta yi ya yi mata nuni da
ta zauna, zama ta yi tana gyaran veil ɗin kanta, kallo ɗaya Ameer ya yi mata ya
ɗauke kai cikin daddaɗar muryasa ya fara mata magana
"Yau kuma tsiwar aka biyo ni har ɗaki a yimin?" Kallonsa ta yi taga ya kalleta tayi
saurin sauke idanunta ƙasa, murmushinsa mai kyau ya yi ya ce "then me ya kawo ki?,
ko zuwa kika yi ki gaida Ameer?" da sauri ta gyaɗa masa kai, waro idanunsa ya yi ya
ce "really?" Ta sake jinjina masa kai. Numfasawa ya yi ya ce"Allah ya yi miki
albarka Lolo" cikin sakin fuska ta ce"Ameen Nagode Ameer, saida safe"
"Laylatan sa'eedan"
Cewar Ameer, bata sake cewa komai ba ta tashi ta fice daga ɗakin, girgiza kansa ya
yi sai kuma ya ɗauko littafin ya cigaba da rubutunsa.
*London*
*Royal Brompton and harefield hospital specialist care*
*9:30am*
Turo ƙofar ɗakin ya yi ya shigo, turus ya yi ganin yanda take haɗa kayanta dake
cikin drawer. Girgiza kansa ya yi bai ce komai ba ya ƙarasa shiga ciki, zama ya yi
kusada ita yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi ba kamar wancen lokacin ba,
ɗago kai tayi ta kalleshi ta galla masa harara ta cigaba da abin da take, gyara
zamansa yayi yana murmushi ya ce"matar wa ya ɓata miki kai?" Yanda ya yi maganar
cikin zolaya ya ƙara fusata ta ta kalleshi kamar zatayi kuka ta fara magana cikin
harshen larabci
"A'a kar ka fara wlh, tunda an san ni aka cuta dole ka ce wa ya taɓa ni, to wlh
bazai yiwu ba kuma ni yau bazan sake kwana ƙasar nan ba kaji na faɗa maka" shafa
kansa ya yi wanda yasha gyara yana murmushi ya kamo hannunta cikin kwantar da murya
ya fara magana"haba matar me ya yi zafi haka?, kiyi haƙuri nan da 3days za'a yi
discharging naki" janye hannunta ta yi tana watsa masa wani kallo ta ce"a'a,
inaaaa, ni zaka yiwa siyasa?, wlh baka isa ba!. Ni yau nakeson barin ƙasar nan
haba!, nagaji" ganin yanda take masifa ya sanya ya tsuke fuska kamar ba shi ba ya
kalleta cikin wata husky voice ya ce" to tashi ki tafi mana" juyowa ta yi ta
kalleshi ganin yanda ya haɗe rai ya saka ta fasa faɗar abin da tayi niyya ta cigaba
da haɗa kayanta tana cewa"mutum sai baƙar zuciya, Ka sauya hali!".
*Al-Udaid Kingdom*
*10:00am*
Zaune take gefen gado tana linke kayanta kasancewar yau Saturday babu lecture, gaba
daya hankalinta baya jikinta, ƙwaƙwalwarta tayi nisa cikin tunanin da take, tana da
buƙatar sanin abubuwa masu yawa game da mijinta da kuma Udaid gaba ɗaya, amma wa
zata tunkara?, wane wanda zai warware mata wannan al'amarin ta fahimceshi?
"Ameer!"
Wani bangare na zuciyarta ya bata amsa, girgiza kanta tayi ta ce a fili"amma zai
sanar dani komai?, ta yaya?" Ajiye rigar hannunta tayi ta kwaɓe fuska kamar ƴar
baby ta zuba uban tagumi, above 5mins kafin ta miƙe tsaye ta sanya ɗan ƙaramin
hijab kan Abayar jikinta ta fice daga ɗakin da sauri.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama, babu kowa a ciki sai
ƙamshin turarensa mai matuƙar daɗi wanda ya haɗe da sanyin ɗakin ya bada wani irin
yanayin mai daɗin gaske, tamkar mayen ƙarfe haka Imara taji ana janta zuwa cikin
ɗakin kai tsaye kuma inda royal bed ɗinsa yake ta nufa. Zama tayi gefensa tana
shafa katifar tana jin wata nutsuwa na saukar mata, kalle-kalle ta shiga yi a
ɗakin, komai tsaf yake tamkar ba babba mutum bane a ɗakin ko ba'a faɗa ba Ameer ɗan
gayu ne ajin farko. Tashi tayi ta ƙarasa gaban dressing mirror ɗin dake kallonta ta
ƙurawa kanta idanu tabbas ta rame sosai kuma hakan nada alaƙa da halin data tsinci
kanta a ciki, sarƙar dake maƙale a wuyanta ta kalla, ta kai hannu ta shafi sarƙar
wacce ke tuna mata rayuwarta ta baya, inama da ta dawo mata, inama ranakun farin
cikin da suka shige su sake maimaita kansu, ɗumin da taji akan fuskarta ya tabbatar
mata da kuka take, hannunta ta sanya ta goge hawayen nata nan da nan fuskarta tayi
jajur.
"Lolona"
A ɗan firgice ta juya sai kuma ta sunkuyar da kanta ganin ya zuba mata idanu, taku
biyu yayi ya ƙaraso gabanta ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta ya ce "why
are you crying?" girgiza masa kai tayi alamar babu komai, murmushi ya yi cikin
nutsuwar da ta gama ratsa shi ya ce"ajiye ina sonki a gefe, daga yau na zama friend
ɗinki, a good friend saboda haka feel free and tell me what's wrong with you, I'm
here with you" kallonsa tayi a karo na farko, kallo na tsanaki ta ce cikin muryar
kuka
"Absolutely sure"
Ya bata amsa, goge hawayen fuskanta tayi ta gyaɗa masa kai, ya miƙa mata hannunsa
kallonsa tayi sai kuma ta kalli hannun da ya miƙa mata kafin ta ɗora nata a kai,
bai ce mata komai ba ya fara tafiya da ita, Library ɗinsa ya nufa da ita, suna
shiga ta zauna kan kujera shi kuma ya nufi inda fridge yake, ruwa mai sanyi ya
ɗauko mata da cup ya dawo ya zauna kujerar dake facing tata ya ɓalle bottle ɗin
sannan ya miƙa mata, ko kallon cup ɗin bata yi ba ta kafa bakinta jikin bottle ɗin
ta fara shan ruwan, cikin sakkanin da basu shige uku ba ta ajiye empty na robar ya
kalleta ganin yanda take sauke numfashi a hankali. Tana matuƙar bashi tausayi, yana
ɗaya daga dalilan daya sanya yake sake jin sonta cikin zuciyarsa. Sun ɗauki mintuna
kafin yaga ta dawo cikin nutsuwarta, ya gyara zamansa yana facing ɗinta sosai ya
ce"now tell me" numfasawa tayi cikin sanyin murya ta ce "Ameer"
"Lolona"
"Kome na tambayeka zaka bani amsa?" Jinjina mata kai ya yi, ta cigaba da faɗin
"To dan Allah Ameer waye Maheer?, meyasa ya aureni?, wace Katalina?, meyasa nake
ganin komai ba daidai bane?, meyasa Maheer ya tsaneni?, meyasa kake sona?" Tunda ta
fara magana Ameer ke kallonta fuskarsa fal da tausayinta. Jin ya yi shiru yasa ta
fashe da kuka tana rufe bakinta da hannunta take faɗin
"Ba zaka faɗa min ba ko?, ba zaka iya ba ko Ameer?, kace kai abokina ne, kenan
bazaka iya taimakona ba?, kafison na cigaba da zama cikin fadar nan har baƙin ciki
ya kasheni?." Sakkowa tayi daga kan kujerar ta tsuguna kan gwuiwarta ta haɗe
hannayenta waje ɗaya alamar roƙo ta cigaba da faɗin "dan Allah dan Annabi Ameer ka
taimakeni, ka sanar dani waɗannan abubuwan ko nasamu wani tudu da zan kama wajen
ganin na sauya rayuwata, ka zame mini aboki nagari kaji dan Allah karka bari na
rasa rayuwata saboda wannan takaicin dan Allah Ameer dan All...Allah...dan..." Ta
kasa cigabawa saboda kukan da yaci ƙarfinta. Shiru Ameer ya yi yana sauraren kukan
nata wnada yake jinsa har ƙasan zuciyarsa,
"IMARA!"
Ɗago jajayen idanunta tayi ta kalleshi cikin shassheƙar kuka ta ce "Na'am" "stop
crying!" Daina kukan tayi ta shiga sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri. Numfasawa
Ameer ya yi ya haɗe hannayensa biyu waje guda idanunsa bisa carpet ɗin ɗakin ya
fara magana cikin tsaftaccen harshen larabci;.
"Zan sanar dake abin da kika buƙaci ki sani, wanda kuma bayan ke babu wanda ya san
da hakan, kema kuma zan sanar dake ne domin na wanke kaina daga zargin da kike
mini, tabbas Imara ina sonki, kuma naji ina ƙaunarki, saidai bansan dalili ba har
yau, ina ji kamar na taɓa rayuwa dake a baya, mun saba kuma mun shaƙu sosai, tun
ranar da Maheer ya kawo ki gidan nan naji sonki ya ɗarsu cikin zuciyata, bansan
wane kalar so bane, ban san dalilin samuwarsa ba, amma naji inason ki kasance a
gefena har na ƙarshen rayuwata. Amma na rantse miki da Allah ban taɓa miki so wanda
yake bana daidai ba, kuma nasan abinda na aikata ba laifi bane dan na furta ina
sonki, ko a wajen Allah ban aikata abin da yake haramun ba" kallonsa tayi kawai ba
tareda ta ce komai ba ya cigaba da faɗin
"Maheer, ya kasance ɗa a wajena, ina kuma matuƙar alfahari da hakan, Maheer mutum
ne mai sauƙin kai saidai idan ba'a fahimceshi ba, amma yana da sauƙin mu'amala.
Rayuwarsa ta shiga wani hali shekaru biyu da suka shige, ya faɗa cikin wani
mawuyacin hali, ya maida damuwa abokiyar rayuwarsa, shin kinsan dalili?"
"Katalina! Saboda Katalina, ta kasance budurwa a wajensa, yana ɗaya daga cikin masu
yi mata lecture a school, two years back ta shirya yin tafiya, a ranar sun haɗu da
Maheer a makaranta bayan ya dawo gida aka kira shi aka faɗa masa ta yi hatsari ta
rasu, Maheer bai yarda ba saida ya je har gidansu, amma iyayenta suka ƙi bashi
damar shiga ya ganta, tun daga sannan rayuwarsa ta canja sabon da yayi da Katalina
ba ƙarami bane takai ta kawo kowa ya gani sunanta yake kira, daga nan muka kai shi
asibiti, anyi iya bakin ƙoƙari kafin a samu kan Maheer lokacin Katalina ta yi
shekara da rasuwa. Bayan ya dawo hankalinsa ne aka tura shi aikin kwangila ƙasar
ku, tun ranar daya fara ganinki ya kirani a waya hankalinsa a tashe ya ce ya ga
Katalina, Ni kaina sanda ya turan hotonki saida na gazgata cewa ita ce, nan yaƙi
yarda yace sai ya tawo dake shine dalilin da aka ɗaura muku aure, saidai tun da
kuka dawo ƙasar nan ya fuskanci ke daban Katalina daban shikenan ya shiga muzguna
miki, duk a tunanin Maheer ke Katalina ce kawai kin rabu dashi ne saboda daman can
iyayenki Basu san alaƙarku, amma ni tun ranar dana ganki na tabbatar da ke ba
Katalina ba ce! Kuma na yarda da ke, nake sonki nake ƙaunarki. Ruwa ya ɗauka yasha
sannan ya cigaba da faɗin "maganar UDAID kuma bazan iya baki labarinta ba domin
nasan ba zaki taɓa fahimta ba, amma idan har kina cikinta watarana zaki gane abinda
ta ƙunsa."
Wata nannauyar ajiyar zuciya Imara ta sauke kafin ta ɗago ta kalleshi cikin sanyin
murya ta ce "yaushe zan koma gidan mu?" Kyakkyawan murmushi ya yi yana girgiza
kansa ya ce "bansani ba nima" kwalla ce ta kawo idanunta ta ce "zan nemi Maheer ya
sakeni na koma gidanmu, tunda ba ni ce wacce yake so ba, duk da zan so sanin
dalilin daya sanya muke kama amma zan bar wa Allah komi zan koma Nigeria na cigaba
da rayuwata kamar yanda nafara ta" shiru Ameer ya yi bai ce mata komai ba, badan
bai ji abin da ta ce ɗin ba, sai dan bai san amsar da zai bata ba dukda yasan abune
mawuyaci barinta da Udaid. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta miƙe tayi hanyar waje
tana tafiya jikinta a sanyaye ba kamar yanda ta shigo ba. Saida ta kai bakin ƙofar
sannan ta juyo ta kalleshi taga ita ya ke kallon muryarta na rawa ta ce "Nagode
sosai Ameer, nagode da kulawa" lumshe idanunsa ya yi bai ce komai ba ta juya ta
fita. Da mamaki Shamma ke kallonta har ta shige nata apartment ɗin, me ya kaita
wajen Ameer?, yaushe ma Ameer ya fara magana da ita?, me suke tattaunawa da har ta
daɗe haka a ciki?.
"Shamma!"
Firgigit ta juya tana kallonsa sai kuma tayi murmushi ta ce "Lafiya son?" Girgiza
kansa ya yi ya ce "sorry I scared you" murmushi ta yi ta ce "ba komai, ka ci
abinci?" Shafa cikin nasa ya yi ya ce "I'm not hungry Shamma, so you don't have to
be worry" harararsa tayi ta ce "hakane" ganin ta dauke idanunta ya sanya ya saƙalo
hannayensa a wuyanta yana murmushi ya ce "I'm sorry to zan ci in sha Allah"
"Promise?"
Jinjina mata kai ya yi ta ce"oya Maza kaje ka ci nima zani wajen Ameer ne" shiru ya
yi sai kuma ya ce"kin gano meke damun nasa?" girgiza kai tayi ya ce " amma why
Shamma?" Numfasawa tayi ta ce "Maheer kasan halinsa yana da kafiya akan abu, nayi
nayi ya sanar dani meke damunsa yaƙi" girgiza kai ya yi ya ce"let me talk to him"
jinjina masa kai tayi, ya yi gaba tana biye a bayansa.
***Tunda ta shiga ɗakin take kai kawo ta kasa zama guri ɗaya, me kunnuwanta suka
jiye mata? Ameer yana son Imara? Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, wane irin
abu ne wannan kamar a Film ko a littafai? Maha ta tambayi kanta. Kasa jurewa tayi
ta ɗauki wayarta ta shiga dialing numbern Joda sai kuma ta katse kiran tana girgiza
kanta a fili ta ce
"No bai kamata ba, babu wanda zan sanarwa, zan cigaba da riƙe abun a raina tunda
babu wanda ya sani"
Daga bakin ƙofa taji an wullo mata tambayar, Shamma ce ta shigo hannunta riƙe da
mug sai tiriri yake, murmushin yaƙe tayi dukda yanda ƙirjinta ke bugawa na tsananin
tashin hankali ta ce "babu komai Shamma, akan wasu coursemates ɗina ne suke soyayya
shine basu san kowa ya sani Ni kuma na sani shine da nake tunanin na faɗawa sauran"
mug ɗin hannunta ta ajiye ta kama hannun Maha tana murmushi ta ce"kul, karki zama
mai tonawa mutane asiri, duk abin da kikaga Allah ya rufe shi to babu shakka ya
kasance a rufen shine mafi Alkhairi, a duk sanda kikaga wani ɗan uwanki musulmi na
cikin matsala ki taimakeshi, idan yana neman rufin asiri ki rufa masa sai kiga kema
Allah ya rufa miki asiri ranar gobe ƙiyama"
Wasu zafafan hawayene suka shiga sintiri kan fuskarta, na tsananin tausayin Shamma,
koda wasa batayi tunanin Ameer zai iya furta irin wannan kalaman ba, sai gashi yana
furta yana son wata, watar ma kuma matar ɗansa. Ganin kamar tunani take ya sanya
Shamma ta shiga goge mata hawayen fuskarta
Murmushi tayi tana share hawayen ta ce"thank you Shamma, Ana ahubbuki( ina sonki)"
murmushi tayi tana jan kumatunta ta ce" nima haka".
A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama, hangensa tayi kan
gadon ya rufe jikinsa da duvet da alama bacci yake, around 12am ne tasan ba ƙaramin
al'amari bane zai sanya ya kwanta a wannan lokacin, ƙarasawa tayi ta zauna gefen
gadon ta zubawa kyakkyawar fuskarsa idanu, Allah sarki haka rayuwa take dama, a
lokacin da kake muradin rayuwa da wani abu a lokacin yake barinka, watarana ayi
farin ciki watarana ayi baƙin ciki, a duk halin da mutum ya tsinci kansa ya godewa
Allah shine kawai abin da ya fi masa, daga sanda ka kasance mai godiya ga Allah,
daga sannan matsalolinka zasu zama tarihi. Ajiyar zuciya ta sauke tana sake tunano
abin da Ameer ya ce mata, da gaske Maheer baya sonta, da gaske Katalina yake so,
amma meyasa ita kullum take jin sonsa cikin zuciyarta?, meyasa take jin kamar shine
abokin rayuwarta?, meyasa take kasa jin zafinsa?
"Soyayya!".
08106608363.
# *IMARA*
# *Bestnovel*
# *2025*
# *Nanameera.**Chapter 7&8*
Taji Maheer ya furta yana buɗe idanunsa, sunkuyar da kanta tayi ba tace komai ba ta
miƙe zata fita, hannunta ya riƙe cikin nasa tayi saurin sauke idanunta ƙasa tana
goge hawayen dake zuba a idanunta da hannu ɗaya. Miƙewa zaune ya yi har sannan yana
riƙe da hannunta, jawota ya yi ya zaunar da ita kusada shi ya zuba mata idanu yana
kallonta, shiru Imara ta yi tana wasada fingers ɗinta sun ɗauki wasu mintuna kafin
ya numfasawa cikin sanyin murya wanda bai san yanada shi ba ya ce
Janye hannunta tayi tana girgiza kanta ta ce"hakane amma yanzu na cire wannan
yardar da nayi maka, kai ɗin ba abun yarda bane, ka cutar da rayuwata, a lokacin da
nake tunanin matsalolina sun zo ƙarshe sai ka shigo cikin rayuwata ka hanani zama
lafiya, ka shiga bijiromin da abubuwa waɗanda suka fi ƙarfina. Kakeson ka cimma
wata manufarka ta hanyar amfani dani, bazan taɓa mantawa da wannan ba Maheer, bazan
manta ba, zan cigaba da tuna irin yanda ka kula dani a baya kafin ka nuna ƙudirinka
na aurena!" Tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin kamar zata tashi sama. Ajiyar
zuciya ya sauke deep down nasa yana jin babu daɗi abin da ya yi mata domin tabbas
ta riƙe shi masoyi kuma abun dogaronta bata taɓa tunanin haka daga gare shi ba, da
wannan tunanin Maheer ya ƙarasa yinin ranar dan ko babban parlon bai sake fitowa
ba.
Washegari.
Da wuri tagama shirin makarantar ta dan akwai abin da takeson faɗawa Rania kafin su
fara lecture, tana ƙoƙarin fita daga ɗakin ya shigo kallonsa ta yi sai kuma ta saki
murmushi ta tsuguna har ƙasa ta gaisheshi, amsawa ya yi da fara'a a fuskarsa ta
tashi tana sunkuyar da kanta ƙasa
"Makaranta za ki?"
Gyaɗa masa kai Imara ta yi, ya jinjina kansa shima ya ce "ki zo mu fita tare sai
driver ya ajiye ki" har zata ce a'a sai kuma ta gyaɗa masa kai ko babu komai zata
samu damar kasancewa tare dashi har ta sake fahimtar wasu abubuwan da ya shafi
Udaid. Da wannan tunanin ta bi bayansa suka fice daga apartment ɗin,
Tunda suka fara sakkowa ta zuba musu idanu tana kallonsu, wani irin abu taji ya zo
ya tsaya mata a ƙirji nan da nan fuskarta tayi jaa na tsananin baƙin ciki, ita
kaɗai ce a parlon hannunta riƙe da mug na tea. Imara ce ta kalleta cikin sakin
fuska ta ce "Sabahul khair Maha" mayar mata da murmushin tayi ta ce "kin tashi
lpy?" "Alhamdulillah" cewar Imara,
"Barka da fitowa Ameer" Maha ta faɗa tana ƙoƙarin barin parlon, jinjina mata kai
Ameer ya yi bai ce komai ba ya fice daga fadar, Imara tabi bayansa.
*London*
10:00am.
Tamkar wacce ke magana da statue haka ya yi mata, daga ƙarshe ma ya sanya Bluetooth
a kunnensa yana jin karatu, baki Jadda ta saka ganin ya yi mata shiru sai kuma ta
kama gefen hijab ɗin dake jikinta ta fara goge kwalla. Gajiya ya yi da zaman ya
miƙe hannayensa zube a aljihu ya ce "idan kin gama kukan ki sameni a waje, if not
wlh zan tafi na barki ƙasar nan" da harara Jadda ta bisa, sai kuma ta cigaba da
haɗa kayan nata tana magana cikin masifa
***Suna fitowa daga lecture Imara ta kalleta ta ce"kinsan me kuwa?" Girgiza mata
kai Rania ta yi ta ce"zo muje zan baki labari" da sauri Rania ta kama hannunta tana
dariya ta ce"nidai wlh ki faɗamin anan kawai" murmushi Imara tayi bayan ta zauna
kan wata kujera ta kalli Rania tana nuna mata gefenta ta ce"zo ki zauna" babu musu
Rania ta zauna ta yi tagumi ta ce"oya ina jinki Maza-Maza" numfasawa ta yi ta
ce"ƙawata ta kirani ta cemin taji daɗi shawararki har tafara sanin wasu abubuwan na
dangin mijin nata" murmushi Rania ta yi ta ce"To Masha Allah, ta cigaba da kaiwa
Allah kukanta in sha Allah komai zai zame mata tarihi" dafata Imara ta yi ta ce"zan
faɗa mata in sha Allah, kema kuma ina godiya" harararta Rania ta yi ta ce"banson
hauka fa" tuntsirewa sukayi da dariya a tare.
MAHEER.
Zaune yake cikin office ɗinsa sai juyi yake kam kujerar tasa, abubuwa dayawa suna
neman shigowa rayuwarsa, tunani yake wani hukunci zai yanke akan Imara tunda dai
yanzu ya gano ba ita ce wacce yake muradin yin rayuwa da ita ba, kodai ya maidata
garinsu?, ko dai ya sanar da ita gaskiyar daya daɗe yana ɓoye mata?, amma wane
kallo zata yi masa?
"Calm down Maheer, calm down!" Ya faɗa yana dukan kansa, ganin tunani na neman
hargitsa ƙwaƙwalwarsa yasa ya miƙe ya ɗauki car key ɗinsa ya fice daga Companyn
gaba ɗaya.
***Fitowa Joda tayi daga motar tana ƙarewa wajen kallo kafin ta saki handle ɗin
motar ta fito tana tafiya cikeda taƙama, hango shi tayi zaune idanunsa maƙale cikin
glasses baƙi ta ƙarasa wajen tana murmushi, zama tayi gefensa cikin fara'ar da
batasan tana da shi ba ta ce "welcome yallaɓai" murmushi ya sakar mata shima cikin
jin daɗi ya ce "thank you beauty" murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya
loma sannan ta ce"ka yar dani ko?" Waro idanunsa ya yi ya ce "ni ɗin?" ta gyaɗa
masa kai tana kwaɓe fuska, girgiza kansa ya yi ya ce "nikam karki min sharri, tunda
kika baro turkey baki nemeni ba sannan ni yanzu ki ce na watsar dake?" rufe bakinta
tayi tana dariya ta ce "kawai a bar maganar, tunda naga ƴar tone tone ce" dariyar
shima ya yi ya ce "kinsan ai kece bakida gaskiya kawai" murmushi ta yi ta
ce"shikenan naji let bygone be bygone, yanzu me zaka ci?".
Wani banzan kallo Maheer ya watsa masa ya miƙe ya ce"kai naga ba'a abun arziki
dakai nayi ta nan" tuntsirewa ya yi da dariya yana riƙe rigarsa ya ce"haba friend
wlh wasa nake zo kaji" doke hannunsa ya yi ya ce" just leave me " shafa kansa Asad
ya yi yana dariya ya ce"zama ka dawo ne yaro".
6:00pm.
Tafiya suke a tare suna ɗan taɓa hira gaba ɗaya sun gaji kasancewar yau sai yammaci
suka tashi daga lecture, ganin yanda take ta kwaɓe fuska yasa Rania ta ce "wai
yaushe kika zama haka ne?, ke da bakida son jiki amma ji yanda kike yi yanzu haba!"
kallonta Imara tayi sai kuma ta yi murmushi tana sake ƙanƙame books ɗin hannunta ta
ce "to ai da kika sani" shiru Rania tayi ganin kamar ba son maganar take ba, waro
idanu Imara tayi ganin wanda yake gabato inda take, gaba ɗaya guards sun zagaye shi
ko ba'a faɗa maka ba kasan babban mutum ne wanda ƙasar ke ji dashi. Murmushi Ameer
ya sakar mata daidai lokacin da yazo dab da ita, baki buɗe Imara ke kallonsa kafin
ta haɗiye yawun bakinta cikin sanyin murya ta ce "ba dai laifi nayi ba?" girgiza
mata kai ya yi ya ce " zuwa nayi tafiya dake" baki buɗe Imara ke kallonsa sai kuma
ta ce"ai da baka zo ba bama yanzu zan tafi, kuma..." shiru tayi ganin yanda Ameer
ya kafeta da idanunsa, da hannunsa ya yi mata nuni da ta shige ta tura baki gaba
sannan tayi gaba tana ɗagawa Rania hannu, murmushi Rania tayi itama tana ɗaga mata
hannun. A back seat ta zauna tana sake ƙanƙame books ɗin hannunta haka kawai take
jin ta uncomfortable musamman da daga Ameer na zaune gefenta duk da ba ita yake
kallo ba ɗan ƙaramin azkar ɗin hannunsa yake ja. Har suka ƙarasa gida babu wanda
yace komai a cikinsu kowanne da abin da yake saƙawa cikin zuciyarsa, tana ganin
motar tayi parking ta kama handle ɗin zata buɗe amma ta ji shi ƙam da alama lock
aka sakawa motar, gyran murya ya yi driving ya fice daga motar Imara ta juyo ta
kalleshi tana rarraba idanu, ganin har sannan bai ɗago kansa ba yasa kamar zatayi
kuka ta ce " zan sauka" ɗago kansa ya yi ya kalleta, saurin runtse idanu Imara tayi
ganin yanda idanunsa suka sauya launi sunyi jajur dasu sun ƙara fitowa. Cikin rawar
murya ta ce
"Am...Ameer lafiya?, wani abu yana damunka?, ko bakada lafiya?" Ta jera masa
tambayoyin lokaci guda, lumshe idanunsa ya yi kawai nan take wani ruwa ya kwanta
cikin idanun, hannunta ta kai zata taɓa shi ko me ta tuna kuma sai ta janye jiki a
sanyaye ta ce
"Mene ne yake maka ciwo?, ko na faɗawa Maheer?, bari na kira Shamma" ta juya tana
kama handle ɗin ƙofar a karo na biyu, tattausan hannunsa ya sanya ya riƙe nata
hannun tana juyowa ya girgiza mata kai, kwaɓe fuska tayi ta ce"to kuma kai bakada
lafiya ba za'a faɗawa kowa ba, ko so kake ka mutu?" Wani murmushi ne ya suɓuce
masa, Imara sakar baki tayi tana kallonsa ganin yanda ya yi wani irin kyau tamkar
ba tsoho ba, ganin kamar tayi nisa cikin tunani ya sanya ya ɗan girgiza ta kallonsa
tayi ta ce "ni ka saukeni"
Ajiyar zuciya Maha ta sauke tana sakin window ɗin, da gaske ne Ameer neman Imara
yake!, yaushe Ameer ya zama haka?, me yake damunsa da har zai iya aikata irin
wannan ɗanyan aikin?, kenan da gaske cin amanar Shamma yake?.
"No, bazai yiwu ba!, bazan bari ba, dole sai nayi maganin wannan matsalar" Maha ta
faɗa cikin ɗaga murya, cikin hanzari ta fita daga ɗakin nata tana tafe kamar wata
zararriya.
***
Tunda suka shiga cikin jirgin bata sake ganin gilmawarsa ba, ta zuba uban tagumi
tana tunanin inda ya shige ya barta, ƙofar VIPn ya buɗe ya fito yana sanye da wasu
English wears t-shirt milk colour sai three-quarter coffee gashin kansa wanda yasha
gyara sai sheƙi yake ya zubo har wajen kafaɗarsa, tafiya yake kamar baya so sai
yamutse fuska yake har ya ƙaraso gabanta. Wani nannauyar ajiyar zuciya Jadda ta
sauke kafin ta kalleshi ta galla masa harara cikin faɗa take faɗin
"Kai dai wannan yaro ka sauya hali!, banda kai sallamamme ne ka yi tafiyar ka ka
barni cikin jimamin inda ka shiga, saboda rashin imani irin naka, to wlh kaida
Allah, kaje idan ka zalunceni ni na yafe maka dan bazan maka baki ba, amma dai ka
sauya hali!" Ta ƙarashe maganar tana nuna shi da yatsa, wani kallo ya yi mata wanda
ya sanyata sauke idanunta ƙasa cikin kwantar da murya ba kamar ɗazu ba ta ce
"Haba mijin sai ka tafi ka barni bayan kasan yanda na damu dakai, banason na mutu
banga aurenka ba" ta kama gefen mayafin jikinta tana goge hawaye, ji ya yi jikinsa
ya yi sanyi ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa yana murmushi ya ce
"Ke da zakiyi shigar amare ranar bikin ai kina nan ma, ko amaryar na tabbata ba
zata faɗa miki kyau ba" washe baki tayi tana kallonsa cikeda fara'a ta ce "to to
Masha Allahu, wa ya ganni bikin mijin ai baza'a gane ni ba" murmushi kawai ya yi
ganin hankalinta ya kwanta kuma daman abin da yakeso kenan.
Maƙalewa Jadda tayi jikin matattakalar jirgin tana ƙarewa garin kallo ganin ba inda
ya dace su kasance ba, zuwa ya yi ya shige ta gabanta tayi saurin figoshi tana
kallonsa ta ce "kai ina ne nan ka kawo ni?" Bai ce mata komai ba ya zare hannunta
daga jikinsa ya ƙarasa sauka daga jirgi, cikin saurin ta irin na tsoffi ta ƙaraso
gabansa ta ce a fusace
"Hala da Fatima kake magana da kayi shiru ko?" A fusace shima ya juyo ya ɗora
hannayensa a ƙugu kamar mace yana zazzare mata idanu ya ce" me kika ce?"
"To ni kuwa me zance ɗan nan?, kawai tambaya nake ina ne nan?"
*Chapter 9&10*
Waro idanu Jadda tayi sai kuma ta shiga tafa hannu, tsabar baƙin ciki ya sanya ta
rushe da kuka tana kallonsa ta ce "Wlh Muhammadu zan nuna maka ɓacin raina da baka
taɓa ganin irinsa ba, kayi gaggawar sauya wannan maganar taka" tunda ta fara magana
yake kallonta, duk abinda ta faɗa daga cikin zuciyarta yake, da gaske batasan zuwa
wajen danginta, ta guji yan 'uwanta, yaushe wannan gabar zata ƙare?. Ganin yanda ta
haɗe rai kamar ba ita ba ya sanya ya kamo hannunta cikin sanyin murya ya fara
magana
"Jadda dan Allah kiyi haƙuri, mene rayuwar?, abin da ya faru ya shige mana, ki dawo
cikin dangin ki, ki daina gudun 'ya'yanki, uhm" kafeshi tayi da idanu bata ce komai
ba, ganin yanda idanunta ya fara sauya launi ya sanya ya girgiza kai ya ce"shikenan
yanzu ki yi haƙuri zan yi mana booking flight ko zuwa dare ne, kafin nan muje gidan
ku gaisa"
"Abaan!"
Yaji ta kira sunansa cikin wata murya mai nuna asalin fushin da take ciki,
"Karka kuskura ka sake furtamin maganar su anan, idan ba haka ba wlh zan saɓa maka,
sannan kuma ni bazan je inda suke ba, har abada!" Shafa kansa kawai ya yi sanin
halin gaddamar Jadda, cikin sanyin murya ya ce"shikenan bari muje hotel sai nayi
mana booking flight"
*UDAID*
7:35pm.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin tana wulla idanunta ciki, babu kowa a ciki sai ƙamshi
dake tashi ko'ina an gyara shi tsaf, ƙarar zubar ruwan da taji yasa ta kalli toilet
ɗin, sai kuma ta yi tsaki ta ƙarasa gaban madubin hannunta ta ɗora kan drawern ta
zubawa fuskarta idanu, abubuwa dayawa zuciyarta ke raya mata.
"Lafiya Maha?"
Ta tsinkayi muryar Imara tana mata magana, wani irin abu taji ya tsaya mata a ƙirji
nan da nan fuskarta tayi jaa, ta juya yana watsa mata wani shegen kallo ta ce"
lafiyar ce ta kawo haka munafuka!" Baki buɗe Imara ke kallonta, Maha ta cigaba da
faɗin
"Saboda ke mahauciya ce baki san me kike ba, shashasha, dabba, me bakin iyaye har
zaki nemi ubanmu ko?, saboda ke daƙiƙiya ce bakisan abinda yake daidai da wanda ba
daidai ba ko?, saboda ke matsiyaciya ce ƴar matsiyata ko?, kin bani mamaki!, nayi
tunanin ke mutuniyar kirki ce ashe ba haka bane, no wonder naga kowa na gudunki a
gidan nan ashe su suka san da wacce suke zaune. Ki rasa wa zaki nema ma sai uban
mijinki, surukinki!,"
Ɗora hannu Imara tayi aka tuni hawaye suka gama wanke mata fuska cikin rawar murya
ta ce
"Sai an faɗa min?, daman kun sanar da wani ne wanda kuke tunanin zai faɗawa wasu?,
abin da kuke tattaunawa a cikin ɗaki, nima Allah ne ya yi nufin tonon asirin ku
yasa naji kuna maganar, kinyi asara wlh kuma na rantse miki da Allah ba zan bar
maganar nan iya haka ba saina tona idan yaso kuwa yaji abin da kuke aikatawa!" Ta
ƙarashe maganar cikin ƙaraji sannan ta fice daga ɗakin. Zubewa Imara tayi kan tiles
ɗin saidai zuwa sannan ko kukan ma ta kasa samun damar yi, sai wata irin rawa da
jikinta ke yi, ta jure jikinta waje guda tana sauke ajiyar zuciya akai-akai.
***Zaune yake gefen gadon nasa sai juya takardar dake hannunsa yake, tunani yake
idan abin da ya yi shine abin da ya kamata, amma ya mutane zasu ɗauki maganar
tasa?, Allah yasa kowa ya fahimceshi. Wani zazzafan numfashi Maheer ya sauke kafin
ya tashi tsaye ya linke takardar ya zura a aljihun trouser ɗinsa sannan ya yi waje,
a bakin stairs ɗin ya hangi Joda tana danna wayarta, ƙarasawa gabanta ya yi without
making any sound yana zuwa ya rufe mata idanu da hannunsa, ɗan murmushin gefen baki
tayi tana riƙe hannayen nasa ta ce
"Wai ka mantani, tun daga nesa na ganka fa"
Waro idanu ya yi yana juyo da ita gabansa ya ce" oh shit!" Tuntsirewa tayi da
dariya ta ce "ina zuwa ne na ga kasha kwalliya?" Harararta ya yi ya ce "inda kika
aikeni" rufe bakinta tayi da hannunta tana dariya ta ce"au nafa manta ba'a
tambayarka inda zaka" girgiza kansa ya yi yana murmushi ya sauka daga Benen.
*DAMEER*
Tunda ya shiga yake kai kawo a cikin ɗakin yana jin ransa babu daɗi, tamkar
zuciyarsa zata fito haka yake ji, turo ƙofar ɗakin tayi ta shigo tana kallonsa ta
ce"Dameer lafiya?" juyowa ya yi ya kalleta idanunsa sun kaɗa sun yi jajur dasu,
yanda ya kafeta da idanu yasa Immi ta ce "ka tsareni da ido, ka sanar dani abin da
ke faruwa" wani zazzafan numfashi ya furzar daga bakinsa ya zuba hannayensa a
aljihu yana kallonta ya ce
"Immi raina ya fara ɓaci da wannan al'amarin, abubuwa sun fara fin ƙarfinmu,
ƙaramar magana na nema ta zama babba, Udaid zata bar hannun mu ki fahimta!" Ya faɗa
yana dafa kafaɗarta. Girgiza kai Immi tayi tana janye shi daga jikinta ta ce" wai
meke damunka Dameer?, ta ya ya?, bazan bari haka ta faru ba!, dole sai nasan yanda
nayi mulkin Udaid ya dawo hannunka, koda kuwa bakada gadonta".
"Immi kin sani na sani ni ba jinin gidan nan bane, ban raɓi Udaid ba!, kin kawo ni
a matsayin Dameer wanda ya mutu tun bayan kwana biyu da haihuwarsa, nasha
gwagwarmaya sosai a cikin fadar nan, har na girma cikinta ina faɗi tashi na yanda
zan samu wani matsayi a cikinta, amma ace har yanzu ban cimma matsaya ba?, banida
wani abun dogaro?, ba zai yiwu ba!, wlh ba zai yiwu ba Immi!"
Kamo hannun tayi ta zaunar dashi kan kujera ta dafa table ɗin dake gabansa tana
kallonsa ido cikin ido ta ce
"Me kake nufi da wannan maganar taka?, meyasa ka sakota cikin zancenmu?, juyan baya
ka shirya yi ne?, so kake wani yaji abin da kake cewa?, karka sake Dameer!, kar ka
kuskura ka sake furta irin waɗannan kalaman ko da kuwa dani ne, kai Dameer ne wanda
aka haifa cikin fadar nan, so you have to be careful!"
Yanda Immi tayi maganar cikin ɓacin rai ya sanya shi yin shiru, bai ce komai ba ya
tashi ya fice daga ɗakin sai sauke ajiyar zuciya yake. Wani gumi ne ya shiga keto
mata wanda batasan na mene ne ba, kodan abun da Dameer ya faɗa ne?, kada watarana
asirinta ya tonu.
"Never!"
Ta faɗa a fili,
"Ke dawa?"
A firgice Immi ta juyo tana kallon Joda wacce ke tsaye kanta hannunta riƙe da
system, doguwar rigar Turkey Abaya ce a jikinta ta ɗaura veil ɗin abayar a kanta,
sosai farinta ya ƙara fitowa kasancewar abayar Black colour. A ɗan daburce Immi ta
ce
Taɓe baki ta yi ta zauna gefen gadon tana kallonta ta ce"kina can zancen zuci"
murmushi Immi tayi tana hamdala aranta da bataji abin da Dameer ya ce ba, ta
kalleta ta ce"zancen zucin me zanyi nida babu abin da ke damuna sai naga kin yi
aure" kallonta Joda tayi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce"aure kuma Immi taɓ!, nidai
a'a wlh" dariya Immi tayi ta ce"ai aure ya zama dole Joda mu duk ba auren muka yi
muka haife ku ba?" Yamutse fuska tayi daidai lokacin wayar hannunta ta fara ƙara,
sunan da tagani akan screen ɗin wayarta ya sanya ta miƙe tsaye da mamaki Immi ta
kalleta ta ce"lafiya dai?" girgiza kai Joda tayi bata samu damar bata amsa ba tayi
waje da sauri. A babban parlon ta tsaya tana sake kallon wayar kafin ta ɗaga kiran
ya katse.
"I'm outside"
Taga text message ɗin ya shigo wayarta, tamkar wacce aka cirewa laka haka taji, ta
kasa gaba ta kasa baya. Nan da nan hawaye ya kawo idanunta, ganin lokaci na shigewa
ya sanya tayi waje da sauri,
Duba gabaɗaya farfajiyar gidan tayi bata hangi kowa ba sai masu aiki da kowa ke
abin da ke gabansa, mayafin kanta ta saki ta yafa sannan ta fice daga gidan da
sauri, daga can tsallake ta hangeshi tsaye ya juya baya kwantaccen gashin kansa mai
kama da na mata ya zubo wajan kafaɗarsa, da gudu ta tsallaka ba tare da ta kalli
titin ba dukda motoci na shigewa tana zuwa ta ƙanƙameshi ta baya tana sakin wani
raunataccen kuka, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana ɗan jan numfashinsa,
hannunsa ya sanya ya jawota gabansa ta sake shigewa jikinta tana cigaba da kukan,
numfashinta har ɗaukewa yake hannunsa ya sanya ya rungumeta sosai ya shiga shafa
kanta ba tareda ya ce mata komai ba, sun ɗauki lokaci a haka kafin ta fara sauke
ajiyar zuciya tana jan numfashi, ɗago kanta tayi tana kallonsa ta shiga shafa
fuskarsa hannunta na rawa
"Ak...Akhi...Akhee!"
Hannunsa ya ɗora akan nata yana ɗan murmushi ya shafi kanta ya ce"kina lafiya?"
Kasa magana tayi ta sake fashewa da kuka tana rungumeshi ta shiga girgiza kanta,
ɗago fuskarta ya yi ya zuba mata idanu gaba ɗaya fuskarta tayi jajur da ita
idanunta sunyi jaa, ko ba'a faɗa maka ba daga ganinta kasan y'ar uwarsa ce dan har
kamar tasu ta ɓaci. Saida yaga ta sami nutsuwa sannan ya janye hannunsa cikin
sanyin murya ya ce
"Duk sanda na sake zuwa kikayi kuka bazan kuma dawowa ba!" Girgiza kanta ta shiga
yi tana rufe bakinta gudun kada kukan nata ya fito ta ce "to kayi haƙuri bazan ƙara
ba" yanda tayi maganar Cikin shagwaɓa ya sanya ya harareta ya ce"yaushe zaki girma
Joda?" Turo bakinta tayi gaba ya yi murmushi wanda ya fito da zallar kyansa ya ce
"shikenan ki koma ciki, duk sanda kike buƙatar wani abu just let me know kinji"
rau-rau tayi da idanunta kamar zata yi kuka ta ce "tafiya za kayi?" Gyaɗa mata kai
ya yi yana ɓame bakinsa kamar yaro ƙarami, wasu sabbin hawayen ne suka fara sintiri
kan fuskarta ya waro idanunsa yana murmushi ya ce"ɓaure sarkin kuka, zo nan"
ƙarasawa tayi ta shige jikinsa ya shafa kanta yana murmushi ya ce"ki fito da miji
nayi miki aure" fashewa tayi da kuka tana dukansa s ƙirji ta ce cikin wata
shagwaɓaɓɓiyar murya
"A'aaaa ni banaso!"
Dariya ya yi ya ce"ai ko dole kiyi aure yarinya" ɗago kanta tayi ta hararesa ta ce
"to kai ma kayi auran" murmushi ya yi ya ce"ai daman na kusa watarana zan nuna miki
matata" murmushi ta yi ta ce"tom Allah ya kaimu" janyeta ya yi a jikinsa ya ce"I'm
coming" jinjina masa kai tayi ya juya inda ya yi parking motarsa ya buɗe, wasu
ledoji ya ɗebo sannan ya dawo wajenta yana murmushi ya ce"guess what?" Lumshe
idanunta tayi ta bude ta ce"chocolate?" dungure mata kai ya yi ya ce"kwaɗayi" turo
baki tayi tana shafa goshinta ta ce"wollah da zafi yaya" "to bari na ƙara miki" ya
faɗa yana kawo hannunsa, saurin yin baya tayi tana tuntsirewa da dariya ta ce"ni
dai a'a" murmushi ya yi ya ce"nidai riƙe zan shige" shiru tayi tana kallonsa ta
karɓi ledojin kamar zatayi kuka ta ce
"Yayaaa!"
Kama hannunta ya yi yana murmushi ya ce"ƴar ƙaramar kanwata " rungumeshi tayi tana
fashewa da kuka ta ce"ni karka tafii, karka barni dan Allah" shafa kanta ya yi yana
sakin ajiyar zuciya ya ce cikin sigar rarrashi
"Kin fi so raina ya ɓaci Joda?" Girgiza masa kai ta yi ya ce"good, saboda haka ki
koma ciki nayi mikin alƙawarin zuwa na tafi dake kinji" sanin halinsa ya sanya ta
gyaɗa masa kai kawai tana sake tusa kanta cikin ƙirjinsa, ɗago fuskarta ya yi ya
shiga goge mata hawayen yana murmushi ya ce"ki daina rigima Joda" murmushi tayi
masa ta ce"to yaya" peck ya yi mata a goshi sannan ya saketa
"Tafi"
Ya faɗa yana kallonta, kallonsa tayi sai kuma ta juya tafara tafiya toward
direction ɗin gidan, tana zuwa ƙofar ta sake juyowa ta kalleshi taga ya ɗaga mata
hannu. Ɗaga masa itama tayi sannan ta shige cikin gidan, wani zazzafan numfashi ya
sauke sannan ya shige motarsa ya bar unguwar.
***Around 9pm ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa tayi idanunta ya
kumbura, da mamaki yake kallonta ya zauna gefenta sake goge idanunta ta yi tana
murmushi ta ce "sannu da zuwa"
Girgiza kai tayi tana goge idanunta ta ce "abu ne ya faɗa min idona" hannunsa ya
ɗora akanta ya ce" yanzu fa?" "Ya fita" ta faɗa da sauri, jinjina mata kai ya yi
sannan ya zaro wata box a bayansa yana murmushi ya ce "gashi nan" karɓa tayi ta
ce"mene ne?" Yunkurin buɗewa tayi ya yi saurin riƙe hannunta yana murmushi ya ce"no
ki bari ba yanzu ba" murmushi tayi ta ce "Nagode"
"Saida safe"
Jinjina masa kai tayi ya tashi ya fice daga ɗakin, a ƙofar ɗakin ya tsaya ya
jingina da bango ya yi shiru kamar wanda wani abu ke damunsa.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, zaune ta hangeshi gefen gado yana jan
cazbahar hannunsa, sallama ta yi ya amsa ba tareda ya kalleta ba, ƙarasawa tayi ta
tsuguna a gabansa cikeda ladabi ta ce "Barka da hutawa Ameer" kallonta ya yi
fuskarsa a sake ya ce"Maha" "na'am Abbiey" murmushi Ameer ya yi ya ce"Masha Allah"
shiru suka yi na wani lokaci, magana takeson tayi masa amma kuma nauyinsa da take
ji ya hanata, kwarjinin Ameer ya hanata amayar da abinda ta ƙunso, ganin bata ce
komai ba ya sanya ya yi gyaran murya. A ɗan firgice ta kalleshi sai kuma ta yi
murmushi ta ce"daman zuwa nayi zan faɗa maka wata magana" gyara zamansa ya yi yana
kallonta ya ce " Tom inaji" cikin sanyin murya ta fara magana a harshen larabci
"Ameer naga wani abu ne ko na ce naji wata magana ne wacce ta sanya naji tsoro,
naji babu daɗi, na shiga ruɗani, hankalina kuma ya tashi,koda wasa ban taɓa tunanin
hakan ba, meyasa Ameer?, meyasa?, why?, why??. Meyasa sai ita?, idan kace wata
kakeso wlh babu wanda zai hanaka aure, tunda ba haramun bane, amma wai IMARA!
IMARA!, IMARA matar Maheer, ita kakeso Ameer?, matar auren matar kuma ɗanka, why
Ameer?, why? Wlh zuciyata gab take da bugawa, naji kamar na gudu na bar gidan nan,
wane irin saɓon Allah ne Ameer?, da girmanka da mutuncinka, ka aikata irin wannan
abun, me Shamma da Immi suka rageka dashi?, dame TA FI SU?(Upcoming novel) Yarinyar
da ba kowan kowa ba, naji ba daɗi Ameer, kuma Wlh wannan abun ba daidai bane, na
zaɓi nayi maganar da kai ne saboda naji ta bakinka, idan har ya tabbata kuma hakane
wlh sai nafaɗa kowa yaji a fadar nan, gwara ayi duk abin da za'a yi da ku cigaba da
wannan rayuwar, bazan bar maganar ba!, wlh bazan bari ba! Ka bani kunya Ameer!, ka
ruguza soyayyar dake tsakanin mu, ka sanya shakku cikin zuciyata, wlh bana son
ganinka! Banason ganinka Ameer!, banaso...bana...b"
Maganar ta maƙale saboda kukan da yaci ƙarfinta, tunda ta fara magana Ameer ke
kallonta bazaka taɓa cewa dashi take ba yanayin nutsuwarsa bai sauya sai idanunsa
da suka kaɗa sukayi jajur, jijiyoyin kansa sun firfito, ganin tayi shiru ya sanya
ya kama hannunta jikinsa na rawa ya fara magana
"Karki yimin mummunar fahimta Maha, babu abin da ke tsakanina da IMARA, kawai dai
nasan ina sonta, son da bansan dalilinsa ba!, tabbas ina ƙaunarta, inajinta har
cikin raina, kuma wlh nafi Maheer sonta, nasan zaki fahimci Ameer ɗin ki, ina nan a
matsayina na masoyinku, bazan taɓa canzaku ba dan Allah kuma karku canzani"
"Dole mu sauyaka domin bazamu cigaba da rayuwa da mahaifi irinka ba!, ba kada imani
Ameer! Wlh bakada Imani!, bazan taɓa barin wannan cin amanar ba saboda haka zaka ga
abin da zan aikata!, zan yiwa tufkar hanci, zan tabbatar ban bar wata alama wacce
za'a gane ka ba, zan rufe maka sirrinka har abada" wata ajiyar zuciya ya sauke ta
samun sauƙi ya miƙe yana kallonta ya ce" daman nasani ba zaki juyamin baya ba Maha,
nasan kina tare da Ameer ɗinki" fashewa tayi da kuka ta shige cikinsa tana rawar
murya ta ce"kayi haƙuri Ameer, wlh bazan jure ba, bazan iya yafe cin amana ba, ka
yafeni Ameer, ka yafeni...wlh ina sonka..ina sonkaa..." Tayi baya tana cire jikinta
daga nasa. Kallonta Ameer ya yi sai kuma ya kalli cikinsa wanda ke zubar jini kamar
an buɗe famfo dafa cikin nasa ya yi ya ɗago yana ƙoƙarin yi mata magana daidai
lokacin Imara ta shigo ɗakin, sandarewa tayi ganin Ameer cikin jini ya durƙusa da
gudu ta tafi ta riƙe shi tana jijjigashi cikin tashin hankali take faɗin
"Ameer, Ameer!!!! Ameer!! Ka tashi kaji kada ka rufe idanunka, zan kira Maheer ya
kai ka asibiti, karka rufe idanun Ameer, karka rufe don Allah!!!!" Ɗago idanunta
tayi da niyyar yiwa Maha magana taga babu kowa a tsaye, a hankali kuma ta kalli
gefenta taga wuƙar da aka kashe shi da ita, an ajiye mata jikinta kuma duk jinin
Ameer ɗin, hannunta na rawa ta ɗauki wuƙar ta shiga juyata daidai nan kuma Shamma
ta bude ɗakin ta shigo. Sakin wuƙar tayi ta sake riƙe shi tana jijjigashi cikin
tsananin tashin hankali take faɗin
"Dan Allah Ameer karka tafi ka barni, ka tashi kaji, kasan me? Ina sonka wlh inama
ina sonka ka tashi kaji!, zan dinga dafa maka abinci mai daɗi ka tashi kajii" gaba
ɗaya ta fice a hayyacinta banda kiran sunansa babu abin da take, wani ihu Shamma ta
saki wanda ya yi sanadiyar shigowar mutane ɗakin da gudu suka ƙaraso wajensa suna
kallonsa
A razane Imara ta ɗago idanunta tana kallon Maha, kafin tayi magana Immi ta
ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, ta kashe shi, wlh ta kashe shi, shikenan
ta kashe Ameer" bin su kawai Imara ta shiga yi da kallo kafin ta miƙe tsaye daidai
nan Maheer ya shigo dakin, da gudu ya ƙarasa wajen Ameer ɗin ya rungumeshi yana
jijjigashi ya ce"Buddy, ka buɗe idanun, stay still, zan kai ka asibiti" hannun
Ameer na rawa ya ɗora kan fuskar Maheer yana ƙoƙarin goge masa hawayen fuskarsa.
Maha ce ta riƙe Imara cikin faɗa take faɗin"me mahaifin mu ya yi miki da zaki kashe
shi?, saboda kina gudun ya tona miki asiri?, ke wace irin mara imani ce?, me ya yi
miki IMARA! Me ya yi miki?" Girgiza kai Imara ta shiga yi tama kasa furta koda
kalma guda ɗaya, hannunta ta kalla taga duk jinin Ameer tamkar ita ce wacce tayi
kisan da gaske, wani irin sarawa kanta ya yi tayi saurin ɗora hannunta aka tana
sakin wani firgitaccen ihu kafin ta juya da gudu ta fice daga ɗakin.
Ɗakinta ta koma ta shiga tana dube-dube kamar mahaukaciya, wajen dressing mirror
taje ta barbazo da kayan dake wajen, juyawa tayi zata fita sai kuma ta dawo da
sauri ta buɗe wardrobe ɗin ta daidai nan Maheer ya shigo ɗakin. Akwatin daya bata
ta ɗauko da sauri ta fara ja da baya tana kallonsa cikin tashin hankali take cewa
"Wlh bani ba ce!, wlh bani ba ce!, ban kashe Ameer ba!, bani ba ce wlh!, tafiya ma
zanyi" kallonta kawai Maheer ya yi bai ce mata komai ba ya ɗauki car key ɗinsa ya
yi waje da sauri, da gudu ta tafi daga ɗakin ta sauka ƙasa bata ko ganin gabanta,
fita tayi daga fadar har sannan bata daina gudun ba, da mamaki Maids ɗin fadar ke
kallonta ganin kamar bata hayyacinta ta fice daga gidan gaba ɗaya.
***Tunda ya fito yake yawo ba tareda ya samu inda ake sayarda irin abincin ba, shi
kaɗai yake jan tsaki yana dukan sitiyarin motar, tun daga nesa ya hangota tana gudu
kamar wata mahaukaciya taɓe bakinsa ya yi a ransa ya furta
"Nonsense!"
Kamar wasa yaga tana ƙara yo inda yake duk ƙoƙarinsa na son ganin ya taka burki
kasawa ya yi bai yi aune ba sai gani ya yi ta faɗi ƙasa, sai a sannan yaja wani
dogon birki ya fito yana hargitsa sumar kansa wacce ta barbareje. Gabanta ya ƙaraso
ya tsaya ya riƙe ƙugunsa wanda ya zamar masa jiki, ɗan siririn tsaki yaja sannan ya
sunkuya dan ganin ko tana numfashi, da sauri ya kalleta ganin ta riƙe hannunsa
bakinta na rawa ta furta
"Papaa..."
Sake kallon fuskarta ya yi jin sunan data ambace shi dashi da kuma muryarta, a ɗan
razane ya durƙusa gabanta ya ɗago kanta waro idanunsa ya yi cikin wani irin yanayi
ya furta
"*IMARA*"
*Wacece IMARA?*
*Da gaske Maheer ya mutu?*
*Wace rayuwa Imara zata faɗa bayan faruwar wannan al'amari?*
*Akwatin me Maheer ya bata?*
*Wacece Jadda kuma mene alaƙarta da Qatar?*
*Wane ne Abaan?, mene alaƙarsa da Joda?*
*Mene ne alaƙar Abaan da IMARA da har ya furta sunanta?*
*Idan Dameer ba ɗan Ameer bane to ɗan wane!?*
*Wacece Katalina kuma mene alaƙarta da IMARA!?*
*Mene ne abin da ya raba Shamma da ƴaƴanta?*
*Shin za'a kama Maha ko kuwa ba za'a ganeta ba?*
*Me IMARA ta rasa a rayuwarta da har ta faɗa wannan ƙangin?*
*IMARA💋*
*Domin samun amshoshin waɗannan tambayoyin ki biya Naira ɗari biyar kacal ₦500 via
7041901078 Hauwa Adamu lawan opay sai a turo da shaida ta 08106608363 Nanameera,
masu Arewabooks kuyi following ɗina Nanameera08 zan dinga posting a can a matsayin
VIP*
*Note:*
*Littafin nan ₦500 ne idan zaki biya ki biya dan Allah 🙏 Ba zanyi ragi ba!, ki biya
ki karanta cikin salama da kwanciyar hankali.*
# *Bestnovel*
# *2025*
# *Ameenatou*
# *IMARA💋💋*
08106608363
Chat me to subscribe yours.
*IMARA 💋💋*
*Chapter 11*
*6:10pm*
A hankali ta turo ƙofar ɗakin tana kallonta, bacci take har sannan da batasan ma an
shigo ba, tsayawa tayi a kanta ta zuba mata idanu tana kallonta cikeda tausayawa.
Girgiza kai tayi sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin tana sauke ajiyar zuciya, a
hankali ta shiga buɗe idanunta tana jujjuyasu saida ta ƙarewa ɗakin kallo tsaf
sannan ta tashi zaune bakinta na rawa tsoro ya bayyana a kan fuskarta, wata iriyar
ƙara ta saki tana ƙoƙarin cire drip ɗin dake hannunta, cikin hanzari ta shigo ɗakin
ta ƙaraso gabanta tana kallonta hankali tashe ta ce
"Daughter wani abun ke miki ciwo?, mene ya baki tsoro?" Kallonta Imara tayi sai
kuma ta sake sakin wata ƙarar tana sauka daga kan gadon daidai lokacin ya buɗe
ɗakin ya shigo, tsayawa ya yi jikin ƙofa ya zuba mata idanu yana kallonta, ganin
tayo bakin ƙofar yasa ta furta
Tamkar da statue ake magana saboda yanda ya yi banza da lamarin sai ma ciro wayarsa
da ya yi daga aljihu ya shiga dannawa, ta gabansa tazo zata shige har sannan kuma
bata daina ƙarar da take ba. Ƙafarsa ya sanya ya taɗeta ta juyo tana neman faɗuwa
ya tallafeta, tsura masa idanu Imara tayi tana kallonsa har sannan jikinta rawa
yake sai ƙifta idanu take, ɗauke kansa ya yi daga kanta ya saketa ƙasa ba tare da
tayi tsammanin haka ba. Fashewa tayi da kuka saboda yanda kanta ya bugu da tiles
ɗin ɗakin ta riƙe kan tana shafawa.
"Mene haka Abaan?"
Kwaɓe fuska ya yi yana kallonta ya ce "Mom meya faru?" sanin halin rainin
hankalinsa ya sanya ta girgiza kai kawai ta ƙaraso ta kama hannunta ta miƙe tsaye
tana shafa mata kan ta ce"sorry muje na shafa miki man zafi" kallonta Imara ta yi
sai kuma ta gyaɗa mata kai tana goge hawayen kan fuskarta. Da idanu ya bisu har
suka fice sai kuma ya taɓe baki yana girgiza kansa ya juya ya fice daga ɗakin shi
ma. Ƙarar tafiyar da taji a stairs ya sanya ta daga idanunta tana kallonsa, ganin
yana shirin fita yasa ta ce"to sallamamme saboda zaman kafurci muke a gidan nan
shine ka shirya zaka fice ko sanar dani baka yi ba ko?" da wani irin expression ya
juyo yana kallonta tsabar takaici ma ya hanasa magana, ganin bai ce komai ba yasa
ta cigaba da cewa "to Uwarka Fatuu ita ka yiwa haka ba ni ba" idanunsa ne suka
sauya kala ya juyo yana kallonta cikin wata kakkausar murya ya fara magana
"Daman sharaɗi aka kafamin na cewa idan zan fita sai na sanar dake?, ko uwata ce
ke?, mene haɗin ki da fita ta?, ki daina yimin irin wannan to!, banason ana shiga
sabgata ki daina wlh!" Bai tsaya sauraren abin da zata ce ba ya juya ya fice daga
parlon yana banko ƙofa. Harara ta galla masa cikin takaici ta yi kwafa ta ce"zaka
san dani kake wlh!"
***A hankali ta fito daga cikin motar tana ɗan ya mutse fuska, gaba ɗaya a gajiye
take ko ta kan jakarta bata bi ba ballantana good flask ɗinta tayi cikin gidan tana
tafiya kamar zata faɗi, babu ko sallama ta shiga ciki ta hango Jadda zaune sai
surfa masifa take ita ɗaya, ƙarasawa tayi ta zauna ƙasanta ta ɗora kanta a cinyarta
kamar zata yi kuka ta ce
"Jaddaaa!"
A shagwabe tayi maganar tana jan ƙarshen sunan, shafa kanta Jadda tayi tana sakin
wata ajiyar zuciya ta musamman ta ce"Shalele kin dawo?" gyaɗa mata kai tayi ta ce
"dan Allah Jadda ki cewa yaya ya cireni a school ɗin nan wlh sun fiye tsanani ni
nafison waccen wlh" kama haɓa Jadda tayi ta ce "keee rufamin asiri wannan yayan
naku mai kamada samudawa sai baƙar zuciya ina zan iya masa, kin san kuwa yanda muka
ƙarke dashi a asibiti, ɗan nan so ya yi ya yi ajalina, ko kaɗan baya ƙaunar zaman
lafiya sai son tashin hankali da kayi magana ya fara ɗaɗɗaga maka ƙirji wai shi
namiji, dan ma dai ni ba tsoransa nake ji ba. Ki dai yi haƙuri kawai ki ƙarasa
makarantar ki huta" bubbuga ƙafa ta shiga yi daidai nan tayi sallama ta shigo,
ƙarasowa tayi ta tsuguna gaban Jadda cikin girmamawa ta ce"Barka da rana Jadda"
kallonta kawai Jadda ta yi sai kuma ta ce "ke wai yaushe zaki waye ne?, kullum
yarinyar kamar wacce ake yiwa baki, ke Ki sauya hali!" turo baki tayi ta ce"to kuma
me nayi miki?, kawai ki dinga yiwa mutane faɗa, ni wlh ki daina zagina kuma na
rantse sai na faɗawa yaya duk abin da kuke" harararta Nana tayi kafin tayi magana
Jadda ta amshe;
"Kee fita a idona na rufe, wato ni kike faɗawa magana ko?, to bari shi uban naku ya
dawo duk zakuyi bayani wlh" tashi Umaima tayi ta ɗauki jakarta tayi sama ba tareda
ta sake cewa komai ba.
"Na rantse Jadda Umaima munafuka ce, ki faɗawa Abbiey ya yi maganinsu wlh kuma ki
ce har zaginki sun yi" rufe mata baki Jadda tayi ta ce"har sai kin faɗa min ai
yanda suka ɓata miki rai yau suma duk sai nasu ran ya ɓaci.
Ɗago idanu suka yi a tare, tsaye yake a kansu yana sanye cikin wata dakkakiyar
shadda ash colour ya ɗora hula zanna akai, farar fatarsa sai sheƙi take, zama ya yi
kusada ita yana kallonta cikin zolaya ya ce"kullum aka shigo gidan nan kina magana,
ki dinga yin shiru Jadda" karkace baki tayi tana harararsa tace "to ɗan nema uban
kwainane kamarya na dinga shiru?, Allah ya tsagamim bakin magana sannan ace nayi
shiru ai uban kuturu ma ya yi kaɗan" tuntsirewa ya yi da dariya yana miƙewa tsaye
ya ce"ai sai ki bada himma" harararsa tayi ta ce "kaji dashi nidai a daina shiga
sabgata sai na kula mutum yawwa!" Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce "Allah ya
huci zuciyarki Hajiya Jadda" washe baki tayi tana murmushi ta ce"ko kai fa, yanzu
daga ina kake kaci wannan kwalliyar?" Waro idanunsa ya yi yana shafa gemunsa ya ce
"zance naje" wani kallon up and down tayi masa wanda ya sanya ya tuntsire da dariya
ya ce"irin wannan kallo haka Jaddarmu?" Kallon Nanah ta yi ta ce"ke tashi muje ciki
mu bar wannan" murmushi kawai ya yi ya haye sama dan ɗauro alwala.
***Kallonta Tayi tana murmushi ta ce"yawwa daughter Kinga yanda kikayi kyau kuwa?"
Kallonta IMARA tayi sai kuma ta kalli kanta a mudubi, wata farar atampa mai adon
baƙi Mamah ta bata, ta ɗaura mata ɗankwali ya zauna kamar ba ita ba, sosai farinta
da kuma zallar kyanta ya sake fitowa, hannunta Mamah ta kama tana murmushi ta ce
"muje kici abinci" bin bayanta Imara tayi ba tareda ta ce mata komai ba. Babu kowa
a parlon sai sautin karatun Alkur'ani dake tashi, lumshe idanunta tayi saboda wani
sanyi da taji yana ratsa duk gaɓɓan jikinta. Zaunar da ita Mamah tayi a parlon ta
shiga jera mata abinci kala-kala, tea tafara zuba mata tana murmushi ta ce "ki fara
gasa cikinki sai kici abincin, zanje nadawo" gyaɗa mata kai kawai Imara tayi dan
batada bakin magana har sannan, tana ganin Mamah ta hau sama ta ɗora kanta akan
dinning table ɗin wasu hawaye suka shiga sakko mata kan kuncinta. Inuwar mutum data
gani ya sanya ta ɗago idanunta tana kallonta, kallo ɗaya Nanah tayi mata ta bar
wajen tana taɓe baki, batasan wace ba dan bata taɓa ganinta ba amma haka kawai taji
ko kaɗan bata kwanta mata ba!. Fasa zama cin abincin tayi ta juya ta bar wajen tana
danna laptop ɗinta hankali kwance, horn ɗin da taji ya sanya ta ajiye laptop ɗin
hannunta tayi waje da gudu, tana ƙarasawa compound ɗin yana fitowa daga motar da
gudu ta rungumeshi tana dariya ta ce
Shafa kanta ya yi yana murmushi ya ce cikin wata murya mai daɗi "ƴar Auta ta dawo
daga school?" Jakar hannunsa ta karɓa tana gyaɗa masa kai ta ce" wlh Abbiey bana
son school ɗin ka cewa yaya a cireni please" kallonta ya yi yana tafiya cikeda
nutsuwa ya ce"menene baki so a school ɗin?, karatun?" Girgiza masa kai tayi ya ce
"then what?" turo baki tayi sanin halinsa ta ce "kawai nafison waccen" "to kiyi
magana dashi sai ya cire ki" shiru tayi bata sake cewa komai ba har suka shiga
gidan. Zaune suka tarar dasu Jadda na ganinsa ta shiga share hawaye da tissue tana
kallon Mamah ta ce "ina faɗa miki yaron nan kamar zai kai mini duka saboda fusata
ko yarsa ba zai yiwa abun da ya yi mini ba" numfasawa Mamah tayi jiki a sanyaye ta
ce "dan Allah Jadda kiyi haƙuri kinsan halin Abaan daman"
"What happened?"
Abbiey ya tambaya daga tsaye, kafin Mamah tayi magana Jadda ta fara bashi labarin
abin da ya faru da ma wanda bai faru ba tana yi tana sharce majina da tissue kaman
gaske, sosai ran Abbiey ya ɓaci yana kallon Mamah ya ce"ina Muhammad?" cikin sanyin
murya ta ce"ya fita bai dawo ba yallaɓai" ƙarasawa wajen Jadda ya yi ya ce"I'm
sorry Jadda, idan ya dawo zan masa magana in sha Allahu" goge hawayen ta shiga yi
tace "tom sai kuma yarinyar nan Umaima itama bakaga abin da tayi mini ba" jinjina
mata kai ya yi ya ce" a gabanki zan hukunta su Jadda, let me take shower first"
gyaɗa masa kai Jadda tayi cikin shassheƙar kuka ta ce "Allah ya yi maka albarka"
murmushi ya yi ya ce"Ameen Jadda".
***A hankali take driven ɗin idanunsa a lumshe gabaɗaya a gajiye yake, kallonsa
tayi ta jikin mudubin ta ce"wai Adeel meke damunka ne?" ɗan buɗe idanunsa ya yi ya
ce" wlh Mom nagaji ne, wai meyasa baku tawo da driver ba?" Harararsa tayi ta
ce"saboda haka mukayi niyya kai zaka kaimu" ta glass ɗin ya kalleta ganin yanda ta
haɗe rai ya saka yayi murmushi ya ce"Allah ya huci zuciyarki Mom" banza ta yi masa
tana kallon gefenta. Girgiza kai tayi ganin yanda ta kwanto akan kafaɗarta tana
baccinta hankali kwance.
*8:30pm*
Zaune suke gaba dayansu sakamakon kiran da Abbiey ya yi musu, shiru kowannensu ya
yi ganin yanda Abbieyn ke musu faɗa abin da ya daɗe bai yi ba Jadda kuma sai hura
hanci take yi. Can ciki ya yi sallama ya shigo parlon yana kallon mahaifin nasa ya
ce "Abbiey gani" da hannu ya yi masa nuni daya zauna, zama Abaan ya yi yana
kallonsa da mamaki
"Muhammad daman Jadda abokiyar wasanka ce ban sani ba?, ko kuma Sa'ar ka ce bamu
sani ba?" cikin sanyin murya ya ce "Abba akwai matsala ne?, wani abun ta ce maka
nayi mata?, me nayi miki Jadda!" Ya ƙarashe maganar yana kallonta, harararsa tayi
ta ɗauke idanunta ba tace komai ba. Abbiey ne ya cigaba da faɗin
"Da ina kake magana ko dani?, na tambayeka kana mayar min da tambaya. Koda wasa
idan na sake jin haka ya faru sai ranka ya ɓaci Muhammad kuma ba kai kaɗai ba da
gaba ɗayanku nake" ya ƙarashe maganar yana kallonsu duka, sunkuyar da kai suka yi
ya ce"ku bata hakuri" ya faɗa yana kallon Abaan
"Kiyi haƙuri Jadda" Abaan ɗin ya faɗa yana tashi daga wajen ya haye sama a fusace,
da harara Jadda ta bishi tana taɓe baki, kallon Umaima ya yi ya daka mata tsawa ya
ce"duk ranar dana sake jin makamancin haka ya faru idan ranki ya yi dubu sai ya
ɓaci, ɓacemin daga gani!" Da gudu ta tashi ta bar parlon tana kuka. Tsaki Abbiey ya
yi yana kallon Ammar ya ce"ina Ibrahim ne?"
***Tunda ta ɗauko box ɗin take jujjuyata tana tuna incident daya faru na ƙarshe,
gaba ɗaya batada nutsuwa, gaba ɗaya ta rasa kuzari tunaninta ɗaya halin da Ameer
yake ciki, ko ya mutu ko kuma yana raye bata sani ba. A hankali ta buɗe box, waro
idanunta tayi ganin wani haɗaɗɗen ring ko ba'a faɗa ba kasan da kuɗi aka siye shi.
Ɗago zoben tayi ta juya shi sai kuma ta saki murmushi mai sauti ta zura a hannunta
tamkar saboda hannun nata aka yi zoben haka ya yi mata. Tana ƙoƙarin rufe box ɗin
idanunta ya sauka kan wata farar welfolded paper ciro papern ta yi ta warwareta ta
shiga karanta rubutun jiki kamar haka
_Nasan zakiyi mamakin wannan takardar dana rubuta miki, amma kuma zaki ji dadin ta
ta wani ɓangaren, na aureki IMARA da niyyar zan kula dake kuma zan so ki, saidai na
yaudareki na kai ki ƙasarmu domin cika wani muradi nawa, a yanzu kuma nagane illar
aikata haka. Kullum kina burin komawa ƙasar ku domin ki cigaba da rayuwarki kamar
yanda kika fara, saboda haka na yanke shawarar rabuwa dake domin na samar miki da
farin ciki. Ni Maheer bin Fahad al-kuwari na sake ki matata IMARA saki uku, Kinga
daman babu idda akan ki, zan tabbatar da na mayar dake ƙasar ku domin ki cigaba da
rayuwarki, ki yafeni na abin da na aikata miki, a sanda zaki iske wannan takardar
nayi miki nisan da ba zaki iya magana dani ba a saboda haka nake neman gafarar ki,
ki yafemin duk abubuwan da nayi miki. Maheer_
*#Bestnovel*
# *IMARA 💋 💋*
# *2025*
# *Nanameera*.
08106608363.
*IMARA 💋 💋*
Chapter 12
Wani irin abu ne ya tokarewa Imara a ƙirjinta, batasan sanda ta saki takardar
hannunta ba, gaba-daya jikinta rawa yake, runtse idanu tayi wasu zafafan hawaye
suka fara sintiri kan fuskarta. Batasan sanda ta silalo daga kan gadon ba ta yi
zaman dirshan a ƙasa, wani zazzaɓi ne ya rufeta wanda yakeda nasaba da abinda
idanunta ya gani, dafe ƙirjinta tayi jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu daya
zarce misali, ƙoƙarin take tayi kuka amma bakinta ya gagara, hawayen ma ya ƙafe
daga idanunta, sai bin ɗakin take da kallo tamkar wata zararriya.
"Mamah wai..."
Turus ya yi ganin wata kyakkyawar budurwa zaune ta zubawa kofar idanu, bai san da
zuwan Imara gidan ba hakan yasa shi yayi mamakin ganin fuskar da bai sani ba a
ɗakin Mamah. Ƙarasawa ya yi yana kallonta ya ce"Hyy, where is Mamah?" jin tayi
shiru yasa ya ɗan haɗe rai yana zare idanu ya ce"kee..baki jina ne?" Shirin da yaji
ta sake yi masa ya sanya ya ƙarasa dab da ita ya taɓa ta, ga mamakinsa sai yaga ta
tafi luu ta faɗi ƙasa sumammiya. Saurin ja da baya Khalil ya yi ya shiga girgiza
kansa daidai nan Mamah ta buɗe kofar ɗakin ta shigo da mamaki take kallonsa sai
kuma ta kalli Imara wacce ke kwance ƙasa tamkar tana bacci, cikin hanzari ta ƙarasa
gabanta ta shiga jijjigata amma shiru babu alamar tana jin abin da take cewa. Tashi
Mamah tayi ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake bi ta kan Khalil ba, tana fita ya
koma inda Imara ke kwance ya tsugana ya zuba mata idanu
"Woww Beautiful"
Khalil ya samu kansa da furta hakan yana sakin wani yalwataccen murmushi, ya saba
ganin kyawawan ƴan mata amma bai taɓa ganin mai kyau irin Imara ba. Yana cikin
wannan tunanin ta buɗe kofar ta shigo ta dawo inda take, not too long shima ya
shigo ɗakin yana sanye da wata jallabiya ash colour, gaba-daya gashin kansa ya rufe
fuskarsa da alama daga wanka ya fito dan babu alamar gyara a kan nasa. Tafiya yake
a hankali kamar ba wanda aka yiwa reporting ciwo ba
Bai ce komai ba sai hannunsa daya sanya ya ɗan hargitsa gashin kansa kafin ya
tsugana daidai inda take, hannunsa ya kai ya taɓa wuyanta, ya yi kamar zai mike
tsaye sai kuma ya sunkuya ya ɗauketa tamkar Baby ya yi waje da ita.
***Zaune take gefen gadon ta zubawa kanta idanu, wayarta ce ta shiga ringing ta
kalli wayar ta taɓe baki ta cigaba da kallon fuskanta, saida akayi 4missed calls
kafin ta ɗauki wayar ta sanyata a flymode ta yi cilli da ita kan gadon. Turo kofar
ɗakin akayi wanda ya sanya ta juya dan ganin wanda ya shigo mata ɗaki, murmushi ta
sakar mata tana ƙarasowa ta ce"har yanzu shirin ne baki gama ba?, Kin fison sai
babanki yazo yana jiranki ko?" mikewa tsaye tayi tana gyara zaman veil din jikinta
ta ce"nafa gama Mom" numfasawa tayi ta ce"yanzu sai yaushe?" langwaɓar da kanta
tayi ta ce"ke da kika koreni, wlh saina daɗe ban zo Kd ba" murmushi Mom tayi ta
ce"Allah ya huci zuciyar Mamana, ba korarki nake ba, halin mahaifinki nasani
banason ya yi miki faɗa ko ya yiwa mahaifiyarki shiyasa amma ke kinsan I'm gonna to
miss you alot" rungume small Mom ɗin tata ta yi tana turo baki ta ce"me too Mom"
shafa bayanta tayi ta ce"muje kar kuyi missing flight.
Tsaye suke a farfajiyar gidan, "A'isha! A'isha" juyowa tayi ta kalleta ta ce"
lafiya dai?" Murmushi tayi tana kallon yar uwar tata ta ce"yau Aunty Jidda zata
koma Kano fa" wani tsalle A'isha tayi ta rungumeta tana dariya ta ce"kai amma naji
daɗi, alhamdulillah, mun rabu da jaraba in Sha Allah ba zata sake dawowa gidan nan
ba" buɗe baki tayi zata yi magana taga ta fito tana jan troley dinta, sanye take da
wata doguwar rigar Egyft Abaya coffee colour ta sanya wani sun glasses a idanunta
hannunta ɗaya riƙe da hand bag ɗinta sai taunar cew gum take. Ta gabansu ta zo zata
shige suka kalleta ba tare da sun ce mata ko a dawo lafiya ba suka shige cikin
gidan, yanda basu nuna sun ganta ba haka itama bata nuna ta gansu ba kanta tsaye ta
shige bayan mota driver ya jata zuwa Airport.
*Kano state*
Murmushi Mamah tana kallon Jadda bata ce komai ba. Riƙe haɓa Jadda tayi tana
ƙanƙance idanu ta ce"au sallamammiya kika mayar dani ko me?, Ina faɗa miki abin da
matar nan tayi min amma kina min dariya? Eh lallai! bari shi wanda na isa dashi ɗin
ya dawo, wlh sai na saka ya saketa idan batayi wasa ba". Girgiza kai Mamah tayi
cikin cool voice ɗin ta kamar koda yaushe ta ce"ki dai yi hakuri Jadda, maybe
gajiyar tafiya yasa bata zo ta gaisheki ba"
"Babu wani gajiya rashin arziki ne irin nata, kuma zata san dani take zancen ba dai
ɗana take aure ba!" Jadda ta faɗa cikin faɗa, Ita dai Mamah bata sake cewa komai ba
gudun kada itama tayi wani laifin.
A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi, ɗakin da take ta ƙarewa
kallo kafin ta fara yunƙurin tashi zaune, kallon hannunta tayi taga an saka mata
drip a hankali memeries ɗin abin da ya faru ya fara dawo mata, wani irin
raunataccen kukane ya kwace mata ta shiga rareshi kamar ƙaramar yarinya, saida tayi
mai isarta sannan ta tashi da niyyar fita daga ɗakin daidai nan ya buɗe wata ƙofa
ya shigo, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai ya nufi gaban gadon, drip din hannunta
ya cire sannan ya ɗago yana kallonta, saurin ɗauke kanta tayi wasu hawayen na biyo
fuskarta. Taɓe baki Abaan ya yi bai sake bi ta kanta ba ya juya ya fice daga ɗakin
gabaɗaya. Da idanu Imara ta bishi sai Kuma ta sake fashewa da wani sabon kukan tana
bubbuga ƙafa.
***Da gudu ta tawo ta rungume mahaifiyar tata tana murmushi ta ce"Mom nayi missing
naki" murmushi itama tayi ta ce"nima haka Jidda, ya hanya?" Bata ba ta amsa ba sai
kallon ƙofar ɗaya apartment ɗin da take, ganin abun take kamar a mafarki hakan yasa
ta kasa ƙarasawa gurinsa ta juyo ta kalli Mom tata bakinta na rawa ta ce"Momm...Mom
ya Abaan ya dawo?" wani kallo Mom ta watsa mata kafin ta ce"yadawo mana, mene
haɗinki da dawowarsa?, ko har yanzu akwai wani abu a zuciyarki ne?, karki fara cewa
zaki yi abin da zai sakani a bakin duniya Jidda, ki fita harkarsa a daina yi mana
kallon waɗanda basu kai ba idan kuma ba haka ba..." Sakar baki Mom tayi ganin Jidda
tayi hanyar Apartment din Babu ma alamar tana sauraren abin da take faɗa.
"Jidda! Jidda!"
Tamkar ba ita da ita take magana ba dan ko juyowa bata yi ba ta shige apartment
ɗin, tsabar takaici kasa motsi Mom tayi ta dinga kallon ƙofar ko zata ga Jidda ta
fito amma shiru babu labarinta
Kallonta tayi bata ce komai ba, ta juya ta bar wajen, da idanu Suhaila ta bita sai
kuma ta ɗaga kafaɗarta irin bai dameta ɗin nan ba tayi waje tana riƙe da car key
ɗinta. Kai tsaye Jidda sama ta haye dan babu kowa a parlon kasancewar lokacin duk
suna gurin aiki, ƙofar dakinsa ta buɗe ta shiga bakinta ɗauke da sallama, shiru
taji da alama ma baya ciki, dan haɗe fuska tayi s shagwaɓe ta ce"ina kuma yaje to?"
Juyawa tayi zata fita taji an buɗe ƙofar bedroom ɗin an fito, da sauri ta juyo
bakinta ɗauke da murmushi saidai abinda ta gani yasa ta yi saurin haɗe fuska kamar
ba ita ba, kallonta Imara tayi da idanunta wanda suka kumbura saboda kukan data sha
bata ce mata komai ba ta zo zata shige ta gefenta. Kasa jurewa Jiddah tayi ta jawo
rigarta tana watsa mata wani banzan kallo ta ce
"Hyy, what brought you here?, Ina mai ɗakin yake?" Kallonta kawai Imara ta yi badan
batasan abin da ta ce ba, yin shirun nata ya sake ɓatawa Jiddah rai cikin masifa ta
ce"keeee! Wane ubanki a garin nan da har ina yi miki magana kina jina?, me kike
taƙama dashi?" Numfasawa Imara ta yi ta sake yunƙurin fita a karo na biyu, a fusace
Jidda ta jawota kafin tayi aune ta sauke mata wani lafiyayyen mari daidai nan Abaan
ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, da idanu ya shiga bin su Jidda tayi saurin ƙarasawa
inda yake tana murmushi ta ce"Yaya daman ka dawo?" kallonta ya yi bai ce mata komai
ba, tasan me yake nufi hakan yasa ta haɗe ranta tana kallon Imara wacce ke tsaye
hannunta ɗaya bisa kuncinta ta ce"wai ina yi mata magana tanaji tayi min banza,
kasan ni kuma bana ɗaukan raini" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta a ƙirji.
Kallon Imara kawai ya yi sannan ya kalli Jiddah cikin cool voice ya ce"get out"
kallonsa Jidda ta yi nan da nan hawaye ya kawo idanunta ba ta ce komai ba ta juya
ta fice daga ɗakin tana banko ƙofar, girgiza kansa ya yi kawai sannan ya ƙaraso
gabanta, wuyanta ya taɓa yaji sanyi klao da alamar zazzaɓin ya sauka,
Abin da kawai ya faɗa kenan ya shige bedroom ɗinsa, da idanu Imara ta bishi kafin
ta juya ta fice daga ɗakin har sannan hawaye bai bar zuba daga idanunta ba.
Mamah na zaune kan kujera idanunta maƙale cikin glasses tana kallon show ɗin da ake
haskawa a TV Jiddah ta sakko daga saman, da idanu ta bita har ta ƙaraso gabanta ta
tsuguna
Ɗan murmushi Jiddah ta yi ta ce"zuwana kenan, shine naga motar Ya Abaan na biyo
shi" jinjina kai Mamah ta yi ta ce"toh sannu da hanya yasu Jamilan?" "Suna nan klao
Alhamdulillah, Ina Jadda?" Murmushi Mamah ta yi ta ce"tana ciki, tunda ta dawo taki
komawa apartment ɗinta" dariya Jidda ta yi ta ce" Jadda rigima, let me take shower
sai nazo na gaisheta" okay Mamah ta ce Jidda ta tashi ta fita. Abbiey ne ya sakko
daga cikin shigarsa ta manyan kaya kamar koda yaushe, kallonsa Mamah ta yi ta
ce"yau ka makara yallaɓai" rollex ɗin hannunsa ya kalla ya ɗan yi tsaki ya ce" ban
san time ya tafi haka ba, ina Abaan yake?" tashi Mamah ta yi ta ce"yana ciki, kasan
halinsa dai, maybe jira yake hutun daya ɗauka ya ƙare ya koma bakin aiki" girgiza
kai Abbiey ya yi ya ce"no munyi magana dashi ai, ya ce yanason a gama komai na
asibitin ne kafin ya koma Abuja so kinga dole a sake bashi lokaci" numfasawa Mamah
ta yi ta ce"Jadda na nemanka tun ɗazu" dafe kansa ya yi ya ce "ya rabb, har zan
manta na fita" "ai kuwa da ka dawo yanzu" ta faɗa tana murmushi, girgiza kansa ya
yi shima yana murmushin ya yi hanyar part ɗin da take.
Yana barin wajen Imara ta sakko tana tafe a hankali, kallonta Mamah ta yi ta ce
"daughter kin tashi?" jinjina mata kai tayi dan bakinta yayi nauyi, kama hannunta
tayi tana kallon fuskarta ta ce"lafiya?, me ya sami fuskarki?, who slapped you?"
girgiza kai Imara tayi tana aro dauriya gudun kada tayi kuka ta ce "babu kowa,
bigewa nayi" shiru Mamah ta yi ba dan ta yarda da abin da ta ce ba, sai dan batasan
ƙureta,
Girgiza kai tayi ta ce"na ƙoshi yanzu" haɗe rai Mamah ta yi ta ce" da kika ci me?"
sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasada fingers ɗinta, tallafo habarta Mamah ta yi
ta ce"ki daina ɓoyemin komai, muje ciki Inason magana dake" kallonta Imara tayi
hawaye na taruwa a cikin idanunta ta ce"Tom Mamah".
***Zaune ya sameta tana jan cazbaha saida ya bari ta idar sannan ya gaisheta,
"Jadda lafiya kike nemana?" Girgiza kai Jadda ta shiga yi tana kallonsa ta ce"wai
kamarni! Kamarni za'a yiwa irin haka ko?, kana sane da matarka bata zo ta gaisheni
ba tunda na dawo daga asibiti?, yau ko zaman kafurci muke da ita ai ya ci tazo ta
dubani ko?, amma wlh matar nan shiru bata zo ba, ina jin sanda suka dawo daga bikin
amma ta kasa shigowa ta cemin sannu ya jiki, haka ake rayuwa Fadeel?, an kyauta min
kenan?, haka taga Fatima nayi?, kullum cikin ɗawainiya take dani yarinyar nan bata
taɓa gazawa ba, shine ita zata dinga wulaƙantani?, me nayi mata?, me na mata
Eh?!..." Ta ƙarashe maganar tana goge hawaye da hijab ɗin jikinta. Shiru Abbiey ya
yi na wasu sakkani, gabaɗaya ransa ya gama ɓaci koda wasa bai yi tunani bata zo ta
duba mahaifiyarsa ba, duk da tasan abin da ya sameta, a hankali ya kamo hannunta
cikin son kwantar mata da hankali ya ce "dan Allah Jadda kiyi haƙuri, zan yi mata
magana, kuma in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, zan sanda yanda zanyi da
wannan matsalar, amma kar ki damu kanki wani ciwon ya sake kamaki kamar da, kiyi
mani wannan alfarmar" jinjina masa kai tayi ta ce "babu komai, ni kawai faɗa maka
nayi, amma ban riƙe kowa a zuciyata ba" ajiyar zuciya ya sauke ya ce"Nagode Jadda,
bari naje" "Allah ya tsare ka, ya yi maka albarka, ya kula dakai da yaranka"
murmushin jin daɗi ya yi ya ce"Ameen ya rabbi Jadda".
***A fusace ta buɗe ƙofar parlon tana zuwa ta faɗa kan mahaifiyar tata tana fashewa
da kuka, girgiza kai Mom tayi cikin ɓacin rai ta ce"dana gargaɗeki ai baki ji ba
Jiddah, kinyi tunanin ko ya sauya ne?, da dai Abaan ya so ki amma tuni aka shiga
tsakaninku, saboda haka tun wuri na faɗa miki ki fita hanyarsa!, ki daina zuwa in
da ma yake kada ke ma ayi miki wani mugun abun" cikin shassheƙar kuka ta ce"wlh
Mommy ina son Abaan kuma ni shi xan aura, wlh shi nakeso, shine wanda zuciyata ta
zaɓa mini kuma zaɓinta zan bi, ki taimakeni Mommy, ki taimaka!" Ta ƙarashe maganar
tana sake rushewa da wani sabon kukan, shiru Mommy tayi dan abun nema yake yafi
ƙarfinta, tsayin lokaci tana neman yanda zata raba wannan al'amari amma abu yaƙi
yiwuwa, tana cikin wannan tunanin ya buɗe ƙofar ya shigo, da sauri Jiddah ta tashi
ta shiga goge hawayen fuskarta ta tsuguna kanta a ƙasa ta ce "ina yini Abbiey"
saida ya ƙare mata kallo sannan ya ce"lafiya klao" daga haka ta tashi ta shige
ciki.
"Yanzu abinda kika aikata daidai kenan?, mahaifiyata ita ce abar rainawarki?, daga
ke har yayanki babu wanda ya iya zuwa ya gaisheta?, kunsan kuma batada lafiya daga
jin ya ta dawo, to bari kiji idan har kina son zama cikin gidan nan ƙarƙashina to
dole sai kin girmama mahaifiyata, idan kuma ba haka ba wlh zan ɗauki mummunan
mataki akan ki, zaki san dani kike!" Yana gama faɗar haka ya juya ya fice daga
ɗakin kamar zai tashi sama, da idanu Mommy ta bishi sai kuma ta taɓe baki
"Allah na tuba matar da ba son ganina take ba me zan je yi mata?" Ta faɗa a fili
tana danna wayarta.
***Kallonta Mamah tayi ganin yanda jikinta ke rawa ta ce"nutsu Imara, faɗamin me
yake faruwa, me kika yi masa ya sake ki?" Batasan sanda ta faɗa jikin Mamah ta
fashe da wani raunataccen kuka mai taɓa zuciya ba, kuka take irin mai fitowa tun
daga ƙasan zuciya, kukane wanda ke nuna zallar damuwar da take ciki, kuka ne irin
wannan ke nuna komai ya ƙare min a rayuwa, yanda take jan numfashinta yasa Mamah
tayi saurin rungumeta tana shafa kanta
# *Bestnovel*
# *Heart touching 💔*
# *IMARA 💋*
# *Nanameera*
# *2025*.
08106608363.
*IMARA 💋💋*
Drivern yake hankalinsa kwance, gefensa wata kyakkyawar balarabiya ce hannunta riƙe
da yar ƙaramar yarinya mai kama da ita sak, murmushi ya yi yana kallonsu ya ce"da
alama kin fi son yarinyar nan dani ko?" girgiza masa kai tayi tana kwaɓe fuska ta
ce"kaiii! Janaan, wlh ba haka bane kai ma kasan ina sonka ai" yanayin maganarta zai
tabbatar maka da ba asalin bahaushiya ba ce, murmushi ya yi ya ce"ni na isa na ce
baki sona?, cewa nayi kin fi son yarki yanzu akaina" rau-rau tayi da idanu kamar
zata yi kuka ta ce"to tunda hakane ka karɓeta ai kai ma naga yarka ce" ta faɗa tana
turo masa baki, tuntsirewa ya yi da dariya yana kallonta ya ce"au hakama zaki ce?,
bari mu ƙarasa sai na karɓeta." Har suka ƙarasa ƙauyen hira suke basu yi shiru ba,
bayan ya yi parking ya karɓi yarinyar ya ɗagata sama yana kallonta ya ce"kinsan
me?, diz girl dake kawai take kama wlh, ni bata yo ni ba" dariya tayi ta ce"na fika
ƙarfin jini shiyasa" harararta ya yi bai sake magana ba su kayi sallama cikin ɗan
ƙaramin gidan, tarba sosai tsohuwar matar tayi masu, bayan sun ci abinci ya kalleta
fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Granny kin fara tsufa fa" daƙuwa tayi masa da
hannu ta ce"ka ji min ɗa, to bazan tsufa ba kake nufi ko me, dan ma inada tsawon
rai ne, kalli fa mahaifiyarka ta rasu ta barni, Allah dai ya jiƙanta da Rahama"
jikinsa a sanyaye ya ce"Ameen ya rabbi" kallon matar tasa tayi ta ce"banda ikon
Allah kaje ka auro balarabiyar mata, kai Ahmad kanada ɗaukowa kai, ita kuma ta bar
iyayenta ta biyo ka!" Haɗe ransa ya yi sanin halinta ya ce"wai granny mene haka?"
Hannunta ta ɗora a bakinta ta ce"tuf! tuf, babu ruwana" murmushi Madiha tayi tana
kallon granny, yarinyar hannunta Granny ta kalla ta washe baki tana dariya ta ce
"a'a kaga ƴar Baba, yama sunanta?" "IMARA" Madiha ta faɗa tana murmushi, karbar ta
Granny tayi tana yi mata wasa ta ce "yo ai sunan ne irin naku, ni ina zan wani
riƙe" girgiza kai Kawai ya yi bai sake cewa komai ba. Sai bayan magrib sannan suka
ɗauki hanyar dutse, kafin suke gida har anyi sallar isha.
***Shigowa ɗakin tayi bakinta ɗauke da sallama, amsawa ya yi yana cigaba da abin da
yake, ƙarasawa gabansa tayi ta haɗe rai, ɗagowa ya yi ya kalleta sai kuma ya yi
murmushi cikin sakin fuska ya ce"wai me aka yiwa matar ne?" kamar zatayi kuka ta
ce"ni wlh sai na bika" riƙe ƙugunsa ya yi kamar mace ya ce"dan Allah ki bar maganar
nan, Granny fa kawai zan mayar gida, beside kuma dare ya yi fa, sannan kinsan Imara
batajin daɗi ai bai kamata ki fita ba, ki bar maganar please!" Tsura masa idanu
tayi ba ta ce komai ba sai hawaye da ya kwanta a kurmin idanun, tausayi ta bashi
sanin cewa ta bar nata dangin saboda kawai tayi rayuwa tare dashi, numfasawa ya yi
ya ce"shikenan ɗauko veil ɗin ki" sai a sannan hawayen ya samu damar sauka a kan
fuskarta, kamo hannunta ya yi cikin sanyin murya ya ce" to kuma ba nace ki zo muje
ba, mene na kukan?" Ya goge mata hawayen ya ce"shirya ki fito maza" ya fice daga
ɗakin, da kallo ta bisa sai kuma ta shiga shiryawa, saida tagama tsaf sannan ta
gyara Imara. Tashi tayi ta buɗe wardrobe ta ɗauko wani ɗan box a can ƙasan kayanta,
buɗewa tayi ta zaro wata sarƙa ta diamond sai sheƙi take, wasu zafafan hawayene
suka shiga sintiri kan fuskarta haka kawai taji tana missing rayuwarta ta da, above
5mins kafin ta goge hawayen ta dawo inda Imara ke zaune tana wasada fingers ɗinta
lokacin tana wata na sha biyar, da haihuwa, kallonta tayi sai kuma ta yi murmushi
ta saka mata sarkar a wuya. Sosai sakar tayi mata kyau duk da cewa tayi mata yawa,
ɗaukanta tayi ta mata kiss sannan ta ajiyeta tana dariya ta ce" yar kyakkyawar
ƴata".
**Fitowa tayi hannunta ɗauke da Imara, ta shirya cikin wata Abaya black colour,
kallonta ya yi yana murmushi ya ce"enyeee kinyi kyau" dariyar ta mai kyau tayi ta
ce"kaima haka" Granny ce ta fito tana kallon su bata ce komai ba, kallonta ya yi
ganin bata shirya ba ya ce "Granny wai na ganki haka dare fa ya yi, gobe fa da safe
zamu tafi Abuja Kinga babu tym ɗin da zan kai ki gida" harararsa tayi ta ce"to ni
bansan hanya bane?, nafasa tafiya yau ɗin sai gobe wlh" sakar baki ya yi yana
kallonta Madiha tayi murmushi ta ce"yawwa Granny daman wlh banason ki tafi, ki
zauna ki cigaba da bani labarin" washe baki tayi ta ce"kaji ƴar gari, shine zai
kaɗani ya ce na tafi gida to bazan tafi ba" girgiza kansa ya yi ya ce "nifa Granny
ban koreki ba, cewa kikayi yau zaki tafi, shine nikuma zan kai ki amma Allah ya
baki haƙuri ya kaimu goben da rai da lafiya" Ameen " tayi saurin faɗa. Tashi ya yi
ya ce"bari naje zanyi magana da guards ɗin nan" "Tom yallaɓai sai ka dawo" jinjina
mata kai ya yi sannan ya yi waje, karɓar Imara tayi tana murmushi ta ce "ke ƴar
gidan soja, gaki kyakkyawa dake tubarkallah Masha Allah shiyasa babanki ya maƙalewa
babarki sai ya aureta dan ya haifi irin kyau, duk da dai shima da kyansa"
tuntsirewa da dariya Madiha tayi ta ce"hajya Granny tamu, bari naje ciki ina zuwa"
toh ta ce mata sannan ta shige apartment ɗin da aka bata.
*Around 3am*
A hankali ta shiga buɗe idanunta, duhu sosai ɗakin hakan yasa ta kunna bedside lamp
ta shiga kallonsa, baccinsa yake hankali kwance tashi tayi ta shige banɗaki ta
ɗauro alwala ta dawo ta fara gabatar da sallolinta na dare, kamar wacce aka tsikara
haka ta tashi ta buɗe wata ƙofa, ta shiga wajen tana hango ƙasan gidan, sosai tayi
mamaki ganin duk tarin securities ɗin gidan babu kowa, sake matsawa tayi without
making any sound, saurin toshe bakinta tayi ganin wasu mutane sun rufe fuskokinsu
da baƙin kyalle sai janye ragowar securities ɗin dake bacci suke, buɗe ƙofar tayi a
hankali ta koma ɗakin da gudu ta ɗauki wayarta da niyya kiran jami'ai, text message
ne ya fado tasa wayar da wata unknown number
_Major Ahmad how far?, na turo maka saƙo gidanka fatan zaka karbesu hannu bibbiyu._
Sakin wayar ta yi ta shiga kiran sunansa tana kuka, cikin tashin hankali ya farka
yana kallonta ya ce"Madiha lafiya?" Wayar data faɗi ƙasa ta shiga nuna masa
hannunta na rawa, ɗaukan wayar ya yi ya karanta sakon ya yi saurin miƙewa tsaye,
hanyar fita ya yi tayi saurin riƙe shi tana kuka kasa ƙasa ta ce"ba wannan ne abun
ji ba, yarmu Janaan, kar wani abun ya samu IMARA, dan Allah kayi wani abun" riƙe
hannunta ya yi yana jinjina mata kai ya ce"in sha Allah babu abin da zai sameku
duka" waje ya yi tana biye dashi, ƙofar parlon farko suka ji ana ƙoƙarin buɗewa ta
sake fashewa da kuka ta ce" ka zo muje wajen Granny, kar wani abun ya same su, ta
tafi da Imara Major!" girgiza mata kai ya yi ya ce"dare ne fa Madiha, kikasan abun
da zai same su idan suka fita?, karki manta ni jami'i ne dole na kare iyalina"
girgiza kanta tayi tana kuka ta ce"duk da haka nidai bari naje" jin sun buɗe ƙofar
farko yasa tayi apartment ɗin granny da gudu, bashida wani zaɓi wanda ya shige ya
bita. Tashin Granny sukayi cikin tashin hankali miƙewa tayi tana salati, goya mata
Imara tayi tana kuka ta ce"dan Allah Granny ki kula min da ita, karki bari tayi
kuka a rayuwa, ku bar garin nan, indai suka san da ita zasu kasheta, ku tafi dan
Allah" kuɗi ya miƙa mata a jaka cikin rauni ya ce"Granny ku tafi, akwai ƙofa ta
baya ku bi ta can, ki kula da *IMARA* ki kula da ita, idan Allah ya yi zamu sake
haɗuwa a rayuwa, idan kuma bai yi ba ki sanar da ita iyayenta na ƙaunarta" kuka ta
saka tana kallonsu ta ce " me yake faruwa ya'yan nan?, ku ina zaku je?" "Babu
lokacin wannan maganar Granny muje na raka ku" Madiha ta faɗa tana riƙe hannun
Granny. Fitowa suka yi daga ɗakin suka shiga wani lokacin har sun buɗe ɗaya ƙofar
sun baza suna nemansu, buɗe musu ƙofar tayi ta can bayan gidan tana kuka kamar
ranta zai fita ta ce"dan Allah Granny ki kula da ita, ki sanyata farin ciki dan
Allah, batada koda sai ke a halin yanzu, nan gaba akwai wanda zai dinga Zuwa yana
dubata ki yarda dashi, shi ɗin jinina ne!, bazai cutar da ita ba, karki bar IMARA
haka ki sakata makaranta! Kuɗin zai isheku ko ba mai tsada ba, ki kula Granny, ki
kula, ku tafi..Idan ta girma ki faɗa mata iyayenta suna sonta sosai... Ki ce mata
mahaifiyarta na sonta! Tana ƙaunarta..." Ta yi saurin sakin hannunta saboda har
bin da ta jiyo, da gudu Granny ta fice daga gidan duk da shekarunta. Komawa gidan
tayi da gudu tana ta tarar sai harbinsu yake duk da shima sun harbeshi a ƙafa,
daskarewa tayi a wajen tana bin su da kallo dan tama gagara ko yin kuka, harbi wani
ya yo inda take da gudu ya ƙarasa ya rungumeta harbin ya sauka a gadon bayansa,
ƙara ta saki tana kuka ta ce"dan Allah Major! Mene haka meyasa kayi haka?" Shafa
fuskarta ya yi kawai yana murmushi dan gaba ɗaya lokacin ƙarfinsa ya fara ƙarewa,
batasan sanda ta karɓi bindigar hannun nasa ba ta cigaba da kai harbin itama, wani
harbin aka sake yo wa daidai saitin zuciyarsa ƙarasawa wajensa tayi ta kare shi
harbin ya sauka akan zuciyarta, wani tari tayi mai haɗe da gudan jini ta fadi a
wajen, wata irin kururuwa ya yi ya ƙarasa wajenta ya rungumeta yana sakin wani irin
kuka mai tsuma zuciya, har bin sa shima akayi ya faɗi ƙasa nan kusada ita. Ɗaya
daga cikinsu ne ya zaro wayarsa ya ɗaukesu hoto, ya tura masa
"Kallon hotunan ya yi, sai kuma ya ce"ina ƴar tasu?" "Bamu sami kowa ba bayan
waɗandan yallaɓai" girgiza kansa ya yi yana kallonsa ta cikin video call ɗin ya
ce"akwai yarinya, duk yanda za'a yi ku samota, a kasheta!" Jinjina masa kai ya yi
sannan ya kashe wayar, ya yi musu alama da su biyo shi suka fita daga cikin gidan,
sai a sannan mutane suka fara shigowa dan suna jin ƙarar harbe-harben da akayi
tsoro ya hana kowa fitowa daga gidansa, sai lokacin aka kira hukuma aka sanar musu.
***Tun da Granny ta baro gidan take kuka, bayan ta samu waje ta zauna, har sannan
Imara bacci take, gaba ɗaya ta fice hayyacinta sai kallon jakar hannunta take, har
akayi sallar asuba tana wajen a zaune, saida taga gari ya fara haske sannan ta
tashi ta cigaba da tafiya, madadin ta nemi motar barin garin kamar yanda suka ce
mata sai ta nemi motar komawa Daƙayyawa ta hau, tana tafe tana kuka har ta sauka
daga motar, bata shiga gidanta ba sai ta shiga gidan ƙawarta aminiya wacce ke baya
kaɗan da gidanta. Zaune ta sameta tana cin abinci tana zuwa ta zauna ta fashe da
kuka
"Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, Maryama lafiya kike kuka?, me ya sameki na
ganki haka?" Kasa magana Granny ta yi ta cigaba da kukanta, saida tayi mai isarta
sannan ta bata labarin duk abin da ya faru, fashewa da kuka Asiya tayi ta ce"an
shiga uku, meyasa mutane basa tuna lahirarsu idan zasu aikata abu?, me Ahamdu da
Matarsa suka yi musu?, yaro mai biyayya marayan Allah, Allah ka yafe mana?" Cigaba
suka yi da kukansu saida aka ɗauki lokaci sannan suka haƙurƙurtar da ransu, kallon
Imara ta yi da ke bacci har sannan ta ce"Allah sarki, Allah ya kula da rayuwarki,
ya sadaki da iyayenki, ya kare shi daga sharrin zamani" Ameen Granny ta ce jikinta
duk a sanyaye, miƙewa tayi ta ce"bari na barta a nan Asiya, zan je gida yanzu,
wannan kuɗin iyayenta ne suka bani na kula da ita zanje na ajiye su" cikin damuwa
ta ce "Tom sai kin dawo Maryama" fita Granny tayi tana tafiya kamar zata faɗi.
Turo ƙofar gidan nata tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama, turus Granny tayi
jikinta na rawa ganin wasu irin mutane tsaye a cikin gidanta, ɗaya daga cikinsu ne
ya ƙaraso inda take yana kallonta ya ce"sai gashi har mun rigaki zuwa gidan" ja da
baya Granny ta fara tana karanto addu'a a zuciyarta, taku ɗaya ya yi ya ƙarasa
gabanta ya shaƙe mata wuya yana kallonta ya ce"ina yarinyar take?, tana ina?"
Girgiza masa kai Granny ta shiga yi idanunta na fitowa waje, watsar da ita gefe ya
yi ya ce"ba zaki faɗa mana inda take ba kenan?" Hawayene kawai ke zuba daga
idanunta ta riƙe wuyanta wanda har yanzu take jin kamar hannunsa na kai, gyaɗa
kansa ya yi yana kallon yaran nasa ya ce"ku a cikin ku wane ya keson ya more ta?"
"Ai wannan ta zama guzuma boss" ɗaya daga cikinsu ya faɗa, tuntsirewa suka yi da
dariya wani narkeke ya ce"A'a nifa inaso dan babu ruwana da tsufanta" jinjina kai
ya yi ya ce " ga tanan, muna jiranka!" Girgiza kai Granny ta shiga yi cikin sanyin
murya take faɗin "kai yaro ka duba tsufana da shekaruna karka yimin irin wannan
tozarcin, Gara ka kasheni kawai" ko ta kanta basu sake bi ba ya shiga lalata da
ita. Fita ɗaya daga cikinsu ya yi ya koma bakin ƙofar gidan ya yi shiru, hangota ya
yi yana tawowa hannunta riƙe da Imara wacce take kuka da sauri ya girgiza mata kai
yana yi mata alama da ta koma, kallonsa ta shiga yi tana kuma kallon gidan
Ya faɗa a tsawace, da gudu ta koma gidan nata ta saka sakata a ƙofar fuskanta ɗauke
da tashin hankali.
"Kai da wa kake magana ne?"
Boss ya faɗa da ƙarfi, dawowa ya yi ya ce"wasu yara nagani shine na korasu" jinjina
kai ya yi, kallon granny ya yi wacce ke kwance jikin jini idanunta a rufe hawaye
sai zuba yake, gaba yayi yana kallon na gefensa ya ce"kill her" harbinta ya yi a
ciki sannan suka fice daga cikin gidan, motarsu suka shiga suka bar unguwar. Asiya
na gidanta ta jiyo bindiga ta zauna ta rushe da kuka kamar ƙaramar Yarinya, tasowa
tayi ta fito daga cikin gidanta dukda yanda take jin tsoro ta shiga gidan Granny,
ƙarasawa gaban Granny tayi bakinta na rawa ta ce"mar...Marya...Maryama!" a hankali
Granny ta buɗe idanunta wanda ke gab da rufe wa ta ce cikin rawar murya
"Da...Dan.. Allah Asiya ki kula da Imara, idan ta girma ki faɗa mata Iyayenta suna
ƙaunarta, wataƙila ta sake ganinsu a rayuwarta, wataƙila kuma saidai a lahira,
akwai sarƙa a wuyanta mahaifiyarta ta ce duk sanda danginta yaga wannan sarƙa zai
ganeta karki bari ta bar wuyanta, ki ɗauki kuɗin nan ki sakata a makaranta dan
Allah Asiya..kimin alƙawari" Jinjina kai tayi tana kuka tama kasa magana.
Cak maganar ta tsaya sai wani numfashi da ta ja, hannunta dake jikin Asiya ya saki,
kallonta ta shiga yi sai kuma ta kalli cikinta kafin ta rusa wani raunataccen ihu.
# *Bestnovel*
# *Heart touching 💔*
# *IMARA 💋*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋 💋*
*Chapter 14*
*4:30pm*
*Daƙayyawa*
Zaune take kan kujerar katako tana tuƙin tuwo, gabaɗaya hankalinta baya wajen aikin
da take, har yanzu mutuwar Granny bata saketa ba, wani yaro ne ya yi sallama ya
shigo yana gara taya, amsa sallamar tayi ya ce"wai ana sallama da matar gidan nan"
"sallama kuma?" Tafada tana kallon yaron, "Eh haka ya ce" tashi tayi ta rufe
tukunyar tana kallonsa ta ce"je ka ce ina zuwa" da gudu ya fita daga gidan, hijab
ta ɗauko a ɗakin, ta tsaya tana kallon Imara wacce ke zaune tana wasa ɗaukanta tayi
ta ce"sarkin haƙuri muje ki rakani" kallonta kawai Imara ta yi ta shiga taɓa mata
fuska, murmushi goggo Asiya tayi sannan tayi waje. Tsaye ta sameshi jikin bishiyar
ƙofar gidan ya juya mata baya, sallama tayi ya amsa yana juyowa, zabura goggo Asiya
tayi ta koma cikin gidan da gudu tana rufe bakinta da hannunta kukan na neman cin
ƙarfinta, shigowa gidan ya yi tayi saurin shigewa ɗaki ta saka sakata cikin kuka ta
ke faɗin
"Dan Allah kayi haƙuri, ka barmu da ran mu, wannan yarinyar bata san komai ba, kada
ka cutar da rayuwarta, kun kashe kowa nata ku barta ta rayu da wannan baƙin cikin
kawai, dan Allah kayi mata wannan alfarmar... Ka taimaka yaro... Dan...Allah!..."
Ta ƙarashe maganar tana rushewa da wani sabon kukan, tsaye yake har sannan a tsakar
gidan hannayensa zube cikin aljihu sai kallon gidan yake ta cikin glasses ɗin dake
maƙale a fuskarsa. Shirun da Goggo Asiya taji yasa ta tsagaita da kukan har sannan
tana rungume da Imara wacce tafara kuka, a hankali ta buɗe ƙofar ta fito, turus
tayi ganinsa zaune kan tabarmar dake shinfiɗe a ɗan tsakar gidan, jikinta ne ya
fara rawa tana ƙoƙarin komawa ya ce"da kin tsaya kin ji abin da ya kawo ni baba"
cak ta tsaya jin sunan daya anbaceta dashi da kuma sanyin murya irin nasa, cikin
rawar murya ta ce
"Me zaka cemin yaro?, dan Allah kar kace zaka kasheta" ɗan murmushin gefen baki ya
yi idanunsa na kallon gabansa ya ce
"Idan da naso kashe yarinyar nan da tun ranar na kasheta, idan da banso cetar
rayuwarta ba da bazan ce miki ki gudu ba, ban zo nan da niyyar cutar da ita ba,
saboda haka ki zauna ki saurareni dan Allah!"
Shiru Goggo Asiya tayi dan gabaɗaya jikinta ya yi sanyi, tabbas ta yarda ta
maganganunsa da yaso cutar da Imara shine zai nuna inda take, zama tayi a hankali
har sannan Imara na jikinta, hannunsa ya miƙo ya ɗauki yarinyar kasancewar ta saba
da ɗaukar babanta ta wangale masa baki tana dariya, murmushin shima ya yi yana
kallonta ya ja mata kumatu. Zaunar da ita ya yi kan cinyarsa ya ɗauko mata
chocolate a aljihu ya miƙe mata, karɓa tayi tana wasada ita, sai a sannan ya mayar
da hankali wajen Goggo Asiya wacce ke kallonsu tun ɗazu.
"Banida kalaman da zanyi magana dasu wajen baki haƙuri, ita rayuwa ba kai kake da
ikon zaɓawa kanka yanda zaka yita ba, nasan abin da aka yi ba'a kyauta ba kuma ba
daidai bane, amma haka Allah ya ƙadarta, wannan yarinyar Allah ne kaɗai yasan abin
da ya ɓoye a cikin rayuwarta, naji sanda mahaifiyarta ke yiwa kakarta wasiyyar ta
kula da ita, na barsu sun tafi dukda na hangesu kuma inada ikon na kashe su a
wannan lokacin, wannan sana'ar tawa ba abun arziki ba ce, ban taɓa nadama ba sai a
lokacin da naga yanda mahaifiyar yarinyar nan ke kukan rabuwa da yarta, an kashe su
ba tareda sun aikata wani laifi ba, tun daga sannan nayi alƙawarin barin wannan
harkar ta kashe-kashen rayukan al'umma, na biyo su ƙauye ne dan ganin inda yarinyar
take kuma na taimaketa idan nasamu dama, sai gashi cikin ikon Allah nasamu damar
tseratar da rayuwarta" numfasawa ya yi sannan ya cigaba da faɗin
"Inason na nemi alfarma a wajenki, dan girman Allah ki bani yarinyar nan na riƙeta
koda hakan zai sanyayamin zuciya, munyi aure da matata shekaru biyar baya amma ko
ɓatan wata bata taɓa yi ba, ki taimaka ki bani yarinyar nan na kula da ita, zan
sakata a makaranta kamar yanda mahaifiyarta ta bada wasiyya, nayi miki alƙawarin
babu abinda zai samu rayuwarta muddun ina raye, sannan lokaci zuwa lokaci zan dinga
kawo miki ita ki ganta"
Tunda ya fara magana Goggo Asiya ke kuka, kallonsa tayi taga shima kukan yake
idanunsa zube akan Imara da keta wasa da ledar chocolate, cikin shassheƙar kuka ta
ce"wlh tsoro nakeji, wannan yarinyar amana ce a wajena, amanarta aka bar min, idan
har nayi abin da zai cutar da rayuwarta Allah bazai barni ba, kuma nima bazan
yafewa kaina ba, bazan iya kare kaina ba a ranar lahira, duk da zan zo tayi ilimi
kodan ta ɗauki fansar abun da aka yiwa iyayenta amma wlh ina tsoron baka ita,
bansan wace rayuwa zata je tayi ba, yarinya ce ƙarama wacce ta gamu da ƙaddarar
rayuwa tun tana yar ƙaramarta, wa yasan me gobe zata haifar?, bansan wace rayuwa
zata faɗa ba idan ta bar hannuna ne, wane wanda zai zame mata bangon da zata
jingina?, dan Allah kayi haƙuri!..." Ta ƙarashe maganar tana fashewa da wani irin
kuka mai tsuma zuciya.
Tashi ya yi ya tsuguna akan gwuiwarsa ya haɗe hannayensa biyu waje guda alamar roƙo
yana kuka ya ce
"Ki taimaka ki yimin wannan alfarmar, ki bani yarinyar nan na raineta, ki taimakeni
na aikata wannan koda shine kaɗai abin Alkhairin da zanyi a rayuwa, ki rufamin
asiri kamar yanda Allah ya rufa miki, nayi miki alƙawarin ni zan zame mata bango
wanda zata jingina, zan bata kariya da rayuwata, zan bata farin ciki iyakar iya
wata, dan Allah ki taimakeni na fito daga cikin wannan ƙangin, ki taimakeni na
aikata aikin Alkhairi "
Ya ƙarashe maganar yana kuka, above 5mins kafin Goggo Asiya ta kalleshi cikin
sanyin murya ta ce"shikenan zan baka ita, amma dan Allah karka barta tayi kuka a
rayuwa, kuma a duk sanda kaga ka gaza da rainonta ka dawo min da ita, zan cigaba da
kulawa da ita, ita ɗin*AMANATA* (upcoming novel) ce, kaji yaro" . Gyara zamansa ya
yi yana kallonta ya ce"Nagode sosai Baba, in sha Allah zan kula da rayuwarta kuma
zan kawo miki ita a duk sanda kika buƙata, ni a cikin garin Dutse nake zaune kinga
bamuda nisa Kenan, zan baki lambata da address ɗin gidana ko dan halin rayuwa"
jinjina kai tayi ta ce" tom shikenan, Allah ya baka ikon sauke nauyin da ka ɗauka"
murmushi ya yi ya ce"Ameen ya rabbi" tashi tayi ta shiga ɗaki ta ɗauko jakar kuɗin
da granny ta bata ta fito, ajiye masa tayi a gabansa ta ce" wannan iyayenta ne suka
bayar saboda a kula da rayuwarta, ka tafi dashi duk abin da take buƙata ka siya
mata" murmushi ya yi ya tura mata jakar gabanta ya ce" cewa nayi zan ɗauki nauyin
ta, idan har na karɓi kuɗinta kenan ba ɗaukan nauyin nata zanyi ba, ki ajiye mata
wannan kuɗin watarana idan ta girma zai mata amfani, amma yanzu dai babu buƙatar
su" girgiza kanta tayi ta ce"to, Allah ya yi maka albarka yaro, amma ya sunanka?"
Murmushi ya yi ya ce"sunana Mubarak" "to, Allah ya rayaka kaima" "Amen ya rabbi"
kuɗi ya zaro a aljihunsa ya ajiye mata yana tashi ya ce"Baba gashi ba yawa" girgiza
kanta tayi kafin tayi magana ya ce"karki damu wannan ba kuɗin da ake bani bane,
wannan da gumina nake nemosu, dan Allah kiyi amfani da su " murmushi kawai tayi dan
daman abin da take tunani kenan, ɗaukan kuɗin tayi ta ce"To Allah ya biyaka" "Ameen
" ya faɗa yana murmushi. Ɗaukan Imara ya yi a hannunsa ta rako shi har ƙofar gidan
sannan suka yi sallama ya tafi bayan ya bata lambar wayarsa. Ajiyar zuciya ta sauke
sanda ya shige motarsa ya bar ƙofar gidan, girgiza kanta tayi ta ce a fili
"Dan Allah Maryama ki gafarceni, ina nema mata kyakkyawar rayuwa ne".
Zaune yake a ƙasa yayinda shi kuma yake zaune kan kujera yana kaɗa ƙafa
"Sir duk abin da ka umarce mu muyi mun aikata shi, yanzu babu wani abu wanda ya
danganci Major Ahmad wanda bai zama tahiri ba" murmushi ya yi yana kallonsa ya
ce"good job, yarinyar da aka gudu da ita akan kamota?" Shiru ya yi sai kuma ya
jinjina masa kai ya ce"yes sir, mun kasheta harma da wacce ta tafi da itan" wani
killer smile ya yi ya ce "haka nakeson ji" wata jaka ya ɗauko ya ajiye masa a
gefensa ya ce" ga shi nan kowannensu ya ɗauki 5millions, kai kuma ka ɗauka 7m"
durƙusawa ya yi yana murmushi ya ce"godiya muke mai gida, Allah ya ja zamaninka,
duk wanda zai shigo hanyarka sai mun tabbatar da cewa mun kawar dashi, mu naka ne
har abada oga" jinjina masa kai ya yi ya ɗauki wani glass cup dake gefensa ya
ce"you can leave" tashi ya yi ya ɗauki jakar ya sake masa godiya sannan ya yi waje.
Tun da ya fara magana take kallonsa har ya gama, tashi tsaye tayi hawaye fal
idanunta ta ce"yanzu me kake nufi Mubarak?" cikin sanyin murya ya ce"ina nufin mu
raineta har ta girma tunda mu Allah bai bamu haihuwar ba!" Girgiza kanta ta shiga
yi tana kuka ta ce"wato abin har ya kai haka?, saboda ban haihu ba!?, dan har yanzu
ban haihu ba shine kaje ka ɗauko tsintacciyar yarinya kace na raina?" With so much
surprised Mubarak ke kallonta zai yi magana ta cigaba da faɗin " bafa zaka rainamin
hankali ba Mubarak!, kai kayi kaɗan, ni bari kaji ma wlh ban yarda iyayenta ne suka
mutu ba saidai idan can kaje ka yi cikinta wata ta haifeta yanzu ta baka yarka, ni
kuma na zauna haka har ƙarshen rayuwata saboda kawai ina sonka to wlh bazai yiwu
ba!, baka isa ba!, na rantse bazan riƙe ta ba!"
Ta katse shi kafin ya ƙarasa faɗar abin da ya yi niyya. Rasa me zai ce mata ya yi
kawai ya tsaya yana kallonta, harararsa ta yi cikeda tsiwa take faɗin
"Bari kaji, idan kanason zaman lafiya dani to ka fita da wannan yarinyar daka cikin
gidan nan, idan ko ba haka ba zakaga abin da zan yi yanzun nan" tashi tsaye ya yi
yana kallonta ya ce"me zaki yi?" Kallonsa ta yi ta ce"babu abin da ya dameka da
abin da zan yi, kuma ba sanar dakai zanyi ba, abin da nakeson ji shine zaka fita da
ita ko bazaka fita ba?"
Ya faɗa yana kallonta, waro manyan idanunta tayi tana kallonsa, tunda suke bai taɓa
yi mata irin haka ba, baya taɓa zallake maganarta saboda irin yanda suke son
junansu, sai gashi yau suna faɗa akan IMARA. Kuka Imara ta saka ya juya yana
kallonta, zaune take kan kujera tana sanye da wasu sabbin kaya daya siya mata,
ɗaukanta ya yi yana jijjigata, ƙarar da cikinta ya yi ya tabbatar masa da yunwa
take ji ya dafa cikinta cikin sanyin murya ya ce
"Sorry marh gurl, muje na siya maki madara" daga haka ya fita daga cikin parlon ba
tareda ya sake kallon Suhaila ba, da gudu ta shige ɗaki tana kuka kamar ranta zai
fita.
***Around 8am ya shigo gidan hannunsa riƙe da Imara sai wasa take da doll ɗin daya
siya mata, siyayya sosai ya yo mata ta kayan sakawa da mayuka sannan ya siyo mata
madarar dan baiga alamar tana cin wani abu ba, a parlon ya ajiyeta ya shiga kitchen
ya haɗo mata madarar ya dawo ya zauna yana bata, tunda ta kafa kanta jikin feedar
bata cire ba sai da ta shanye tass, cirewa tayi ya kalleta yana murmushi ya ce" a
ƙaro?" Kamar taji me yace ta gyaɗa masa kai tana ƙura masa idanu, wata ya sake haɗa
mata ya bata tasha. Tana gama sha kamar wacce ke jira tafara bacci hankalinta
kwance, tashi ya yi ya kai ta ɗaki sannan ya shiga ɗakin Suhaila amma ga mamakinsa
sai ya samu bata ciki, fita ya yi ya dawo dan duk zatonsa tana banɗaki saidai har
yayi wanka ya shirya ya dawo Suhaila bata fito ba, sunanta ya kira yaji shiru hakan
yasa ya tura ƙofar banɗakin amma sai yaga wayam babu ita babu dalilinta, duk inda
ya kamata ya duba a gidan saida ya duba amma bai ga Suhaila ba, har maƙota ya shiga
bai ganta ba hakan yasa ya dawo gida ya ɗauki waya ya shiga kiranta, ringing ɗin
duniya bata ɗauka ba daga ƙarshe ma sai ta kashe wayar tata. Zaunawa ya yi a parlon
ya dafe kansa ko ba'a faɗa ba yasan Suhaila gidansu ta tafi, dan damar gwanar
ƙorafi ce. Daren ranar haka ya kwana a parlon ba tareda ya yi bacci ba, da yaga
lokaci na tafiya a banza ya tashi ya ɗauro alwala ya fara salloli yana roƙon Allah
ya gafarta masa zunubansa, har akayi sallar asuba yana zaune sai a sannan ya tashi
ya leƙa ɗakin da Imara ke kwance, bacci ya tarar tana yi har sannan sai kawai ya
rufe mata ƙofar ya fito harabar gidan wacce batada girma ya shimfida sallaya ya bi
jam'in anan.
***Around 9am ya yi parking a ƙofar gidan, a hankali ya fito daga motar ya shiga
gidan yana tunanin abin da zai je ya tarar, a babban compound ɗin gidan ya tsaya ya
aika mai gadin domin ya yi masa iso,saida aka ce ya shigo sannan ya shiga. A parlon
Daddy aka kaishi bayan sun gaisa ya kalleshi ya ce"Mubarak me ya haɗaka da
Suhaila?" Cikin ladabi ya bashi labarin duk abin da ya faru, Daddy bai ce masa
komai ba yasa akayi kiranta suka shigo ita da Mommy idanunta ya kumbura da alama
taci kuka, bayan sun zauna Daddy ya kalleta ya ce"yanzu Mamana mene a ciki dan kin
riƙe marainiya?, kinsan ladan riƙon maraya kuwa?" fashewa tayi da kuka ta ce "ni
wlh Daddy bata yimin ba, kuma kawai ya mayar da ita wlh indai ni ce bazan riƙeta
ba!" Kallonta Mubarak ya yi bai ce komai ba, Daddy ya ce"ya maidata ina?, ki ma bar
wannan maganar, kawai magana ɗaya ce yanzu kai Mubarak tunda kanason ka riƙe
yarinya to ka samo mata mai aiki wacce zata dinga rainonta har zuwa sanda zatayi
hankali ke kuma ki koma gidan mijinki"
"Ta koma ina?, wlh babu inda zata je!, indai har bazai mayar da wannan shegiyar
yarinyar da ba'a san asalinta ba saidai ya saketa!".
# *Bestnovel*
# *IMARA 💋*
# *Lolo*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
*Chapter 15*
Da sauri Mubarak ya ɗago idanunsa yana kallon Mommy, harararsa tayi ta ce"Eh ka
kalleni da kyau!, wlh saidai ka zaɓa ko Suhaila ko kuma yarinyar kaji na faɗa
maka!" Ta ƙarashe maganar tana haki, girgiza kai Daddy ya yi yana kallon Suhaila ya
ce"ke tashi ki bi mijinki, kai kuma Mubarak ka nemawa yarinyar mai raino kamar
yanda nafaɗa maka" har ƙasa ya sunkuya cikeda ladabi ya ce"Nagode sosai Daddy,
Allah ya ƙara girma" "Ameen" cewar Daddy yana cigaba da kallon labaransa, tashi ya
yi yana kallonta ganin yanda take tura baki gaba kallon iyayen nata tayi sannan ta
yi waje fuu kamar zata tashi sama. "Gaskiya yallaɓai wannan ba shawara ba ce ya
yarinya zata kawo kuka miji ya yi mata abin da bai dace ba sannan ka ce mata ta
koma without taking any action, nan gaba idan ya sake mata abu ai ba zata ji kwarin
gwiwar dawowa gida ba"
"Kwarin gwiwar!?, au daman akwai wata kwarin gwiwa a yin yaji?, mene ne abun tashin
hankali anan?, dan ya ce zai riƙe yarinya shine ya yi laifi?, tunda su Allah bai
basu haihuwar ba, ba zasu ɗauki na wasu su raina ba kenan?, saboda ku mata
ƙwaƙwalwarku ƙarama ce!"
"Amma yallaɓai..."
"Kar na sake jin bakinki akan wannan maganar, na rufe babinta" shiru Mommy ta yi ba
tareda ta so hakan ba.
***Yana gama parking ɗin motar tayi waje kamar zata tashi sama da, da idanu Mubarak
ya bita har ta shige gidan, ya girgiza kansa kawai sannan ya gyara parking ɗin
motar ya fito. A parlon ya sameta tana zaune ta haɗe kai da gwiwa tana kuka, zama
ya yi gefenta yana kallonta ya ce "Suhaila nayi tunanin komai ya wuce ai?" Tashi
tsaye tayi tana watsa masa wani kallo ta ce"ya wuce yaje ina?, to bari kaji babu
abinda ya wuce wlh, muddin wannan yarinyar na cikin gidan nan to ka dinga gamuwa da
ɓacin rai kala-kala kenan, idan kai baka fasa ba nima bazan fasa ba!" ta juya ta
bar parlon, dafe kansa ya yi na rashin sanin abin yi, tunawa ya yi da Imara hakan
yasa ya tashi ya ɗauki car key ɗinsa ya yi waje. Gidan maƙotansa ya yi sallama
bayan an yi masa iso ya shiga, zaune ya samesu suna hira Imara kuma na gefenta sai
wasa take abin ta, zama ya yi suka sake gaisawa sannan yayi musu godiya, murmushi
Sulaiman ya yi ya ce "haba ai babu komai Mubarak, duk abinda Suhaila zata iya maka
ai Fatima ma zata yi maka shi" jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce"ai ko Nagode
sosai, yanzu daman wata alfarma nake nema a wajenki Fatima"
"Alfarma kuma?"
Jinjina kansa ya yi ya ce, "Eh, dan Allah idan babu damuwa inason ki samo min wacce
zata dinga rainon Imara, amma irin babba mai hankali nakeso wacce zata riƙeta da
amana" murmushi Fatima tayi ta ce"indai wannan ne babu damuwa bari yanzu na kira
wacce take kawo min yan aiki naji", ajiyar zuciya ya sauke ta samun sauƙi, ko babu
komai zai bawa Imara irin kulawar da yake son bata, duk da zuciyarsa cike take da
tunanin yanda rayuwarsa zata kasance muddin oga ya gane baya tare da su, har aka
kira wayar yana wannan tunanin, bayan matar ta bata tabbacin za'a samu, sosai ya yi
farin ciki sannan ya gode musu ya tashi zai ɗauki Imara
"Tunda dai nasan yanzu Maybe fita zaka yi to wajen wa zaka barta a gidan?" Fatima
ta faɗa tana kallonsa, girgiza kansa ya yi fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce"to ya zan
yi, da tafiya zanyi da ita" girgiza kai tayi ta ce"a'a a wannan sanyin, kawai ka
barta anan zan kula da ita har anjima mai rainonta ta zo" murmushi ya yi ya
ce"Nagode sosai da karamci Fatima" murmushi ta yi bata ce komai, sukayi sallama da
Sulaiman sannan ya fita yana tunanin ina ma Suhaila ce ta ke yin haka.
Washegari da safe bayan sun gama breakfast ya shiga gidan Sulaiman ya samu har mai
rainon ta zo, babbar mace ce kuma kana ganinta kaga mai hankali, da alama ba yar
ƙauye ba ce dan babu alamar hakan a tattare da ita tsananin kuncin rayuwa ne kawai,
zama ya yi ya lissafa mata abubuwan da yakeson ta dinga yi wa Imara kuma ta amince
da hakan, sannan ya danƙa mata Imara a hannunta. Godiya ya sakewa Fatima sannan
suka bar gidan, a corridor ɗin gidan ya nuna mata wani part suka shiga, parlon ne
madaidaici sai kitchen a cikinsa sai wani ɗakin kwana mara girma da banɗaki a ciki,
kallonta ya yi ya ce "yawwa Baba nan ne inda zaku dinga zama" jinjina kanta tayi ta
ce"tom Alhaji mun gode" murmushi ya yi ya ce"babu komai, zuwa anjima zan fita nayi
muku siyyayar abinda zaku ci da kuma na amfani, nidai fatana kawai ki riƙe yarinyar
nan da amana dan marainiya ce" girgiza kanta tayi ta ce"Allah sarki, Allah ya jiƙan
iyayenta, in sha Allah ba zaka samu wata matsala daga ɓangarena ba zan kula da ita
iyakar iyawata in sha Allah" sosai ya ji daɗin haka ya yi mata sallama ya fita. Kai
tsaye ɗakinta ya shiga tana tsaye jikin curtains ɗin ɗakin ta kalleshi murya kasa
ƙasa ta ce" wace wannan wacce ka shigo da ita?" yana cire agogon hannunsa ya
ce"wacce zata raini Imara ce tunda ke ba zaki iya ba!" harararsa tayi tana taɓe
baki ta ce"Eh bazan yi ba tunda ba dolena ba ce, ba zan raini ƴar da bansan taya
aka haifeta ba" a fusace ya ɗago yana kallonta cikin wata kakkausar murya ya ce"ki
dinga sassauta kalamanki akan yarinyar nan Suhaila idan ba haka ba zan baki mamaki
wlh"
"Me zaka yi!?, Na ce me zaka yi?, zaka sakeni ne?, idan zaka iya sakeni Mubarak!,
na ce ka sakeni!"
Kwafa ya yi sannan ya juya ya bar wajen ba tareda ya tanka ta ba, harararsa tayi
sannan ta fice daga ɗakin itama.
Zaune take tsakar gidan tana wanke-wanke, banda taɓa kwanukan babu abinda take yi
dan babu alamar tama iya wanke-wanken, gashin kanta ne duk ya rufe mata fuska hakan
ya sa ta miƙe tsaye tana tsalle sai kuma ta fashe da kuka, da gudu ta fito tana
kallonta ta ce"Imara lafiya?, me ya saka ki kuka?, wane ya sakaki wanke-wanke?"
Ƙarasawa wajenta tayi tana kuka ta ce a shagwaɓe "Umma gashina ne!, gashina ne!, ni
ki haɗe min shi" ta ƙarashe maganar tana bubbuga ƙafa, murmushi tayi ta ce"Allah ya
yaye miki wannan rigimar" turo baki tayi, girgiza kai Umma tayi sannan ta haɗe mata
gashin kan nata irin na larabawa sak ta ɗaure mata waje guda, nan fuskarta ta fito
sosai, kyakkyawa ce ajin farko dan ko ba'a faɗa maka ba kasan ma jinin yan Nigeria
ba ce ba, kallon idanunta wanda suka kasance manya tayi sannan ta ce "me ya sameki
a fuska?, naga tayi ja?" Turo baki ta yi ta ce "ba Aunty ce ta dakeni ba, kuma ta
ce nayi mata wanke-wanke, kuma ta ce idan na faɗawa Daddy sai ta yanka niii!"
"What!?"
Suka ji saukar muryarsa a bayansu, girgiza kai Imara ta shiga yi ta rufe bakinta da
ɗan ƙaramin hannunta, ƙarasowa gabansu ya yi ya kama hannunta cikin sanyin murya ya
ce"me Aunty tayi miki?" Girgiza kanta ta yi, ya daka mata tsawa. Fashewa tayi da
kuka ta shige jikinsa jikinta na rawa, rungumeta ya yi yana shafa bayanta ya
ce"shikenan ya isa faɗamin me tayi miki?, laifi kika yi mata?" Girgiza kanta tayi
cikin shassheƙar kuka ta ce"indomie nakeso shine kuma babu anan, na shiga ciki zan
ɗauka shine ta mareni ta ce nayi mata wanke-wanke, amma dan Allah Daddy karka faɗa
mata ta ce idan nafaɗa maka sai ta yanka ni, ni banason na mutu Daddy!!" Sosai
ransa ya ɓaci bai ce komai ba ya kama hannunta suka shiga gidan, zaune suka sameta
tana cin cake tana kallon draman da ake a MBC Bollywood,
"Me tayi miki da har zaki ɗauki hannu ki mareta?, a matsayinki na wa?, akan me zaki
sakata aikin da yafi ƙarfin shekarunta?, ke koma aikin da zata iya ne ki a
matsayinki na wa zaki sanyata aiki?" Tashi tsaye tayi tana kallonsa baki a buɗe,
"Bari kiji bakisan wahalarta ba, baki raineta ba, babu abin da ya haɗaku saboda
haka karna sake jin kin shiga harkarta, idan ko haka ba wlh saina ɓata miki rai!"
"Okay, saboda na saka yar da ake riƙo a gidana aiki shine laifi?, ko kuwa dan na
hukuntata?, kenan babu wanda ya isa ya gyara mata idan tayi ba daidai ba?, naga..."
"Akwai mana!, akwai mutanen da suka dace su gyara mata idan tayi kuskure, amma ke
bakya ɗaya daga cikinsu, bakida wannan damar, baki isa ba!, ke baki kai ba, saboda
haka ki kama kanki, idan har kika cigaba da irin wannan nuna kin isan da ita zan
baki mamaki!"
Yana gama faɗin hakan ya kama hannun Imara suka yi waje, part ɗinsu ya mayar ya
daina ya zauna yana kallonta ya ce"kiyi haƙuri kinji, bari zan fita sai na siyo
miki man zafi, kinyi karatu sosai a school ko?" Murmushi tayi har saida beauty
point ɗinta ya loma ta ce"Eh Daddy, uncle John ya ce nafi kowa ƙoƙari a class ɗin
mu, naji daɗi Daddy" murmushi ya yi ya ce"yawwa, that's my girl, keep it up kinji,
inason kiyi karatu sosai ki zama lawyer "
"Lawyer kuma Daddy?, why not Doctor?" Girgiza kai ya yi ya ce"No, lawyer nakeson ki
zama kinji" gyaɗa masa kai tayi ta ce"your command is my wishes Daddy" girgiza
kansa ya yi yana dariya ya ce"yawwa Baby na, yanzu bari naje nayi wanka, zan zo
muje shopping" tashi tayi tana tsalle ta ce"yehh, daman inason siyan chocolate da
Pringles" murmushi ya yi ya ce"oyha je ki shirya ki zo mu tafi " da gudu ta shige
bedroom ɗin ya girgiza kansa sannan ya yi waje.
***Kallonta tayi ganin har sannan batayi shiru ba ta ce"wai ke idan ba zakiyi shiru
ba ki tashi ki bar nan, tunda kika zo kike kuka, nayi miki maganar duniya kin yimin
banza, tun da ba zaki fadi abin da ya kawo ki ba sai ki tashi ki bani guri"
shassheƙar kuka ta fara tana kallonta ta ce"Mommy wlh nagaji, nagaji da abin da
Mubarak yake yimin akan yarinyar nan, kwata-kwata baya kulani, idan kinga ya yi min
magana to saidai akan yarinyar nan, yana fifitata akan komai Mommy, ni bansan me
nayi masa ba, kuma ban isa na hukunta yarinyar ba sai ya hau yimin bala'i kamar zai
dakeni, ya zanyi Mommy?, ya zan masa, nagaji wlh, idan babu dama sai na haƙura da
auren nasa!"
"Ki haƙura!?, ki haƙura fa kika ce?, bama kida hankali, kenan wannan yarinyar da
aka haifeta a gabanki ita zata fitar dake daga gidan mijinki, to idan kin fito sai
ki auri wa?, kinsan dai babu mai aurenki bakya haihuwa shima ɗin saboda yana cin
arzikin ubanki yake zaune dake, amma badan haka ba tuni wani zancen ake. Ke bakida
wayo, cikin ruwan sanyi zaki fitar da ita, akwai wata ƙawata wacce ta taɓa sakawa
aka yimin aiki akan Alhaji naga bai ci ba na haƙura bari na kirata ta zo ta rakamu
muje ayi ta ta ƙare"
Goge hawayenta tayi ta ce"ni Mommy so nake kawai a kasheta kowa ma ya huta, ko kuma
a haukatar min da ita".
# *Bestnovel*
# *IMARA 💋*
# *Heart touching 💔*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
08106608363
*Chapter 16*
Murmushi Mommy ta yi ta ce"karki damu, wannan duk nasan abin da ya kamata a yi musu
duka, yanzu kedai ki koma gidanki ki zauna karki nuna wani abu ma ya faruwa, ina
mai tabbatar miki zakiga abun da zai faru" rungume mahaifiyartata tayi ta
ce"shiyasa nake sonki Mommy, Nagode sosai".
***Da gudu ta shigo gidan tana kwalawa Umma kira, fitowa Umman tayi daga kitchen
tana kallonta ta ce"Imara lafiya kike min wannan kiran?" Turo baki ta yi tana ajiye
school bag ɗinta ta ce"ni Daddy nake nema zan faɗa masa abu" girgiza kai Umma ta yi
ta ce"amma ai kinsan bai dawo ba ko?, shine ni zaki dameni?" kallonta tayi da dara-
daran idanunta kamar zatayi kuka ta ce"to kira min shi a waya, magana zan masa fah"
haɗe rai ta yi ta ce"ita maganar ba zaki iya jira sai ya dawo ba?, bansan fa rigima
Imara" tashi Imara tayi bata sake ce mata komai ba ta shige bedroom tana zuwa ta
faɗa kan gado fashe da kuka tana burgima. Shiga ɗakin Umma tayi ta tsaya tana
kallonta kafin ta nisa ta ce"me aka yi miki na kuka kuma?"
Ajiyar zuciya Umma ta sauke ta ce"bari na ɗauko wayata to" daga haka ta fice daga
ɗakin, tashi zaune Imara tayi ta shiga goge hawayen fuskarta tana shassheƙar kuka.
Umma na fita ɗaukan waya ya yi sallama ya shigo, murmushi ta yi ta ce"Allah ya kawo
ka ma shikenan na huta" murmushin shima ya yi ya ce"meya faru?" "daga dawowarta
daga makaranta ta hanani sakat sai an kiraka wai abu zata faɗa maka" girgiza kansa
ya yi yana dariya ya shige bedroom ɗin, zaune ya sameta har sannan tana shassheƙar
kuka tana ganinsa ta tashi tsaye ta rungumeshi, zaunar da ita ya yi gefensa ya
ce"mene ya faru?, wa ya taɓa min gimbiyata?" murmushi ta yi ta ce "Daddy daman anyi
mana hutu ne, shine nakeson naje ƙauye wajen granny" waro idanunsa ya yi ya
ce"ƙauye kuma?, A'a, ki bari sai anyi hutun third term kinga shine mai tsayi sai ki
tafi, kina dawowa ki shiga primary 4 ko?" Girgiza kanta tayi tana kwaɓe fuska ta
ce"ni yanzu nakeson naje, ka kaini gobe Daddy!, gobe Daddy, dan Allah" numfasawa ya
yi ya ce"shikenan, Allah ya kaimu goben sai na kai ki amma one week zakiyi ki dawo
gida" gyaɗa masa kai tayi alamar ta yarda ya shafa kanta ya ce"ohya tashi kiyi
sallar magrib kizo muyi karatu" jinjina masa kai tayi sannan ta tashi da gudu ta
shige toilet ɗin, girgiza kansa ya yi ya tashi ya fita. A parlon ya samu Umma ya ce
ta haɗa mata kayanta sannan ya yi waje.
***Zaune yake a katafaren parlon ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, hannunsa riƙe da
system yana dannawa a hankali kuma yake sauraren abin da yake faɗa masa,
"Sir, munyi nasarar gano inda Mubarak yake, yanzu kawai muna jiran muji daga
bakinka ne, wane hukunci za'a yanke masa na juya mana baya da ya yi?"
Murmushi ya yi yana cigaba da abin da yake ya ce"inason ka gayyato min shi nan,
inason magana dashi" sunkuyawa ya yi ya ce"angama sir" jinjina kansa ya yi kafin ya
ce "shikenan je ka".
Washegari.
***Da gudu ta ƙarasa ta rungumeta tana tsalle, murmushi Goggo Asiya ta yi ta ajiye
rariyar hannunta ta ce"yau kuma ziyara aka kawo min?" zama Imara tayi a gefenta
tana dariya ta ce"Eh mana Granny, harda Daddy fa muka tawo na gudu na barshi a
waje" ta ƙarashe maganar tana tafa hannu, girgiza kai Goggo Asiya ta yi ta ce"ai
kam dai ki daina gudu yarinya, dan kamar ki basa gudu anan, idan ba haka ba samari
su yi miki dariya"
***Tun daga nesa ya hangosu tsaye a bakin gidansa, a hankali ya yi parking motar ya
fito yana kallonsu da mamaki, ƙarasowa ogan ya yi yana murmushi ya ce"Alhaji
Mubarak!" shiru Mubarak ya yi bai ce komai ba, ogan ya cigaba da faɗin "haka kawai
sai muka daina ganinka babu wani notice, what a surprised?" haɗe rai Mubarak ya yi
yana kallonsa ya ce"kaga ni yanzu banida wani business daku, na rigada na bar
wannan harkar, zan cigaba da neman abincina ta hanyar halal, duk wani abun more
rayuwa zanyi na daidai ƙarfina ba tareda nafaɗa halaka ba, saboda haka dan Allah ku
bar ƙofar gidan nan" sigarin hannunsa ya yar a ƙasa yasa ƙafa ya murjeta yana
girgiza kansa ya ce"kenan daman ka shirya munafuntarmu, akwai wani abu a zuciyarka,
ko kuma akwai wanda ka kewa aiki" girgiza kai ya yi ya ce"ni babu wani wanda nake
yi wa aiki, kawai na fita daga cikin irin wannan sabgar ta saɓon Allah ne, har
abada bazan sake cutar da wani rai ba, ina rokon ubangiji laifukan dana aikata a
baya ya yafemin" tuntsirewa ya yi da dariya, ya juya yana kallon sauran suma suka
sheƙe da dariyar rainin hankali, haɗe rai ya yi lokaci ɗaya ya ɗaga musu hannu,
kowa yayi tsit. Kallon Mubarak ya yi ya ce"kaci Sa'a oga da kansa ya ce yana son
ganinka, amma da ni da kaina zanyi maganinka, saboda haka shige muje"
"Babu inda zan je ni!, na fita daga wannan harkar kuma har abada bazan koma ba,
wannan shine abinda na yankewa rayuwata, kuma babu wanda ya isa ya sakani na
sauya!" Numfasawa Ogan ya yi ya ce"kaii!, nutsu, umarnin oga ne kuma dole ka bi, ko
ka tafi ko kuma mu kaika da kanmu" baki buɗe Mubarak ke kallonsa, ganinsa irin
kallon da yake masa yasa ya yi yaran alamar su zo da hannu, tawowa suka yi duka, ya
ce"ku saka shi a mota" kafin kiftawar ido suka cacimeshi suka zura cikin mota suka
bar bar unguwar.
***Girgiza kai Goggo Asiya ta yi ta ce"a'a Imara bakisan kogin nan ba, ni banason
ma ki je wlh, ki bari nasamu yaro a aika ya ɗebo min" turo baki gaba tayi ta ɗauki
tulun ta ce"ni wlh ni zan je nafa sani Granny, kawai ki barni na ɗebo miki, yanzu
zan dawo" murmushi ta yi ta ce"uwar kafiya, je ki, Allah ya tsare" da gudu ta fita
daga gidan tana dariya, girgiza kai Goggo Asiya ta yi ta cigaba da kunna wutar da
take. Tana tafe tana yan waƙoƙinta har ta kai kogin, murmushi tayi har saida beauty
point ɗinta suka loma, ta ƙarasa gabansa ta tsuguna tana kallon ruwan wanda yake
gwanin ban sha'awa, sunkuyawa tayi ta ɗebi ruwan, zata miƙe ta hangi wani mutum
fuskarsa a rufe daga can wani gefe na kogin, murmushi tayi a fili ta ce "laa shima
ya zo ɗi ban ruwa" daga haka ta ƙarasa inda yake, sunkuyawa tayi daidai gefen
fuskarsa wacce take a rufe ta ce"Hello" shiru ta ji ya yi mata hakan yasa ta ce"ko
Hausa kake ji, kuma na ganka fari irina, ya sunanka?, kaima Granny ɗinka zaka
ɗibarwa ruwa?, Eh?" Shirun da taji ya yi har sannan yasa ta kwaɓe fuska ta ce"to
kai baka ji ne?, ko baka magana irin peter na school ɗin mu, ni sunana IMARA
kaifa?" Sai a sannan ya juya ya kalleta, fuskarsa a lulluɓe take baka ganin komai
sakamakon glasses ɗin daya sanya akan idanunsa kuma lulluɓin ya rufe har goshinsa,
hannunsa kuma sanye suka da safar hannu, murmushi Imara ta yi ta ce"kai ya
sunanka?, ka zama abokina mana" bai ce mata komai ba sai tashi da ya yi daga zaunen
da yake ya zuba hannunsa a aljihu ya shiga kallon kogin, haɗe rai tayi ta tashi
tsaye itama, gabaɗayanta bata kai ƙugunsa ba, ta ɗaga idanu ta kalleshi sai kuma ta
harareshi tana murguɗa baki ta ce"wai dan ya fini tsayi, to ni wlh karka ganka
babba ko duka nakewa mutane, kuma nama daina kulaka Dodo kawai" tana faɗin haka ya
juyo ya kalleta, da gudu ta bar wajen, ta koma inda a ajiye tulun ruwanta ta ɗauka
ta bar wajen tana tafe tana sheƙar da ruwan har ta ƙarasa gida. Ajiyewa tayi tana
riƙe ƙugunta ta ce"wash! nagaji granny" girgiza kai Goggo ta yi ta ce"to ba dole
ba, ji yanda kika jiƙa jikinki" murmushi tayi tana kallon jikin nata ta ce"to ai
dodo nagani shine na gudo kar ya kamani"
Ƙarasowa tayi kan tabarmar ta ce"wlh granny dodo ne baya magana fa, gashi fuskarsa
a rufe" ta tuntsire da dariya tana tafa hannu, girgiza kai Goggo tayi tana murmushi
ta ce"shikenan tashi ki cire waɗannan kayan ki sauya wasu, a kuma zuwa ɗiban ruwan
ai" tashi tayi ta shige ɗakin tana dariya.
*Dutse*
*12:43pm*
Zaune yake kan kujera yana karkaɗa ƙafa yayinda su kuma suke zaune a ƙasa, idanunsa
kan Mubarak wanda ke kallon wani waje daban fuskarsa a haɗe kamar bai taɓa dariya
ba, girgiza kai ya yi yana murmushi ya ce"kuma shikenan Mubarak sai ka ɗauke
ƙafarka baka sanarwa da kowa ba, ka daina kula kowa tsawon waɗannan shekarun?"
Kallonsa ya yi ya ce "nayi hakane saboda kada ma a dakatar dani, saboda tsakanina
da Allah na shiryu kuma, kuma ina yi muku fatan shiriyar gaba ɗaya" tashi Ogan nasu
ya yi ya shiga zagaye ɗakin kafin ya juyo ya kalleshi ya ce "yanzu kenan ka bar
cikinmu kake nufi?, kuma ba zaka dawowa ba?" Jinjina masa kai ya yi ya ce"Eh ka
nemi wani" murmushi ya yi ya kalli shugabansu ya ce"Papa ku mai dashi gida, sannan
ka bashi kuɗi naira miliyan biyu ya samu yaja jari ya yi wata sana'ar " tashi
Mubarak ya yi ya ce"a'a zan koma da kaina, sannan Nagode amma bana buƙatar kuɗinka,
Allah ya rufamin asiri, Nagode da kyautatawa " yana gama faɗin haka ya juya ya fice
daga parlon, da idanu kawai ya bishi sai kuma ya yi murmushi ya koma ya zauna yana
kallon Papa kafin ya yi magana ya ce"yallaɓai ya zaka barshi ya tafi?, idan kuma ya
tona mana asiri fa?, nifa nafi tunanin wani yake wa aiki wlh" lemon dake ajiye akan
table ya tsiyaya yasha sannan ya kalleshi ya ce"to kai da mene tunaninka?, na hana
shi tafiya?, ai bazai yiwu ba, ku barshi ya je gida, duk wanda ya fara aiki dani to
dole ya ƙarashe rayuwarsa a tare dani ba'a juyamin baya, ku barshi ya huta na yau,
zuwa gobe Inason naji labarin mutuwarsa s gidajen rediyo da kafar sada zumunta"
sunkuyar da kai suka yi duka suka haɗa baki wajen faɗin
"Angama"
# *Bestnovel*
# *IMARA 💋*
# *Heart touching 💔*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋 💋*
Chapter 17
Kallonta granny tayi ganin yanda ta haɗe kai da gwiwa ta ce"lafiya Imara?" Turo
baki tayi tana kallon gefe guda ta ce"ko ba Daddy nakeson gani ba" a shagwaɓe tayi
maganar kamar zatayi kuka, girgiza kai Granny tayi ta ce "au daga zuwan naki yau
shine zaki ce Daddy kikeson gani?, to ƙaniyarki, kuma babu wanda zaki wahalar sai
kinyi sati a garin nan" tsam Imara ta tashi daga inda take ta dawo kusada granny ta
fasa ƙara ta kwanta a wajen tana burgima, riƙe baki granny tayi ta ce"nashiga uku
ni Asiya, me kuma nayi miki?"
"Ni wlh Daddy nakeson na gani!, ki kira shi a waya ya zo, ni sai ya zo wlh!" Kuka
take sosai tamkar wata jaririya gabaɗaya ta ɓata kayan jikinta da ƙasa. Tashi
Granny tayi ta shige ɗakinta ta ɗauko wayarta ta fara kiran lambar Mubarak, saida
tayi ringing sau biyu sannan ya ɗaga bakinsa ɗauke da sallama, gaisawa suka yi
sannan ta faɗa masa abin da yake faruwa, murmushi ya yi ya ce ta bata wayar,
kallonta tayi ta ce"ki zo ga baban naki" da sauri ta tashi tana goge hawayenta ta
karbi wayar
"Da..Daddy!"
Ta faɗa cikin shassheƙar kuka, murmushi ya yi ya ce"na'am ƴar gidan Daddy mene ne?"
"Ni ka zo yanzu!" waro idanunsa ya yi kamar tana gabansa ya ce"yanzu kuma Imara?,
me ya faru" kuka ta saka ta ce"ni kawai ka zo yanzu" "kin fasa kwana a gurin Granny
ɗin?" girgiza kanta tayi ta ce"nidai ka zo yanzu Daddy, ni ka zo, abu zan faɗa
maka" murmushi ya yi ya ce" to ki faɗamin a wayar mana" maƙale kafada tayi ta
ce"nidai a'a sai kazo" girgiza kansa ya yi ya ce"to Imara ki bari saida safe mana"
fashewa tayi da sabon kuka ta ce"ni yanzu nakeson ka zo Daddy!, yanzu fa" numfasawa
ya yi ya ce "shikenan gani nan" murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma
ta ce"safe trip daddy" murmushin shima ya yi sannan ya kashe wayar. Kallonta granny
tayi ganin yanda fuskarta tayi jajur ta harareta da wasa ta ce"kuma ba zaki kwanar
min a gida ba, yau saidai ku tafi tare" turo baki tayi tana maƙale kafaɗa" .
***Shigowa ɗakin tayi tana kallonsa da mamaki ganin yana ƙoƙarin saka hula, tsayawa
tayi a cikin bango har saida ya gama tsaf sannan ta kalleshi fuska a haɗe ta ce"ina
kuma zaka je da daddaren nan?" girgiza kansa ya yi ya ce"wlh wai Imara ce ke
kirana, sai kuka take na zo, shine zan je amma ba dadewa zan yi ba"
"Imara na kiranka!?, sai kuka take?, kuma ba dadewa zaka yi ba?. Bangane ba, imaran
jaririya ce?, ko kuwa tana da wata lalura ne?, nifa bangane wannan rikitaccen
al'amarin ba wlh, tana kuka akan me?" Yana ƙoƙarin ɓalle bottle ɗinsa ya ce"dan
tana son ganina shine ai bu?, ko kuwa dan tayi kuka, ko kin manta yarinya ƙarama ce
ne?, har kwaya nawa imaran take?, she's just 9yrs old fa"
Tunda ta fara maganar yake kallonta bai ce komai ba, yana ganin tayi shiru ya ratsa
ta gefenta zai fita, jawo shi tayi tana huci ta ce"mahaukaciya ka mayar dani
kenan?, wlh babu inda zaka je kaji na faɗa maka!" Tsaki ya yi yana kallon waje ya
ce"tun kafin raina ya ɓaci Suhaila ki sakeni, banason nazo nayi abinda zai ɓata
mana rai duka, saboda haka let go of me, or else..."
"Kayi duk abin da kake ganin zaka yi, amma wlh babu inda zaka fita, baka is..."
Maganar ta tsaya dalilin wasu maruka da ya yi mata, dafe kuncinta tayi nan take
hawaye suka fara ambaliya ta kalleshi bakinta na rawa ta ce"ni!?, ni ka mara
Mubarak?, ka mareni?"
"Nan gaba idan kika sake yimin irin wannan ba marinki kaɗai zai yi ba, saina karya
ki, ni ba sa'an wasanki bane, baki isa ki dinga yimin irin cin kashin da kika so
ba!" Ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama, da idanu kawai Suhaila ta bishi sai
kuma ta sulale a wajen ta rushe da wani irin kuka kamar ranta zai fita.
***Har ya isa ƙauyen ransa a ɓace yake, yana zuwa ya tarar da ita zaune gefen
granny tayi shiru, tana ganinsa ta tashi da gudu ta rungumeshi tana dariya,
murmushi ya yi yana shafa kanta ya ce "sarkin rigima!" turo baki tayi bata ce komai
ba, ta rike hannunsa suka ƙarasa inda aka shimfida tabarma, zama ya yi ya kalleta
ya ce"to gani nazo" murmushi tayi ta ce"yawwa Daddy na shiyasa nake sonka wlh, har
naji daɗi dana ganka" girgiza kai granny ta yi ta ce"kuma ka tafi da yarka ni bazan
iya wannan abun nata ba" juyowa tayi ta kalli Granny sai kuma ta maƙale kafaɗa ta
ce"ni wlh anan zan kwana" dariya ya yi ya ce"ai daman ba tafiya zanyi dake ba,
ummanki ma ta tafi garinsu ɗazu, ta ce ba zata iya zaman gidan babu ke ba" murmushi
tayi ta ce"yawwa Daddy". Nisawa ya yi sai kuma ya ce"me zaki faɗamin?, dare nayi"
murmushi tayi ta ce"daman ce maka zanyi ina sonka, i love you Daddynaaaaa" waro
idanu ya yi ya kama kunneta ya ce"akan wannan kika taso ni Imara?" gyaɗa masa kai
tayi tana dariya, murmushi ya yi ganin yanda take farin ciki ya ce"Allah ya
dawwamar miki da farin cikin nan har ƙarshen rayuwarki Baby" "Ameen" cewar granny
itama tana murmushi. Har mota ta rakoshi tana murmushi ta ce"Daddy gobe ma kazo
kaji dan Allah" murmushi ya yi ya ce"gobe inada abubuwa dayawa, amma in sha Allah
jibi zan zo ki ganni" langwaɓar da kai tayi ta ce"Tom shikenan sai ka zo Daddy" Bye
bye tayi masa shima ya daga mata hannu sannan ya shiga motarsa, saida ta daina
hango motar sannan ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta koma cikin gidan.
Washegari.
Cikin sanɗa ta fito daga ɗakin gudun kada granny ta ji ta ta ɗauki tulun ɗiban ruwa
tayi waje da gudu, tana tafe tana yan waƙe-waƙenta na yan makaranta har ta ƙaraso
kogin, lumshe idanu Imara tayi haka kawai taji tana ƙaunar zuwa wajen ruwan,
Tsugune take bakin Kogin tana ƙoƙarin ɗiban ruwa tana jin sanda yazo ya tsaya a
bayanta hakan yasa ta miƙe tana kallon fuskarsa da take a rufe ta ce" yauma ka sake
zuwa ko?, wai ya sunanka?" da idanu kawai taga yana binta hakan yasa ta tura baki
gaba tana harararsa ta ce"wannan kaman kurma baya magana, kai kana jina? Yayane
sunanka?" Shiru nan ma taji ya yi mata ta galla masa harara ta ɗora tulunta aka
tashige ta gefensa saida tayi nisa sannan ta tsaya ita kaɗai take cewa" to kodai
nayi masa turanci inaga baya jin Hausa" da wannan tunanin ta koma inda yake tsaye
har sannan tana kallonsa ta ce" kai what's ur name? Kanajin turanci? Ni sunana
Imara gurin granny na nazo wannan ƙauyen kai ya sunanka? ko kai bature ne? nima
mama ta ce inada kyau kai kaga kyan?" Ganin har sannan bai ce mata komai ba kuma
bai buɗe fuskarsa ba ya sanya ta haɗe rai tana ƙoƙarin fashewa da kuka ta sanya
hannunta a baki cikeda shagwaɓa take cewa"sai kai ta tsaiwa nonse kawai ni babu
ruwana ma dakai aljani kawai". Shiru ya yi mata kamar rannan hakan kuma ba ƙaramin
ɓata mata rai ya yi ba, dan a rayuwarta ta tsani ta yiwa mutun magana ya yi mata
shiru, tulunta ta ɗauka ta harareshi sannan ta bar wajen tana tafe tana mita. A
ƙofar gidan taga mota hakan yasa ta shige gidan da sauri tana murna ganin yau ma
Daddynta yazo, turus tayi ganin ba shi bane, amma data hango ummarta sai ta tafi da
gudu ta faɗa jikinta tana dariya, murmushi Umman tayi dukda yanda jikinta yake a
sanyaye ta ce cikin sanyin murya" ɗiban ruwa kika tafi?" gyaɗa mata kai tayi tana
murmushi, shafa kanta Umma tayi ta ce"tashi ki ɗauko hijab ki zo zamu tafi"
"Tafiya kuma Umma?, meyasa?, ni fa ba yau zan koma ba" kallonta granny tayi ta
ce"ai zuwa zamu yi mu dawo" kasancewar Imara nada saurin fahimtar abu yasa ta ce"to
me akeyi da zamu je?" murmushi Umma tayi ta ce"wani abun mamaki ne fa, kedai idan
mun je zaki gani" juya kanta tayi kawai sannan ta tashi ta ɗauko ɗan baby hijab
ɗinta ta ɗora kan rigar jikinta tashi Umma suka yi ta kama hannunta suka fito daga
gidan, shiga motar suka yi, ganin abokin Daddynta yasa tayi murmushi ta gaisheshi,
amsawa ya yi cikin sakin fuska sannan suka bar unguwar.
# *Bestnovel*
# *Heart touching*
# *IMARA 💋*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋 💋*
*Chapter 18*
Motar nagama parking Imara ta fito, ɗaya bayan ɗaya take bin mutane dake tsaye a
ƙofar gidan da kallo, ɗan turo baki tayi ta riƙe gefen rigar Umma kasancewar
batasan taron mutane. Hannunta Umma ta riƙe suka shiga cikin gidan, cak Imara ta
tsaya duk da jan hannunta da Umma ke yi, abinda idanunta suka hango mata shine ya
hanata yin gaba, zare hannunta tayi daga jikin Umma ta shiga takawa a hankali
idanunta kamar zasu faɗo, jikinta na rawa ta ƙarasa inda ta hangi Suhaila tsugune
tana zuwa ta dafata bakinta na rawa ta ce"Mommy meya faru?, wane ya mutu?, ina
Daddyna?" Wani sabon kukan ne ya kwacewa Suhaila tayi saurin kifa kanta ta shiga
rera shi gwanin ban tausayi, tsugunawa Imara tayi hannunta na rawa ta riƙe gefen
likkafanin, runtse idanunta tayi sannan ta yaye fuskar, wa iriyar ƙara ta saki tana
yin baya, da sauri Umma ta ƙaraso ta rungumeta, ɓuya tayi a jikin Umma bakin na
rawa amma ta kasa furta komai sai girgiza kanta take yi, kowa na wajen saida Imara
ta bashi tausayi dan gaba ɗaya ta fice hayyacinta har aka fita da Mubarak bata sani
ba.
***A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi, surutu taji sama-sama
a ɗakin, ta tashi zaune tana bin ƴan tsirarin mutane dake ɗakin da kallo, Umma ce
ta ƙaraso inda take ta zauna gefen kujerar tana kallonta ta ce"kin tashi Imara?"
jinjina mata kai tayi, sai kuma ta tashi tsaye kamar wacce aka tsikara ta ce"wajen
Daddy zan je" idanun Umma ne ya kawo ruwa cikin sanyin murya ta ce"ba yanzu ba
Imara, Daddy baya nan, dawo ki zauna" maƙale kafaɗa tayi kamar zatayi kuka ta ce"ni
Allah wajensa zanje, abu zan faɗa masa fa, wani mafarki nayi fa Umma" kamo hannunta
tayi ta ce" mafarki ƙaryane Imara, Daddy baya nan, ba sai kin faɗa masa ba, kiyi
addu'a kawai" kallonta Imara tayi da dara-daran idanunta, saurin sunkuyar da kai
Umma tayi saboda hawayen dake zuba a fuskarta. Shiru Imara tayi kamar mai nunanin
wani abu sai kuma ta tashi ta fice da gudu daga ɗakin, tashi Umma tayi ta bita da
sauri gudun kar ta yi wani wajen saidai ganin ta nufi hanyar cikin gidan yasa ta
tsaya a wajen har sannan kuma bata daina kuka ba.
"Daddy!, Daddy!, Daddy!" Da idanu mutanen ɗakin ke bin ta, Suhaila ta taso tana
kallonta ta ce"wa kike nema Imara?" cikin saurin baki ta ce"Mommy Daddy, Daddy nake
nema, zan faɗa masa wani abu" fashewa Suhaila tayi da kuka ta kama hannun Imara
tana girgiza mata kai, Mommy ce ta ƙaraso wajen fuskarta a haɗe kamar bata taɓa
dariya ba ta ce"ke lafiya?, meya faru kike kuka kuma?" kasa magana Suhaila tayi sai
hannun Imara data kama, saurin fizge hannun Mommy tayi ta hankaɗa Imara, kasancewar
jikinta babu wani kwari yasa ta fadi a ƙasa, yarfe hannu Imara ta shiga yi hawaye
na zubowa kan siririyar fuskarta. Baki buɗe Suhaila ke kallonta cikin shassheƙar
kuka ta ce"Mommy mene haka?"
"Tambayata kike mene haka?, to ban sani ba!, nace ban sani ba!" Ta maida idanunta
kan Imara wacce ke kallonta ta ce"abinda ya haɗa ya raba, Mubarak ya kawo ki gidan
nan, babu yanda bamu yi ba mu fitar dake abu ya gagara, Yanxu kuma wanda ya kawo
kin baya duniya, saboda haka babu abinda ya haɗaki da ita, ke tsintacciya ce, wacce
ba'a san ma su wane iyayenki ba, kin ci albarkacin Mubarak daya kafe sai ya raineki
saboda haka yanzu babu shi bakida wata alaƙa da gidan nan ko mutanen cikinsa, ke je
can ki nemi iyayenki, idan kinada rabon ganinsu kenan, idan kuma a duniya aka
sameki sai kema ki ɗora daga inda suka tsaya!" Tunda ta fara magana Imara ke
kallonta, duk abubuwan data faɗa ta fahimta kuma ta haddacesu a ƙwaƙwalwarta, abu
daya ne yake mata yawo arai, daman ba mafarki tayi ba?, da gaske Daddynta mutuwa ya
yi?, saurin girgiza kanta tayi ta miƙe tsaye da niyyar fita saidai wani jiri ya
ɗabeta ta fadi ƙasa sumammiya. Da gudu Suhaila ta ƙarasa ta ɗagota jikinta haka
kawai taji tana tausayin yarinyar, jijjigata tashiga yi amma shiru babu alamar tana
numfashi, shigowa Umma tayi Granny na biye da ita da sauri suka ƙarasa wajen Imara
suka karɓeta. Ƙarasowa Mommy tayi ta janye Suhaila tana yi mata wani mugun kallo ta
ce "karna sake ganin kin taɓa ta, shashasha kawai, bansan yaushe kika zama haka ba"
kuka ta saka tana riƙe rigar Mommy ta ce "yarinyace ƙarama Mommy, kar wani ciwon ya
sameta, me ɗawainiya da ita ma kaɗai duniya ne, dan girman Allah ki sassauta mata,
Mubarak baya nan, bana jin haushin yarinyar nan ko kaɗan wlh, na tabbata zai yi
farin ciki idan yaji na kula da rayuwarta bayan ransa kuma..."
"Ki kula da wa?, hala hauka kike yi?, a matsayinta na wa zaki kula da ita?, yar ki
ce?, ko ƴar mijinki ce?, ko ƙanwarki ce?, to bari ki je keda yarinyar nan har abada
wlh!" Tana kallon su Granny ta nuna su da yatsa ta ce
"Ku ɗauketa daga nan, sannan kuma har abada karna sake ganinta, nan gidan bana
Mubarak bane, gidan mijina ne ya basu aro su zauna, kuma yanzu ya mutu saboda haka
dole ta bar cikin gidan nan, tunda ba yar sa ba ce, batada gadonsa, ke koma tanada
shi to wlh ba za'a bata ba, balle ma tsintacciya ce mara asali da tushe, shima
Mubarak ɗin dan Suhaila ta matsa sai ta aure shi ne amma kwata-kwata ni ba yimin ya
yi ba, kuma shima bashida wasu dangi wanda zai nuna ya ce nasa ne, wama ya sani ko
a abokan nasa wani ya kashe shi. Dan haka ku tattara yanzu ba sai anjima ba ku bar
gidan nan, Allah ya raka taki gona" banda kuka babu abinda suke yi, domin babu
kalar cin mutuncin da Mommy bata yi musu ba, basu kaɗai ba harma Mubarak ɗin, tana
yi yan uwanta na tayata.
Girgiza kai Granny tayi tana kallonta ta ce"babu komai Hajiya, riƙonma da ya yi
mata Allah ya saka da Alkhairi, daman ba dolensa ba ce, amma zan so ki bari ayi
sadaƙar uku sai mu tafi da ita, ko ba komai nasan akwai ƙawayenta wanda zasu zo yi
mata ta'aziyya, idan bata nan ba zasu samu damar ganinta ba, ki yi mana wannan
alfarmar" tsaki Mommy tayi cikeda masifa take faɗin
"Ke ɗin banza, wlh yau kuma a yanzu sai kun fita daga cikin gidan nan, ku ba
danginsa bane, kai ko ku danginsa ne zan iya korarku tunda ba gidansa bane, saboda
haka yanzu ku ɗauketa ku bar cikin gidan nan, tun kafin nasa a naɗa muku duka kuma
sannan na koreku" murmushin takaici kawai granny tayi ta ƙarasa inda Umma ke
tsugune da Imara tayi mata alama data tashi, tashi Umma tayi ta goya Imara a
bayanta suka yi waje, da sauri Suhaila ta biyo su Mommy tayi saurin riƙeta tana
harararta, cikin kuka ta ce"wannan ba daidai bane Mommy, dan girman Allah ki bari
naje inda suke, ki bari ko numbern wayarsu na karɓa, idan ta tafi babu yiwuwar na
sake ganinta har ƙarshen rayuwata"
"To sai me idan baki ganta ba?, na ce sai me?, ai daman ba dolenki ba ce ita,
bakuda wata alaƙa wacce zaki ce dole sai kin sake ganinta a rayuwa, wlh bazan bari
ku sake haɗuwa ba Suhaila kinji har na rantse miki!"
Zubewa ƙasa tayi ta fashe da wani raunataccen kuka, Mubarak ya tafi ya bar baya da
ƙura, ya rabu dasu a lokacin da suke tsananin buƙatarsa, ya fara aiki da ƙareshi
saidai Allah, ya tafi ya bar su marayu.
***A ƙofar gidan suka tsaya Umma ta kalleta ta cikin kuka ta ce"yanzu mu kaita
asibiti daga nan sai ku wuce gida, zan nemo bayanai wanda zai ɗebo kayanta" kasa
magana granny tayi sai kuka ta dake kamar ƙaramar yarinya, tausayin rayuwar Imara
take, duk wanda ta riƙe shi a matsayin majingina sai ya rabu da ita, mutuwa nayi
mata yankan ƙauna, ta gamu da jarrabobin rayuwa tanada ƙananun shekaru, Allah ne
kaɗai yasan abin da ya shiryawa rayuwarta. Tana wannan tunanin ya ƙaraso gabansu da
mamaki ya ce
"Umma ina kuma zaku je?, daga kai shi ƙabari?" cikin sanyin murya ta ce"Bashir
asibiti zamu kai Imara ta suma ne, ko zaka taimaka ka kai su a motarka, ni zan samu
ɗan dako ne" "ɗan dako kuma?" ya maimaita yana kallonta, miƙa masa Imara tayi ba
tareda ta sake cewa wani abu ba ya karɓeta ya sakata a mota, Granny ta shiga sannan
suka bar ƙofar gidan. Wani private hospital ya kai su a Dutse bayan likitoci sun
dubata suka tabbatar da ta kamu da ciwon zuciya saidai bai yi ƙarfi sosai ba, iyaka
tashin hankali Granny ta shige shi tayi kuka kamar ranta zai fita, tausayin
yarinyar ya cika mata zuciya, a daddafe suka yi kwana uku kafin ta dawo hayyacinta
saidai har sannan bata cewa komai sai kallo da idanu, a haka aka sallame su kai
tsaye kuma Daƙayyawa suka shige.
Fitowa tayi daga ɗakin hannunta riƙe da tsintsiyar laushi da alama shara tayi,
kallonta Granny tayi ta saki baki ganin yanda ta zubawa abincin idanu, ajiye
tsintsiyar hannunta tayi ta ƙarasa gabanta tana kallonta ta ce"Imara meyasa baki ci
abincin ba?" shirin da taji tayi mata yasa ta taɓa ta a firgice ta kalleta, girgiza
kai Granny tayi ta ce"ba na hanaki tunani ba?, so kike sai wani ciwon ya sameki
wanda zai dame mu?" kallonta Imara tayi da idanunta wanda suka faɗa, gabaɗaya ta
rame ta zama so silent kamar ba ita ba, cikin sanyin murya ta ce"Granny da gaske
Daddyna ya rasu?, ya ce min zai dawo shine ya tafi ya barni?, granny ina iyayena?,
meyasa Mommy ta ce min tsintacciya?, me nayi granny?, wane..." Tari ne ya
turnuƙeta, da sauri Granny ta miƙo mata ruwa girgiza kanta tayi tana cigaba da
tarin ta, kallonta granny tayi gwanin ban tausayi ta ce"da gaske Daddynki ya mutu
Imara, amma ki sani hakan ba wai yana nufin dan kin yi wani abu bane, koda da tasa
ƙaddarar, kuma yanda Allah ya hukunta maka haka zaka rayu, Allah ya yi ba zaki
tashi da iyayenki ba shiyasa ya ɗaukesu tun kina ƙarama, kada kiyi fushi, ki cigaba
da addu'a watarana sai labari, rayuwarki zata zama abar sha'awa ga kowa in sha
Allah IMARA!" Kwanciya tayi akan cinyar Granny ta shiga sauke ajiyar zuciya a jere,
shafa kanta Granny ta shiga yi zuciyarta fal tunanin mafita a haka har ta fara jin
saukar numfashinta alamun bacci ya ɗauketa. Gyara mata kwanciyar tayi kasancewar
lokacin ana zafi yasa bata shiga da ita ɗaki ba, sun ɗauki lokaci mai tsawo a haka
kafin ta tashi ta koma ciki dan ƙarasa aikin da ita, tana tashi Imara ta buɗe
idanunta, kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe tsaye duk da jikinta babu kwari ta
fice daga gidan.
# *Bestnovel*
# *heart touching 💔*
# *IMARA*
# *2025*
# *Nanameera.*
*IMARA 💋 💋*
Tafiya kawai take bata ko kallon gabanta, burinta ɗaya ta ƙarasa inda tayi niyyar
zuwa, babu kowa a wajen kogin sai mutum ɗaya da ta hanga daga can gefen kogin,
ajiyar zuciya ta sauke tayi saurin ƙarasawa inda yake, zama tayi gefensa tana
kallon kogin kamar yanda yake shima, sun ɗauki tsawon lokaci a haka kafin ta juyo
ta kalleshi, kamar kullum yau ma fuskarsa a rufe dake, numfasawa tayi ta ce"Dodo!"
ko kallonta bai yi ba dan babu alamar ma yaji abin da tace, haɗe fuska tayi tana
kallonsa ta ce "ba zaka kulani ba?, bakasan an yimin mutuwa ba?, Daddyna ya mutu ya
barni, ya tafi, sai ni kaɗai, banida kowa yanzu, Umma ma ta tafi, kuka nakeson
nayi, ni so nake nayi kuka, ƙirjina zafi yake min Dodo, ka taimakeni" ta ƙarashe
maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka, kallonta ya yi sai kuma ya ɗora
kanta bisa cinyarsa yana shafa gashin kanta ya ce
Tamkar yana zugata haka ta sake rushewa da wani kukan, bai yi yunƙurin hanata ba,
ta ɗauki tsawon lokaci tana kuka kafin a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya,
shirun da yaji yasa ya ɗago idanunsa ya zuba mata idanu, yarinya ce ƙarama amma
gabaɗaya damuwa ta gama wanzuwa akan fuskarta, ko ba'a faɗa maka ba da ka ganta
zaka gane tana cikin jarrabawa, hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen fuskarta,
lumshe idanunta tayi wasu hawayen suka samu damar sakkowa gefen fuskarta, shiru
tayi tana shassheƙar kuka a hankali, har bacci ya ɗauketa, ajiyar zuciya ya sauke
shima sannan ya gyara mata kwanciyar ta a jikinsa ya cigaba da kallon kogin da
yake. Fitowa Granny tayi hannunta riƙe da tsintsiyar tana cewa
"Amma dai kin cinye abincin nan ko Imara?, dan akwai maganin da zan baki" shiru
taji hakan yasa ta ce"ka jimin yarinya, ina miki magana kin yimin shiru?" Juyowa
tayi taga wayam babu Imara babu alamarta a wajen, yar da tsintsiyar hannunta tayi
ta dafe ƙirji tana salati ta ce "subhanallahi, ina yarinyar nan ta shige ni Asiya?"
"Imara! Imara! Imara!" Jin shiru yasa ta leƙa banɗakin, saidai babu alamar ma wani
ya shiga banɗakin, jikin granny na rawa ta ciri hijabi a igiya tayi waje, maƙota ta
shiga tana neman Imara amma babu wanda ya ganta, yawo kwararo-kwararo babu inda
Granny bata je ba amma bata samu Imara ba, zuwa sannan gabaɗaya jikinta ya yi
sanyi, fargaba da tashin hankali ya ziyarceta tunanin inda marainiyar yarinya ta
shige, har bayan awa ɗaya bata samo Imara ba, hakan yasa ta dawo gida maƙota suka
shigo suna yi mata jaje.
***A hankali ta shiga buɗe idanunta, saurin tashi zaune tayi tana kallonsa taga
bama ita yake kallo ba, turo baki tayi cikeda shagwaɓa ta ce"Dodo zan ci abinci"
waro idanunsa ya yi ya ce"wane ya ce miki sunana Dodo?" washe baki tayi ta ce"laaa,
daman kana magana?" girgiza kansa ya yi bai ce mata komai ba ya tashi tsaye, tashi
itama tayi ya kalleta kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"idan baki zauna ba ina
zan kawo miki abincin?" Maƙale kafaɗa tayi ta ce"ai bin ka xanyi, rakaka zanyi"
girgiza kansa ya yi ya juya tayi saurin riƙe gefen rigarsa tana murmushi. A bakin
wata Range rover ɗin mota baƙa ya tsaya ta kalleshi sai kuma ta kalli motar, buɗe
motar ya yi ya ɗauko mata wata leda ya miƙa mata, langwaɓar da kanta tayi ta
ce"ayyah ni ka barni na zauna anan" ta nuna motar, bai kalleta ba ya buɗe mata back
seat ta shiga tana murmushi. Gaba ya shiga ya zauna ya kunna karatun Alkur'ani a
motar, buɗe ledar tayi taga takeaway na fried rice wacce taji wadatattun kayan haɗi
sai kaza akanta, ɗayan takeaway ɗin kuma soyayyen dankalin turawa ne sai aka yi
garnishing na soyyayn kwai akai, lumshe idanunta tayi ta buɗe fried rice ɗin ta
shiga ci tana lumshe ido alamar abincin ya yi mata daɗi. Saida ta cinyeta tas
sannan ta ɗauki ruwa ta sha ta mayar da ledar ta ajiye tayi gyatsa tana kallonsa ta
ce "nagama" jinjina kansa ya yi sannan ya juyo ya kalleta kamar ba zai magana ba
sai kuma ya ce"tafi gida kar Azo ana nemanki" turo baki tayi ta ce "ni ka tafi
dani, nan babu daɗi bana zuwa makaranta, ni so nake na koma makaranta ka kai ni ka
ji" waro idanunsa ya yi ya ce a hankali "to ai ni banida kuɗin kai ki makaranta"
kallonsa tayi ta ce"kaiiii, wlh kanada shi, gashi har mota ka siya" murmushi ya yi
wanda bata sani ba ya ce"wane ya ce miki motata ce?, ta uban gidana ce, ni driver
ne kawai" shiru tayi sai kuma ta ce"to ka aramin kuɗin ka kaini makarantar, idan na
samu zan biyaka" girgiza kansa ya yi yana jinjina hauka irin na yarinyar ya ce"wane
zai bani aran?" murmushi ta yi ta ce"me gidan naka, kace ya ara maka, ni makaranta
nakeso, kuma a dutse nakeson makaranta banaso anan garin Allah " murmushi ya yi ya
ce"keda za'a arawa kuɗi kece kike kafa sharaɗin makarantar da zaki je?" Turo baki
tayi, ya kalleta ta mudubi ya girgiza kansa kawai. Shirin da taji ya yi yasa ta
kalleshi ta ce"zaka aramin ɗin?"
Ya bata amsa a takaice, taɓe baki tayi ta fashe da kuka, juyowa ya yi ya zuba mata
idanu ganin yanda take kuka babu dalili, ganin yanda yake kallonta yasa tayi shiru
ta rufe fuskarta da hannayenta tana leƙensa, murmushi ya yi ya ce"Rigimammiya
kawai!" kifa fuskarta tayi a cinyarta taƙi ɗagowa, y sanya hannunsa ya ɗago
fuskarta yana murmushi ya ce"kema dai kinji kunya, ki je gida kar granny ta nemeki"
Gyaɗa mata kai ya yi, tayi murmushi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce
"thank you Dodona" lumshe idanunsa kawai ya yi bai ce mata komai ba, ta ɗauki ledar
takeaway ɗin ta sauka daga motar. Saida ya daina hangota sannan ya yiwa motar key
ya bar ƙauyen.
***Taɓe baki Baba Hansatu tayi ta ce"wannan yarinyar akwai fitinanniya ko ina ta
baɗaɗa oho!" kallonta kawai granny tayi tama kasa magana, shigowa Imara tayi,
saidai ganin mutane a tsakar gidan ya saka ta taja ta tsaya ba tareda ta ce komai,
tashi Baba Hansatu tayi zata tafi sukai ido huɗu da Imara, tafa hannu ta shiga yi
tana kallonta ta ce"to ga ja'irar yarinyar nan ta dawo" da sauri granny ta miƙe
tsaye, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin data hango Imara, da sauri ta
ƙaraso gabanta ta riƙeta cikin sanyin murya ta ce"Imara ina kika je?, meyasa kika
fita baki faɗa min ba?, meyasa!" kallonta kawai Imara tayi bata ce komai ba, Baba
Yabi ta ce"ta yiwa mutane shiru kamar wata gunki, yarinyar mai kamada fatalwa"
kallonta Imara tayi sai kuma ta fashe da kuka, ta shige ɗaki da gudu. Taɓe baki
Baba Hansatu tayi ta ce"lallaima to wlh wannan yarinyar ki binciketa, ji fa harda
wata leda ta yan gayu a hannunta, yanda take kamar balarabiyar nan babu wuyar an
janyeta, saboda haka ki sanya idanu akanta!" Ta fice daga gidan, bin bayanta sukayi
Granny ta bisu da kallo. Numfasawa tayi sannan ta shige ɗakin tana kiran sunan
Imara.
Zaune ta sameta gefen katifa tana kuka a hankali, zama tayi kusada ita ta jawota
jikinta, rungumeta tayi tana shafa bayanta ta ce"dan Allah Imara karki sake fita
baki faɗa min ba, hankalina ya tashi sosai, ki faɗa min ina kika je?, wane kuma ya
baki wannan ledar" lamo Imara tayi a jikin granny kasancewar ta mai son jiki,
ɗanyatsanta ta sanya a baki tana tsotsa cikin shassheƙar kuka ta ce "ni ba yawo na
tafi ba, wajen Dodo naje, shine ya bani abinci, kuma ya ce zai aramin kuɗi ya sani
a makaranta" kallonta granny tayi ta ce"har yanzu kina ganin Dodon?, Imara kar fa
ki je aljani ne ba mutum ba" saurin ɗagowa zaune tayi tana kallonta ta ce"mutum ne
wlh, kuma yanada mutunci, muryarsa mai daɗi, kuma fari ne shima kamar ni, ba aljani
bane, ya ce min shi Dodo ne ba'a ganin fuskarsa" murmushi Granny tayi ta ce"ke
daɗina dake shirme, Allah ya kyauta dai".
Cikin lokaci ƙanƙani Imara ta saba da Dodonta, kusan kullum sai ta haɗu dashi, har
granny saida ta san shi, haka kawai kuma ta ji ta aminta dashi, hidima sosai yake
musu, duk wani abun buƙata yana yi musu tun kafin ma su tambaye shi.
Cunkoson daya hanga ya sanya ya tsaya da motar, dan gabaɗaya sun cike wajen babu ta
inda zai samu ya shige, ɗan siririn tsaki ya ja sannan ya kashe motar ya sakko,
ratsawa ya yi ta gefensu zai shige ya hangeta tana ta masifa kamar bakinta zai
yage, tsayawa ya yi yana ganin ikon Allah ganin yanda yarinyar ƙaramar kamarta ta
iya tashin hankali. Wata budurwa ce ta kalleta ta ce"ke me kamada aljanu kin ishi
mutane, kinsan ai sun rigaki kice sai kin ɗiba, ke ba zaki bi layi ba?" wani banzan
kallo Imara tayi mata tana riƙe kugu ta ce"wlh sai na ɗiba, dan wasa zan yi dashi,
ai naga ƙaramin bokiti ne, kuma karki sake cemin aljana saidai idan kece aljana ba
ni ba" ihu wajen ya ɗauka yara sai dariya suke suna sake tura Imara, hankade
bokitan wajen tayi ta saka nata, wani yaro ya ture nata bokitin ya takashi ya
fashe, wata iriyar ƙara ta saki ta fadi s wajen ta shiga burgima a cikin ƙasa. Baya
yaran wajen suka yi suna cewa wai aljanunta sun tashi, ganin abun nata bana ƙare
bane yasa ya ƙaraso wajen, darewa akayi ya ƙarasa inda take kwance ya ɗagota,
kallonsa tayi sai kuma ta sake faɗuwa ta cigaba da kukanta, bai ce komai ba ya
sunkuya ya ɗauketa kamar jaririya ya bar wajen da ita, mota ya sanya ta sannan ya
yiwa motar key ya bar wajen. A ƙofar gidansu ya yi parking har sannan kuka take, ya
kalleta fuska babu annuri ya ce"ke yimin shiru" tsit ta daina kukan sai ajiyar
zuciya data shiga saukewa tana kallonsa, saida yaga tayi shiru sannan ya ce "meya
kai ki wajen ɗiban ruwa bayan akwai famfo a gida?, ke bakison zaman lafiya ko?, duk
inda ake tashin hankali sai kin je wajen ko?, Allah yasa na sake ganinki a wajen
sai nayi miki duka" tura baki ta shiga yi tana kallon gefe, girgiza kansa ya yi ya
ce"sauka ki tafi gida, idan kin shiga ki kiramin Granny" a ƙufule ta ce"batanan!"
murmushi ya yi ya ce"to sauka ki ban waje, ko bana ce miki karki sake shiga harkata
ba?" kallonsa tayi da idanunta wanda hawaye ya kwanta ta ce"ai bani na kula ka ba,
ni babu ruwana da kai, na daina kulaka har abada" kafin ya yi magana ta sauka daga
motar ta shige gida da gudu. Fitowa ya yi daga motar daidai nan Granny s fito daga
cikin gidan, gaisawa suka yi ya ce"daman kayan makarantar Imara ne, in sha Allah
ranar Monday zata fara zuwa, akwai driver da zai dinga zuwa yana ɗaukanta in sha
Allah" murmushi Granny tayi ta ce"Allah sarki, ubangiji ya biyaka ɗawainiyar da
kake mana, Allah ya saka maka da Alkhairi ya kula da naka ya'yan, na daɗe ban yi
farin ciki irin na yau ba, Nagode sosai" murmushi ya yi ya ce"Ameen Granny, amma
babu godiya tsakanina da Imara, duk wani abun da kika ga nayi mata, nauyi ne a
kaina nayi mata shi, wanda kuma idan har banyi ba Allah zai iya tsaidani akan haka,
Imara tamkar 'ya take a wajena, ita ɗin AMANATA ce, nauyinta a wuyana ya rayata
saboda haka ki daina min godiya dan Allah" murmushi tayi ta ce"duk da dai bansan
alaƙarka da ita ba, zanyi shaidarka a ko'ina, idan alƙawari ka yiwa wani zaka kula
da ita to tabbas ka cika alƙawarinka, idan kuma ita ɗin jininka ce to ka kasance
ɗan uwa nagari, Allah ya albarkaci rayuwarka" ajiyar zuciya ya sauke ya ce"Ameen ya
rabbi, idan kin shiga ki ce tazo" to ta ce masa sannan ta karɓi kayan ta shiga
gidan. Zaune ta hangeta kan tabarma tana shassheƙar kuka, ƙarasawa tayi ta zauna
kan kujerar dake gefen tabarmar tana kallonta ta ce"to ɓaure sarkin kuka, ki je ana
kiranki" kallonta tayi tana kuka ta ce"ni bazani ba, wlh ba zani ba, na daina kula
shi, shima ya daina kulani, babu ruwana dashi" murmushi granny ta yi ta
ce"shikenan, ya zo da abin daɗi ya ce kije zai baki chocolate" da sauri ta kalleta
sai kuma ta ce"amma wlh bazan masa magana ba, kawai karɓowa zanyi na tawo gida, na
daina kula shi" jinjina kai tayi ta ce"je ki to" tashi ta yi ta fice daga gidan.
# *Bestnovel*
# *heart touching 💔*
# *IMARA 💋*
# *Dodo*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
*Chapter 21-22*
Tsaye ta sameshi jikin motarsa yana danna wayar dake hannunsa, ƙarasawa tayi daf
dashi ta miƙa hannunta ɗaya ta ɗauke kanta tana kallon gefe sai jijjiga ƙafa take
yi, juyowa ya yi ya kalleta sannan ya kalli hannun nata, ɗan murmushi ya yi ya
ɗauke kansa ya cigaba da danna wayar. Shirun da Imara taji ya sanya ta ɗan juyo
tana kallonsa ta gefen ido, ganin kamar ma bai san tana wajen ba yasa ta juyo gaba
ɗaya tana turo baki ta ce "ka bani zan tafi gida" ta miƙa masa hannunta, wayarsa ya
zura aljihu ya juyo yana kallonta, kwaɓe fuska Imara tayi tana kallonsa, hannunsa
ya harɗe a ƙirji yana kallonta ya ce"lafiya?" kamar zatayi kuka ta ce"chocolate ɗin
zaka bani, ni tafiya gida zan yi ka bani kawai"
"Who stop u?", ya furta yana kafeta da idanunsa dake cikin glasses, wani kwarjini
ya yi mata wanda ya hanata sake faɗar wata kalmar, ta juya zata koma gida. Taku
ɗaya ya yi ya kamo hannunta ya dawo da ita gabansa yana kallonta ya ce"sarkin
rigima!" shiru tayi masa tana sake haɗe fuska tamau ita bata yarda ba fushi take
dashi, murmushi ya yi ya ce"shikenan yi murmushi na baki wani abu" kallonsa tayi
hawaye ya zubo idanunta, hannunsa ya sanya ya share mata hawayen yana cewa"wannan
hawayen naki daraja gare su, ki daina bari suna zuba koda yaushe" faɗawa jikinsa
tayi ta fashe da kuka, murmushi ya yi kawai ya shiga patting bayanta har saida yaga
tayi shiru. Ɗago kanta tayi tana kallonsa bakinta na rawa ta ce
"To ba kai bane, ka ce ka daina kulani, me nayi maka?, kuma kasan banida kowa, ni
Daddyna ya mutu, banida ƙawaye, ni kaɗai nake zama sai Granny, na daina kulaka
nima, babu ruwana da kai" ta dunƙule hannunta tana dukansa, sake rungumeta ya yi
yana dariya ya ce"shikenan I'm sorry babyn Dodonta kiyi haƙuri kinji, yanzu ina
kulaki, bazan sake faɗa dake ba, kinsan me?" Girgiza kanta tayi har sannan tana
ƙirjinsa sai sauke numfashi take a hankali, murmushi ya yi ya ce "Monday zaki fara
zuwa school" wani tsalle tayi tana barin jikinsa, ta tafi ƙofar gidansu ta tsaya ta
rufe bakinta tana dariya, kallonta ya shiga yi yana murmushi shima, dawowa gabansa
tayi ta ce"ina kayana?, ka ara kudin?" shiru ya yi yana kallonta ta langwaɓar da
kai ta ce" kake kallona haka?, to wa zai dinga bani kuɗin makaranta?, kaga banida
kuɗi" numfasawa ya yi ya ce "ke zaki dinga biya mana" shiru tayi sai kuma ta ce"ai
kasan banida kuɗi, duk ka ranta min, kuma ka siyomin abinci, ni da abinci nake
tafiya makaranta" murmushi ya yi ya ce" Tom duk za'a baki," daga haka ya buɗe back
seat na motar ya ciro wasu ledoji, miƙa mata ya yi ta karɓa cikin sanyin murya ta
ce"Nagode sosai " harararta ya yi ya ce"bar nan" murmushi tayi sannan ta juya ta
shige gida da sauri, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya shiga motar ya bar unguwar.
*Monday*
7:15am
Tsaye take ƙofar ɗakin hannunta riƙe da wani ƙaramin mudubi tana kallon fuskarta,
Granny ne ce ta fito tana murmushi ta kalleta ta ce"oh, su oh'oh za'a fara zuwa
makaranta" murmushi Imara tayi tana kallon mudubin ta ce"ya kika ganni?, nayi
kyau?" jinjina kai granny ta yi ta ce"ai daman kinada kyanki, kin yi kyau Masha
Allah" dariya ta yi ta ce"yawwa, kuma granny naga har yanzu bai zo ba?, ko ba shine
zai kai ni ba?" Dafe kai tayi ta ce"yau naga hayyatacciyar yarinya, ba sai ya gama
abin da yake ba zai zo?" langwaɓar da kanta tayi ta ce"ai sauri nake ne"
"Sai ki tashi sama ai" granny ta ce tana barin wajen, turo baki tayi ta ajiye
mudubin ta shiga gyara akwatin dake gabanta, ganin har ta gama bai zo ba yasa ta
koma kan tabarma ta zauna ta zuba uban tagumi kamar wacce aka yiwa mutuwa. Ƙarfe
bakwai da rabi daidai granny ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da rediyo tana jin
kanun labarai, wani abu ne ya zo ya tokarewa Imara a ƙirji ganin kamar ma granny
bata damu da lamarin nata ba, kujera granny ta samu ta zauna tana sauraren
labaranta hankali kwance.
Kwantawa tayi a kan tabarmar ta shiga burgima tana kuka, kallonta granny ta shiga
yi baki buɗe, tana ƙoƙarin yin magana aka yi sallama aka shigo. Tsam ta tashi zaune
ta shiga share hawayen nata, tabarma granny ta shinfiɗa masa ya zauna bayan sun
gaisa ya ce"me aka mata kuma?" jiki a sanyaye granny ta ce"wai saboda baka zo ba
shine take kuka" kallonta ya yi yaga tana share hawaye, murmushi ya yi ya ce "in
dai makaranta ce sai ta gundireki, keda zaki je ki zauna a can?" turo baki tayi
bata ce komai ba, suka yi sallama da Granny sannan ya tashi ya fita. Tashi itama
tayi tana kallon granny, da gudu ta faɗa jikinta tana kuka, granny was couldn't
help it but cry, gaba ɗaya tausayin yarinyar ya kamata, tunanin yanda zatayi rayuwa
a makaranta na tsawon wani lokaci. Saida sukayi mai isarsu sannan ta rakota har
bakin mota, ta shiga tana ɗaga musu hannu har suka ɓacewa ganinta.
Murmushi ya yi yana kallonta ganin yanda ta fara mitsi mitsi da idanu ya ce"ohya
tafi mana" turo baki tayi tana shirin yin kuka ta ce "ni anan zaka barni?" jinjina
mata kai ya yi yana zura wayarsa a aljihu ya ce "Eh mana, kiyi karatu da kyau kin
ji ƴar albarka" fashewa tayi da kuka ta rufe fuskarta da hijab ɗin jikinta,
kallonta Directorn ya yi yana murmushi ya ce"ƴar Baba me rigima, ke da zaki shiga
secondary school kece kike kuka?, ai murna zaki yi, babu abin da za'a yi miki a
school ɗin nan, zaki yi rayuwarki kamar a gida, kuma ai time to time zai dinga kawo
miki ziyara" tashi tayi ta fice daga office ɗin tana kuka, tashi shima ya yi yabi
bayanta. Tsaye ya sameta jikin wani block ta rufe fuskarta sai kuka take, ƙarasawa
ya yi, ya sanya hannu ya tallafi fuskarta yana murmushi ya ce"bansan rigima fa
Imara, school ɗin ne kuma baki so yanzu?" cikin shassheƙar kuka ta ce"ni ba school
ce bana so ba, ni bazan kwana ba, ni a gida zan dinga kwana, banason boarding, ka
maidani gida Dodo, wlh indai nan ne banaso to" shiru ya yi yana tunanin hanyar da
zai ɓullo mata, above 5mins kafin y ce" idan har baki yarda kin zauna a school ɗin
nan ba, bazan sake zuwa inda kike ba, ba zaki sake ganina ba har abada, zan rabu
dake ne" ɗago runannun idanunta tayi ta zuba masa ido, ɗauken kansa ya yi yana
kallon gefe ya ce"shige mu je" goge hawayenta tayi ta yi gaba, numfasawa ya yi
sannan yabi bayanta, ga mamakinsa sai yaga tayi hanyar inda aka kwatanta musu
hostel ɗin nasu, cigaba ya yi da bin ta har suka je ƙofar hostel ɗin sannan ya ga
ta tsaya. Kallonta ya shiga yi ta juyo a hankali tana sake goge idanunta ta ce"ka
tafi kawai, zan zauna anan, koda bazan ji daɗi ba, zan yi karatu mai yawa kodan
nasamu na biyaka kuɗin ka, zan zauna karka damu, Daddyna kafin ya mutu ya cemin na
karɓi duk abin da ya zo min a rayuwa, ta iya yiwuwa wannan shine Alkhairin nawa, in
sha Allah zan karbe shi hannu bibbiyu" . Tunda ta fara magana yake bin ta da kallo,
kalamanta sun fi ƙarfin shekarunta, tanada kaifin basira sosai kuma ta iya faɗar
magana, ya ɗan nisa kafin ya ce"idan kinga baki son makarantar nan sai na sauya
miki Imara" murmushi tayi mai haɗe da hawaye ta ce"Karka damu kanka, zan zauna
anan, Nagode sosai" ba dan ransa ya so ba, sai dan baya son yana dinga ja in ja da
ƙaramar yarinya ya yi murmushi ya ce"shikenan, kiyi karatu da kyau kinji IMARA "
jinjina masa kai tayi tana murmushin itama. Sallama suka yi ya bar makarantar ita
kuma ta shiga hostel ɗin nasu. Tun daga wannan ranar Imara ta maida hankalinta kan
karatu, duk wani abu da za'a yi na cigaban makaranta zaka sameta a gaba, hatta
malamai saida suka shaidata akan wannan, saidai batada ƙawa ko guda ɗaya, rayuwarta
take ita kaɗai batasan mene ne zama ayi hira da ƙawaye ba, iya ka cinta da ƙawa a
gaisa. Tun daga wannan ranar kuma Dodonta bai sake zuwa ba, tun tana saka ran zata
ganshi har ta fara cirewa, saidai duk sanda ta samu dama ta zauna tayi kuka, dukda
bata taɓa rasa abun buƙata ba, dan duk wani abu wanda zata buƙata da ma wanda bai
zama dole ba saida ya wakilta wanda zai dinga bata, lokaci zuwa lokaci granny ta
kan kawo mata ziyara ta tawo mata da wani abun itama. A haka rayuwa ta cigaba da
garawa mintuna na shuɗewa yi zuwa awanni, awanni na shuɗewa i zuwa kwanaki, kwanaki
na shuɗewa i zuwa watanni, watanni na shuɗewa i zuwa shekaru har Allah ya kawota
ajin ƙarshe, kuma satin ƙarshe.
***Zaune suke a ƙasan wani block wasu suna riƙe da wayoyi, wasu kuma suna faman
hira, Imara kuwa na can gefe kusada wasu ciyayi ta zauna, tunani ne fal ranta, babu
abin da take marmari sai komawa gida, Allah Allah take su ƙarasa papern yau wacce
ta kasance catering craft ce ta koma gida, tana cikin wannan tunanin ta zo ta
dafata. Zama tayi gefenta tana murmushi ta ce"Mrs so silent, ke koda yaushe shiru
abin ki?, yau fa zamu yi candy amma kin kasa sakar jikin ki da kowa?, kina gani
anata ɗaukan pictures an zo da zafafan wayoyi amma ke kina nan zaune kina tunani,
wai meke damunki ne?" ɗan murmushi Imara tayi cikin wata daddaɗar murya ta fara
magana
"Ni banga aibu da na zauna ni kaɗai ba, beside ma kinsan ni I'm not familiar with
people, nafison na zauna ni kaɗai a kammala exams muyi assembly na tafi gida" taɓe
baki Fahima tayi ta ce"taɓ, kina koko, bar ma wannan, sai yaushe zaki bawa brother
na dama ne Imara?, kinsan yanda yake son ki kuwa?, wlh mun kasa gane kan yaya
basheer saboda ke, kowace mace sai ya ce bata yi masa ba, kinsan daman shi a
tsarinsa yana son auren mata kyakkyawa, irin shuwa haka, kema kuma gaki da kyau
kamar balarabiya, fatan dai ba wani kika rigada kika mallakawa zuciyar taki ba, dan
nasan babu wani namiji da zai ganki ya gyale", kallon Fahima kawai tayi ta ɗauke
kanta tana wasada fingers ɗinta wanda suka kasance dogaye masu kyau, sanin halinta
yasa Fahima tayi dariya ta ce"to bebiya, tunda ba zaki yi magana sai ki tashi muje
an kawo paper" "tom, mu je" taji Imara ta furta bayan ta miƙe tsaye, girgiza kai
kawai tayi ta ce"Allah ya shirye ki"
12:45pm
Shiru wajen assembly ɗin ya ɗauka kasancewar Directorn da aka sauya mace ce kuma
mafaɗaciya, bayan ta kammala jawabai aka fara kiran ɗaliban da suka kasance masu
hazaƙa a cikin makaranta. Sunan Head girl aka fara kira wato Imara Ahmad, tafi
wajen ya ɗauka wasu na fito, kowa ya yarda Imara ta cancanci girmamawa daga
makaranta, bayan an bata kyaututtuka aka yi musu hoto da malamai sannan aka sallami
kowa. A bakin gate kowa ya samu danginsa sun zo tafiya dashi, da idanu Imara ta
bisu tana tunawa da Daddynta ta tabbata da yana raye shine zai fara zuwa kafin uban
kowace Yarinya,
A ɗan firgice ta juya, tsaye yake cikin wasu kananan kaya na riga da wando ya sanya
glasses baƙi a idanunsa, ɗan dogon namiji ne amma bashida haske saidai kana ganin
fatar tasa kasan a wuce yake, ganin kamar ta ɗan yi nisa yasa ya kyasta hannunsa,
kallonsa Imara tayi sai kuma ta ɗauke kai, murmushi ya yi ya ce"ko bakya magana ne
Imara?" ɗan sunkuyawa tayi ta ce"ina yini" murmushi ya yi ya ce"lafiya klao, an
gama exams lafiya?" "Alhamdulillah" ta furta a gajerce. Fahima ce ta ƙaraso gurin
tana murmushi ta ce"Yaya mu tafi na matsu naga Mommy" kallonta ya yi ya ce"Tom yar
gidan Mommy, mu tafi mu bar ƙawar taki?" kallon Imara tayi ta ce"haba mu tafi tare
sai mu kai ta gida" ta jawo hannun Imara ta ce"muje friend" girgiza kai Imara tayi
tana sake ƙanƙame gifts ɗin hannunta ta ce"no zan tari napep ya kaini kawai ku je,
Nagode" harararta Fahima ta yi ta ce" dalla banason irin haka, ki shige muje na ce"
murmushi kawai Imara tayi dan idan batayi niyyar yin abu ba babu wanda ya isa ya
sanya ta tayi, ganin ta cake yasa Basheer ya ce"rabu da ita Imara, saboda Allah
shiga na sauke ki, karki daɗe baki je gida ba, ko bakison kiga relatives naki ne?"
gyaɗa masa kai kawai tayi sannan ta bude motar ta shiga, a boot aka sanya trolley
ɗin nasu sannan suka bar makarantar.
# *Bestnovel*
# *IMARA 💋*
# *Dodo*
# *Granny*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
Chapter 23-24
A ƙofar gidansu ya yi parking, ya kashe motar ya juyo yana kallonta fuskarsa ɗauke
da murmushi. Haɗe gifts ɗinta tayi tana ƙoƙarin buɗe motar ya ce"a'a, ko sallama
babu zaki tafi?" hannunta akan handle ɗin ƙofar ta ce"Nagode Sosai Allah ya saka da
Alkhairi" ɗan murmushi ya yi ya ce"shikenan, tunda naga gidan zan zo" da sauri ta
kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta. Fahima dake kallonsu tun ɗazu ta ce"tom
friend, bye, Allah ya ƙaddara saduwarmu" murmushi Imara tayi tana kallonta ta
ce"Nagode sosai Fahima sai anjima" murmushi suka yi a tare ta buɗe motar ta sauka.
Sauka shima yayi ya ciro mata trolley ɗinta yana murmushi ya ce"sai na zo" ɗan
murmushi tayi baya bata ce komai ba ta juya ta shige gida.
Da ɗan saurinta ta shiga gidan tana murmushi ta ce"Granny! Granny! Granny!, ki fito
na dawo, I'm back" shiru Imara taji hakan yasa ta ɗan haɗe rai ta ce"grannyyy! kina
ina?" Ajiye kayan hannunta tayi akan tabarma sannan ta shige ɗakin da sauri
"Granny ina ta kiranki kina bacci, ko zuwa ki ɗaukeni ba kiyi ba" tafada tana
faɗawa kan katifar, murmushi tayi ta shiga janye bargon data rufa tana cewa "a
wannan zafin kike rufa granny, gaskiya..." Kasa ƙarasa maganar tayi saboda ganin
yanda Granny ke rawar sanyi, a firgice ta ce"subhanallahi, bakida lafiya ne Granny,
zazzaɓi kike ne?" hannunta Granny ta kama jikinta na rawa ta ce"Fatima" kallonta
Imara tayi tana hawaye ta ce"na'am Granny, sannu, bari na kira likita ya duba ki,
ko muje asibiti ne?" ɗan murmushi tayi ta ce"ai ciwona bana asibiti bane Imara,
kedai ki dinga yimin addu'a kinji, ki daina wannan kukan" tafada tana share mata
hawaye, riƙe hannunta Imara tayi tana girgiza kai ta ce"a'a Granny, wlh bansani ba
ma dana nemi excuse a school nazo, ki tashi muje asibiti dan Allah, ni banason naga
mutum bashida lafiya, barin ma kuma ke, ki tashi Granny" ta miƙe daga kan katifar
ta buɗe kayansu ta ɗauko mata hijabi, kallonta kawai granny take tana murmushi mai
haɗe da hawaye, dawowa Imara tayi ta saka mata ta ɗagota ta ce"Granny tashi mu
tafi, daure kinji" girgiza kanta tayi idanunta na neman rufewa ta ce"a'a Imara,
daina taɓa ni, ciwon dake jikina baya son a taɓa shi, akwai wasu maganganu da
nakeson faɗa miki.
IMARA ki kula da rayuwa ki yarda da duk ƙaddarar data zo miki ba lallai yanzu ki
fahimci abinda yake akwai ba amma tabbas watarana zaki gane abinda nake yawan gaya
miki idan kinada rabo zaki iya haɗuwa da iyayenki idan kuma ubangiji bai ƙadarta ba
to shikenan ke dasu har abada, hannunta ta sanya cikin samirar dake gefenta ta xaro
wata kyakkyawar sarƙa sai kyalli take cikin kakkarwar hannu ta danƙa mata cikin
nata siririn hannun tana kallonta da idanunta wanda suka fara rufewa ta ce"wannan
ita kaɗai ce ragowar abinda yake mallakinki ki kula da ita karki bari tabar wuyanki
IMARA domin ita ɗin ƙaddararki ce ki kul..." Tsit ɗan ƙaramin ɗakin ya ɗauki shiru
na wasu sakwanni kafin Imara ta mayar da idanunta kan mahaifiyar tata ta kalleta da
son sanin abinda ya sanya tayi shiru saidai yanda taga idanunta sun ƙafe ya sanya
ta saki wani razanannen ihu, sakinta Imara tayi ta shiga girgiza kai bakinta na
rawa ta ce"granny banason irin wannan wasan, ki bari, ni ki daina yimin, ki tashi
kawai wlh" jin tayi shiru bata ce komai ba yasa ta tashi a firgice tayi waje.
Makotansu gidan Baba Hansatu ta shiga, zaune ta sameta tana yanka kuɓewa ta ƙarasa
cikin tashin hankali ta ce"Baba zo muje ki ganta, granny ce, granny Baba" tashi
Baba Hansatu tayi ta ce"mene ya faru?" Waje Imara tayi tana ihu, mayafi ta zara
akan igiya tayi waje ƙafarta babu ko takalmi.
Zanin dake gefenta Baba Hansatu ta sanya ta rufe fuskarta, wata zabura Imara tayi
ta ƙarasa wajen ta yaye zanin ta rungume granny jikinta sai wata irin kyarma yake,
hannunta Baba Hansatu ta kama tana kuka ta ce"kiyi haƙuri Imara, Allah ya yiwa
Asiya rasuwa, daman tunda kika tafi makaranta ciwo ya zo ya ci ƙarfinta, gashi kuma
yanzu ya yi ajalinta kiyi mata addu'a kawai" girgiza kai Imara ta shiga yi tana
sauke ajiyar zuciya dan kuka ma ya gagara ta yisa, tashi Baba Hansatu tayi ta fita
dan faɗawa sauran maƙota su shigo ayi mata suttura a kaita gidanta na gaskiya.
*Days later*
Zaune take kan tabarma a tsakar gidan, ta cure jikinta waje guda, tunanine fal
zuciyarta, tun ranar da aka kai granny ƙabari bata sake samun nutsuwa ba, shikenan
ita yanzu batada kowa, kowa ya tafi ya barta, babu Daddynta babu Umma, babu granny
babu Dodo, kowa ya gudu ya barta, ita kaɗai, kuka ne ya ci ƙarfinta ta kifa kanta
tana yi babu ƙaƙƙautawa. Sallama aka yi ta ɗago kanta ba tareda ta amsa ba, kwanan
abinci ta ajiye mata ta ce"gashi nan in ji baba ta ce a kawo miki" kallon kwanon
abincin tayi sai kuma ta kalli yarinyar ta sake sunkuyar da kanta, girgiza kai
Asabe tayi ta juya ta fice daga gidan. Haka Imara ta cigaba da rayuwa a cikin gidan
ba tareda kowa ba, babu wani mai ɗauke mata kewa ko kuma ya yi hira da ita, gaba
ɗaya ta rame saboda damuwa da tayi mata yawa, a haka har akayi arba'in ɗin mutuwar
Granny.
Tashi tayi babu ruwa a gidan dan famfon nasu ya daina yi, hakan yasa ta ɗauki
bokiti dan ta samo wanda zata yi amfani dashi, tafiya kawai take ba tareda tana
kallon gabanta ba, tunani ya yi mata yawa, bata banbance a gida take ko kuma a
hanya. Duk irin horn ɗin da suke mata bata ji ba, wani wawan burki yaja dan sauran
kaɗan ya kaɗeta, sai a sannan ta dawo cikin hankalinta ta kalli motar dake gabanta.
Kallonsa ɗaya na cikin motar ya yi cikin harshen larabci ya ce"lafiya dai?" kashe
motar ya yi bai ce masa komai ba ya sauka daga motar, ƙarasawa wajenta ya yi ta ɗan
kalleshi a rikice ta ce" I'm sorry dan Allah ban ganku ba" shiru taji ya yi yasa ta
sunkuyar da kanta, fitowa ɗayan ya yi yana kallonsa ya ce "wai Maheer mene haka ka
manta abubuwan dake gabanmu ne?" ko ta kansa Maheer bai bi ba, sai ma sake kallonta
da yake yana murmushi, cikin sanyin murya ya ce"sannunki" kallonsa tayi ta
ce"yawwa, kuyi haƙuri na ɓata muku lokaci" ta faɗa tana kallonsa, murmushi ya yi ya
ce" ba komai yarinya, ina zaki je haka?" kallon bokitin hannunta tayi ta ce"ruwa
zan ɗan ɗebo" shiru ya yi sai kuma ya ce"ɗebo ruwa kuma da kanki?" jinjina masa kai
tayi dan maganar ta fara damunta. Murmushi ya yi ya ce"anyway, I'm Maheer bin Fahad
al-kuwari, mun zo aiki ne daga Qatar kuma naji ina sonki idan babu damuwa zan
aureki" da sauri Imara ta kalleshi sai kuma ta ɗauke kanta tana wasada fingers
ɗinta, jin bata ce komai ba yasa ya ce"kefa ya sunanki?, ina ne gidanku?, bakiyi
kamada yar nan garin ba kodai kin zo hutu ne?" ɗan murmushi tayi ta ce"a'a anan
nake, gidanmu yana can baya babu nisa" numfasawa ya yi ya ce"muje naga gidan to, ki
bar ɗiban ruwan za'a kawo muku" toh kawai ta ce dashi sannan tayi gaba yana bin ta
a baya. Kallonsa Tareeq ya yi sai kuma ya girgiza kai ya biyo su. A ƙofar gidan ta
tsaya ta ce"nan ne gidanmu, amma babu kowa a ciki sai ni kaɗai" dan waro idanu ya
yi ya ce"meyasa?, ko sunyi tafiya ne?" gyaɗa masa kai tayi saboda kukan daya tawo
mata ta shige gidan ba tareda ta sake cewa komai ba. Da idanu ya bita har ta shige
sai kuma ya juyo ya kalli Tareeq, harararsa ya yi ya ce"ai sai ka shige mu tafi ko,
nasan meyasa ka biyota ai, koni nayi mamaki sosai, kamar Katalina fa" ɗan haɗe rai
ya yi ya ce"bansan ana kiran sunanta ka sani, zan samo information ɗin yarinyar nan
da ita zan koma Qatar" tuntsirewa da dariya Tareeq ya yi ya ce"idan kaje tanada
wanda take so fa?, har zaka wani yi confirming na tafiya da ita?" tsaki ya yi bai
ce masa komai ba ya hangi wani yaro, da hannu ya yi masa alamar da ya zo yaron ya
zo yana kallonsa ya ce"akwai manya a gidan nan? ya nuna gidan Baba Hansatu, gyaɗa
masa kai yaron ya yi ya ce"Eh akwai, gidan Baba Hansatu ne" ajiyar zuciya ya sauke
ya ce"yawwa Boy, cene ana sallama da ita kaji" da gudu ya bar wajen ya shige gidan.
Kallon Tareeq ya yi ya ɗaga masa gira, dariya kawai ya yi ya cigaba da danna
wayarsa.
Fitowa Baba Hansatu tayi tana wurga idanu ganin jajayen fata, cikin rawar murya ta
ce"sann... sannu yaro, Allah dai yasa ba wani abun nayi ba?" murmushi Maheer ya yi
cikin harshen Hausa wanda ba zaka yi tunanin ya iya ba ya fara magana "ko kaɗan
bakiyi laifi ba Baba, kawai wasu tambayoyi nake son nayi miki idan babu damuwa"
jinjina kai tayi ta ce "to...to.naji Allah ya sa na sani" jingina ya yi da jikin
wata bishiya yana kallonta ya ce"wannan yarinyar ta gidan nan, wata fara ta cemin
ita kaɗai ce a gidan Inason sanin gaskiya al'amarin" girgiza kai tayi ta ce"Imara
kake nufi kenan, Allah sarki, ita da kakarta ne a gidan to kakar ta mutu, kai
asalima ba wannan ce kakar tata ba, ƙawar kakarta ce, aka kashe iyayenta kakar ta
ɗaukota daga birni to itama aka biyota aka kashe shine ta bawa wannan riƙo kuma
yanzu Allah ya yi mata rasuwa. Ita kaɗai take rayuwa a gidan ko ƙawa batada ta
kammala makarantar sakandire ma" numfasawa ya yi ya ce"Allah sarki, Allah ya
jiƙansu da Rahama, yanzu Baba idan inason aurenta wa zan samu kenan?" Zaro idanu
tayi ta ce"aurenta zaka yi?" Gyaɗa mata kai ya yi ta ce"da kuwa ka taimaka mata,
akwai mijina sai ya zamar mata waliyyi kai kuma ka kawo naka waliyyin a ɗaura
auren" murmushi ya yi ya ce"ai kuwa da na gode sosai in sha Allah zuwa anjima zamu
dawo" jinjina masa kai tayi tana murmushi ta ce"To Allah ya kaimu lafiya, an gode
sosai" kuɗin Nigeria Tareeq ya zaro ya miƙa mata bandir biyu, a kiɗime ta amshi
kuɗin jikinta na ɓari ta ce"kai kai kai, yaro an gode muku ku kam, meyasa sai
anjima zaku dawo a ɗaura auren?, ai kawai ayi yanzu, malam yana ciki yanzu a ɗaura
ku tafi da ita" murmushi Tareeq ya yi ya ce"tom Baba mun gode Allah ya ƙara girma,
kira shi ɗin" komawa tayi da sauri kamar zata tashi sama, da kallo Tareeq ya bita
sai kuma yayi murmushi.
"Malam!! Malam!! Malam!!" "Na'am" ya furta yana fitowa daga ɗakin, kallonsa tayi ta
ce"malam abun arziki har gida, kalli kaga" ta nuna masa kuɗin dake hannunta,
ganinsa tayi a gabanta ya yi saurin karɓar kuɗin yana juyasu ya ce "Hansatu ina
kika sami wannan maƙudan kuɗaɗen?" dafe haba tayi tana faɗin "kai dai bari malam,
ai arziki Allah ya saukar mana, wannan yarinyar wajen Asiya tazo mana da Alkhairi,
aurenta za'a yi shine aka bani wannan, muje yanzu za'a ɗaura auren kai ne
waliyyinta" naɗe hannun babbar rigar dake jikinsa ya yi ya ce"Allah mai iko, to
muje, kawo a ajiye wannan" ya fita yana tafiya kamar zai fadi.
Anan ƙasan bishiyar aka ɗaura auren Imara da Maheer akan sadaki naira miliyan 1,
Tareeq ne ya ce"ya kamata a kira yarinyar dan a bata sadakinta a hannunta" girgiza
kai Malam ya yi ya ce"a'a, ba sai an kirata ba kawai a bani zan ajiye mata"
murmushi Tareeq ya yi ya ce"ai yanada kyau a sanar da ita sannan ta karɓi haƙƙinta
da kanta" ba dan ya so ba aka aika yaro ya yi kiranta. Fitowa tayi tana sanye da
hijab onion colour, hangosu da tayi yasa ta ɗan tsaya tana waro idanunta, da hannu
Baba y yi mata alama da ta zo ta ƙaraso, cikin sanyin jiki ta ƙarasa wajen murmushi
ya yi yana kallonta ya ce"yawwa ƴar albarka daman kiran ki aka yi a nuna miki
mijinki a kuma baki sadakin ki" cikin rawar murya ta ce"sa...sadaki kuma Baba?,
sadakin wa?, mijin wa?" murmushi ya yi ya ce"wannan bawan Allah ne ya aureki yanzu,
arziki ya zo miki har gida Imara, yanzu ma dashi zaku tafi" girgiza kanta ta shiga
yi sai kuma ta tafi luuu ta fadi ƙasa a sume.
# *Bestnovel*
# *Heart touching 💔*
# *IMARA 💋*
# *Maheer*
# *Nanameera*
# *2025*
08106608363.
https://chat.whatsapp.com/KLWdQLCbhFwJz1pDjuOvYD
*IMARA 💋 💋*
25&26
08106608363
A hankali ta shiga buɗe idanunta, a ɗan firgice ta tashi zaune tana ƙarewa ɗakin
kallo, turo ƙofar ɗakin a kayi, tayi saurin kallon wajen dan ganin wanda zai shigo.
Wata irin bugawa zuciyar Imara tayi sanda tayi ido biyu dashi, ya ƙaraso hannunsa
riƙe da tray. A kan table ɗin dake gefen gadon ya ajiye sannan ya zauna kusada ita
yana kallonta, saurin matsawa tayi muryarta na rawa ta ce"a'a, lafiya?, ina ne
nan?, dan Allah ka mayar dani gidanmu" murmushi Maheer ya yi bai ce komai ba ya
zaro wayarsa yana dannawa a hankali, kallonsa Imara tayi sai kuma ta sake kallon
daƙin, tayi saurin miƙewa tsaye tana kallonsa ta ce"ni ka mayar dani gida, bangane
wannan abun ba" wayarsa ya mayar aljihu ya miƙe tsaye yana kallonta ya ce"ya kamata
ki kwantar da hankalinki Imara, ki zauna ki ci abinci" wani kallo tayi masa ta
ɗauke kanta tana jijjiga ƙafa, murmushi ya yi ya ce "shikenan, zauna ki ci abinci
sai muyi maganar" kallonsa tayi sai kuma ta kalii inda ya ajiye tray ɗin abincin,
yunwa take ji sosai hakan yasa ta nemi waje can gefe dashi ta zauna. Kallonta
Maheer ya yi ya ɗauko tray ɗin ya ajiye mata a gabanta ya juya ya fice daga ɗakin,
da idanu ta bishi sai kuma ta gyara zamanta ta buɗe abincin, Irish potato ne aka
soya shi da kwai sai plantain da akayi garnishing da ita. Tea ta haɗa sannan ta
fara cin abinci. Saida ta cinye komai tas saboda yunwar dake cikinta, ta yi gyatsa.
Kamar jira yake ta gama ci ya shigo ɗakin, wannan karan ya sauya kaya, t-shirt ce
white colour a jikinsa sai wando jins blue colour, kallo ɗaya tayi masa ta sunkuyar
da kanta tana wasa da fingers ɗinta. Ƙarasowa ya yi ya zauna gefenta, ƙamshin
turarensa ya daki hancinta tayi saurin lumshe idanunta, a ɗan firgice ta juyo ganin
yanda ya riƙe hannunta cikin nasa, kallonsa tayi taga murmushi yake, saurin janye
hannun nata tayi tana turo baki ta ce"akan me zaka dinga riƙeni?" Maheer couldn't
help it but smile, above 2mins kafin ya ce"tashi mu je" tana kallon wani wajen
daban ta ce"ina zaka kaini?, gida?" girgiza kansa ya yi ya ce"idan mun je zaki
gani" taɓe baki tayi ta ce"ni to babu inda zanje" ta faɗa tana tura baki gaba.
Murmushi ya yi ya ce"idan bazaki iya tafiya ba sai na ɗaukeki" da sauri ta miƙe
tsaye tana zaro ido ta ce"Allah ya kiyaye" da hannu ya yi mata da su tafi, ta
kalleshi sai kuma ta kalli hanyar, kamar wacce kwai ya fashewa a jiki haka ta fara
tafiya.
A bakin shopping mall ɗin ya yi parking, ta kalli wajen, idan bata manta ba sun
taɓa zuwa wajen da Daddynta, sunkuyar da kanta tayi tana jin wata irin kewa, Allah
sarki rayuwa ta tabbata idan da Daddynta na raye da zuwa yanzu ba wannan ƙaddarar
ce ta afka mata ba, Daddynta bazai taɓa aurar da ita a shekarunta ba. Kallonta
Maheer ya tsaya yana yi ganin kamar bata jin abin da yake cewa, taɓa ya yi tayi
saurin kallonsa sai kuma ta haɗe fuska,
"Meke damunki?"
Shiru tayi masa, ya ce"mu je ko?" sauka tayi daga motar ta tsaya tana jiransa,
kashe motar ya yi ya fito yana kallonta ya ce"muje" tafiya ta fara yi tana
kallonsa, suna shiga ya nemi kujera ya zauna, ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ce
tazo tana kallonsa ta ce"u are welcome sir" jinjina mata kai ya yi ta ce" me ake
so?" Imara ya nuna mata ya ce "kaya wanda zai yi mata nakeson ki haɗa" cikin
girmamawa ta ce"okay sir, ta kalli Imara ta ce"mu je Madam" kallonsa Imara tayi ya
gyaɗa mata kai sannan tabi bayanta. Kaya sosai aka siya mata masu tsada kafin su
bar mall ɗin, a wani restaurant ya tsaya ya yi parking yana kallonta ya ce"mu je
kici abinci" da sauri ta kalleshi sai kuma ta ɗauke kanta tana kallon titi ta
ce"bayan wanda naci, ni bana jin yunwa" murmushi Maheer ya yi ya ce"ai tunda rana
kika ci abinci, kuma kinga yanzu magrib akayi"
"Nidai a ƙoshe nake, naga ɗazu naci abincin, kawai ka mayar dani gida mana" ta faɗa
ba tareda ta kalli inda yake ba. Bai sake magana ba ya sauka daga motar kai tsaye
kuma cikin restaurant ɗin ya nufa, binsa tayi da harara a ƙufule ta ce"aikin banza,
ko ana dole" .
Bayan minti goma Maheer ya fito hannunsa riƙe da ledoji guda biyu, kallo ɗaya Imara
tayi masa ta ɗauke idanunta, har suka je gida babu wanda ya sake magana a cikinsu.
Bayan ya yi parking ya kalleta ya ce"ki shiga ciki zan je na dawo" bata ce masa
komai ba ta buɗe handle ɗin motar ta sauka, ledojin daya miƙo mata ta kalla sai
kuma ta ce"amma nace maka na ƙoshi ko?" murmushi ya yi ya ce"ai ba cewa nayi ki ci
ba, ki shiga dashi kawai" ɗan tura baki ta yi sannan ta amsa ta juya ta shige
gidan. Da idanu Maheer ya bita sai kuma ya girgiza kansa fuskarsa fal murmushi ya
yiwa motar key ya bar gidan.
Imara nashiga ta wuce sama kai tsaye, ɗakin da ta zauna ɗazu nan ta shiga. Ta ajiye
veil ɗinta kan gadon sannan ta shige toilet ta ɗauro alwala, tana fitowa ta tsaya
jikin mudubi tana kallon veil ɗin data ajiye, ya yi ƙarami da sallah hakan yasa ta
buɗe wardrobe ɗin dake ɗakin ko zata samu wani abu, ɗan kwaɓe fuska tayi ganin babu
komai a ciki, ta koma ta zauna ta zuba uban tagumi.
Sai bayan sallahr magrib sannan Maheer ya shigo gidan, time ɗin tana zaune bayan ta
idar da sallah da veil ɗin nata, sallama ya yi ya turo ƙofar ya shigo, a ciki ta
amsa sallamar ya ƙaraso ya zauna gefenta yana kallonta ya ce"tashu muje ƙasa kici
abinci" kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta ce "sai yaushe zaka mayar dani
gidanmu?" numfasawa ya yi ya ce "Imara Inason kibar wannan maganar, idan Allah ya
kaimu next week zamu tafi gida, kinsan yanzu ke matata ce, saboda haka ni ne nakeda
ikon tafiya dake duk inda zani, kuma bakida wani waje sai inda na ajiye ki, nayi
miki alƙawarin zan kula da ke fiye da yanda kike tunani. Zan kai ki cikin ahalina,
zan zame miki uwa zan zame miki uba, abinda kawai nakeso shine yardar ki" ya
ƙarashe maganar yana dafa hannunta, kallon hannun nata tayi sai kuma ta kalli
fuskarsa, haka kawai ta ji ta yarda da Maheer, ta yi shiru na wasu mintuna sannan
ta ce"meyasa ka aureni?" murmushi Maheer ya yi ya ce"saboda ina sonki" cikin rawar
murya ta ce"zan yarda da kai amma dan Allah karka juyamin baya, karka sakani kuka,
ka ɗaukeni matsayin ƙanwarka wacce ba zaka cutar da ita ba, kaji Yaya!"
Da sauri Maheer ya ɗago ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya kamo hannunta ya riƙe
cikin nasa ya ce"Thank you" ɗan murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma
ta ce"nima nagode" hannunta ya kama ya tashi ya ce"muje ki ci abinci" gyaɗa masa
kai tayi ya nuna mata hanya, tayi gaba ya bita a baya.
Tun daga wannan ranar suke zaune lafiya da Maheer a kullum shaƙuwa ƙara shiga
tsakaninsu take, a haka har suka ƙarasa wannan satin, ranar Lahadi tana zaune bakin
mirror tana gyara kanta ya shigo, ƙarasowa gabanta ya yi yana murmushi ya tsaya a
gefenta yana kallonta ta jikin mudubi, kallonsa itama tayi tana murmushi
"Madam idan kin kammala muna iya tafiya" tashi tsaye tayi bayan ta yi parking
gashin nata ta ce"Eh na shirya" gyaɗa kai ya yi sannan ya kama hannunta suka fita
daga ɗakin. A compound ɗin gidan suka tsaya, ya buɗe mata backseat ta shiga sannan
shima ya shiga driver ya ja motar suka tafi, kai tsaye airport suka shige, not too
long kuma jirgin su ya tashi i zuwa Qatar.
Around 7pm suka shigo fadar, babu kowa a babban parlon hakan yasa kai tsaye yaja
hannunta zuwa ɗakinsa, haɗaɗɗen ɗaki ne wanda yaji kayan more rayuwa, komai na
ɗakin blue colour ne, domin shine favourite colour na Maheer, kallonta ya yi yana
murmushi ya ce"yawwa Katalina shiga kiyi wanka, akwai kayan ki zan ɗebo miki" da
wani irin mamaki Imara ta kalleshi sai kuma tayi murmushi ta ce"yaya manta sunan
nawa kayi?, ko kuma tsokanata kake?" girgiza kai ya yi fuskarsa babu alamar
murmushi saɓanin ɗazu ya ce"akan me zan manta sunan ki?, sunan da kika ji na ambace
ki dashi shine sunan dana zaɓa miki, kuma muddin kina cikin fadar nan shine sunan
da zaki dinga amfani dashi"
Tunda ya fara magana Imara ke kallonsa baki buɗe, kwata-kwata bata gane abinda yake
faɗa, ƙwaƙwalwarta ta tunkushe tunani ya yi mata yawa, ganin yana shirin fita yasa
tayi saurin shan gabansa tana riƙe rigarsa ta ce cikin rawar murya
"Yaya Maheer bangane abinda ka faɗa ba, ka daina yimin irin wannan wasan, tsoro
nakeji, zan daina kula ka wlh, banaso, tsoro nakeji...!" Ta ƙarashe maganar tana
fashewa da kuka, ta rungumeshi, ɗan tsaki Maheer ya yi kafin ya janyeta daga
jikinsa yana kallon fuskarta wacce ta jiƙe da hawaye ya ce"it's better for you to
obey my rules or else..." Ya yi mata gargadi da hannunsa sannan ya fice daga ɗakin.
Zubewa Imara tayi akan tiles ɗin ɗakin, banda tsuma babu abinda jikinta ke yi, wace
irin masifa ce ta tunkarota?, wane hannu ta faɗa?, wace Katalina?, me Maheer ke
nufi?, ko dai mafarki take, tunanin hakan yasa tayi saurin dukan fuskarta idan ma
mafarki take ta farka, amma ga mamakin ta sai taga idanunta biyu. Kifa kanta tayi
bisa gwuiwoyinta ta fashe da wani sabon kukan.
Ƙarfe takwas da rabi Maheer ya buɗe ɗakin ya shigo, zaune ya sameta kan tiles
idanunta sun kumbura, ƙarasawa ya yi ya sanya hannunsa ya ɗagota yana watsa mata
wani kallo ya ce"kee!, ina wasa dake ne?, baki ji abin da na ce miki ba?, kina son
ranki ya ɓaci right?" girgiza kai Imara ta shiga yi ta ce"a'a wlh, tsoro naji yaya,
dan Allah mu koma Jigawa, ka mayar dani gida, tsoro nakeji, bazan iya zama a nan
ba" wani tsaki yaja yana kallonta ya ce"karki sake kiramin sunan wani gari anan, ki
shirya yanzu ki sakko ƙasa, nasan kin iya yaren su, dan basa jin Hausa" juyawa ya
yi ya fita kafin ta buɗe bakinta. Dafe kanta tayi ta jingina da wardrobe cikin wata
raunatacciyar murya ta ce"inna lil lahi wa ina ilayhi raji'un, nashiga uku, wayyo
Allahna, meke faruwa da rayuwata ne?, wace irin masifa nashiga?" Rashin sanin wanda
zai bata waɗannan amsoshin ya sanya ta sake fashewa da wani sabon kukan.
A hankali tafara taka stairs ɗin benan, sanya take da wata Abaya white colour ta
yafa veil ɗin Abayar tana tafiya tana kallon fadar. Daga can gefe taji ance
"Tabarakallah"
A ɗan firgice ta juya, sai kuma ta hangi jama'ar gidan zaune akan dinning table. A
hankali ta ƙarasa bakinta na rawa ta gaishesu cikin harshen larabci, fuska a sake
suka amsa mata musamman Shammah, ta kalleta cikin sakin fuska ta ce"zauna mana" ta
faɗa cikin harshen larabci, cikin sanyin jiki Imara ta zauna ta sunkuyar da kanta,
a hankali ya tura kujerar ya tashi, da sauri suka kalleshi, Immi ta ce"lafiya?" bai
ce mata komai ba ya juya ya bar wajen, da idanu duk suka bi shi, banda Imara wacce
har sannan kanta yake a sunkuye. Girgiza kai Shamma tayi ta cigaba da cin abincin
ta, dakyar Imara taci abincin bayan takurawar da Shamma tayi mata.
12:30am.
Zaune take gefen gadon ta jingina da jikinsa, tunani ne fal zuciyarta, duk da dare
ya yi sosai amma babu alamar bacci a tare da ita, tanada buƙatar ta yi magana da
Maheer. Ta kasa gane abin da yake shirin faruwa da rayuwarta. Tana cikin wannan
tunanin ya shigo ɗakin yana sanye da wasu pyjames black colour, s hankali ta saki
ajiyar zuciya dan har ga Allah taji daɗin shigowar tasa, zama ya yi gefen gadon
yana kallonta, gyara zamanta ta yi, tana ƙoƙarin magana ya ɗaga mata hannu.
"Nasan abinda zaki ce, nasan me za ki tambaya, wane ne ni?, meyasa na aureki?, me
nake nufi dake?. To bar kiji, ni Maheer ne kamar yanda kika sani, kuma ɗa ga Amir
wato Sheikh Fahad bin saleem al-kuwari, na aureki saboda wani dalili, ba lallai
bane na sanar dake, the main thing shine ki yi duk wani abu dana umarce ki, daga
yau ba irin wannan shigar nakeson kiyi ba, kuma daga yau sunanki Katalina a idona
ba IMARA ba, idan har kika kuskura kika ce zaki saɓamin to ba zaki ji daɗin zama
cikin fadar nan ba, saboda haka ki kasance yanda nakeso shine kawai abinda zai
ceceki.
Kallonsa kawai Imara take tana hawaye, cikin rawar murya ta ce"daman ba saboda
Allah ka aureni ba?, daman ƙarya kayimin?, meyasa zaka yaudareni?, meyasa zaka
sanya mini soyyarka a zuciya sannan ka cutar dani?, akan me ka rabo ni da dangina?,
meyasa! meyasa Maheer!!"
Tashi tsaye ya yi yana kallonta ya ce"ke kika ga zaki iya wahalar da kan ki, kina
sona, bakya sona wannan bai dameni ba, abinda nakeso shine kawai abinda nake
aiwatarwa, saboda haka zaɓi ya rage naki, kiyi biyayya ki zauna lafiya. Kuma ma da
kike magana akan na raboki da kasarku, wa kike dashi a ƙasar?, wane gatanki?, zaman
kanki fa kike, ai auranki da nayi taimako ne a gareki, saboda haka ni ba abin
rainawar ki bane, fact.
Da idanu Imara ta bishi har ya ɓacewa ganinta, ta sauke wata nannauyar ajiyar
zuciya, dan kuka ma ya gagareta sai na zuci, komawa tayi ta jingina da gadon tana
numfashi sama sama, kafin kuma ta samu ta fashe da wani raunataccen kuka mai shiga
zuciyar mae sauraro. Yanda Imara taga rana haka taga dare cikin masarautar Udaid
sanda taji anfara kiran sallah asuba ta tashi ta ɗauro alwala ta zauna kan ladduma
tana roƙon Allah ya kawo mata mafita.
A haka ta cigaba da rayuwa a cikin gidan cikin takurawar Maheer, ko kaɗan baya
barinta ta sake, gabaɗaya ta rame kamar ba ita ba, kullum sai zama a ɗaki tana
kuka. Yau ma kamar kullum tana zaune kan kujera cikin ɗakinta ta zuba uban tagumi,
akayi sallama aka shigo, a hankali ta ɗaga kanta jin ba muryar Maheer ba, Ameer da
ta gani ya sanya tayi saurin miƙewa tana ƙaƙalo murmushin ƙarya ta ce"sannu da zuwa
Ameer" lumshe idanunsa ya yi sannan ya buɗe su akanta, cikin rawar baki ta ce"na
manta Ameer ka zauna" gyaɗa mata kai ya yi sannan ya zauna gefen gadonta cikin wata
kamilalliyar murya ya furta
"Bismillah"
Zama Imara tayi itama tana kallonsa ta ce "Ameer lafiya?" kallonta ya yi da dara-
daran idanunsa ya ce"IMARA"
"Na'am Ameer"
Numfasawa ya yi sannan ya ce"nasan zaki yi mamakin abinda zai fito daga bakina, duk
da nima abun ya zo mini a bazata, bansan yaushe ba, bansan kuma dalili ba, amma
naji na kamu da sonki tun ranar dana fara ɗora idanuna akan ki, inaji kamar ba
ranar nafara ganinki ba. Nayi ƙoƙarin ganin na cire tunanin daga raina amma nakasa,
inason ki Imara, ina sonki, soyyaya irin wacce bansan iyakarta ba, duk da ke matar
ɗana Maheer ce amma ina faɗa miki haka, wlh ina sonki har cikin raina"
A ɗimauce Imara ta tashi tsaye tana nuna shi da yatsa amma ta kasa cewa komai, ta
shiga girgiza kanta hawaye na zuba akan fuskarta, tayi saurin dafe kanta tana rusa
kuka, tashi tsaye Ameer ya yi yana kallonta sai kuma ya girgiza kai ya ce"ban faɗa
miki sirrin dake zuciyata dan naga hawayen ki ba Lolo, Inason ki zauna kiyi tunani
akan magana"
Cigaban labari.
Banda kuka babu abinda take yi Mama na taya ta, saida tayi mai isarta sannan ta
ɗago kanta tana kukan ta ce "meyasa Mama?, bayan duk wannan wahalar dana sha ya
rabu dani, duk wanda ya raɓeni a rayuwa da niyyar naji daɗi sai ya tafi ya barni,
kowa baya zama tare dani, nafiso ma na mutu. Ta kalli Mama dake kuka ta ce"dan
Allah Mama ki bani abinda zanci ko nasha na mutu, nagaji da rayuwar, banida kowa,
banida kowa Mamah! Ni marainiya ce, wacce batada mai sonta, duk sun mutu, meyasa ni
nake a raye Mamah?, meyasa!?, dan Allah ki bani abin mutuwa..." Rungumeta Mamah
tayi tana shafa kanta ta ce"karki sake cewa haka Imara, kinada kowa, mu zamu zama
dangin ki, ba za ki sake maraici ba IMARA, ki daina kuka kinji" ta cigaba da shafa
sumar kanta, ajiyar zuciya Abaan ya sauke kafin ya juya ya bar wajen ba tareda ya
shiga ɗakin ba.
# *Heart touching 💔*
# *IMARA💋💋*
# *Nanameera*
# *2025*.
https://chat.whatsapp.com/KLWdQLCbhFwJz1pDjuOvYD
*IMARA 💋💋*
27&28.
08106608363
Around 7pm Mamah ta turo ƙofa ta shigo hannunta ɗauke da tray, da idanu Imara ta
kalleta sai kuma ta sake sunkuyar da kanta. Ƙarasowa Mama ta yi ta zauna gefen
bedside drawer tana kallonta ta ce"ki daina damuwa Imara, ko baki yarda dani ba
ne?" Ɗago idanunta tayi ta kalleta sai kuma ta girgiza kanta cikin sanyin murya ta
ce"na yarda Mamah" shafa kanta tayi ta ce"then ki daina damuwa, banason ganin ɓacin
rai akan fuskarki, nan ma gidanku ne" jinjina kai tayi, Mamah ta ce "kici abinci
gashi nan, idan kin gama sai ki sakko ƙasa wajensu Jadda tana bada labari" to kawai
ta ce tana wasada fingers ɗinta. Kallonta Mamah tayi bata ce komai ba ta tashi ta
fice daga ɗakin. Tana jin ta rufe ƙofar ta ɗago kanta, sai kuma ta sake fashewa da
wani sabon kukan, gabaɗaya zuciyarta ta ƙi aminta da halin da take ciki, gani take
kamar mafarki take wanda zata farka nan bada jimawa ba. Tanason ganin Maheer domin
taji dalilin daya sanya ya saketa, kuma tanason sanin halin da Ameer yake ciki, duk
da yanzu ita a matsayin wacce tayi kisan kai take a wajensu hakan bai sa taji
batasan komawa ba. Sannan zama cikin gidan Mamah ba abu bane mai yiwuwa, dan ta
fuskanci ya'yan gidan basu shirya amsarta a matsayin baƙuwa ba. Wadannan tunanin su
ne suke damunta a koda yaushe, gabaɗaya ta rame kamar ba ita ba. Cigaba da zama
tayi cikin ɗakin tayi har aka kira sallar isha'i ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro
alwala ta fito ta tada sallah.
Zaune suke sunyi da'ira a falon sai kallon Jadda suke wacce take faman basu
labarurruka masu abun dariya, Nanah ce ta tashi daga gefenta tana miƙe ƙafarta ta
ce"kai Jadda kuma to ya aka yi ta yarda" murmushi tayi ta ce"ke dalla to ya'yan
yanzu da sun ji daɗin gidan miji mantawa suke da abin da ya faru, tuni ta haƙura ta
zauna" tuntsirewa suka yi da dariya. Daga bakin ƙofa suka ji an ce
A firgice suka kalli inda yake sai kuma suka sunkuyar da kansu, shigowa ya yi yana
sanye da jallabiya hannunsa riƙe da counter irinta zamani yana ja, kallonsa Jadda
tayi sai kuma ta taɓe baki tana kallon gefe ta ce"Allah na tuba mutum sai baƙin
hali ya ajiye, banda haka ina ruwansa da jikokina. Banza Abaan ya yi mata ba dan
bai ji abin da ta ce ba, sai dan baya son ya shiga harkarta. Buɗe ƙofar parlon
akayi suka shigo bakinsu ɗauke da sallama, sanye suke duk da jallabiya da alama
daga masallaci suke shi ya riga su yo gaba. Zama Abbiey ya yi kan cushion yana
kallonsa ya ce"Muhammad lafiya dai?" yana shafa gemunsa ya ce"ba komai Abbiey"
"Yo jaraba ce ta ishe shi, yaro ya girma ya zama babban mutum yana shirin zama
tuzuru bai yi aure ba, sa'anninsa duk sun ajiye iyali shi yana nan sai zama a gidan
uba, ana dafa abinci ana sammasa, sai shegen girman kai da faɗin zuciya. "
Jadda tayi maganar tana harararsa. Murmushi Abbiey ya yi ya kalleshi, ba zaka taɓa
cewa da Abaan take magana ba, domin idanunsa a lumshe suke, girgiza kai ya yi ya
kalli Jadda ya ce"to ay Jadda dan mutum ya girma ba shine yake nufin sai ya yi aure
ba, duk da muna son muga ya yi auren amma dole sai mun yi masa uzuri tunda ba'a san
abinda ya hana shi ba. Kame haɓa tayi tana firfito da idanu waje ta ce"aaa wannan
rashin adalci ne gaskiya, ka daina haka, wane irin uzuri?, kana goyan bayan ɗanka
kawai, amma dai wannan yaron yafi ƙarfin ace ayi masa uzuri." Hawaye ta shiga
gogewa da gefen rigarta tana cewa
"Kawai dai so yake har sai Allah ya ɗauki raina sannan, bayason ya yi aure na kalla
ya'yansa, rashin yin aurensa yasa babu wani a cikin ƙannensa da yake da niyyar yin
aure"
Sai a sannan ya buɗe idanunsa wanda suka sauya launi zuwa jaa ya zuba mata.
Murmushi Adeel ya yi ya ce"haba old woman karki wani damu, idan shi bai yi aure ba,
ni nakusa yi, zakiga ya'ya na, dan yaya bai yi aure yanzu ba hakan ba yana nufin ba
zai yi bane, komai a lokacine" ya ƙarashe maganar yana dariya. Wata uwar harara ta
maka masa cikin hayaƙi take cewa"to tattabara, daga an yi maganar aure ya wani fara
washe baki, saboda masifa ta masa yawa. To a hir ɗinka ko zaka ruɓe ba zaka yi aure
ba sai yayanka ya yi. Harda wani washe min baki"
Wani sassanyan hawaye ne ya ziraro kan fuskarta, ji tayi dama ace ita ce take zaune
cikin yan'uwan ta irin haka, yanayin yanda suke zaune suke nishadi sai taji ya
burgeta.
"Imara"
Da sauri ta juyo sai kuma ta goge fuskarta, hannunta Mamah ta kama taji ɗumi hakan
yasa ta taɓa wuyanta. Zafi sosai taji alamar zazzaɓi mai zafi. Cikin sanyin murya
ta ce"Imara meya faru?, kukan me kike?" Murmushi tayi tana riƙe hannun Mamah ta
ce"babu komai Mamah, kawai naji ina ma ni ce" murmushi Mamah tayi ta ce"zo muje ki
zauna".
Kallonsu Jadda ta shiga yi har suka ƙaraso wajen, zatayi magana Abbiey ya ce"Imara
zo ki zauna anan" da sauri ta kalleshi sai kuma ta ƙarasa inda ya nuna mata ta
zauna a ƙasa, girgiza kai ya yi ya ce"no tashi ki zauna anan" girgiza kanta tayi ta
ce"a'a zan zauna anan Abbiey" hannunta Abbiey ya kama ya ɗagota ta zauna kan
kujerar dake kusada tashi. Tunda Mamah ta bashi labarinta yake matuƙar tausaya
mata, musamman daya kalli yarinya ce ƙarama, wacce bata shige ace tana makaranta
tana karatu yanzu ba, amma ta zama bazawara. Kallon Umaima Mamah tayi ta ce"ke ku
tashi kuje kuyi sallah, dan na tabbata bakuyi ba kuna nan kuna hira" tashi suka yi
Nana ta ce" ni fa Mamah bari nayi idan zan kwanta sai nayi" wata harara tayi mata
daya sanya ta shigewa ba tareda ta sake cewa komai ba. Jadda ce ta kalli Abbiey ta
ce"ni bangane wannan al'amari ba, wannan yarinyar kuma daga ina?, tun a jirgi muke
tafe tare" murmushi Abbiey ya yi ya ce"baƙuwarmu ce Jadda" taɓe baki tayi ta
ce"too, Allah ya kyauta". Mamah ce ta kalli Abaan ta ce"doctor ka sama mata magani,
tun jiya take zazzaɓi kuma baya sauka" tashi ya yi ya shige ciki ba tare da ya amsa
ba, lura da abin da yake nufi yasa Mamah ta kalli Imara ta ce"je ki ya baki magani
dear" tashi Imara tayi jiki a sanyaye tabi bayansa. Saida ta bar wajen Jadda ta
kalli Mamah ta ce" wace Irin rayuwa ce wannan haka?, ta bishi ina?, akai ta asibiti
mana" murmushi Mamah tayi ta ce"ai Jadda gani nayi akwai kayan aiki a gida, kinga
ba sai anje asibiti ba ko?" girgiza kai tayi ta ce"wannan ba hujja bace bari kiji,
ni ban yarda ba, wannan yarinyar kwata-kwata bata kwanta min ba, saboda haka kar a
dinga haɗata da yan gidan nan yawwa" murmushi Abbiey ya yi sannan ya ɗan bata
labarin Imara. Allah sarki Jadda harda kukanta ta kalli Abbiey tana share majina ta
ce"Allah sarki baiwar Allah, amma taga masifar rayuwa, to yanzu kenan ita batada
kowa haka take rayuwa?, baiwar Allah, Allah ya bamu ladan riƙon maraya" murmushi
sukayi duka kowa ya ce Ameen.
A hankali ta shiga ɗakin tana kalle kalle, zaune ta sameshi kan kujera yana danna
wayarsa, cikin rawar murya tayi sallama kafin ta ƙarasa inda yake, tsugunawa tayi
tana kallonsa cikin sanyin murya ta ce"gani" banza ya yi mata ya cigaba da danna
wayarsa. Ta gyara zamanta tana kallon ƙasa, saida ya kwashe mintunu biyar kafin ya
ajiye wayar hannunsa ya tashi ba tareda ya kalleta ba ya shige bedroom ɗinsa, ɗago
idanunta tayi ta bi shi da kallo haka kawai taji ranta yana ɓaci dan a rayuwarta ta
tsani mutum ya shareta. Tana nan zaune har bacci ya fara ɗauketa bai fito ba, a
hankali ta tashi tana kallon ƙofar ɗakin sai kuma ta tura baki ta ƙarasa wajen, duk
da yanda take jin tsoro ganin yanda yake haɗe rai hakan bai hanata tura ƙofar ɗakin
ba. Wani irin ƙamshi mai sanyi ne ya daki hancinta wanda ya haddasa mata da mutuwar
jiki, a hankali ta jingina da murfin ƙofar tana dafe ƙirjinta. Kamar tasan irin
wannan ƙamshin saidai ta kasa tuna inda ta san shi, a hankali ta buɗe idanunta
wanda ta rufe su ba tareda ta sani ba. A kwance ta hangeshi ya rufe jikinsa da
duvet da alama ma ya manta da wani babin ta. Haɗe fuska tayi kamar za ta yi kuka,
ta ƙarasa gabansa. Zama tayi kan bedside drawer ɗin wajen tana kallon bargon daya
rufe jikinsa, turo baki tayi sai kuma ta jingina da bangon ɗakin ta lumshe ido nan
da nan bacci ya kwasheta a zaune.
Ƙarfe 11:20pm Mamah ta turo ƙofar bedroom ɗin ta shigo. Wani irin ajiyar zuciya ta
sauke tana dafe ƙirji kafin ta ƙarasa inda take baccin. Sosai ta bata tausayi ganin
yanda take bacci a zaune bata ko tsoron wuyanta ya yi ciwo. Girgiza jikinta Mamah
tayi, ta yi saurin buɗe idanu tana kallonta hannunta ta kama suka fita gudun kada
su tashe shi. Saida ta kai ta har ɗakinta sannan ta kalleta ta ce"ya ba ki
maganin?" Kamar zatayi kuka ta girgiza mata kai, murmushi Mamah ta yi ta ce
"shikenan bari na samo miki paracetamol kafin zuwa da safe muje asibiti" jinjina
mata kai Imara tayi ta kwanta gefen gadon, ita kuma ta juya ta fita. Bayan ta dawo
ta tashe ta ta bata maganin sannan ta gyara mata wajen kwanciya, saida taga ta koma
bacci sannan tayi mata addu'a ta bar ɗakin.
2:45am.
Tsaye yake cikin bedroom ɗinsa ya kasa zama sai kai komo yake. Tunda ya saka
idanunsa kan yarinyar ya kasa samun nutsuwa tunanin yanda zai ɓullowa al'amarin
yake. Amma tabbas ko ta wane hali sai ya san yanda zai sameta. Da wannan tunanin ya
koma ya kwanta kafin bacci ya ɗaukeshi.
Yanda Imara taga rana haka taga dare ranar, dan tun bayan fitar Mamah ta buɗe
idanunta, tsananin ciwon kai da zazzaɓi shine ya dameta, gefe guda kuma mararta da
take mata wani irin azabbaben ciwo. Tana idar da sallahr asuba ta kifa kanta akan
gwuiwarta ta fashe da kuka, ganin kukan ba zai kai mata ba ya sanya ta tashi tana
dafe kanta ta fice daga ɗakin. Hanyar ɗakinsa ta nufa tana zuwa ta tura ƙofar ta
shiga bata ko ganin gabanta, babu kowa a parlon sai ƙamshin turarensa dake tashi.
Cikin bedroom ɗin ta shige, zubewa tayi a ƙasa ganin nan ma babu kowa, ta dafe
mararta tana runtse idanunta, above 5mins kafin ya buɗe ƙofar ya shigo, kafeta ya
yi da idanu sai kuma ya shige ciki, system ɗinsa ya ɗauko ya nemi waje ya zauna
bayan ya ɗauko yogurt ya buɗe ya yi bismillah ya fara sha, kafin ya cigaba da danna
system ɗinsa hankali kwance. Wani irin ihu da yaji ya sanya ya ɗago kansa, kwance
ya ganta a wajen tana kuka tana burgima. Ɗan ƙaramin tsaki yaja kafin ya tashi ya
ƙarasa inda take hannunsa riƙe da kwalin yogurt ɗin, tsugunawa ya yi a gabanta ya
sanya hannunsa ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce
"Mene?"
Kamar jira take ta sake rushewa da wani sabon kukan tana yarfe hannunta, numfasawa
ya yi sannan ya ɗagota zaune idanunsa zube kan fuskarta ya ce "idan bakida abin
faɗa tashi ki bani waje" cikin shassheƙar kuka ta ce " ka bani magani, zan mutu
cikina ciwo yake, nashiga uku" taɓe baki ya yi ya ce"Allah ya jiƙanki" daga haka ya
tashi ya fice daga ɗakin, wata irin kartawa mararta tayi ta saki wata irin ƙara sai
kuma ta faɗi ƙasa a sume.
# *IMARA 💋*
# *Nanameera*
# *Bestnovel*
# *2025*
*IMARA 💋💋*
29&30.
08106608363.
Yanda tayi maganar kamar tana kuka yasa ya juyo ya kalleta sai kuma yaja ya tsaya a
wajen, sunkuyar da kanta tayi tana wasada fingers ɗinta. Ɗan siririn tsaki yaja
sannan ya dawo inda take zaune ya ya kamata ta tashi tsaye ya ce"to mu je" sake
kwaɓe fuska tayi ta ce"ni ba zan iya tafiya ba" ƙura mata idanu ya yi sai kuma ya
yi kamar zai sunkuya ya ɗauketa kamar yar Baby ya fita da ita.
A corridor ɗin benan suka haɗu dashi yana sanye da suit black colour daga alama
shiryawa ya yi zai tafi aiki, cike da girmamawa ya sunkuya ya ce"Barka da safiya
doctor " jinjina masa kai kawai Abaan ya yi sannan ya juya ya bar wajen, kai tsaye
kuma ɗakin Mamah ya shiga. Zaune ya sameta gefen gado tana sanye cikin wata
embroidery atampa milk da adon baƙi tayi kyau kai ba zaka ce ita ce wacce ta haife
shi ba. A gefen gadon ya ajiye Imara ya kalli Mamah cikeda girmamawa ya ce"Barka da
safiya" fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi ta ce"ka tashi lpy son?"
"Alhamdulillah"
***Turo ƙofar ɗakin akayi ta ɗaga kanta daga kwance da take ta kalleta sai kuma ta
cigaba da danna wayarta
Ƙarasowa Amrish tayi tana murmushi ta ce"sarkin fushi, ai gani dai nazo, tunda na
ce miki zan zo ai kinsan ina hanya" tashi zaune Jidda ta yi ta ajiye wayarta tana
kallonta ta ce "nakasa bacci jiya, hankalina ya tashi Amrish, bazan iya cigaba da
rayuwa a haka ba, nadawo daga Zaria amma takaicin dana tarar saida na gwammace ban
dawo gida ba" numfasawa tayi ta ce
"Kema Jidda, ki daina wani tada hankalin ki, kin sani Abaan yana matuƙar son ki,
kuma ba zai taɓa yin abin da zai raba ki dashi ba, tun kina ƙarama yake ɗaukan duk
wata ɗawainiyarki. To meyasa yanzu kike tadawa kanki hankali akan abin da yake
mallakin ki?, dan kawai jiya bai kula ki ba ai ba hakan yana nufin ya daina sonki
ba, kuma kinsan halinsa na shariya"
Girgiza kai Jidda tayi ta ce"you can't understand Amrish, Abaan bafa irin sauran
maza bane, kinsan halinsa kuwa?koda sau ɗaya kika ga ya sauya fuska to tabbas akwai
abin da ba daidai ba, banason matsala wlh"
Dafata Amrish tayi ta ce"don't worry ƙawata, Abaan naki ne ke kaɗai, kawai ki
cigaba da son shiga zuciyarsa har kiyi nasara, koma akwai wata wacce yakeda muradi
ya ji ta daina burgeshi"
Wani murmushin jindadi tayi wanda ya fito da zallar kyanta ta ce"shiyasa nake sonki
ƙawata, yanzu kin san me?, bari na shirya muje muyi breakfast" gyaɗa mata kai
kawai tayi, ta tashi daga kwancen ta shige toilet dan yin wanka, da idanu kawai
Amrish ta bita sai kuma ta zaro wayarta ta shiga dannawa.
***Washe baki Jadda tayi tana cewa"kaga ɗan albarkan jika, shiyasa duk cikin
jikokina nafi sonka, saboda yanda kake ji dani" kallonta kawai Abaan ya yi da manya
manyan idanunsa ta cigaba da faɗin" yawwa yanzu wannan bazawarar daka kawo gidan
nan fa?, naga yarinyar tanada kyau, narasa inda nasan me irin kamarta, tana kamada
wata wlh" shi dai Abaan sai kallonta yake, zata cigaba da magana Mamah tayi sallama
ta shigo falon Imara na biye da ita. Murmushi Jadda tayi tana kallonta ta ce
Jiki babu kwari Imara ta tsuguna cikin cool voice ɗinta ta ce "ina kwana" shiru
Jadda tayi ta zuba mata idanu, jin bata ce komai ba ya sanya Imara sunkuyar da
kanta. Wani irin jiri take jin yana ɗibanta a zaune ga mararta dake mata wata
iriyar karta. Tashi tsaye Abaan ya yi ya kalli Mamah ya ce"sai nadawo" daga haka ya
fice ba tare da ya sake bi ta kan Jadda ba. Hannun Imara Mamah ta kama ta miƙar da
ita tsaye sannan ta ce"ki je kar ya tafi ya barki" jinjina kai kawai tayi sannan ta
yi waje tana tafiya a hankali.
***Durus tayi a bakin entrance ɗin falon, sai kallon ko'ina take, yawan motocin
data gani yasa ta kasa gane wacce ya shiga. Ganin yanda rana ke facing ɗinta yasa
ta tsuguna a wajen tayi tagumi nan da nan hawaye suka fara zuba kamar an buɗe
famfo. Tunda ta fito Abaan yake kallonta har zuwa sanda ta zauna, yana zaune cikin
backseat ɗin wata baƙar mota ko ba'a faɗa maka ba kasan irin motocin nan ne wanda
aka saka kuɗaɗe aka siya. A hankali ya ƙaraso gabanta hannayensa zube cikin aljihu,
saurin ɗago kanta tayi saboda inuwar mutum data gani, murmushi Adeel ya sakar mata
a hankali ta tashi tsaye bakinta na rawa ta ce
"In...ina kwana?"
Bai amsa mata ba sai murmushin da ya cigaba da yi, ganin haka ya sanya Imara ta
sunkuyar da kanta ƙasa tana wasada fingers ɗinta wanda suka kasance dogaye,
numfasawa ya yi sai kuma ya ce"me kike anan Imara?" buɗe baki tayi zata yi magana
ta hangeshi tsaye ya kafeta da idanunsa, saurin maida kanta ƙasa tayi dan bata iya
jurar haɗa idanu dashi. Ganin inda ta kalla ya sanya Adeel ya juya, rissinawa ya yi
cikin ladabi ya ce"Barka da safiya yaya" Cikin sakin fuska ya ce"Ka tashi lpy
Adeel?" Jinjina kai ya yi ya ce "Alhamdulillah" gyaɗa kai kawai ya yi sannan ya
kama hannunta ya bar wajen.
Wani Kallo Jidda ta bisu dashi har suka shiga motar bayan ya amshi key ɗin ya zauna
a driver seat ita kuma ta zauna a gefensa, ta lumshe idanunta. Ya yiwa motar key ya
bar gidan da gudu kasancewar kwalta ce a ciki. Saurin riƙe hannun Amrish tayi
bakinta na rawa ta shiga nuna mata inda suka tafi, hannunta Amrish ta kama suka
shiga mota ta amshi key ɗin dan tasan ba lailai tayi driving ɗin ba. Saida suka hau
kan titi sannan ta kalleta ta ce"wacece wannan yarinyar?" murmushin yaƙe Jidda tayi
ta ce"nima bansani ba, na ganta a ɗakinsa rannan, nd yau kuma naga ya fita da ita,
koma wace i must find out sannan kuma zan mata abun da ba zata taɓa mantawa dani
ba"
"Me za ki yi mata?"
Girgiza kai Jidda tayi ta ce"karki wani tambayeni, ki bari idan na aiwatar sai kowa
ya gani, amma wlh sai tayi danasanin shigowa gidan nan" murmushi Amrish tayi ta
ce"bana jin ki ƙawata, nasan za ki yi abin da ya dace, amma karki yi abin da zai yi
causing problem" kwafa tayi ta ce"babu wanda zai haddasawa matsala sai wanda ya
jawo matsala da kansa, sai na tabbatar da na wulaƙanta ta, domin wlh babu wacce ta
isa ta raɓi Abaan, koda kuwa bayan raina ne" ajiyar zuciya Amrish tayi tana kallon
titi ta ce
***A bakin wata ƙaton asibiti na KFJ ya yi parking, iya ka haɗuwa asibitin ya haɗu
dukda babu wasu masu shige da fice a cikinsa da alama ma ba'a kai ga buɗeshi ba.
Buɗe motar ya yi ya sauka sannan ya zagayo ta inda take ganin kamar bacci take,
handle ɗin ƙofar ya buɗe ya taɓa kanta ya ji har sannan da zafi sosai, ya tashe ta
sannan ya shige ciki, a baya ta biyo shi har cikin asibitin. Lift suka hau sannan
suka je second floor na asibitin, ɗakuna ne birjik sai threater ya buɗe wani office
ya shiga, babban office ne wanda ya gaji da haɗuwa ko a asibitocin ƙasar waje iya
kar abin da za'a yi masa kenan. Ya ƙarasa ya ajiye wayarsa sannan ya juyo ya
kalleta ya ce"zauna" waje ta samu ta zauna kan wata kujera ya juya ya fita. Bayan
5mins ya dawo hannunsa riƙe da injection da drip tana ganin haka tayi saurin
langwaɓar da kanta jikinta na rawa, a kusada ita ya zauna ya haɗa allurar sannan ya
tashi ya tattare hannun rigarsa yana kallonta ya ce"gyara" ya faɗa a takaice, rawar
jiki ta fara yi tana kallonsa nan da nan wasu sabbin hawayen suka sake wanke mata
fuska. Ikon Allah Abaan ya tsaya yana kallo kafin ya haɗe rai lokaci ɗaya ya ce
"Hey! Cry cry baby, ce miki a ka yi banida wani abin yin ne?, ki gyara nayi miki
injection"
Sake rushewa tayi da kuka ta sanya hannayenta biyu ta rufe fuskarta tana girgiza
masa kai, baki buɗe yake kallonta sai kuma ya ce"Ke, Imara ke ki ko wa?, wa za ki
yiwa yarinta anan wajen?, ki nutsu kin ji ko!" Cikin shassheƙar kuka ta ce"dan
Allah kar ka yimin, tsoro nakeji wlh, zan mutu ni, wayyo Allahna" zuba mata idanu
Abaan ya yi kafin ya ajiye injection ɗin a gefen desk ya kalleta sai kuma ya ja
kujera dake facing tata ya zauna yana kallonta ya ce
"Shikenan na ajiye"
A hankali ta shiga zare hannayenta daga kan fuskarta tana leƙensa, hannunsa ta
kalla taga babu injection ɗin hakan yasa ta yi saurin buɗe fuskarta ta shiga share
hawaye wanda ya yi mata kaca -kaca da fuska harda majina. Ɗan murmushi ya yi har
saida beauty point ɗinsa suka loma kafin ya ce
Saurin gyaɗa masa kai tayi tana kwaɓe fuska kamar yar Baby, haɗe rai ya yi ya ce
"Bakida baki?"
"Ina da shi"
Murmushin da bata yi niyya ba tayi ta ce"dan Allah karka yimin allura ka ji ko,
bana sonta, tun da ma banaso, tun ina yarinya"
Da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta ta ce"na girma mana, kuma Dodona
ya cemin zan yi saurin girma gashi yanzu na girma sosai" shiru ya yi yana kallonta
ta sake cewa
"Tunda ya tafi ya barni a makaranta bai sake dawowa ba, koma ya sani Umma ta rasu?,
bayasona, bayan ya ce ba zai taɓa tafiya ya barni ba, shine ya gudu, ina jin tsoro
sosai, inason na sake ganinsa, inason ganin fuskarsa, shima ya ce min yanada kyau
irina. Kamar kai kuma sannan..."
Ɗago idanunsa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce"ki cigaba mana" langwaɓar da kai tayi
ta ce"kawai bana son shi ne, na daina kula shi. Koda na ganshi babu ruwana dashi,
tunda ya saɓa alƙawari, ni Maheer nakeson gani."
Wani zazzafan numfashi Abaan ya sauke sannan ya ce"to kika sani ko ya yita nemanki
bai ganki ba" girgiza kanta tayi hawaye na kawowa idanun ta ce"bai nemeni ba, ya
tafi ya barni bai sake zuwa ba, yana sane ya tafi. Saboda ya ce a dinga bani
abinci, bai san halin da na shiga ba a sanda ya tafi ya barni, ya ƙarya
alƙawarinsa, saboda haka babu ruwana dashi. Har abada!" Ɗan murmushi Abaan ya yi ya
ce"shikenan, ke bakida yafiya?, anyway tashi muje na saka miki drip ko shi ma bakya
so" tashi tayi tabi bayansa suka fita daga office ɗin, wani ɗaki a gefen office ɗin
ya shiga. Akan gado ta zauna ya haɗa ruwan sannan ya sanya mata bayan ta saka kukan
shagwaɓa, a cikin drip ɗin ya sanya allurar wacce ta haddasa mata da bacci lokaci
guda. Zama ya yi gefenta ya ƙura mata idanu yana kallonta, a ɗan firgice ta ɗago ta
ɗora kanta akan cinyarsa cikin baccin tana faɗin
# *IMARA 💋*
# *Dodo*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*
*IMARA 💋💋*
31&32.
08106608363.
***Turo ƙofar parlon tayi ta shigo tana jan jakarta, Jadda dake zaune kan kujera ta
hakimce tana taunar nama. Zama Umaima tayi akan kujera ta ɗan zame jikinta ta
kwanta. Wani banzan kallo Jadda ta watsa mata sai kuma ta ce
"Ke kam wannan yarinya an yi malalaciya, ji yanda kika wani kwanta kamar ruwa, yara
duk kun saba da sangarta to ki sauya hali"
A fusace Umaima ta tashi zaune ta kalleta kamar za ta yi kuka ta ce"to dan Allah
ina ruwan ki dani Jadda?, Saboda bakisan wahalar dana sha ba. Tun safe nake yawo a
school amma shine nadawo za ki kama ki rufeni da faɗa. Saboda daman kin tsaneni"
Umaima ta tashi daga falon tana goge hawaye. Riƙe baki Jadda tayi tana cewa
"Karki yarda ki yimin sharri, yaushe nayi miki faɗa?, salon ubanku ya dawo ya ji
kisa ya tsaneni, to ta Allah ba ta ki ba wlh" Umaima bata sake bi ta kanta ba ta
haye sama kai tsaye kuma ɗakinta ta shiga.
***Kallonta Amrish tayi ganin sai juya smooth ɗin gabanta take ta ce"wai me kike
tunani kuma ?" girgiza kai tayi tana cire hannunta daga kan smooth din ta ce"nakasa
yarda da abin da nagani ne wlh!, Gaba-daya yanzu tunanina ya ta'allaka akan na gano
wacece wannan yarinyar. A ina Abaan ya santa?, Me yasa kuma take biye dashi and he
can't scold her, why?" Murmushi Amrish ta yi bayan ta ajiye pork ɗin hannunta ta ce
"Jidda! Jidda! Jidda, ki daina sakawa kan ki damuwa. Kinsan dai yana yin lafiyarki,
karki manta an rigada an yi miki baiko keda Abaan, so probably zaki aure shi,
wannan kina damun kan ki ne a banza kawai. Wacece wannan yarinyar, a ina ya santa?,
Duk bai dame ki ba, tunda kina da tabbacin Abaan ba mai kule-kulen mata bane,
saboda haka dan Allah ki daina damun kan ki kawai ki ja mana masifa"
Numfasawa tayi ta miƙe ta ɗauki car key ɗin ta tana kallon agogon hannunta ta
ce"yamma ya yi already, tun safe muka fito gida zan tafi. Nasan maybe yanzu Abaan
ya dawo, zan je na ganshi ne"
Ta shi itama tayi ta ce"haka ne, muje sai ki ajiye ne a Tahir saboda mun yi da
Alhaji zamu haɗu acan"
***Ƙarfe 7:04 Jidda tayi parking ta fito kai tsaye kuma apartment ɗin su ta nufa.
Tana shiga ta sami Mommy zaune ta ci uwar kwalliya sai taunar chew gum ta yi,
murmushi Jidda ta yi ta ƙarasa ta zauna gefen ta ta ce"Hajiya Mommy irin wannan
kwalliya haka?" Kallonta Mom tayi sai kuma ta harareta ta ce"ke fita a idona, ki je
kiyi wanka ki shirya ina nan ina jiran ki" langwabar da kai tayi ta ce"okay Mommy".
Wani kallo Umaima ta watsawa Nana kafin ta ce"ina ruwan ki da ita?, A kanki take?,
Wlh ki shiga taitayinki kinsan dai wanda ya kawota gidan" turo baki Nana ta yi ta
ce"to ai gaskiya nafaɗa, kawai ta zo ta takura mana, ni wlh bata yimin ba"
harararta Umaima tayi ta ce"tunda a rayuwa kana zaɓar wanda ya yi maka da wanda bai
maka ba. Ki je kiyi ta yi, watarana sai kin jawo masifar da zata dame ki wlh"
Ɗaga kafaɗa Nana tayi irin bai dame ta ɗin nan ba, ta tashi zata fita.
Kallon kayan jikinta ta yi, t-shirt ce baka sai wani jeans 3-quarter wanda ya tsaya
iya gwuiwarta, ta tufke gashin kanta ya zubo har bayanta. Turo baki ta yi ta ce"to
me shiga ta tayi?, Naga wajen Jadda zan je" gyaɗa kai Umaima ta yi ta ce" Allah ya
taimaka" fita Nana tayi ba tare da ta sake magana ba.
Kallon inda ya yi parking ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta, bai ce mata komai ba
ya sauka daga motar hakan yasa ita ma ta sakko tana binsa da idanu. Kai tsaye cikin
mall ɗin ya nufa ita kuma ta bi bayansa, bayan ya shiga wata ma'aikaci ta zo tana
murmushi ta ce
"Welcome sir"
"Kaya na budurwa kamar ta, banda ƙananun kaya, I mean only Abaya"
Jinjina kai tayi sannan ta juya ta bar wajen. Imara na nan wajen a tsaye har aka
kai kayan cikin mota ya bada atm card suka cira sannan ya juya ya bar wajen. Tun da
suka shiga Mota ta shiga share hawaye tana kuka, Abaan na lura da ita amma bai ce
komai ba har suka ƙarasa gida. Bayan ya yi parking ya kalleta sai kuma ya fito daga
motar ya shige gida dan daman saida ya yi sallar isha'i sannan ya shigo, a falon ya
samesu suna kallo Jadda na fam zuba kamar yanda ta saba,
Wata razananniyar tsawa ya daka mata, wacce tasa ta bar falon da gudu tana kuka.
Tsaki ya yi Sannan ya kalli Mamah ya ce"wace irin shiga ce wannan yarinyar ta ke yi
ne haka?, nd kuma kina kallo ba za ki yi mata magana ba?"
"Yanzu Abaan ba gashi ka yi mata ta ji ba, nayi maganar amma Jadda ta hanani wai na
rabu da ita"
Ko kallonta Abaan bai yi ya bar wajen. Ajiyar zuciya Jadda ta sauke sai kuma ta
kalli Mamah ta ce
"Karki sake yimin irin haka a gabansa, ba kiga yanda ya haɗe rai ba ne"
Girgiza kai Mamah kawai tayi, ta tashi ta bar wajen. Sai a sannan Imara ta yi
sallama ta shigo parlon, kallon Jadda ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta ta
gaisheta cikin rawar murya.
"Imara me aka yi miki?, Meyasa ki ke kuka?, Wani abun yaya ya yi miki?" Imara
couldn't help it but cry, ta cigaba da kukanta. Riƙota Umaima tayi ai kuwa kamar
jira take ta faɗa jikinta tana kuka, sosai ta bawa Umaima tausayi kai da ka ganta
kasan tana cikin jarrabar rayuwa gata kuma da ƙananun shekaru. Shafa kanta ta shiga
yi cikin lallashi ta ce
"Ki daina kuka, addu'a ita ce mafita a koda yaushe, ki dinga faɗawa Allah buƙatar
ki, tabbas nasan zai share kimi hawaye. Kin sha wahalar rayuwa Imara amma hakan ba
shine dalilin da zai sanya ki maida damuwa abokiyar rayuwarki ba"
"Tsoro nake ji, naji tsoro, irin haka Maheer ya kai ni ya siyamin kaya, ya ce zai
zauna dani, ba zai taɓa barina ba, zai zame mini garkuwa, ba zan sake kuka ba. Amma
hakan bai faru ba, Maheer ya gujeni, Maheer ya barni daga ƙarshe kuma ya sakeni.
Shi ma yanzu ya siyomin kaya, ina tsoron na bar gidan nan, dan Allah ki taimakeni,
tsoro nake ji"
Rungumeta Umaima tayi, sai a sannan ta san dalilin kukan nata, dafata tayi ta
ce"babu abin da zai faru sai alkhairi Imara. Na tabbata tun da yaya Abaan ya kawo
ki gidan nan ba zai bari a cutar dake ba, dan ya siya miki kaya hakan ba yana nufin
ya shirya korarki ba, muna nan, gidan nan ya zama gidanki. Ki daina damun kan ki,
kada kuka yasa wani ciwon ya sameki Imara"
Haka Umaima ta yita rarrashinta har saida taga tayi shiru, ta ɗago fuskanta tana
kallonta ta ce"je ki wanke fuskarki ki zo muje, Jadda ce ta aikoni na kira ki"
gyada mata kai Imara tayi sannan ta tashi ta shiga toilet ta wanko fuskarta kamar
yanda Umaima ta ce mata, murmushi Umaima ta yi ta ce"yawwa, kinga har kin yi kyau,
muje" bin bayanta Imara tayi tana tafiya a hankali.
"Shine nace ki tsaya kika tafi ko?, Ko furar tawa ce bakya so?, Yarinya ba abun
mutuwa zan saka miki ba" murmushi Imara ta yi ta ce"alwala naje nayi Jadda" jinjina
kai tayi ta ce"to har naji daɗi, zauna maza na zuba miki" zama Imara ta yi akan
carpet tana kallon su. Haɗe rai Nana ta yi kamar zata yi kuka tana kallon Jadda ta
gama zubawa Imara furar ta miƙa mata, amsa Imara tayi tana murmushi ta ce"nagode
Jadda"
A hankali ta fara shan furar tana lumshe idanunta saboda daɗin ta, Umaima ce ta
kalli Jadda ta ce"Granny nifa?" wani banzan kallo Jadda ta yi mata ta ce"waye zai
baki, Allah na tuba, ai nafaɗa miki wannan da kike gani ta babban gidan nan ce
daman shi na ajiyewa" murmushi Umaima ta yi ta ce"to wane ya ce miki yaya zai sha?"
Tashi Umaima ta yi ta ce"Allah ya huci zuciyarki, Allah yaso muma Abbiey yana siyo
mana yogurt kuma ba za ki sha ba" riƙe haɓa Jadda ta yi ta ce"iyeeee, to uwarki ita
kika yi wa ba ni ba" ko kallonta Umaima ba ta yi ba ta haye sama da sauri. Taɓe
baki Nana ta yi ta ce"ai shikenan Jadda tun da kin fifita wata akan jikarki"
girgiza kai Jadda ta yi ta ce"ke ba'a haka, baƙuwa ce shiyasa, kuma kina ji aka ce
mijinta ne ya saketa gashi marainiya ce ai kinga akwai samun lada cikin riƙon
maraya" a fusace Nana ta ce"to nan gidan ai bai yi kamada gidan yan gudun hijira
ba, ko kuma gidan zawarawa, dan batada iyaye ai ba haka ke nufin batada dangi ba,
ni banason takura wlh" hannunta Jadda ta kama ta ce"ke ba'a haka, ki sauya hali"
tashi Nanah ta yi ta bar parlon kamar zata tashi sama. Imara dake saurarensu tun
ɗazu ta sunkuyar da kanta, tabbas haka ne dan batada iyaye ba haka ke nufin batada
dangi ba. Amma saidai batasan su wanene dangin nata ba, da wannan tunanin ta ajiye
cup ɗin furar ta miƙe zata bar wajen.
Gudun kada Jadda taga hawayenta yasa ta ƙi juyowa cikin rawar murya ta
ce"na...naƙoshi Jadda" kafin Jadda ta buɗe bakinta Mamah ta fito daga kitchen tana
kallonta ta ce"yawwa daughter je ki kitchen akwai tray na abincin Abaan ki kai
masa" to kawai Imara ta ce ta shiga kitchen ta ɗauko tray ɗin ta hau sama.
A corridor ɗin ɗakunan nasu ta ganshi yana ƙoƙarin rufe ɗakinsa, kallo ɗaya ta yi
masa ta juya zata bar wajen.
"Imara!"
"na'am"
"Mamah ce ta aikeni"
Kallon agogon hannunsa ya yi sai kuma ya ce"okay tom je ki, karna tsayar dake"
kamar jira Imara take ta bar wajen da sauri, tana zuwa ta tura ƙofar ɗakin nasa ta
shiga, da idanu Khalil ya bita sai kuma ya juya ya sauka ƙasa.
Zaune ta hangeshi kan kujera yana danna system ɗin sa wacce koda yaushe ba'a raba
shi da ita. Sallama ta yi sannan ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a gabansa ta tashi
zata fita.
"Zo nan"
Hannunsa ta ga ya miƙo mata, ta ɗora nata akai ta miƙe tsaye ta zauna gefensa inda
ya nuna mata. Numfasawa ya yi sai kuma ya ce
Shassheƙar kuka tafara ya girgiza kansa ya ce"kuka na ce kiyimin dama?" cikin kuka
ta ce"dan Allah Inason na tafi" waro idanunsa ya yi a kanta sai kuma jingina da
kujerar har sannan yana kallonta ya ce"ki je ina?"
"Jigawa"
"Wajen wa?"
Ya faɗa a takaice, shiru Imara ta yi dan tabbas babu wanda zata je wajensa a Jigawa
tunda babu wanda ta sani, jin ba ta ce komai ba yasa ya ce"I'm talking to you"
"Ko?"
Jin yanda ya yi maganar a hasale yasa ta kalleshi taga ya haɗe rai, sunkuyar da
kanta ta yi ta ce"nan ai ba gidan zawarawa bane, Inason na tafi na nemo dangina,
zan zauna a cikin su koda kuwa basa ƙaunata, bazan taɓa ƙorafi ba,k kuma..." Kasa
cigabawa ta yi saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Shiru Abaan y yi na ɗan lokaci sai
kuma ya ce
"Ki shirya gobe za'a kai ki makaranta, nd kiyi concentrating akan karatun ki, banda
wasa okay?"
Da sauri ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta girgiza kanta ta ce" dan Allah banaso, dan
Allah, kayi haƙuri, banason karatun"
Fashewa ta yi da kuka ta tashi ta zauna a ƙasa tana kuka, shiru Abaan ya yi mata ya
shiga danna wayarsa, saida ta yi mai isarta sannan bacci ɓarawo ya ɗauketa a wajen.
Saida ya gama abin da yake gabansa sannan ya ɗago jin ta yi shiru. Gani ya yi ta yi
bacci a wajen, girgiza kansa ya yi sai kuma ya yi murmushi har saida haƙoransa suka
fito. Tashi ya yi ya ɗauketa kamar baby ya fita da ita daga ɗakin, ɗakinta ya kai
ta ya kwantar da ita ya yi mata addu'a sannan ya ƙaro gudun AC ɗin ya juya ya fita.
Wani zazzafan numfashi Khalil ya sauke lokacin da yaga Abaan ya fito daga ɗakin,
zuciyarsa a cunkushe ya juya ya koma ɗakinsa ya kashe fitila.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Heart touching 💔*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
33&34.
08106608363
Washegari da wuri Mamah ta shigo ɗakinta, zaune ta sameta gefen gado tana ninke
kayan da Abaan ya siya mata jiya. Tana ganin Mamah ta tsuguna ta gaisheta, fuska a
sake Mamah ta amsa ta zauna gefenta ta ce"inyee kayan sun yi miki kyau?" gyaɗa mata
kai tayi kanta a ƙasa. Murmushi Mamah ta yi ta ce"shikenan ajiye wannan aikin, ki
tashi ki shirya za'a tafi kai ki school" da sauri Imara ta kalleta sai kuma ta tuna
da abin da Abaan ya ce mata jiya.
Waro idanu ta yi ta ce"meyasa?, bakison ki zama babbar mace?, karatu shine gatanki
Imara" buɗe baki ta yi zata yi magana Mamah ta dakatar da ita ta ce
"Banason sake jin wannan maganar a bakin ki, ba kece kika ce kina son zama lauya
dan ki gano su wane suka kashe iyayenki ba?, saboda haka karatu ya zamar miki dole,
maza je ki shirya kinji"
Imara bata sake cewa komai ba, ta tashi ta shige toilet tana tafiya cikin sanyin
jiki. Ajiyar zuciya Mamah ta sauke sannan ta kwashe duk kayan ta zuba a wardrobe ta
juya ta fita. Bayan mintuna goma ta fito, ajiyar zuciya ta sauke ganin Mamah
batanan, shiryawa ta fara, duk da har cikin ranta batasan zuwa makarantar amma ba
zata iya musu da Mamah. Tana cikin rolling veil ɗin ta Umaima ta buɗe ɗakin ta
shigo. Sanye take cikin wata rigar atampa Holland coffee mai manyan zane, ta yafa
veil babba akanta, kallon Imara ta yi sai kuma ta saki murmushi. Umaima kyakkyawa
ce irin sosai ɗin nan, da ka ganta kasan suna da jiɓi da wata ƙabilar wacce bata
hausawa ba, amma duk da kyanta Nana ta fita, ita kawai rashin kirki ne fal a
cikinta.
"Imara!"
Sosai Imara ta ji daɗin furucin Umaima, hakan yasa ta yi murmushi ta ce"Tom in sha
Allah, zan yi yadda kika ce" jan kumatunta Umaima ta yi ta ce"yawwa beauty, tashi
muje maza" ta shi ta yi suka fice daga ɗakin.
A dinning area suka sami kowa na gidan banda Jadda da Abaan, wanda daman wajen ba
gurin zamansu bane. Murmushi Mamah ta yi ganin yanda suka fito a nutse ta ce"yawwa
ku yi sauri ku gama" ɗaya bayan ɗaya Imara ta gaisheda duk mutanen falon, Khalil
kam ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta ta
gaishe shi, cikin sakin fuska ya amsa ta zauna. Abbiey ne ya kalleta ya ce"Imara
kina son makarantar dai?" murmushi ta yi ta ce"Eh Abbiey" jinjina kai ya yi ya
ce"Masha Allah, to ki yi karatu da kyau kinji, duk abin da baki gane ba sai ki
tambayi Nana tun da ajin ku ɗaya, itama this year ta shiga" Tom kawai ta ce sannan
ta fara cin abincin ta.
Ƙamshin turarensa ne ya gauraye falon, juyawa suka yi suka kalleshi banda Imara
wacce take cin abincinta a nutse, cikin sakin fuska ya gaisar da iyayen nasa sannan
ƙannen nasa suka gaishe shi. Da idanu Umaima ta bi Imara ganin kowa ya gaishe shi a
wajen banda ita, girgiza kai ta yi ba tare da ta ce komai ba ta ja kujera ta tashi,
hand bag ɗinta ta ɗauka tana kallonsu ta ce"nidai na tafi kar nayi late, Imara sai
kin dawo" ɗaga mata hannu Imara ta yi tana murmushi. Kai tsaye apartment ɗin Jadda
ya nufa, dan babu ranar banza da zai fita daga gidan ba tare da sun gaisa ba. Tana
gama ci ta tashi, Mamah ta kalleta ta ce
Da sauri ta tashi ta fice daga falon, tashi Nana ta yi ta fice ita ma. A compound
ɗin gidan ta hangeta tsaye jikin wata flower ta yi shiru, wani mugun kallo ta watsa
mata sai kuma ta ƙarasa gabanta. Veil ɗinta ta ja yasa Imara ta juyo, ta kalleta
sai kuma ta yi murmushi
"Nana"
"Riƙe sunanki bana buƙata, Inason na sanar dake wani abu ne, kar ki ga za'a kai ki
makarantar da nake ki yi tunanin ke kin kai matsayina, koda wasa kar ki kuskura ki
nuna kin sanni a makaranta, idan ba haka ba wlh sai na wulaƙantaki a gaban mutane.
Ke ba yar uwata ba ce, babu abin da ya haɗani dake!"
"Nana"
Da sauri ta juya sai kuma ta yi murmushi ta ce"Aunty Jidda" ƙarasowa Jidda tayi
tana sanye da wata Abaya maroon colour ta sanye wani glass mai manyan idanu,
hannunta riƙe da car key ɗin ta.
Ta faɗa tana kallon Imara, taɓe baki Nana ta yi ta ce"wai Yaya ne ya tsinceta shine
ya kawota" wani kallo Jidda ta yiwa Imara sai kuma ta ce
"Bansani ba, look kin san wace ni?, kinsan gidansu wane wannan?, kinsan wane ne mai
gidan nan?, behave ur self, ki kama kanki, nan ba gidan matsiyata bane, kuma ki
fita a harkar Abaan kin ji ko?"
Runtse idanu Imara ta yi, ta sake jingina da flower gudun kada ta faɗi. Murmushi
Nana tayi jin ta ci mata mutunci ta ce"Aunty ki yi dropping ɗina mana" okay Jidda
ta ce sannan ta yi gaba, Nana ta bita da sauri.
Suna barin wajen ta tsuguna a ƙasa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita.
"Kee"
Abaan ya faɗa yana tsaye a kanta, ƙin ɗago kanta tayi saida ya maimaita sau uku
sannan ta ɗago ta kalleshi da idanunta wanda suka yi jajur, girgiza kansa ya yi ya
ce"tashi anan wajen" tashi tsaye tayi har sannan kuma shassheƙar kuka take. Kallon
veil ɗin jikinta ya yi sai kuma ya ce"da wannan za ki fita?" kukanta kawai take
bata ce masa komai ba, ganin kamar ba za tayi magana ba yasa kawai ya ja hannunta
suka bar wajen. Bayan ya sun fara tafiya ya kalleta yaga har sannan kukan take ba
tada alamar yin shiru. Bai ce mata komai ba ya cigaba da driving ɗinsa a nutse, a
wani boutique ya yi parking ya fita, not too long ya dawo hannunsa riƙe da wata
leda babba. Har suka ƙarasa makarantar ba tayi shiru ba, saida ya yi parking sannan
ya kashe motar ya juyo ya kalleta ya ce
"Imara!"
Banza ta yi masa ta cigaba da kukanta, hannunta ya kama ya riƙe cikin nasa ya ce"ya
isa faɗa min meya faru?, me aka yi miki?, ke dawa?uhm?" cikin shassheƙar kuka ta ce
"Ni banason makarantar, Jigawa nakeson zuwa, ni gida zan tafi" waro idanu ya yi sai
kuma ya sanya hannunsa ya zare hannayenta daga fuskarta yana kallonta ya ce"wani
abun aka sake miki?, shikenan zan kai ki Jigawan, amma not today kinji" ɗan buɗe
idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta turo baki ta ce"to ni banason zama a gidan,
ka maidani garinmu, bazan zauna anan ba Allah" murmushi ya yi ya ce"to naji, amma
yanzu ki fara zuwa school, ko kin manta alƙawarin da kika yiwa wani?, kin ce za ki
yi karatu ki biya shi kuɗin da ya ranto miki, ba ke kika faɗa ba?" kwaɓe fuska ta
yi sai kuma ta ce"ai to ya tafi ya barni, koda na gansa ma bazan kula shi ba, kuma
ba zai gane ni ba" kallonta kawai ya yi sai kuma ya ce"duk da haka, amma ai
alƙawari kika ɗaukar masa, kuma kinsan alƙawari kayane, sannan wane ya ce miki ba
zai dawo ba?"
Juyowa ta yi tana kallonsa ya buɗe ledar gefensa ya ɗauko hijab ya miƙa mata.
Kallonsa ta yi sai kuma ta kalli hijabin ta buɗe, babba ne sosai dan zai rufe mata
har ƙafafunta. Turo baki ta yi ta ce"ni wannan ai ya yi min girma" bai ce mata
komai ba ya sauka daga motar hakan yasa itama dole ta sauko bayan ta zura hijabin,
tafiya ya fara yi tana bin bayansa sai turo baki take tana jan hijabin.
***Saida aka kai ta aji sannan ya bar makaranta. Zaune ta hangi Nana ita da
ƙawayenta wanda kana ganinsu kaga ya'yan manya. Wani desk ta gani babu kowa a kai
ta ƙarasa ta zauna ba tare da ta kalli kowa ba. Tana nan zaune har wani lecture ya
shigo, bayan ya gama yi musu karatu ya kalleta cikin harshen turanci ya ce "sabuwa
ce ke?" Gyaɗa masa kai ta yi ya ce"bakya magana ne?" kamar za ta yi kuka ta ce"Eh"
"What's ur name?"
"Imara Ahmad"
Da sauri Nana ta juyo ta kalleta sai kuma ta taɓe baki. Murmushi Sir Jawad ya yi
ya ce"wow, nice name" dan murmushi ta yi sannan ya juya ya fita.
***Wani kallo Jidda ta yi musu sai kuma ta taɓe baki ta ce " nifa dama yarinyar
bata taɓa burgeni ba, amma yanzu da naji Abaan ya kawota gidan, naji tsanar da nake
mata ta nunku, kuma wlh sai na koreta daga gidan!"
Murmushi Majida ta yi ta ce"ke kam mene abun ɗaga hankali?, an fa saka ranar
auranki dashi, kuma ke ɗin zaɓin iyayenku ce, damuwa da kishi ba naki bane?"
Cewar Amrish tana kallonta, kwafa Jidda tayi kawai ta miƙe ta ɗauki jakarta ta
ce"ni dai na tafi gida, tun an gama lecture sai gobe kuma" daga haka ta fice daga
ajin dan batason cigaba da maganar.
***Wajejen Ƙarfe 4 suka tashi daga school, Nana ce ta fara fitowa suna hira da
ƙawayenta. Tana ganin driver ya zo ɗaukansu ta kalli ƙawarta Maryam ta ce"yawwa
dear sai gobe an zo ɗaukata" ɗaga mata hannu ta yi sannan ta bar wajen, Imara na
ganin ta yi wajen motar ta biyo bayanta tana tafe da takardu a hannu, Nana na
kallonta ta shige motar ta sauke glass tana kallon drivern ta ce " muje" kasancewar
umarninta drivern ke ji yasa ya tada motar Ba tare da ya kalli Imara wacce ke tsaye
ba. Da idanu kawai Imara ta bisu har suka fice daga makaranta, shiru ta yi hawaye
na kawowa idanunta. Rashin sanin yanda zata yi ya sanya ta fara tafiya toward
direction ɗin fita daga makaranta. Saida ta zo gate sannan ta zubawa titi idanu,
akwai abin hawa dayawa a wajen, saidai batasan inda zata je ba, dan ko sunar
unguwar bata sani ba, gashi babu ko sisi a hannunta. Wannan tunanin ya sanya Imara
fashewa da kuka ta maƙale jikin gate ɗin makarantar, kasancewar babu ruwan kowa da
wani yasa babu wanda ya je inda take bare ya tambayeta abin da ya dameta. Tunawa ta
yi da takardar hannunta wacce aka bata a office ɗin director, tayi sauri ta buɗe
tana duba inda aka sanya address,
Shine sunan da ta gani a rubuce, da sauri ta ƙarasa wajen wani mai saida man fetur
da ta gani cikin sanyin murya ta yi sallama. Amsawa ya yi ta ce"dan Allah Baba ina
ne Nassarawa G.R.A?" shiru ya yi sai kuma ya ce "nan ma dai Nassarawa ce, amma idan
wajen G.R.A kike tambaya to adaidaita za ki samu ki faɗa masa sai ya kai ki". Shiru
Imara ta yi sai kuma ta ce"to Baba dan Allah ko zaka aramin kuɗi na hau mota, gobe
idan zan zo makaranta sai na kawo maka" waro idanu ya yi ya ce"yarinyar kin ganni
nan nima fafutuka nake na samu abin da zan je na bawa iyalina, banida kuɗin da zan
ara miki, amma za ki iya tsaida mai napep idan ya kai ki unguwar sai ki shiga gida
ki karɓo" to kawai ta ce sannan ta bar wajen, titi ta tsallaka ta tsaida adaidaita
kamar yanda ya ce mata sannan suka tafi.
Wani haɗaɗɗen hadari ne ya haɗo, lokaci ɗaya gari ya yi wani irin jaa, sosai Imara
ta tsorata ta shiga kwaɓe fuska dan idan akwai abin da ta tsana to ruwan sama ne.
Yayyafi aka fara da ƙarfi, tsayawa mai adaidaitan ya yi ya ce
Wani tsaki ya ja ya ce"sauka to, ni juyawa zan yi" tsoro ya bata yasa ta sauka,
cikin kuka ta ce"to ai sai mun je gidan zan baka kuɗin" wani mugun kallo ya watsa
mata ya ce"lallaima kin raina ni, kinsan da bakida ko sisi kika hawo min mota?"
Girgiza kai kawai ta shiga yi jikinta na rawa saboda sanyin daya fara yi mata yawa.
Tsaki kawai ya ja sannan ya juya ya shiga adaidaitar ya bar ta a wajen. Wani sabon
tsoro ne ya kama Imara, ta fashe da kuka ta tsuguna a wajen ta dunƙule jikinta tana
kuka.
***Umaima ce ta shigo ɗakin tana kallonta ta ce"ki je inji Mamah?" Nana dake danna
wayarta ta ɗago ta ce"okay". A hankali ta shiga takowa falon tana kallonsu sai kuma
ta ƙarasa inda Mamah ke zaune ta ce"Mama gani"
Okay Umaima ta ce sannan ta koma saman, not too long ta dawo ta ce"Mamah ai
batanan, kamar ma bata dawo ba fa"
"What?" Abbiey ya faɗa yana sake kallon Umaima, Mamah ce ta kalli Nanah ta ce"ke ba
tare kuka dawo ba?, ko ta fita ne?" murya ƙasa ƙasa ta ce"ni ba tare muka dawo ba
Mamah, ni kaɗai driver ya ɗauko"
Rufe bakinta ya yi daidai da sakkowar Abaan ya kalleta cikin wata kakkausar murya
ya ce"me kika ce?, acan kika barta kenan?" kuka ta fara yi ta shiga girgiza kanta.
Waje Abaan ya yi ba tareda ya sake kallon kowa ba, wani wawan mari Mamah ta sakar
mata, sosai ta gigice ta shiga kuka tana riƙe kuncinta. Murmushi Jidda dake zaune
gefen Jadda tayi tana addu'ar Allah yasa kar a ganta.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
35&36.
08106608363.
Kai tsaye makarantar su ya nufa, har sannan kuma ruwa ake sosai. Shiga makarantar
ya yi har office ɗin director saidai bai same shi ba, dan ya fita, shiru Abaan ya
yi sai kuma ya fito daga gate ɗin makarantar. Mai saida man fetur ya gani ya ƙarasa
wajensa ya yi sallama cike da girmamawa ya ce
"Baba dan Allah ba kaga wata yarinya ba?, yar fara haka"
Shiru ya yi sai kuma ya ce "to ina yawan ganin fararen yara suna fitowa daga
makarantar nan, amma da zan ga koda hotonta zan iya shaidata"
Wayarsa ya ciro ya nuna masa wani hoton Imara wanda batasan ma an dauke shi ba.
Saurin jinjina kai ya yi ya ce "Eh tabbas naganta. Yarinyar ta zo take tambayata
hanyar da za ta yi ta kai ta Nassarawa G.R.A to na ce dai ta samu me Napep ya kai
ta, kuma ina ganinta ta hau Napep" shiru Abaan ya yi sai kuma ya yi masa sallama ya
koma motarsa. Indai har ta shiga motar zuwa Nassarawa to tabbas tana cikin unguwar
kenan.
***Banda kuka babu abin da Nana ke yi ta takure waje guda, kallonta Mamah ta yi ta
ce"za ki gane bakida wayo, saboda rashin hankali ki tawo ki barta acan bayan kinsan
yarinyar ba yar nan ba ce. Duk abun da ya sameta ai mune a ciki tunda baƙuwarmu ce"
"A'a Mamah maybe fa ko ganin yarinyar ne ba ta yi ba, kuma kinga an tashi daga
makaranta ai mutum so yake ya dawo gida, ko Nana?"
Da sauri Nana ta ɗaga kai tana kallon Jidda ta ce"A'a Aunty Jidda ba haka bane, na
ganta fa, na ce mata ta taso mu tafi ta yimin banza, sau uku ina kiran sunanta ko
kallona ba ta yi ba saboda lokacin tana tsaye da wani ɗan ajin mu, daman ko a aji
bata nuna ta sanni ba, shiyasa kawai na tawo na barta"
Ta ƙarashe maganar tana kuka, cikeda masifa Jidda ta ce"ni daman nasan wlh akwai
saka hannun ta, saboda tun da naga yarinyar naga tanada rawar kai" tsaki Mamah ta
yi ta ce"ba sai ki kira waya ki faɗa ba, ai idan aka yi mata magana za ta tawo ko?"
Tashi Jadda ta yi ta kama hannun Nana tana cewa
"Karki wani ce za ki yiwa yarinya masifa, tun da ita waccen ce taga tafi ƙaunar
zama a makaranta. Ke mu je ciki" daga haka ta ja Nana suka bar parlon, shidai
Abbiey shiru ya yi bai ce komai ba yana kallonsu. Umaima kuwa girgiza kanta ta yi
dan ta tabbatar Nana ƙarya take, babu yanda za'a yi Imara ta ƙi yarda ta dawo gida,
tunda bata da inda ya fi nan.
***Wani burki ya ja ganin ya kusa karo da wata mota, ya yi tsaki sannan ya sake
kunna motar, ƙin tashi ta yi ya gwada har sau uku taki koda motsi. Sauka ya yi
lokacin ruwan ya daina zuba sai yayyafi, tayar motar ya kalla yaga ta yi faci ya ja
tsaki. Kasancewar ya kusa gida yasa ya fara tafiya yana kalle kallen hanya ko zai
hangota. Can gefe ya hangeta a tsugune fuskarta a rufe, babu ko haufi ya ƙarasa
inda take ya dafata, a razane ta ɗago tana wani irin numfashi. Tsungunawa ya yi a
gabanta ya shiga girgiza ta, faɗawa tayi jikinsa tana wata iriyar karkarwa,
rungumeta ya yi tsam a jikinsa ya shiga shafa kanta cikin cool voice yake faɗin
Ko kaɗan Imara ba ta jin abin da yake cewa, dan gabaɗaya hankalinta baya jikinta.
Tashi ya yi da ita a jikinsa ya yi mata ɗaukan jarirai, bata da nauyi ko kaɗan
hakan yasa ya fara tafiya toward direction ɗin gidan.
Har sannan suna zaune a parlon babu wanda ya tashi, da sauri Mamah ta ƙarasa inda
yake tana kallonsa ta ce"lafiya?, meya sameta?" bai ce mata komai ba ya shige ciki
da ita, ajiyar zuciya Mamah ta sauke tana dafe ƙirjinta, murmushi Umaima ta yi sai
kuma ta shige ciki da gudu itama. Jidda da baƙin ciki ya isheta taji ƙirjinta ya
fara yi mata nauyi ta yi saurin fita daga apartment ɗin, da idanu Abbiey ya bita
sai kuma ya ce
"Alhamdulillahi"
Murmushin jin daɗi Mamah ta yi ta ce"har naji daɗi wlh" jinjina kai kawai ya yi
sannan ya tashi ya bar parlon. Shi kuwa oga Khalil wani irin abu ne ya zo ya tokare
masa zuciya, idan ya buɗe idanunsa babu abin da yake gani sai Imara kwance a jikin
Abaan, takaici yasa ya bar falon without looking at anybody.
***Fitowarsa kenan daga wanka ya kalli inda take a kwance, har sannan bacci take,
numfasawa ya yi sannan ya ƙarasa gaban mirror ya shiga gyara jikinsa. Saida ya
shirya tsaf cikin wasu kananan kaya, riga armless milk colour sai wanda cargon 3-
quater baƙi, gashin kansa yasha gyara sai sheƙi yake, ya feshe jikinsa da turaren
roja. Fita ya yi daga ɗakin ya zauna a parlon yana kallon Al-jazeera. Yana nan
zaune har lokacin magrib ya ƙarato, kasancewar ruwan ya sake dawowa yasa basu fita
masallaci ba kowa ya gabatar da sallah a gida.
A hankali ta shiga buɗe idanunta tana kallon inda take kwance, tashi zaune ta yi
tana jin jikinta na wani irin ciwo, ga kuma zazzaɓi wanda har sannan bai saketa ba.
A hankali take sauke numfashi saboda yanda ƙirjinta yake a cure, tuna abin da ya
faru ta yi sai kuma ta fashe da kuka, wanda hakan ya yi daidai da shigowarsa. Kallo
ɗaya ya yi mata ya ƙarasa inda take ya kama hannunta ya zare drip ɗin, bai kalleta
ba ya juya zai fita.
"Ni ka mayar dani gida, wlh bazan sake zama anan gidan ba, banaso, bazan sake zuwa
makarantar ba!"
Juyowa ya yi ya watsa mata wani shegen kallo wanda ya sanya ta sunkuyar da kanta ya
juya ya fice ba tare da ya ce mata komai ba, sake rushewa tayi da wani sabon kukan
na shareta da ya yi ta kwanta akan gadon tana burgima.
Sai wajen ƙarfe 8:30pm sannan ya dawo ɗakin, lokacin ta yi shiru sai kalle kalle
take a kwance, zama ya yi gefen gadon ya kalleta ya ce"ke tashi anan" tashi zaune
ta yi ta tana kallonsa, cikin whiskey voice ya ce
"Koda wasa kar na sake jin kin ce wai ba za ki je makaranta ba, ko ke baki son
makaranta, dole ne ki je makaranta, dole ne kiyi karatu, kuma dole ne ki zauna a
gidan nan. Sannan irin haka banason ta sake faruwa ki tabbata kun dawo tare kullum,
idan ita tanada baki ke bakida shi ne!?"
Yanda yake maganar babu wasa ya sanya ta sunkuyar da kanta tana hawaye kawai. Turo
ƙofar ta yi ta shigo tana sunkuyar da kanta, zama ta yi a ƙasa ya kalleta ya ce
"Khadijah!"
"Nasan abin da kika faɗa ba shine abin da ya faru ba, kece kika tawo ki ka barta,
koda ban je na tambaya ba nasan abin da za ki iya aikatawa, ita ɗin ki ɗauketa
matsayin ƴar uwarki kuma ƙawarki, ba zaku shige shekaru ɗaya ba saboda haka banason
jin tashin hankali, duk ranar da irin haka ya sake faruwa ko kuma kika yi mata gori
zan tabbatar da cewa na hukuntaki kamar yanda na faɗa miki. Saboda haka ku zauna
lafiya, ku je makaranta tare ku dawo tare, tashin hankali ba naku bane, banason
faɗa banason baƙar magana kin ji ko?" Cikin rawar murya ta ce
"In sha Allah bazan sake ba, Imara dan Allah kiyi haƙuri" ta faɗa tana kallonta,
shiru Imara tayi tana kallonta ita ma
Murya can ƙasa ta ce"na haƙura, kema ki yi haƙuri" tashi Nana tayi ta zo ta
rungumeta, murmushi suka yi a tare ya kallesu ys ya ce "ku tashi ku je" jan
hannunta Nana ta yi suka fice daga apartment ɗin nasa. Akan idanun Khalil suka fito
daga ɗakin, kwafa kawai ya yi sannan ya bar wajen. Ɗakin Nana suka shiga, ita dai
Imara sai bin ta take da kallo, ganin ta tsaya yasa Nana ta ce"ki zauna mana, bari
na kawo mana abinci" a gefen gadonta Imara ta zauna ita kuma ta fice daga ɗakin.
***Ɗago kanta ta yi tana share mata hawayen ta ce"Jidda, ki daina wannan kukan,
kinsan dai ni a rayuwa banason naga abin da zai saka ki kuka, in dai Abaan ne ki
daina damun kan ki" cikin shassheƙar kuka ta ce"wlh Mommy banason ganin yarinyar
nan, ni kawai so nake na daina ganinta. Ko kuma Abaan ya daina ganinta, ko dai ta
bar gidan ko kuma ni da Abaan mu bar gidan, kawai a dawo da maganar saka ranar
auren nan dan Allah Mommy, ki faɗawa Abbiey, nagaji da jiransa, dan Allah Mommy wlh
idan ba haka ba za'a samu matsala, zan iya kamuwa da ciwon zuciya" saurin rufe mata
baki ta yi ta ce"kar na sake jin kin fadi irin wannan maganar, ki saka a ranki
kamar an yi auren ki da Abaan an gama. Za ki aure shi nan da ɗan lokaci wanda ko ke
ba kiyi tunani ba"
Goge hawayen ta shiga yi ta ce"Nagode Mommy, nasan duk abin da nakeso za ki yimin"
shafa kanta ta yi ta ce"zan yi komai saboda ke gudaliya ta"
Washegari da wuri suka shirya driver ya ɗaukesu, tare duk suka tafi aka fara ajiye
su sannan aka ƙarasa da Umaima, yau a waje ɗaya suka zauna saɓanin ji da suka raba
wajen zama. Kasancewar duk suna da kokari yasa suka iya karattunka su na ranar
ƙarfe 4 suka fito daga lecture kamar jiya. Suna tafiya a second floor ya hangesu,
ƙarasowa ya yi suka gaisheshi, murmushi ya yi ya ce"Imara ko?, ya kike ya gida?"
cikin sakin fuska ta ce"Alhamdulillah sir" jinjina kai ya yi ya ce"ba dai gida za
ki tafi ba?" gyaɗa masa kai tayi kawai ya ce"to mu je sai nayi dropping naku"
kallon Nana tayi sai kuma ta girgiza kanta ta ce"a'a driver ya zo ɗaukar mu yana
ƙasa, Thank you" ɗan murmushi ya yi ya ce"okay tom sai gobe" sallama suka yi masa
sannan suka cigaba da tafiya. Saida suka sauka ƙasa Nana ta kalleta ta ce"wato daga
zuwan ki makaranta har kin yi saurayi ko?, sai na faɗawa Uma" kwaɓe fuska Imara
tayi tana kallonta ta ce"mene haka dan Allah, kina gani fa malami ne, wane ya ce
miki cewa ya yi yana sona?" Tuntsirewa da dariya Nana ta yi ta ce"ai idan kaga kare
na shinshinar takalmi to ɗauka zai yi, wlh ko kaffara bazan yi ba sonki yake,
kinsan yanda yake ignoring mutane kuwa, taɓ" turo baki Imara tayi ta ce"to nidai
babu ruwana, dan ni ba yar iska ba ce, karatu nazo yi ba soyyaya ba" dafata Nana ta
yi ta ce"kin ga Malama lokacin abu a yi shi, idan mun je gida ki cewa Yaya ko
Abbiey a siya miki waya saboda assignment, kinga sai ku dinga gaisawa ko?" kallonta
Imara kawai tayi sai kuma ta shige mota ba tare da ta bata amsa ba.
***Driver na yin parking ta buɗe motar ta fito tana riƙe da takardun ta, a ƙofar
entrance ɗin gidan ya ganta tana ƙoƙarin shiga
"Imara"
Juyowa ta yi sai kuma ta ƙara inda yake zaune ta sunkuya ta gaida shi, murmushi
Khalil ya yi ya ce"an dawo?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"sannu, fatan dai kina
ƙoƙari?" gyaɗa masa kai tayi tana murmushi, daidai nan Nana ta ƙaraso wajen ta
kalleshi ta ce"yawwa yaya dan Allah ka siya mata waya, ana bada assignment kuma
batada ita" murmushi ya yi ya ce"to shikenan kuje ku huta, idan anyi magrib sai
muje shopping right?" Tsalle Nana ta shiga yi ta ce"yawwa shiyasa nake sonka" ta
janye hannun Imara suka shiga gidan.
Mamah ce zaune a parlon sai Jadda tana faman aikin bada labari, tana ganinsu ta
ce"an dawo?" murmushi Nana ta yi ta ce"kuma yunwa muke ji Mamah"
"To acici ke wannan yarinya wanda ya aureki ya gamu da wahala, ba zaki bar masa
abinci ya huta ba"
Kallon Jadda ta yi sai kuma ta murguɗa mata baki ta ce"to ai naga Abbiey ne dai ya
siyo abincin" sakar baki Jadda tayi sai kuma ta ce"Muhammadu Rasulullahi, au gori
za ki yimin, to ai ko shi uban naki da ban haifeshi ba bazai samu dukiyar da har
kike taƙama da ita ba" ɗaga kafada Nana tayi tana tafiya ta ce"ai ko baki haifeshi
ba wata zata haifeshi" kwafa Jadda tayi ta ce"za ki zo har nan ki sameni" .
Kallon Imara tayi wacce ke tsaye ta ce"yawwa ƴar albarka je ki ɗakina ki daukon
wata roba a kusada gadona ki zo na baki abin daɗi" to Imara ta ce sannan tayi
apartment ɗin Jaddan, Murmushi kawai Mamah tayi tana binsu da kallo.
Around 7pm Umaima ta shigo tana kallon su ta ce "naga kun yi shiri ina za ku je?"
Nana dake rolling mayafi ta ce "unguwa"
"Unguwa kuma?"
Umaima ta maimaita.
"Eh Yaya Khalil ne ya ce mu shirya zai kai mu shopping"
Turo ƙofar ɗakin ya yi ya shirya cikin wata shadda gezner blue colour sai zuba
ƙamshi yake. Kallonsu ya yi ya ce"kun gama?"
A compound ɗin gidan suka sameshi yana tsaye jikin motarsa, ƙarasawa suka yi Ita
dai Imara a hankali take tafiya, murmushi ya yi ya ce"wannan hijabin fa Imara?"
kallon jikinta tayi sai kuma ta sunkuyar da kanta. Murmushi Umaima ta yi ta ce"Yaya
ai kasan hijabin yafi mata kyau" jinjina kansa ya yi ya ce "to muje", gaban motar
ya buɗe mata ta kalleshi sai kuma ta shiga a hankali. Shiga baya sukayi sannan
shima ya zagaya ya shiga sannan suka bar gidan. Glasses ɗin idanunsa ya zare ya
tashi daga saman benan ya juya ya koma ɗakinsa.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.*IMARA 💋💋*
37&38.
08106608363.
Shopping sosai suka yi, kowa sai ɗaukar abin da yake so yake, bayan sun kammala ya
biya sannan suka baro wajen. Wani shago na saida wayoyi ya tsaya ya yi parking yana
kallonta ya ce"mu je ko?" gyaɗa masa kai kawai tayi sannan ta sauka daga motar.
Biyo bayansu Nana ta yi ita kuwa Umaima ta yi zamanta a mota tana danna wayarta,
wayar iphone 13pro max ya siya mata sannan suka bar wajen. Basu dawo gida ba sai
wajen 9:45pm, babu kowa a parlon sai tv dake faman aiki, kallonsu ya yi ya ce"oya
dare ya yi aje a kwanta" murmushi Umaima ta yi ta ce"mun gode Yaya" harararta ya yi
sannan ya shige ciki ya bar su a wajen, Imara na ganin ya bar wajen ta zare hijabin
jikinta. Kallonta Nana ta yi ta ce"muje muyi sallar isha'i sai mu kunna wayar muga,
kinga yanzu koda ya tambayeki numbern waya kinada ita"
"Waye zai tambayeta?"
Kallon Umaima tayi sai kuma ta ce"idan aka tambayeta a school fa" okay ta ce sannan
ta ɗauki ledarta ta bar parlon.
***Washegari suka shirya dan tafiya makaranta, ganin tana ƙoƙarin saka hijabi yasa
Nana ta ce"wai kullum hijabi za ki dinga sawa kenan?" gyaɗa mata kai Imara ta yi
kawai ta ɗauki jakarta ta fice daga ɗakin. Ta ƙofar ɗakinsa ta zo shigewa, haka
kawai ta ji tana son ganinsa, tura ƙofar ɗakin ta yi a hankali ta shige. Babu kowa
a parlon sai tashin ƙamshi da alama Mamah ta shigo ta gyara masa, yogurt ta gani
akan table ta ƙarasa ta ɗauka ta zauna kan kujera ta ɓalle murfin ta fara sha.
Saida ta shanye tas sannan ta yi gyatsa ta miƙe tsaye tana gyara zaman hijabinta
A razane ta juyo dan ba tayi tunanin yana wajen ba, turo baki ta yi tana wasada
fingers ɗinta ta ce"yunwa nake ji shiyasa" kallonta ya yi sai kuma ya ƙaraso
gabanta. Zama ya yi kan kujerar har sannan idanunsa na kanta, sunkuyar da kai Imara
ta yi tana kwaɓe fuska.
Wayarsa ya ɗauko ya shiga dannawa ba tareda ya sake ce mata komai ba, juyowa ta yi
taga ba ita yake kallo ta sunkuya ta ɗauki jakarta zata fita.
Kamar za ta yi kuka haka ta dawo ta zauna a ƙasan carpet, wayarta ce ta fara ƙara
ya juyo ya kalli jakar tata. Ciro wayar ta yi taga sunan Nana, za ta ɗaga kiran ya
karɓe wayar ganin an saka Nana yasa ya ɗaga ya saka a handsfree
Kashe wayar ya yi kawai ya ajiyeta gefensa, kusan 5mins bai ce komai ba ta kalleta
murya can ƙasa ta ce
"Na tafi?"
Idan kujerar da Abaan ke kai ta yi magana to tabbas shima ya ce wani abu, ganin
haka yasa Imara kifa kanta akan gwuiwarta ta yi shiru tana tunani. Saida yaga dama
sannan ya ajiye wayar tasa ya ɗago yana kallonta ya ce
"Wane ya baki izinin fita jiya?, wa kika tambaya?, wane ya baki waya?"
A hankali ta ɗago kanta tana kallonsa ta ce"Cewa ya yi muje ya kaimu, kuma naga duk
su Nana sun shirya "
"Ko?"
Sunkuyar da kanta ta yi ganin ya haɗe rai. Cikin kakkausar murya ya ce"daga yau duk
ranar da wani ko wata zasu je wani wajen kika ce za ki bisu ko a kace ki zo aje
dake kika tafi za ki gane bakida wayo!" Gyaɗa masa kai kawai Imara ta yi ya tashi
ya shige bedroom ɗinsa.
Fitowa ya yi bayan ya sauya kaya zuwa wani yadi mai shara-shara coffee colour ana
ganin farar singlet ɗin daya sanya a ciki. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauki car key
ɗinsa ya fice daga ɗakin, biyo bayansa tayi da gudunta.
Babu wanda ta samu a parlon duk kowa ya fita Jadda kuma bata fito zama ba ranar,
waje ta yi da sauri lokacin har ya shiga motarsa, ƙarasawa tayi ta buɗe front seat
ta zauna, saida ya yi warming motar sannan suka bar gidan. Sun yi nisa sosai ta ji
cikinta ya fara murɗawa saboda yunwa, jakarta ta buɗe ta ɗauko biscuit wanda ta
siyo jiya ta fara ci, ta gefen idanu ya kalleta sai kuma ya cigaba da tuƙinsa, ga
mamakinta sai taga ya yi parking a cikin asibiti. Kallonsa ta yi sai kuma ta
langwaɓar da kai tana taunar biscuit ɗinta, sauka ya yi daga motar ya fara tafiya,
da idanu kawai ta dinga bin sa har ya ɓacewa ganinta. Saida ta cinye biscuit ɗin
tas sannan ta ɗauki ruwa ta sha, sosai taji ta ƙoshi dan daman ita batada yawan cin
abinci.
Tana nan zaune har sama da awa ɗaya ba taga ya fito, zuwa lokacin ta gaji da zaman,
buɗe motar ta yi ta sakkowa tayi daga motar ta gyara hijabinta. Rufe motar tayi da
makulli sannan ta fara tafiya, kasancewar ta gane inda ya kai ta rannan yasa
batasha wahala ba, tana zuwa ta tura ƙofar office ɗin, zaune ta hangeshi yana danna
system ɗinsa. Ƙarasawa tayi ta zauna kujerar kusa da shi kamar za tayi kuka ta ce
Ganin bai kalleta ba yasa ta tashi ta koma inda yake zaune ta shiga jan rigarsa,
sai a sannan ya ɗago ya zuba mata idanu, sunkuyar da nata idanun ta yi dan ba zata
jure kallon cikin idanunsa ba.
"Mene kuma?"
Zumɓura baki ta yi ta ce
"Ni na makara, kawai ka bani kuɗi na hau napep, ko kuma ka bani key ɗin motar na
tafi kawai" ta faɗa tana yarfe hannu. Girgiza kansa kawai ya yi ya ce"ai kin daina
zuwa makaranta"
Waro idanu ta yi ta kalleshi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce"dan Allah ka bari, ni
inason na je makaranta, kaji" ture hannunsa ya yi daga jikinsa ya harareta ya
ce"karki sake taɓani"
"To meyasa?"
Girgiza mata kai ya yi yana rufe system ɗin sa, buga ƙafa ta shiga yi tana kallonsa
ta ce"to ya isheni ni, zafi nakeji, kowa mayafi yake sakawa fa"
Murmushi ta yi ta ce"Eh ni ba kowa ba ce, ni Imara ce yar gatan Allah sai kuma
Mamah sai kuma..."
Kallonsa ta yi ya ce"sai kuma me?" Girgiza kia ta yi ta ce"ba komai" taɓe baki ya
yi, bai sake magana ba ya fice daga office ɗin,
Ganin inda yake tafiya daban yasa ta ce"ba school ɗin zaka kai ni ba?"
"Eh".
Shiru ya yi mata, ta ce"ni banason ana yimin shiru fa, ka ce ka haƙura" banza ya
sake yi mata ai kuwa ta fashe da kuka, tsaida motar ya yi yana kallonta ya ce"ko
kiyimin shiru ko kuma ranki ya ɓaci" ƙara volume ɗin kukan ta yi ya kalleta ya ce
Washe baki tayi ta ce"tarawa zan dinga yi, har sai sun kai na siya gida na koma"
jinjina kai ya yi yana murmushi ya ce"au gida ma za ki siya kenan".
"Eh, babban gida nakeso, harda yan aiki su dinga yimin girki nikuma ina kwance"
Murmushi Abaan ya yi yana jinjina yarinta irin ta IMARA, ganin bai ce komai ba yasa
ta ce"ayyah, ai zan bar mai gadi ya buɗe maka idan ka shigo. Saboda Dodo ya taɓa
cemin kada na saka Alkhairi da sharri, to ai kaga kaima ka yimin Alkhairi tunda ka
kawoni gidan ku kuma ana bani abinci ko?"
Dariya mara sauti ya yi ya ce"Ni za'a barni na shigo kenan?" Gyaɗa masa kai ta yi
ya ce"kenan kina yarda da maganarsa?" Saurin gyaɗa kai tayi ta ce"Eh mana, to ai
shima yana sona, kuma shine ya kai ni makaranta, inason na ganshi"
Turo baki ta yi ta ce"ai idan na ganshi ba magana zan yi masa ba, tunda ya tafi ya
barni, kuma Umma ta mutu bai zo ba. Kuma nazo aka aura min Maheer nan ma bai zo ba.
Ya barni na sha wahala, kuma gashi Maheer ya sakeni, yanzu kuma babu wanda zai
aureni ko?"
Tunda ta fara magana Abaan ke kallonta dan parking motar ma ya yi, hawaye ya gani
akan fuskarta ya sanya hannunsa yana goge mata. Da sauri ta kalleshi sai kuma ta
kalli hannun nasa, murmushi ya yi ya ce"kika sani ko wani babban dalili ne ya sanya
shi ya tafi ya barki?" Girgiza kanta ta yi ta ce"amma ai da ya faɗa min, kowa haka
yake cemin banida dangi kuma da gaske banida kowa, ni kaɗai ce kawai. Ni nafison na
mutu ma wlh "
Zuwa sannan kuka sosai Imara ke yi, jawota jikinsa ya yi ya rungumeta yana shafa
kanta. Yana jin tana shassheƙar kuka
"Ki daina kuka kin ji, ba gani nan ba uhn, bazan bari wani abu ya sake samunki ba,
ki daina kuka kinji"
Gyaɗa masa kai ta shiga yi, suna nan zaune a haka har bacci ya ɗauketa. Ɗago
fuskarta ya yi yana kallonta sai kuma ya yi murmushi ya ce"cry cry baby".
***Ƙarfe 4:56pm Jadda ta tafi daga apartment ɗin ta tana ƙwalawa Mamah kira, fitowa
daga kitchen Mamah tayi tana kallonta ta ce"gani Jadda"
"Maza maza kira min Fadeel a waya, duk inda yake Inason ganinsa yanzu" cikeda
damuwa Mamah ta ce"Jadda lafiya dai?"
"Malama banason tambaya kiyi abun da nace miki kawai" da idanu kawai Mamah ta bita
sai kuma ta hau sama ta ɗauko wayarta, ringing ɗaya Abbiey ya ɗaga bayan tayi
sallama ta sanar dashi saƙon Jadda, sosai ya yi mamaki rashin sanin dalilin kiran
yasa ya ce ta ce mata gashi nan. Ala dole ya tashi daga abin da yake driver ya
ɗauko shi zuwa gida.
"Aure kuma Jadda?, amma naga yanzu ba shine lokacin daya dace ba ko..."
Dakatar dashi ta yi ta ce"banason jin wata magana da Fadeel, idan har na isa dakai,
kai kuma ka isa da Jidda da Abaan to Inason ka shirya maganar aurensu daga nan zuwa
ƙarshen wannan watan da muke ciki, idan kuma kai ma zaka wulaƙanta ni ne kamar
yanda ɗan uwanka ya yi to shikenan, sai na san haihuwa bata yimin rana ba"
"Wane bakin nasa?, kenan sai yanaso zaka aikata, idan ya nuna baya buƙata a haƙura
ko?, to bari ka ji banason wani ji ta bakinsa, kai ne ma ɗaurin aurensa saboda haka
kawai a ɗaura aure koda yardarsa ko kuma babu"
Wani irin bugu ƙirjin Mamah yake yi, an ya kuwa Jadda lafiya klao take?, tasan me
take cewa?, ya za'a yi Abaan ma ya yarda?!, wannan tunanin ya sanya ta fara kiran
innalil lahi a cikin ranta.
Ajiyar zuciya Abbiey ya sauke ya ce"shikenan Jadda, yanda kikeso haka za'a yi in
sha Allah" jinjina kai tayi daidai lokacin Abaan ya yi sallama ya shigo Imara na
biye dashi.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *JADDA*
# *Nanameera*
# *2025.*
*IMARA 💋💋*
39&40.
08106608363.
Ajiyar zuciya Abaan ya sauke yana kallon Abbiey ya ce"Abbiey why?" Girgiza kai ya
yi cike da damuwa ya ce"Muhammad abun ne ya fi ƙarfina ka dai san halin kakarka,
bansan mene ya sameta ba da har ta yanke irin wannan hukunci, ba zan iya yi maka
dole akan auren Jidda ba amma ina tunanin abin da zai je ya dawo. Shiru ya yi yana
kallon Abbiey kafin ya miƙe tsaye ya yi hanyar fita daga parlon
Da sauri Abbiey ya juyo ya kalleshi zuwa sannan kuma ya fice daga falon. Ajiyar
zuciya ya sauke yana godiya ga Allah domin da Abaan bai yarda da auren nan ba bai
san abin da zai ce da Jadda ba.
***Tun da ta shiga ɗaki ta nemi waje ta zauna, haka kawai ta ji ba ta jin daɗi
zuciyarta na bugawa da ƙarfi, buɗe ɗakin a kayi ta ɗaga idanun ta kalli Nana wacce
ta shigo ɗakin, zama ta yi gefenta tana murmushi ta ce"shine yau ki ka ƙi zuwa
makaranta ko?, muna ta jiranki baki fito ba" cikin sanyin murya Imara ta ce"to ai
na je wajensa ne kuma shine ya ce ba zan je makarantar ba"
"Wane haka?"
Turo baki ta yi ta ce"wannan mana, babban yayan gidan nan" tuntsirewa da dariya
Nana ta yi ta ce"wai Yaya?" Gyaɗa mata kai ta yi, Nana ta ce "lallaima, to Yaya
Abaan sunan sa, Babban soja ne da kike ganinsa kuma ba ɗan ƙasar nan bane" taɓe
baki Imara ta yi, kamar an tsikareta kuma ta gyara zamanta tana kallon Nana ta ce
Gyaɗa mata kai Nana ta yi, Imara ta tashi tsaye ta fara tafiya a ɗakin tana
murmushi, biyo bayanta Nana ta yi tana kallon ikon Allah, ganin kamar ta samu
matsala yasa ta ɗan dafata can ƙasa da murya ta ce
"IMARA"
Juyowa ta yi sai kuma ta rungumeta tana dariya ta ce"wlh ina son shi, shi nakeso
ni, ina sonshi sosai wlh, kuma shi zan aura"
A fusace Nana ta ture ta daga jkinta tana yi mata kallon kin yi hauka ta ce"me ki
ka ce?, kina cikin hayyacinki kuwa?, Yayan ki ke so?, Yaya Abaan ɗin?, kinsan kuwa
wane shi?"
Ɗaga kafaɗa Imara tayi irin bai dame ta ba ta ce"ni fa babu ruwana da ko wane shi,
jami'in tsaro nakeso na aura kuma gashi na same shi, I'm so lucky wlh"
Nana was speechless, sai bin Imara take da kallo tamkar wata zararriya. Girgiza
kanta kawai ta shiga yi dan da alama wasu aljanun sun shiga jikin Imara ba tare da
kowa ya sani ba.
***Around 9pm ya shigo hannunsa riƙe da wasu ledoji guda biyu, kai tsaye apartment
ɗin Jadda ya shige, zaune ya sameta kan ladduma tana jan tsazbaha, zama ya yi a
ƙasa kusa da ita har sai da ta idar sannan ta juyo ta kalleshi, murmushi ya yi ya
ce"Jadda" ajiyar zuciya ta sauke ta shafa kansa ta ce"Abaan, sannu ka ji, sannu da
ƙoƙari, Allah ya yi maka albarka" lumshe idanunsa ya yi ya ɗora kansa bisa
cinyarta, sosai ta ji tausayin sa, a duk san da ya yi mata haka ta gane kewar
mahaifiyarsa yake. Shafa kansa ta shiga yi tana karanto masa addu'o'i, tana jin
yanda yake sauke numfashi a hankali har bacci ya yi gaba da shi.
Sanye take cikin wata doguwar riga ta atampa, a-shape ta rufe gashin kanta da wani
veil ya zubo ta bayanta, a hankali take tafiya fuskarta fal murmushi. Zaune ta sami
su Umaima suna cin abinci ta zauna a kusa da Umaima tana kallon Nana wadda ke yi
mata wani irin kallo kamar me tsoronta. Dariya Imara ta yi, Umaima ta kalleta ta
ce"Lafiya dai Imara?" Nuna mata Nana ta yi wadda ke faman zare ido. Dariya ita ma
Umaima ta yi ta ce"lafiya me aka yi mata?" shiru Imara tayi har sannan murmushi
take. Harararta Nana ta yi ta ce "ni ki daina kallona" gwalo ta yi mata ta ce"na
kalla ɗin, ni zo ki ga" a hankali Nana ta taso ta dawo inda take zaune ta zauna ita
ma, kallo Umaima ta kunna a wayarta hakan yasa suka fasa aikin suka maida
hankalinsu kan kallon da suke. Kiran wayar Umaima a aka yi hakan yasa ta tashi ta
bar wajen, murmushi Nana ta yi ta ce"ki ce masa ina nan ina jiransa a Naija"
harararta kawai ta yi ta shige kitchen da sauri. Kallon Imara Nana ta yi ta ce
***Wani ihu Umaima ta saki wanda y saka Nana shiga kitchen ɗin da sauri. Tana
ganinta ta rungumeta tana dariya ta ce
"Yaya ya dawo, Yaya ya dawo Nana, I'm so happy wlh" ihu suka sake saki a tare
daidai nan Mamah ta shigo kitchen ɗin, kallonsu ta yi ta ce
"Mamah Yaya Kamal ne ya dawo daga Uk kinga kuwa dole mu yi murna, yanzu ma zamu
fara tunanin abin da zamu yi masa gobe idan ya zo ne"
"Da gaske, kai amma na ji daɗi sosai Yarinya, Allah ya yi miki albarka" murmushi
kawai Imara ta yi, Jadda ta ce"kuma ina da wani alkaki da aka yomin, gashi wannan
sangartaccen yaron ya zo ya wani kwanta min a jiki" dariya Imara ta yi ta ce"to ki
tashe shi Jadda man" girgiza kai Jadda ta yi ta ce"a'a fa, ai ba'a tashin sa yana
bacci tun yana yaro" jinjina kai Imara ta yi sai kuma ta leƙa fuskarsa, haɗe rai ta
ga ya yi ta ɗago ta kalli Jadda ta ce
Da sauri Jadda ta kalli inda Abaan yake sai kuma ta ce"ke bacci man yake, ina jin
saukar numfashinsa ɗazu"
"N rantse Jadda ya tashi, bari kiga" tana faɗin haka ta tashi ta koma daidai inda
fuskarsa take ta kwalla ƙara. Da sauri Abaan ya tashi zaune ya shiga bin ta da
idanu. Tuntsirewa ta yi da dariya tana kallon Jadda ta ce"kin gani ko, wlh ya tashi
daga baccin fa" kallonta Jadda ta yi sai kuma ta kalle shi ta ce"kaga ƙaton banza,
kai yanzu da ba baccin gaske ka ke ba ka bi ka taushe min ƴar ragowar cinyar tawa"
langwaɓar da kai ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce"Jadda bacci fa nake ji"
Gyaɗa mata kai Imara ta yi tana murmushi, kwafa Abaan ya yi ya kalleta kawai bai ce
komai ba, wata robar dambun kaza Jadda ta kawo mata, ta ajiye a gabanta. Ganin
yanda yake ganin robar yasa Jadda ta ce"tashi ki je kitchen ki ɗauko leda ki ɗan
sammasa ko kaɗan ne kar mu shiga haƙƙinsa ido guba" kallonsa Imara ta yi taga ya yi
murmushi, turo baki ta yi batasan yi wa Jadda musu ya sa kawai ta tashi ta shiga
kitchen ɗin. Miƙewa Abaan ya yi ya kalli Jadda ya ce"sai da safe, na tafi" riƙe
haɓa ta yi ta ce"au ba zaka ci dambun kazar ba?" Kallon robar ya yi sai luma ya
saka hannu ya ɗauke duka ya yi waje, daidai nan Imara ta fito daga kitchen hannunta
riƙe da farar leda. Kallon Jadda ta yi ta ce"Jadda ina ya tafi dashi kuma?"
Da gudu Imara ta bi bayansa, saidai bata same shi ko a falo ba, hakan yasa ta haye
sama da sauri. Zamewa ta yi, tayi baya zata faɗi ya riƙe ta, ɗagowa tayi ta
kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta ta ce "ina yini"
"Lafiya klao Imara, wannan gudun fa?, so ki ke sai kin ji wa kan ki rauni?" Girgiza
kai ta yi ta ce"abu na zan amso, bana son ya cinye ina zuwa" daga haka ta shige ta
bar Khalil tsaye a wajen. Ƙofar apartment ɗin Abaan ya ga ta shige sai kawai ya ja
ya tsaya a wajen yana jiran fitowarta.
***Babu kowa a falon hakan yasa kai tsaye ta shige ɗakinsa, dan ba baƙonta bane,
kama ƙugu ta yi ta rike ganin nan ma baya nan, ƙarar zubar ruwan da ta ji a banɗaki
ya sanya ta nemi waje ta zauna a gefen gadonsa. Above 10mins kafin Abaan ya fito
daga wanka yana sanye da bathrobe, sarai ya ganta sai kawai ya ɗauke kansa ya
ƙarasa wardrobe ɗinsa, wasu pyjames White colour ya ɗauko sannan ya dawo gaban
dressing mirror ya fara gyara gashin kansa, tana zaune har sai da ya kammala duk
wasu abubuwan dake gabansa sannan ya sanya rigarsa. Runtse idanu Imara ta yi ta
sanye hannayenta duka biyun ta rufe fuskarta, duk abin da take yana kallonta ta
mudubi bai kula ta bar ya kammala nan da nan ɗakin ya ɗauki wani sassayan ƙamshi.
Remote ya ɗauka ya ƙaro gudun AC, lumshe idanu Imara ta shiga yi tana jin wani
bacci na sanɗarta. Fridge ya buɗe ya ɗauko ruwa ya sha sannan ya dawo ya zauna akan
sofar dake ɗakin ba tare da ya kalleta ba, ganin yanda ya shareta ya sa Imara ta
taso ta dawo kan kujerar da ya zauna ta zauna itama tana kallonsa ta ce"ka bani
dambuna in ji Jadda"
"Mene haka?"
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025**IMARA 💋💋**IMARA 💋💋*
41&42.
08106608363
Girgiza kanta ta yi, sai kuma ta janye fuskarta a hankali ta ce"sai da safe"
hannunta ya kama ya ɗora mata robar naman ya ce"Allah ya tashemu lafiya, karki
manta ki yi addu'a" gyaɗa masa kai Imara ta yi sannan ta fice daga ɗakin. Ajiyar
zuciya Abaan ya sauke ya koma ya cigaba da aikin gabansa. Ko kaɗan ba ta lura da
Khalil ba ta tura ƙofar ɗakinta ta shiga tana wasa da robar hannunta. A gefen gado
ta ajiye robar sannan ta shige toilet dan watsa ruwa, tana fitowa ta sanya sleeping
dress ta ɗaure gashin kanta sannan ta kwanta akan gadon ta lumshe idanunta.
***A hankali ta juya da niyyar komawa ɗaya ɓangaren, rufar da ta gani ya sanya ta s
buɗe idanunta, a firgice ta tashi zaune tana kallon mutumin dake tsaye a kanta.
Baya ta fara yi tana girgiza kanta gabaɗaya jikinta rawa yake, ganin yanda ta tsora
ta ya sanya Khalil kunna hasken ɗakin, kallonsa ta yi sai kuma ta saki ajiyar
zuciya ta dafe ƙirjinta. Sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya ce"ki yi haƙuri na
tsorata ki" Imara ba ta ce masa komai ba ta sauka daga kan gadon ta ɗauko ruwa a
fridge ta ɓalle murfin, sai da ta kusa shanyewa sannan ta ajiye ta dawo ta zauna
can nesa dashi. Sun ɗauki mintuna babu wanda ya ce wani abu, Khalil na son aiwatar
da abin da ya kawo shi sai dai yana fargabar yanda Imara za ta karɓi al'amarin.
Turo baki ta yi dan bacci ta ke ji gashi ba za ta iya ce masa ya bar ɗakin ba, can
ƙasa da murya ta ce
"Yaya Khalil dare ya yi sosai fa, kuma gobe da safe ina da makaranta"
Zazzafan numfashi Khalil ya sauke kafin ya juyo ya kalleta ya ce"Na sani Imara,
yanzu ne lokacin da ya fi dacewa na zo inda ki ke shiyasa" ƙura masa idanu Imara ta
yi tana mamakin furucin bakinsa. Numfasawa ya yi sai kuma ya ce
"Imara tun ranar da idanuna suka yi tozali dake ki ka shiga raina, ki yi haƙuri da
abin da zan faɗa amma har cikin zuciyata ina ƙaunarki, nasan ba lallai ne na zama
wanda ya fara faɗa miki haka ba, amma ina da tabbacin zan yi nasara akan su duka.
Ina da niyyar mallakar ki matsayin matata ta sunna, ina fatan ba za ki juyamin baya
ba Imara"
Ras! Haka Imara ta ji gabanta ya faɗi, tashin hankali ƙarara ya bayyana akan
fuskarta, cikin rawar murya ta fara cewa
"Yaya amma ni ai kamar ƙanwarka nake, kuma ma kaga kai saurayi ne, ni kuma na taɓa
aure. Ina jin tsoro, dan Allah a bar maganar nan"
Ɗan murmushi Khalil ya yi ya miƙe tsaye ya ce"sanin haka yasa na fallasa miki
asirin zuciyata, nasan ba za ki ƙini ba, ina da wannan tabbacin Imara. Zan baki
lokaci ki yi tunani, amma ina fatan samun babban matsayi cikin zuciyarki." Da idanu
kawai Imara ta bi shi har ya fice daga ɗakin, wani irin gumi ta ji yana tsatstsafo
mata, duk da Ac dake kunne a ɗakin, me Khalil ya ke nufi?, idan har ya furta yana
son ta a gaban mutane ba za ta iya bijirewa ba kodan hallacin da mutane gidan suka
yi mata, haka kuma ba za ta iya haƙura da soyyayar Abaan ba!. Da wannan tunanin ta
koma ta kwanta, sai dai duk yanda ta yi da bacci ya ƙi zuwar mata, daga ƙarshe
kawai ta tashi ta shige toilet ta ɗauro alwala, sallar nafila ta hau yi, kafin daga
bisani ta zauna tana roƙon Allah ya zaɓa mata abin da ya fi Alkhairi a rayuwarta.
***Haka Imara ta cigaba da rayuwa a cikin gidan, duk yanda Khalil yake son magana
da ita haka take avoiding ɗinsa, domin bata fatan abin da zai haɗa su. A haka har
suka fara exams ta first semester a makaranta.
Zaune suke cikin wani ɗan ƙaramin restaurant dake cikin makarantar, da idanu Nana
ta bi Imara wadda ta zuba tagumi tun shigowar su. Har aka kawo musu abin da suka yi
order Imara ba ta sani ba, tsaki Nana ta yi sannan ta ɗan daki table ɗin gabansu, a
ɗan firgice Imara ta kalleta sai kuma ta shiga murje idanunta. Harararta Nana ta yi
ta ce
"Wannan tunanin babu abin da zai haifar miki sai wahala Malama, it's better for you
to stop it"
Ƙarfe 4:20pm suka fito daga paper, dafe kai Imara ta yi ta ce"wayyo uwata, nagaji
wlh" dariya Nana ta yi ta ce"za ma ki yi bayani ne Hajiya, gobe ma akwai paper"
zaro idanu Imara ta yi ta ce"Allah gamu gareka"
Waro idanu Nana ta yi ta ce"kai, kinga Yaya Khalil ne ya zo ɗaukar mu fa" da sauri
Imara ta kalli motar, shiru ta yi suka ƙarasa, fitowa ya yi yana kallonsu ya ce"yan
makaranta" dariya Nana ta yi ta ce"kai yaya, akwai wahala school wlh" dariya ya yi
yana kallon Imara ya ce"beauty wai haka?" gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi,
Khalil ya ce"to ai sai ku dage ku yi passing, idan kun gama exams za mu je yawo"
tsalle Nana tayi ta ce"shiyasa nake mugun son ka Yaya" dariya kawai ya yi sannan
suka shiga mota suka tafi. Sai da ya biya dasu mall ya siya musu chocolate sannan
suka tafi gida. Yana gama parking Imara ta sauka da sauri ta shige gida gudun ka da
ya yi kiranta, da idanu kawai Khalil ya bita sai kuma ya yi murmushi. Turus ta yi
ganin akwatina na kaya a zube a parlon, Jadda da wasu tsofaffi sai buɗe kayan suke.
Imara ta tambaya tana kallon Nana. "Yaya Abaan man, Aunty Jidda zai aura, gashi har
an kawo kayan lefe"
Wani irin abu ne ya tokarewa Imara a ƙirji, ta kalli Nana sai kuma ta sake kallon
tulin akwatinan, girgiza kanta ta yi muryarta na rawa ta ce"Jad... Jadda wai haka?"
"Eh mana, ashe baki sani ba, Aure zai yi kuma kwa huta, yaro ya girme a gida ya
zama magidanci babu aure" tamkar wadda aka zarewa laka haka Imara ta ji jikinta, ba
ta sake cewa komai ba ta shige ciki tana tafiya tana haɗa hanya. Da idanu Nana ta
bi ta sai kuma ta girgiza kai tana tausaya mata domin tasan abin da ke cikin
zuciyarta.
***Imara na shiga ɗaki ta nemi waje a ƙasa ta yi zaman dirshin, kuka takeson yi
amma ko kaɗan babu wani ruwan hawaye da ya rage a idanunta, gabaɗaya ƙwaƙwalwarta
ta tunkushe waje ɗaya, ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana maimaita furucin Jadda.
Daman aure zai yi ya barta?, ba ta ko samu damar sanar dashi sirrin zuciyarta ba
shine zai yi aure ya bar ta?. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma hawaye
ya biyo kuncinta, ta shiga rera kuka a hankali.
***Da gudu Jidda ta shigo kitchen ɗin ta na zuwa ta rungume Mommy tana dariya ta ce
"Mommy gaskiya Nagode sosai, an kawo kayan aurena fa, kuma yaya Adeel ya ce wai
sati uku za'a saka. Gaskiya nayi farin ciki, wannan malamin aikinsa yana yi"
girgiza kai Mommy ta yi tana dariya ta ce"da ai kina ɗauka ba zan iya ba, sai gashi
ta cikin ruwan sanyi mun buraɗa tsohuwar yanda ita kuma za ta tada musu hankali,
kinga yanzu kin zama surukar babban gida" tuntsirewa da dariya Jidda ta yi ta
ce"wlh kam naga aiki, yanzu dai kina ji Mommy ba wannan ba, ni banason zaman wannan
yarinyar a gidan nan please, idan mun koma wajen mutumin nan zan yi masa bayani.
Haka kawai na ji hankali bai kwanta da zamanta cikin gidan nan ba wlh" taɓe baki ta
yi tana wanke kayan miya ta ce"to ke mene na ki na damuwa da ita?, ke da za ki bar
mata gidan?, ai sai ta yi ta zama a cikinsa, ke da za ki tafi gidan aurenki?" Kwaɓe
fuska ta yi ta ce"ni a'a wlh Mommy, na riga da nayi alƙawarin sai na fitar da ita
daga gidan nan, saboda haka Allah hankalina ba zai taɓa kwanciya ba muddin ina
ganinta. Kuma Jadda sai wani jan ta take a jiki" murmushi Mommy ta yi ta
ce"shikenan, idan mun koma sai a yi masa maganar ta, ko kuma ki bari mu gama da
maganar aurenki, saboda dai kinsan me ya faru, dole ne kiyi abin da ya dace"
jinjina kai tayi ta ce" Haka ne Mommy, sannan kuma ni sai an dawo da hankalin Yaya
Abaan kai na, dan ko magana fa ba ya wani yimin, idan na kula shi kuma sai ya dinga
amsawa sama-sama, inason ya daina yarda da maganar kowa sai ta wa, ya daina ganin
ko wace mace a gabansa sai Jidda" murmushi Mommy ta yi ta ce"ke a tunaninki zamu
bar shi haka ne?, ai kawai ki zuba min idanu, ni nasan abubuwan da zan aikata"
rungumeta ta sake yi tana murmushi ta ce"shiyasa nake ƙara ƙaunar ki Mommy"
murmushi ta yi ta ce"nima haka Jiddona, duk wani abu da zai sanyaki farin ciki
shine abin da nake mudarin yi, zan yi komai domin farin cikin ki".
(Ba dai-dai bane a rayuwa uwa ta ce za ta yi wa ɗiyar ta duk wani abu da take so
koda kuwa hakan ya saɓawa shari'a ko kuma Addini, Iyaye mata a dinga kiyayewa,
farantawa yaro abu ne mai kyau, amma ban da saɓawa mahalicci wajen faranta ran ɗa.
Allah ya sa mu dace)
"Imara kinga yanda ki ka rame kuwa?, daga jiya zuwa yau, kar ki saka damuwa a ran
ki ki zo ki cuci rayuwarki akan abin da ba za ki samu ba, Yaya Abaan ya riga da ya
yi miki nisa Imara. Ka da ki manta Aunty Jidda ita ce wacce zai aura, ina da
tabbacin ba za ta taɓa bari ya aure ki ba. Kuma kema kin san da haka, saboda haka
ki maida hankalin ki akan karatun ki, shine kawai abin da zai taimaki rayuwar ki,
kina da buƙatar ki yi karatu Imara, domin shine kawai gatanki"
Goge hawayen fuskarta Imara ta yi tana kallon Nana ta ce"Nagode Nana, amma ba zan
iya cire shi a raina ba. Amma kamar yanda kika faɗa zan maida hankalina akan abin
da yake rayuwata, tunanin wani abu bana mara gata irina ba ne, tunanin wani zai so
ni ba abu bane mai kyau. In sha Allah zan cire shi daga raina, zan yi ƙoƙarin ganin
na gina rayuwata"
Dafa ta Nana ta yi ta ce"ni burina bai shige na ga kin kammala karatun ki lafiya
ba" murmushi ta yi ta ce"in sha Allah zan yi haka Nana".
***Tun daga wannan ranar Imara take gujewa kanta duk wani abu da zai haɗata da
Abaan, da zarar ta dawo daga makaranta take shigewa ɗaki ba za ta sake fitowa ba
sai gobe idan zata tafi makaranta. Ko da Mamah ta yi cigiyarta sai ta ce karatune
ya rike ta a haka har suka kammala jarrabawar aka basu hutu, lokacin kuma sauran
sati ɗaya bikin Abaan da Jidda. Zaune take kan kujera ta zubawa tv idanu duk da ba
fahimtar abin da ake cewa take ba. Ƙamshin turarensa ta ji nan da nan bugun
zuciyarta ya sauya, da idanu Mamah ta kalleshi ganin kamar ba shi ba ta ce"Son
lafiyarka kuwa?" girgiza kai ya yi ya ce"ki bada abinci a kawomin Mamah" sosai ta
yi mamaki ganin yau da bakinsa ya ce a kawo masa abinci, tashi ta yi ta shiga
kitchen ta haɗa masa tray na abincin sannan ta fito parlon. Zaune ta iske Imara har
sannan bata ko motsa ba
"IMARA"
*IMARA💋💋*
43&44.
08106608363
***A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Babu kowa a
parlon sai ƙamshin turare mai daɗi dake tashi, lumshe idanu ta yi kafin ta ƙarasa
ta ajiye tray ɗin akan ɗan centre tables ɗin dake tsakiyar parlon, zama ta yi kan
kujera tana tunanin rabonta da shigowa ɗakin, a ƙalla ta kai wajen sati uku ko
magana ba ta haɗata da Abaan ba. Tura ƙofar da a ka yi ya sanya ta ɗaga idanunta
tana kallonta, da wani irin kallo ta shiga bin Imara kafin ta ƙaraso gabanta, taɓe
baki ta yi fuska babu walwala ta ce"ke uban me ki ke yi a ɗakin nan?" kallonta
Imara ta yi sai kuma ta ɗauke kanta ba ta re da ta ce komai ba, baki buɗe Jidda ta
kalleta sai kuma ta yi kwafa ta ce"kee!, har kina jin ke wata ce da ina yi miki
magana za ki yimin shiru?, wane uban ki a ƙasar nan?, dame ki ke taƙama?"
"Duk abin da za ki yi, ki yi shi a kaina, amma kar ki kuskura ki sake sako ubana a
ciki, idan kuma ki ka sake wannan gangancin wlh sai na yi miki abin da ba ki taɓa
tunani ba!"
Imara ta faɗa tana huci, mamaki ya hana Jidda magana, har ita wannan yarinyar za ta
tsaya tana faɗawa magana, kwafa ta yi sai kuma ta ɗaga hannunta da niyyar marinta,
riƙe hannun ta ji an yi, ta juya tana kallonsa. Sanye yake cikin wata t-shirt black
colour sai wando 3-quater blue a jikinsa, gashin kansa sai wani sheƙi yake. Cikin
rawar murya ta ce"dan Allah ka ci ka min hannuna, na rantse da Allah sai na hukunta
ta" kallonta kawai ya yi sai kuma ya saki hannunta ya ƙarasa kan kujera ya zauna ya
shiga danna wayarsa, ban da huci babu abin da Jidda ke yi, ko da yau ba ta hukunta
ta ba, to ta ɗauki alƙawarin yi mata abin da har abada ba za ta taɓa mantawa da ita
ba. Ganin Abaan bai ce mata komai ba ya sanya ta juya ta fice daga ɗakin kamar za
ta tashi sama. Da idanu kawai Imara ta bi ta sai da taga ta bar ɗakin sannan ita ma
ta juya zata fita.
"Zo nan"
Abin da kawai ta ji ya furta kenan, turo baki ta yi sai kuma ta dawo ta zauna a
ƙasan in da yake zaune ta sunkuyar da kanta, sai da ya gama danna wayarsa sannan ya
ajiyeta a gefe ya kalleta ya ce"da me ki ke tunani?, kin korar min mata shine kuma
kema za ki tafi" fashewa da kuka Imara ta yi ta rufe fuskarta, murmushi kawai Abaan
ya yi sannan ya kamo hannunta, janyewa ta yi ya sake riƙeta ya dawo da ita gefensa,
hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta ya zuba mata idanu, ɗauke idanunta ta yi tana
kallon wani wajen tana hawaye.
Imara ta faɗa da sauri, girgiza kai Abaan ya yi, ta haɗe rai ta ce"to ba zan aure
shi ba, nima soja kawai zan aura" murmushi ya yi ya ce"to me yasa sai soja za ki
aura?, shi da baya zama a gida "
"Saboda idan wani ya yimin abu zan faɗa masa ya rama min, nikuma daman na zama
lawyer kaga babu wanda zai dinga yimin abu. Kowa zai dinga jin tsorona"
Tuntsirewa da dariya Abaan ya yi yana jinjina shashanci irin nata, turo baki ta yi
kamar za ta yi kuka ta ce"yanzu kai aure za ka yi ko?, kuma wannan Jiddar za ka
aura?, ni bana sonta" haɗe rai ya yi ya ce"kar na sake jin kin ce bakya son mutum,
ba'a cewa haka" gyaɗa masa kai ta yi kawai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Janyeta
Abaan ya yi ya tashi ya buɗe food flask ɗin, tuwon shinkafa ne miyar egusi wadda ta
ji wadatattun kayan haɗi, serving kansa ya yi sannan ya zauna a ƙasa ya tankwashe
ƙafafunsa ya yi bismillah ya fara ci, Imara na nan zaune har ya kammala cin abinci
sannan ya tashi ya shige bedroom ɗinsa, da idanu kawai ta bi shi sai kuma ta fashe
da kuka, ta sunkuyar da kanta akan kujera. Bayan mintuna ashirin ya fito cikin wata
sabuwar shigar, kallonta ya yi ganin yanda ta kifa kanta, bai ce mata komai ba ya
juya ya fice daga ɗakin, ya rufe ta ta waje.
***Zaune ya samu Jadda a parlon ita da su Umaima tana basu labari kamar yanda ta
saba, Jadda na ganinsa ta washe baki ta fara cewa "ango kasha ƙamshi, ina zuwa
haka?" Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"idan zan fita sai na faɗa miki inda
zani?, ki daina gulma" harararsa ta yi ta ce"ubanka ke gulma bani ba ɗan nema"
tuntsirewa da dariya Umaima ta yi tana kallon Jadda ta ce"Jadda Yaya fa zai biya ta
wajen siyarda nama"
"Haba?"
Ta faɗa tana washe baki, gyaɗa mata kai Umaima tayi, ta kalli Abaan wanda ke juya
mukullin motarsa ta ce"Allah sarki yaron kirki, Allah ya dawo da kai lafiya, dan
Allah idan ka tashi siyomin banason naman nan mai romo, nafison wannan mai dan
yaji-yajin wanda zan daɗe ina ci"
"Ko?"
Abaan ya faɗa, bai sake kuma bi ta kan Jadda ba ya yi waje abin sa. Yana shirin
fita daga gidan shi kuma ya shigo, kallo ɗaya Abaan ya yiwa motar sai kuma ya ɗauke
kansa, a compound ɗin gidan ya yi parking ya fito, sanye yake da wani farin yadi
mara nauyi, yanayin kwalliyarsa zaka gane akwai arziki a tare dashi duk da
kasancewar sa baƙar fata. Fuskarsa kamar gonar audiga haka ya ƙaraso wajen Abaan
yana zuwa ya tuntsire da dariya. Tsaki Abaan ya yi ya ce
"Mahaukaci kawai"
Sake tuntsirewa ya yi da dariya ya ce"kaga mutumin, ango kasha ƙamshi, kaga yanda
ka ke wani glowing, ko dai har Amaryar ta fara kula da kai ne?" Duka Abaan ya kawo
masa ya kauce yana dariya ya ce"ai wlh kai ma kasan wuce nan"
Gwalo ya yi masa, yana yin yanda suke wasa da dariya zai tabbatar maka da akwai
shaƙuwa mara misaltuwa a tsakaninsu. Girgiza kai Abaan ya yi ya ce"kai baka da
hankali shiyasa, ni kaga tafiya ta, dariya ya yi ya jawo hannunsa ya ce"haba Dude
mu je tare, ina za ka je na raka ka?" kallonsa kawai Abaan ya yi sai kuma ya shige
mota, a ɓangaren mai zaman banza ya zauna. Murmushi kawai Kamal ya yi sannan ya
zauna a driver seat, yana kallonsa ya ce"sarautar taka zaka nuna min kenan?, Allah
ya so nima dai Babana Sarki ne, ba iya ku kaɗai ku ke da sarauta ba"
Banza Abaan ya yi masa ya shiga danna wayarsa, murmushi kawai Kamal ya yi sannan
suka bar gidan.
***Sai bayan magrib sannan ta farka daga baccin daya ɗauketa, tashi ta yi ta sake
ƙoƙarin buɗe ƙofar, amma ta sake jin ta a rufe. Hawaye ta fara yi dan gabaɗaya ta
gaji da zaman ɗakin, ta juya ta koma ciki, abincin da ya rage ta zuba ta fara ci,
tana lumshe idanu dan ba karamin daɗi tuwon ya yi ba, kuma daman gata masoyiyar
tuwo. Tana gama ci ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito, rasa
abin yi ta yi hakan yasa ta shiga gyara ɗakin duk da ba datti ya yi ba, bayan ta
kammala gyara parlon ta shiga bedroom ɗin domin shima ta gyara shi. Sakewa gadon
bedsheet ta yi sannan ta kunna turare, Zama tayi a kan bedside drawer tana kalle-
kalle. Kamar wadda aka tsikara haka ta tashi ta shiga buɗe drawer, takardu ne duk a
ciki. Tsaki kawai ta yi sannan ta rufe, tana shirin mayarwa wani envelope ya fado,
ɗaukansa ta yi ta buɗe, hotuna ta gani a ciki a kuwa ta gyara zamanta ta shiga buɗe
su. Hoton farko wasu yara ne mace da namiji a tsaye, daga gani namijin shine babba
domin ya fita tsawo da jiki nesa ba kusa ba. Murmushi ta yi sannan ta sake ciro
wani hoton, nan ma hoton yaran ne sai dai wannan karan akwai ƙarin wani babban
mutum daga gani kasan mahaifinsu ne, kai daga ganin hoton kasan asalin larabawa ne,
sake ware idanunta ta yi dan gani ta yi kamar ta taɓa ganin irin fuskar sai dai ta
manta in da ta santa. Ɗaya hoton kuma hoton Abaan ne sanye da kayan sojoji, gefensa
kuma wani babban mutum ne shima sanye da irin kayan nasa, da alama gaba yake dashi
ko a wajen aiki. Murmushi kawai Imara ta yi dan ba ƙaramin kyau hoton ya yi, haka
kawai ta ji hoton ya burgeta, turo ƙofar ɗakin da a kayi ya sanya ta yi saurin
mayar da hotunan ba tare da ta kammala kalla ba. Da idanu Abaan ya bita sai kuma ya
ƙaraso in da take zaune, zama yayi gefen gadon yana kallonta ya ce"kin gaji ne?"
Saurin gyaɗa masa kai ta yi kamar za ta yi kuka ta ce"ni ka buɗe min na fita" ɗan
murmushi kawai ya yi sannan ya tashi ya fara cire agogon dake hannunsa yana ƙoƙarin
shiga toilet ya ce"ai yau anan za ki kwana!"
# *IMARA 💋💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*Sauran posting 3 na kammala book 1, and book 2 paid book ne ₦500, wanda suke yin
payment kafin na kammala book 1 zasu bada ₦400 a matsayin promo, nan da kwana biyu
zan kammala book 1, saboda haka a cigaba da payment na book 2 kafin lokaci ya ƙure,
nafison a fara da kowa, a tura kuɗi ta wannan account ɗin 7041901078 Hauwa Adamu
lawan opay, sai a turo shaida ta number ta, 08106608363 Nanameera, Nagode.*
41&42.
08106608363
Girgiza kanta ta yi, sai kuma ta janye fuskarta a hankali ta ce"sai da safe"
hannunta ya kama ya ɗora mata robar naman ya ce"Allah ya tashemu lafiya, karki
manta ki yi addu'a" gyaɗa masa kai Imara ta yi sannan ta fice daga ɗakin. Ajiyar
zuciya Abaan ya sauke ya koma ya cigaba da aikin gabansa. Ko kaɗan ba ta lura da
Khalil ba ta tura ƙofar ɗakinta ta shiga tana wasa da robar hannunta. A gefen gado
ta ajiye robar sannan ta shige toilet dan watsa ruwa, tana fitowa ta sanya sleeping
dress ta ɗaure gashin kanta sannan ta kwanta akan gadon ta lumshe idanunta.
***A hankali ta juya da niyyar komawa ɗaya ɓangaren, rufar da ta gani ya sanya ta s
buɗe idanunta, a firgice ta tashi zaune tana kallon mutumin dake tsaye a kanta.
Baya ta fara yi tana girgiza kanta gabaɗaya jikinta rawa yake, ganin yanda ta tsora
ta ya sanya Khalil kunna hasken ɗakin, kallonsa ta yi sai kuma ta saki ajiyar
zuciya ta dafe ƙirjinta. Sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya ce"ki yi haƙuri na
tsorata ki" Imara ba ta ce masa komai ba ta sauka daga kan gadon ta ɗauko ruwa a
fridge ta ɓalle murfin, sai da ta kusa shanyewa sannan ta ajiye ta dawo ta zauna
can nesa dashi. Sun ɗauki mintuna babu wanda ya ce wani abu, Khalil na son aiwatar
da abin da ya kawo shi sai dai yana fargabar yanda Imara za ta karɓi al'amarin.
Turo baki ta yi dan bacci ta ke ji gashi ba za ta iya ce masa ya bar ɗakin ba, can
ƙasa da murya ta ce
"Yaya Khalil dare ya yi sosai fa, kuma gobe da safe ina da makaranta"
Zazzafan numfashi Khalil ya sauke kafin ya juyo ya kalleta ya ce"Na sani Imara,
yanzu ne lokacin da ya fi dacewa na zo inda ki ke shiyasa" ƙura masa idanu Imara ta
yi tana mamakin furucin bakinsa. Numfasawa ya yi sai kuma ya ce
"Imara tun ranar da idanuna suka yi tozali dake ki ka shiga raina, ki yi haƙuri da
abin da zan faɗa amma har cikin zuciyata ina ƙaunarki, nasan ba lallai ne na zama
wanda ya fara faɗa miki haka ba, amma ina da tabbacin zan yi nasara akan su duka.
Ina da niyyar mallakar ki matsayin matata ta sunna, ina fatan ba za ki juyamin baya
ba Imara"
Ras! Haka Imara ta ji gabanta ya faɗi, tashin hankali ƙarara ya bayyana akan
fuskarta, cikin rawar murya ta fara cewa
"Yaya amma ni ai kamar ƙanwarka nake, kuma ma kaga kai saurayi ne, ni kuma na taɓa
aure. Ina jin tsoro, dan Allah a bar maganar nan"
Ɗan murmushi Khalil ya yi ya miƙe tsaye ya ce"sanin haka yasa na fallasa miki
asirin zuciyata, nasan ba za ki ƙini ba, ina da wannan tabbacin Imara. Zan baki
lokaci ki yi tunani, amma ina fatan samun babban matsayi cikin zuciyarki." Da idanu
kawai Imara ta bi shi har ya fice daga ɗakin, wani irin gumi ta ji yana tsatstsafo
mata, duk da Ac dake kunne a ɗakin, me Khalil ya ke nufi?, idan har ya furta yana
son ta a gaban mutane ba za ta iya bijirewa ba kodan hallacin da mutane gidan suka
yi mata, haka kuma ba za ta iya haƙura da soyyayar Abaan ba!. Da wannan tunanin ta
koma ta kwanta, sai dai duk yanda ta yi da bacci ya ƙi zuwar mata, daga ƙarshe
kawai ta tashi ta shige toilet ta ɗauro alwala, sallar nafila ta hau yi, kafin daga
bisani ta zauna tana roƙon Allah ya zaɓa mata abin da ya fi Alkhairi a rayuwarta.
***Haka Imara ta cigaba da rayuwa a cikin gidan, duk yanda Khalil yake son magana
da ita haka take avoiding ɗinsa, domin bata fatan abin da zai haɗa su. A haka har
suka fara exams ta first semester a makaranta.
Zaune suke cikin wani ɗan ƙaramin restaurant dake cikin makarantar, da idanu Nana
ta bi Imara wadda ta zuba tagumi tun shigowar su. Har aka kawo musu abin da suka yi
order Imara ba ta sani ba, tsaki Nana ta yi sannan ta ɗan daki table ɗin gabansu, a
ɗan firgice Imara ta kalleta sai kuma ta shiga murje idanunta. Harararta Nana ta yi
ta ce
"Wannan tunanin babu abin da zai haifar miki sai wahala Malama, it's better for you
to stop it"
Ƙarfe 4:20pm suka fito daga paper, dafe kai Imara ta yi ta ce"wayyo uwata, nagaji
wlh" dariya Nana ta yi ta ce"za ma ki yi bayani ne Hajiya, gobe ma akwai paper"
zaro idanu Imara ta yi ta ce"Allah gamu gareka"
Waro idanu Nana ta yi ta ce"kai, kinga Yaya Khalil ne ya zo ɗaukar mu fa" da sauri
Imara ta kalli motar, shiru ta yi suka ƙarasa, fitowa ya yi yana kallonsu ya ce"yan
makaranta" dariya Nana ta yi ta ce"kai yaya, akwai wahala school wlh" dariya ya yi
yana kallon Imara ya ce"beauty wai haka?" gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi,
Khalil ya ce"to ai sai ku dage ku yi passing, idan kun gama exams za mu je yawo"
tsalle Nana tayi ta ce"shiyasa nake mugun son ka Yaya" dariya kawai ya yi sannan
suka shiga mota suka tafi. Sai da ya biya dasu mall ya siya musu chocolate sannan
suka tafi gida. Yana gama parking Imara ta sauka da sauri ta shige gida gudun ka da
ya yi kiranta, da idanu kawai Khalil ya bita sai kuma ya yi murmushi. Turus ta yi
ganin akwatina na kaya a zube a parlon, Jadda da wasu tsofaffi sai buɗe kayan suke.
Imara ta tambaya tana kallon Nana. "Yaya Abaan man, Aunty Jidda zai aura, gashi har
an kawo kayan lefe"
Wani irin abu ne ya tokarewa Imara a ƙirji, ta kalli Nana sai kuma ta sake kallon
tulin akwatinan, girgiza kanta ta yi muryarta na rawa ta ce"Jad... Jadda wai haka?"
"Eh mana, ashe baki sani ba, Aure zai yi kuma kwa huta, yaro ya girme a gida ya
zama magidanci babu aure" tamkar wadda aka zarewa laka haka Imara ta ji jikinta, ba
ta sake cewa komai ba ta shige ciki tana tafiya tana haɗa hanya. Da idanu Nana ta
bi ta sai kuma ta girgiza kai tana tausaya mata domin tasan abin da ke cikin
zuciyarta.
***Imara na shiga ɗaki ta nemi waje a ƙasa ta yi zaman dirshin, kuka takeson yi
amma ko kaɗan babu wani ruwan hawaye da ya rage a idanunta, gabaɗaya ƙwaƙwalwarta
ta tunkushe waje ɗaya, ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana maimaita furucin Jadda.
Daman aure zai yi ya barta?, ba ta ko samu damar sanar dashi sirrin zuciyarta ba
shine zai yi aure ya bar ta?. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma hawaye
ya biyo kuncinta, ta shiga rera kuka a hankali.
***Da gudu Jidda ta shigo kitchen ɗin ta na zuwa ta rungume Mommy tana dariya ta ce
"Mommy gaskiya Nagode sosai, an kawo kayan aurena fa, kuma yaya Adeel ya ce wai
sati uku za'a saka. Gaskiya nayi farin ciki, wannan malamin aikinsa yana yi"
girgiza kai Mommy ta yi tana dariya ta ce"da ai kina ɗauka ba zan iya ba, sai gashi
ta cikin ruwan sanyi mun buraɗa tsohuwar yanda ita kuma za ta tada musu hankali,
kinga yanzu kin zama surukar babban gida" tuntsirewa da dariya Jidda ta yi ta
ce"wlh kam naga aiki, yanzu dai kina ji Mommy ba wannan ba, ni banason zaman wannan
yarinyar a gidan nan please, idan mun koma wajen mutumin nan zan yi masa bayani.
Haka kawai na ji hankali bai kwanta da zamanta cikin gidan nan ba wlh" taɓe baki ta
yi tana wanke kayan miya ta ce"to ke mene na ki na damuwa da ita?, ke da za ki bar
mata gidan?, ai sai ta yi ta zama a cikinsa, ke da za ki tafi gidan aurenki?" Kwaɓe
fuska ta yi ta ce"ni a'a wlh Mommy, na riga da nayi alƙawarin sai na fitar da ita
daga gidan nan, saboda haka Allah hankalina ba zai taɓa kwanciya ba muddin ina
ganinta. Kuma Jadda sai wani jan ta take a jiki" murmushi Mommy ta yi ta
ce"shikenan, idan mun koma sai a yi masa maganar ta, ko kuma ki bari mu gama da
maganar aurenki, saboda dai kinsan me ya faru, dole ne kiyi abin da ya dace"
jinjina kai tayi ta ce" Haka ne Mommy, sannan kuma ni sai an dawo da hankalin Yaya
Abaan kai na, dan ko magana fa ba ya wani yimin, idan na kula shi kuma sai ya dinga
amsawa sama-sama, inason ya daina yarda da maganar kowa sai ta wa, ya daina ganin
ko wace mace a gabansa sai Jidda" murmushi Mommy ta yi ta ce"ke a tunaninki zamu
bar shi haka ne?, ai kawai ki zuba min idanu, ni nasan abubuwan da zan aikata"
rungumeta ta sake yi tana murmushi ta ce"shiyasa nake ƙara ƙaunar ki Mommy"
murmushi ta yi ta ce"nima haka Jiddona, duk wani abu da zai sanyaki farin ciki
shine abin da nake mudarin yi, zan yi komai domin farin cikin ki".
(Ba dai-dai bane a rayuwa uwa ta ce za ta yi wa ɗiyar ta duk wani abu da take so
koda kuwa hakan ya saɓawa shari'a ko kuma Addini, Iyaye mata a dinga kiyayewa,
farantawa yaro abu ne mai kyau, amma ban da saɓawa mahalicci wajen faranta ran ɗa.
Allah ya sa mu dace)
"Imara kinga yanda ki ka rame kuwa?, daga jiya zuwa yau, kar ki saka damuwa a ran
ki ki zo ki cuci rayuwarki akan abin da ba za ki samu ba, Yaya Abaan ya riga da ya
yi miki nisa Imara. Ka da ki manta Aunty Jidda ita ce wacce zai aura, ina da
tabbacin ba za ta taɓa bari ya aure ki ba. Kuma kema kin san da haka, saboda haka
ki maida hankalin ki akan karatun ki, shine kawai abin da zai taimaki rayuwar ki,
kina da buƙatar ki yi karatu Imara, domin shine kawai gatanki"
Goge hawayen fuskarta Imara ta yi tana kallon Nana ta ce"Nagode Nana, amma ba zan
iya cire shi a raina ba. Amma kamar yanda kika faɗa zan maida hankalina akan abin
da yake rayuwata, tunanin wani abu bana mara gata irina ba ne, tunanin wani zai so
ni ba abu bane mai kyau. In sha Allah zan cire shi daga raina, zan yi ƙoƙarin ganin
na gina rayuwata"
Dafa ta Nana ta yi ta ce"ni burina bai shige na ga kin kammala karatun ki lafiya
ba" murmushi ta yi ta ce"in sha Allah zan yi haka Nana".
***Tun daga wannan ranar Imara take gujewa kanta duk wani abu da zai haɗata da
Abaan, da zarar ta dawo daga makaranta take shigewa ɗaki ba za ta sake fitowa ba
sai gobe idan zata tafi makaranta. Ko da Mamah ta yi cigiyarta sai ta ce karatune
ya rike ta a haka har suka kammala jarrabawar aka basu hutu, lokacin kuma sauran
sati ɗaya bikin Abaan da Jidda. Zaune take kan kujera ta zubawa tv idanu duk da ba
fahimtar abin da ake cewa take ba. Ƙamshin turarensa ta ji nan da nan bugun
zuciyarta ya sauya, da idanu Mamah ta kalleshi ganin kamar ba shi ba ta ce"Son
lafiyarka kuwa?" girgiza kai ya yi ya ce"ki bada abinci a kawomin Mamah" sosai ta
yi mamaki ganin yau da bakinsa ya ce a kawo masa abinci, tashi ta yi ta shiga
kitchen ta haɗa masa tray na abincin sannan ta fito parlon. Zaune ta iske Imara har
sannan bata ko motsa ba
"IMARA"
*IMARA💋💋*
43&44.
08106608363
***A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Babu kowa a
parlon sai ƙamshin turare mai daɗi dake tashi, lumshe idanu ta yi kafin ta ƙarasa
ta ajiye tray ɗin akan ɗan centre tables ɗin dake tsakiyar parlon, zama ta yi kan
kujera tana tunanin rabonta da shigowa ɗakin, a ƙalla ta kai wajen sati uku ko
magana ba ta haɗata da Abaan ba. Tura ƙofar da a ka yi ya sanya ta ɗaga idanunta
tana kallonta, da wani irin kallo ta shiga bin Imara kafin ta ƙaraso gabanta, taɓe
baki ta yi fuska babu walwala ta ce"ke uban me ki ke yi a ɗakin nan?" kallonta
Imara ta yi sai kuma ta ɗauke kanta ba ta re da ta ce komai ba, baki buɗe Jidda ta
kalleta sai kuma ta yi kwafa ta ce"kee!, har kina jin ke wata ce da ina yi miki
magana za ki yimin shiru?, wane uban ki a ƙasar nan?, dame ki ke taƙama?"
"Duk abin da za ki yi, ki yi shi a kaina, amma kar ki kuskura ki sake sako ubana a
ciki, idan kuma ki ka sake wannan gangancin wlh sai na yi miki abin da ba ki taɓa
tunani ba!"
Imara ta faɗa tana huci, mamaki ya hana Jidda magana, har ita wannan yarinyar za ta
tsaya tana faɗawa magana, kwafa ta yi sai kuma ta ɗaga hannunta da niyyar marinta,
riƙe hannun ta ji an yi, ta juya tana kallonsa. Sanye yake cikin wata t-shirt black
colour sai wando 3-quater blue a jikinsa, gashin kansa sai wani sheƙi yake. Cikin
rawar murya ta ce"dan Allah ka ci ka min hannuna, na rantse da Allah sai na hukunta
ta" kallonta kawai ya yi sai kuma ya saki hannunta ya ƙarasa kan kujera ya zauna ya
shiga danna wayarsa, ban da huci babu abin da Jidda ke yi, ko da yau ba ta hukunta
ta ba, to ta ɗauki alƙawarin yi mata abin da har abada ba za ta taɓa mantawa da ita
ba. Ganin Abaan bai ce mata komai ba ya sanya ta juya ta fice daga ɗakin kamar za
ta tashi sama. Da idanu kawai Imara ta bi ta sai da taga ta bar ɗakin sannan ita ma
ta juya zata fita.
"Zo nan"
Abin da kawai ta ji ya furta kenan, turo baki ta yi sai kuma ta dawo ta zauna a
ƙasan in da yake zaune ta sunkuyar da kanta, sai da ya gama danna wayarsa sannan ya
ajiyeta a gefe ya kalleta ya ce"da me ki ke tunani?, kin korar min mata shine kuma
kema za ki tafi" fashewa da kuka Imara ta yi ta rufe fuskarta, murmushi kawai Abaan
ya yi sannan ya kamo hannunta, janyewa ta yi ya sake riƙeta ya dawo da ita gefensa,
hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta ya zuba mata idanu, ɗauke idanunta ta yi tana
kallon wani wajen tana hawaye.
Imara ta faɗa da sauri, girgiza kai Abaan ya yi, ta haɗe rai ta ce"to ba zan aure
shi ba, nima soja kawai zan aura" murmushi ya yi ya ce"to me yasa sai soja za ki
aura?, shi da baya zama a gida "
"Saboda idan wani ya yimin abu zan faɗa masa ya rama min, nikuma daman na zama
lawyer kaga babu wanda zai dinga yimin abu. Kowa zai dinga jin tsorona"
Tuntsirewa da dariya Abaan ya yi yana jinjina shashanci irin nata, turo baki ta yi
kamar za ta yi kuka ta ce"yanzu kai aure za ka yi ko?, kuma wannan Jiddar za ka
aura?, ni bana sonta" haɗe rai ya yi ya ce"kar na sake jin kin ce bakya son mutum,
ba'a cewa haka" gyaɗa masa kai ta yi kawai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Janyeta
Abaan ya yi ya tashi ya buɗe food flask ɗin, tuwon shinkafa ne miyar egusi wadda ta
ji wadatattun kayan haɗi, serving kansa ya yi sannan ya zauna a ƙasa ya tankwashe
ƙafafunsa ya yi bismillah ya fara ci, Imara na nan zaune har ya kammala cin abinci
sannan ya tashi ya shige bedroom ɗinsa, da idanu kawai ta bi shi sai kuma ta fashe
da kuka, ta sunkuyar da kanta akan kujera. Bayan mintuna ashirin ya fito cikin wata
sabuwar shigar, kallonta ya yi ganin yanda ta kifa kanta, bai ce mata komai ba ya
juya ya fice daga ɗakin, ya rufe ta ta waje.
***Zaune ya samu Jadda a parlon ita da su Umaima tana basu labari kamar yanda ta
saba, Jadda na ganinsa ta washe baki ta fara cewa "ango kasha ƙamshi, ina zuwa
haka?" Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"idan zan fita sai na faɗa miki inda
zani?, ki daina gulma" harararsa ta yi ta ce"ubanka ke gulma bani ba ɗan nema"
tuntsirewa da dariya Umaima ta yi tana kallon Jadda ta ce"Jadda Yaya fa zai biya ta
wajen siyarda nama"
"Haba?"
Ta faɗa tana washe baki, gyaɗa mata kai Umaima tayi, ta kalli Abaan wanda ke juya
mukullin motarsa ta ce"Allah sarki yaron kirki, Allah ya dawo da kai lafiya, dan
Allah idan ka tashi siyomin banason naman nan mai romo, nafison wannan mai dan
yaji-yajin wanda zan daɗe ina ci"
"Ko?"
Abaan ya faɗa, bai sake kuma bi ta kan Jadda ba ya yi waje abin sa. Yana shirin
fita daga gidan shi kuma ya shigo, kallo ɗaya Abaan ya yiwa motar sai kuma ya ɗauke
kansa, a compound ɗin gidan ya yi parking ya fito, sanye yake da wani farin yadi
mara nauyi, yanayin kwalliyarsa zaka gane akwai arziki a tare dashi duk da
kasancewar sa baƙar fata. Fuskarsa kamar gonar audiga haka ya ƙaraso wajen Abaan
yana zuwa ya tuntsire da dariya. Tsaki Abaan ya yi ya ce
"Mahaukaci kawai"
Sake tuntsirewa ya yi da dariya ya ce"kaga mutumin, ango kasha ƙamshi, kaga yanda
ka ke wani glowing, ko dai har Amaryar ta fara kula da kai ne?" Duka Abaan ya kawo
masa ya kauce yana dariya ya ce"ai wlh kai ma kasan wuce nan"
Gwalo ya yi masa, yana yin yanda suke wasa da dariya zai tabbatar maka da akwai
shaƙuwa mara misaltuwa a tsakaninsu. Girgiza kai Abaan ya yi ya ce"kai baka da
hankali shiyasa, ni kaga tafiya ta, dariya ya yi ya jawo hannunsa ya ce"haba Dude
mu je tare, ina za ka je na raka ka?" kallonsa kawai Abaan ya yi sai kuma ya shige
mota, a ɓangaren mai zaman banza ya zauna. Murmushi kawai Kamal ya yi sannan ya
zauna a driver seat, yana kallonsa ya ce"sarautar taka zaka nuna min kenan?, Allah
ya so nima dai Babana Sarki ne, ba iya ku kaɗai ku ke da sarauta ba"
Banza Abaan ya yi masa ya shiga danna wayarsa, murmushi kawai Kamal ya yi sannan
suka bar gidan.
***Sai bayan magrib sannan ta farka daga baccin daya ɗauketa, tashi ta yi ta sake
ƙoƙarin buɗe ƙofar, amma ta sake jin ta a rufe. Hawaye ta fara yi dan gabaɗaya ta
gaji da zaman ɗakin, ta juya ta koma ciki, abincin da ya rage ta zuba ta fara ci,
tana lumshe idanu dan ba karamin daɗi tuwon ya yi ba, kuma daman gata masoyiyar
tuwo. Tana gama ci ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito, rasa
abin yi ta yi hakan yasa ta shiga gyara ɗakin duk da ba datti ya yi ba, bayan ta
kammala gyara parlon ta shiga bedroom ɗin domin shima ta gyara shi. Sakewa gadon
bedsheet ta yi sannan ta kunna turare, Zama tayi a kan bedside drawer tana kalle-
kalle. Kamar wadda aka tsikara haka ta tashi ta shiga buɗe drawer, takardu ne duk a
ciki. Tsaki kawai ta yi sannan ta rufe, tana shirin mayarwa wani envelope ya fado,
ɗaukansa ta yi ta buɗe, hotuna ta gani a ciki a kuwa ta gyara zamanta ta shiga buɗe
su. Hoton farko wasu yara ne mace da namiji a tsaye, daga gani namijin shine babba
domin ya fita tsawo da jiki nesa ba kusa ba. Murmushi ta yi sannan ta sake ciro
wani hoton, nan ma hoton yaran ne sai dai wannan karan akwai ƙarin wani babban
mutum daga gani kasan mahaifinsu ne, kai daga ganin hoton kasan asalin larabawa ne,
sake ware idanunta ta yi dan gani ta yi kamar ta taɓa ganin irin fuskar sai dai ta
manta in da ta santa. Ɗaya hoton kuma hoton Abaan ne sanye da kayan sojoji, gefensa
kuma wani babban mutum ne shima sanye da irin kayan nasa, da alama gaba yake dashi
ko a wajen aiki. Murmushi kawai Imara ta yi dan ba ƙaramin kyau hoton ya yi, haka
kawai ta ji hoton ya burgeta, turo ƙofar ɗakin da a kayi ya sanya ta yi saurin
mayar da hotunan ba tare da ta kammala kalla ba. Da idanu Abaan ya bita sai kuma ya
ƙaraso in da take zaune, zama yayi gefen gadon yana kallonta ya ce"kin gaji ne?"
Saurin gyaɗa masa kai ta yi kamar za ta yi kuka ta ce"ni ka buɗe min na fita" ɗan
murmushi kawai ya yi sannan ya tashi ya fara cire agogon dake hannunsa yana ƙoƙarin
shiga toilet ya ce"ai yau anan za ki kwana!"
# *IMARA 💋💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*Sauran posting 3 na kammala book 1, and book 2 paid book ne ₦500, wanda suke yin
payment kafin na kammala book 1 zasu bada ₦400 a matsayin promo, nan da kwana biyu
zan kammala book 1, saboda haka a cigaba da payment na book 2 kafin lokaci ya ƙure,
nafison a fara da kowa, a tura kuɗi ta wannan account ɗin 7041901078 Hauwa Adamu
lawan opay, sai a turo shaida ta number ta, 08106608363 Nanameera, Nagode.*
*IMARA 💋💋*
45&46
08106608363.
Mikiya writers asso...
Da idanu kawai ta bisa har ya shige toilet ɗin, tashi ta yi ta buɗe drawern ta zari
hoton da yake tare da wani ta yi saurin barin ɗakin. Kai tsaye ɗakinta ta shige
tana zuwa ta buɗe wardrobe ɗinta ta saka shi can ƙasan kaya sannan ta mayar ta
rufe, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta fita zuwa wajen Jadda. Zaune ta
hangesu a parlon suna hira, ƙarasawa ta yi tana kallonsa ta ce"ina yini" murmushi
Kamal ya yi ya ce"lafiya klao Imara, ya gida ya shirye-shirye?" "Lpyklao
Alhamdulillah" jinjina kai ya yi yana kallon Umaima ya ce"sauran na mu ko?"
sunkuyar da kai Umaima ta yi. Murmushi Imara ta yi ta ce"dan kuwa mun ƙagu a zo
auren Uma" dariya Kamal ya yi ya ce"ai duk na fi ku ƙaguwa Imara, ni yau zan wa
Abbiey magana kawai na bada sadaki a ɗaura yau, sai a haɗe shagalin dana Doctor"
rufe baki Imara ta yi tana dariya ta ce"da kuwa mun ji daɗi Yaya" dariya kawai ya
yi ta juya ta shige apartment ɗin Jadda".
****Zaune ta samu Jadda tana cin nama, tana ganin an turo ƙofa ta yi saurin naɗe
ledarta, sai da taga Imara ce sannan ta mayar ta ajiye tana washe baki ta ce"au, na
yi tunanin wannan zilamammiyar yarinyar ce ashe ke ce" zama ta yi tana murmushi ta
ce" ni ce Jadda, Barka da dare" sai da ta kai tsokar nama bakinta sannan ta
ce"sannu da zuwa yarinya, ya shirye-shirye?, na ji ɗazu wannan 'ya ta ce wai gobe
za'a fara bikin" ɗan murmushi Imara ta yi ta ce"ban ma sani ba Jadda, Allah ya
sanya Alkhairi" . Girgiza kai Jadda ta yi ta ce"oh Allah dai ya yarda, wannan aure
kamar ba za'a yi shi ba, ai gara ma ya yi auren shima ya huta, duk sa'annin suna da
iyali shi ya tsaya ko me yake jira ohho?" Shiru Imara ta yi sai kuma ta ce"to Jadda
kuma yana sonta?" Kallonta Jadda ta yi sai kuma ta yi murmushi ta ce"sanda tana
yarinya ba'a taɓa ta saboda Abaan, ba ya son yara amma yanda yake kula da yarinyar
abin da sai da ya fara bawa kowa mamaki, tun tana ƴar ƙaramarta yake sonta, oh
lokacin an ga abu, idan tana kuka Abaan ko zama ba ya yi, idan kuwa suka yi faɗa da
Adeel ya daketa to ranar Allah ne kawai zai kwaci Adeel a hannunsa."
Girgiza kai kawai Imara ta yi sannan ta fice daga ɗakin, da idanu kawai Jadda ta
bita sai kuma ta ce"oh, kome ke damunta Allah masani"
Ba ta tarar da kowa a parlon ba, haka ita ma bata tsaya ba, kawai ta haye sama kai
tsaye kuma ɗakinta ta shiga. Tana zuwa ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, ina ma
bata tambayi Jadda ba, ina ma ba ta sauka ƙasan ba, kenan Abaan yana son Jidda har
haka?, kenan auren soyayya zai yi?. Sake rushewa ta yi da kuka ta dafe kanta, tana
nan zaune ta ji an turo ƙofar, da sauri ta kalli ƙofar sai kuma ta shiga goge
idanunta. Zama Mamah ta yi gefen gadon tana kallonta ta ce"lafiya ki ke kuka?" can
ƙasa da murya ta ce"kaina ne yake ciwo"
"Ciwon kan ki ke wa kuka Imara?, ko da wani abun ya sameki?, nasan bakya ɓoyemin
abu ki sanar dani me ya sameki?" Girgiza kai ta yi ta ce"babu komai Mamah kawai
ciwo kaina yake, amma yanzu na sha magani" ajiyar zuciya Mamah ta sauke tana
murmushi ta ce"Tom Allah ya sawwaƙe, daman wata magana ce nakeson muyi dake Imara"
gyara zamanta ta yi tana kallon Mamah ta ce"Tom ina ji" numfasawa ta yi ta fara
magana
"Imara daman ina neman wata alfarma ne, kuma sannan ina son na baki shawara, Imara
nasan Khalil ya yi magana dake wattanin baya, sai dai har yanzu ba ki ce komai ba,
ban sani ba ko kin ji bai miki bane, ko kuma kina gudun faɗawa irin hannun da kika
faɗa a da. Ina son na baki shawara a matsayina na mahaiyarki, ki nutsu ki zaɓi
mijin aure wanda zai dace da rayuwarki, ki auri mijin marainiya wanda zai kula da
ke koda yasan ba kida kowa. Ki auri wanda yake sonki tsakani da Allah wanda ba za
ki yi danasanin aurensa ba, nasan halin Khalil, idan har ya furta yana son wani abu
to tabbas yana son abun ne, idan har da dama Imara Inason ki yarda da Khalil ki yi
aurenki ki cigaba da karatun ki cikin ɗakin ki. Na tabbata ba za ki yi dana sani
ba"
Wasu hawayene suka shiga sintiri akan fuskarta, girgiza kai Mamah ta yi ta kama
hannunta ta ce"a'a Imara, idan har kinsan akwai wani a zuciyarki ki bar wannan
maganar, ba wai dole zan miki ba kin ji" fashewa ta yi da kuka ta shige jikin
Mamah, rungumeta Mamah ta yi itama tana hawaye ta shiga shafa kanta. Cikin
shassheƙar kuka Imara ta ce"ni babu kowa a zuciyata Mamah, idan ma akwai to na
yarda ƙaddara ta raba mu, zan ɗauki duk wata shawara da ki ka bani, sannan zan
karɓi Yaya Khalil hannu bibbiyu, na tabbata ba za ki yi abin da zai cutar da ni ba
Mamah, ina da wannan yaƙinin, kawai ki dinga yimin addu'a, Allah ya yaye mini
damuwata dan Allah Mamah" jinjina kai Mamah ta yi ta ɗago fuskarta tana goge mata
hawayen ta ce"in sha Allah Imara, za ki yi farin ciki a rayuwa, komai zai mana
tarihi, karki damu kin ji" gyaɗa mata kai ta yi sannan ta sake rungumeta.
Washegari da safe Nana ta shigo ɗakin, zaune ta sameta tana kallon hoto, zama ta yi
gefenta ta ce"a ina ki ka samu hoton yaya?" murmushi ta yi ta ce" a ɗakinsa mana"
Ɗaga kafaɗa Nana ta yi alamar ba ta sani ba, girgiza kai Umaima ta yi sannan ta
koma ɗakin Imara. Kwance ta sameta ta yi ruf da ciki, ƙarasawa ta yi ta zauna gefen
gadon ta taɓa
"Imara"
Saurin goge hawayenta ta yi sannan ta tashi zaune tana kallon Umaima ta ce"na'am"
"Mene haka Imara?, ki tashi mu tafi, ko kin fi so mu makara ne?, idan mun je da
wuri ai da wuri zamu dawo gida, kinga ai ya fi" dafe kanta ta yi ta ce"ni bana so
fa, ku je kawai, ni ba zan je ba" haɗe rai Umaima ta yi za ta yi magana wayar
hannunta ta fara ƙara, kallon screen ɗin ta yi sai kuma ta ce"kinga har an fara
kiranmu ko?, ki tashi mu tafi mana" girgiza kai Imara ta yi ta ce"na ce miki kawai
ku tafi, ni banaso ba zan je ba" . Babu yanda Umaima ba ta yi da ita ba amma ta ce
ba za ta je ba, daga ƙarshe ma ta tashi a ta shige toilet. Gajiya Umaima ta yi ta
tashi ta fita, tsaye ta hangeshi jikin bene yana danna wayarsa, da sauri ta ƙarasa
fuskarta babu walwala ta ce"Yaya" ba tare da ya kalleta ba ya ce"mene ne?"
"Ka yiwa Imara magana, wai ta zo mu je gyaran kai da ƙunshi wai shine ba za ta je
ba, tun ɗazu ta ƙi fitowa" ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce"call her" da
sauri ta koma ɗakin nata. Zaune ta sameta gefen gado ta kifa kanta, ƙarasawa ta yi
ta ce "ki je in ji Yaya Abaan" ɗago kanta ta yi ta kalleta sai kuma ta sake
sunkuyar da kanta, Umaima ba ta sake cewa komai ba ta fice daga ɗakin, tsaye ta
same shi inda ta bar shi tana zuwa ta ce"na faɗa mata yaya" idanunsa maƙale cikin
glasses ya ce"to je ki" sauka tayi tana juyowa ta ga ko ta fito. Above 5mins kafin
Imara ta fito, tana sanye da wata Abaya maroon colour ta yafa veil ɗinta akai, a
hankali take tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a jiki, ta ƙaraso ba tare da ta
kalleshi ba ta ce"gani" sai da ya ƙarasa abin da yake sannan ya mayar da wayar
aljihu ya ɗago ya kalleta kamar ba zai magana sai kuma ya ce"why?" turo baki ta yi
ta ɗauke kanta tana jin wasu sabbin hawayen na son zubo mata. Zuba mata idanu ya yi
yana kallonta, cikin rawar murya ta ce"ni bana so ba zan je ba"
"Ko?"
****Wani saloon and spa ya kaita, kai daga ganinsa kasan gurin kashe kuɗi ne,
ɓangaren maza ya shiga ya zauna kafin ɗaya daga cikin matan ta zo ta tambayeshi
yanda za'a mata, bayani ya yi mata yanda zata gane sannan ya bada atm ɗinsa, da
idanu kawai Imara ta bi shi sai kuma ta ce "ni kar ma ka bada kuɗinka ko an yimin
sai na lalata shi wlh" dariya sosai ta bashi amma ya dake fuskarsa a haɗe ya ce"me
ki ka ce?" shiru ta yi tana zumɓura baki gaba.
"Me ki ka ce?"
Juyowa ta yi ta kalleshi ta ga ya haɗe ransa kamar ba shine yanzu yake raha ba,
turo baki ta yi ta ce"haka Mamah ta ce shi zan aura, kuma shima ya ce yana sona,
kai ma ai Jadda ta cemin kana son Jidda sosai tun tana 'yar ƙarama shiyasa
yanzu..."
Abaan ya daka mata wata tsawa wadda ta sanya jikinta ya fara rawa, bai sake ce mata
komai ba ya buɗe ƙofar ya fice daga motar, sauka ita ma ta yi ta bi shi da kallo
har ya shige ciki. Harararsa ta yi sannan ita ma ta yi hanyar gidan, zaune ta same
su a parlon kowanensu da ƙunshi ja da baƙi a hannunsa, saɓanin ita da iya ja aka yi
mata dan Abaan hana wa yayi a yi mata baƙin, ƙarasawa ta yi ta zauna bayan ta yi
sallama, kallonta Nana ta yi ta ce"au ashe kuma kin je?" da idanu kawai Imara ta
bita sai kuma ta ɗauke kanta, murmushi Umaima ta yi ta ce"mu ga ƙunshin?" Ɓoye
hannayen nata ta yi, Umaima ta dawo inda take ta buɗe hannayen, ba ƙaramin kyau
ƙunshin ya yi akan hannunta ba, kasancewarta fara tas ya sanya jan ƙunshin ya yi
kamar an dasa shi a hannunta. Suna nan zaune suna hira har uku da rabi hakan yasa
suka tashi dan fara shin tafiya cocktail.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*Sauran posting 2 na kammala book 1, kamar yanda nafaɗa book 2 paid book ne ₦500,
an fara payment tuntuni saboda haka wadda ba ta yi ba ga account number nan
7041901078 Hauwa Adamu lawan opay, sai a turo shaidar biya ta wannan numbern
08106608363, Yanzu mu ka fara tafiyar, akwai abubuwa dayawa a gaba💃kar ki bari a yi
babu ke sister, ki biya ₦500 ɗin ki kacal na tabbata ba za ki yi danasani ba, taku
har kullum Nanameera.**IMARA 💋💋*
47&48.
08106608363
"Amma Nana ya za'a yi a ce bata je ba?, akan wane dalili?" jan hannunta Nana ta yi
ta ce"kin ga fa, ba dole ne sai mutum ya je ba, maybe bata ra'ayin zuwa irin
waɗannan tarukan tunda kinga bata da shiga mutane, just leave her"
Suka tsinkayi muryar Mamah a bayansu. Girgiza kai Nana ta yi ta ce" ba kowa, wai
daman Imara ce ta ce ba zata je partyn yau ba, shine na ce a ƙyaleta, maybe bata
saba bane" shiru Mamah ta yi na ɗan wasu sakkani sai kuma ta ce"ku je kawai, bari
na yiwa Abaan magana maybe shi ta ji maganarsa. Idan bata je ba ai sai ya zama abin
magana" murmushi Umaima ta yi dan har ga Allah tafi son ace Imara taje wajen.
****Zaune ta sameshi kan kujera ya tankwashe ƙafafunsa idanun zube bisa system ɗin
dake gabansa, zama ta yi kusa da shi tana murmushi ta ce"amma dai kasan yanzu ba
lokacin wannan aikin bane ko?" ɗago kansa ya yi ya zuba mata idanu, murmushi ta yi
ganin yanda idanunsa suka faɗa yasa ta ce"ba ka cin abinci ko?, sai yaushe zaka
daina irin wannan abun ne Abaan?" langwaɓar da kansa ya yi kamar wanda aka yiwa
dole ya ce"Mamah nagaji" dafa kansa ta yi ta ji zafi, girgiza kai ta yi cike da
tausayinsa ta ce"sannu, kaga har zazzaɓi zai kamaka, ka tashi ka yi wanka, lokaci
na tafiya, kar azo ana jiran ango bai zo ba" kamar zai yi kuka ya ce"Mamah ni fa
nagaji wlh" dungure masa kai ta yi ta ce"banason shashanci, maza ka tashi, zan aiko
Imara ta kawo maka ruwan tea kasha sai ka zo ka tafi. And kuma ka yi mata magana
ance ta shirya taƙi wai ba zata je ba" bai ce komai ba ya rufe system ɗin ya tashi
ya shige bedroom ɗinsa, da idanu kawai Mamah ta bishi sai kuma ta fice daga ɗakin.
****Zaune suke gidan makeup ɗin bayan an gama yi mata, sosai ta yi kyau dan daman
da kyanta Masha Allah. Murmushi Amrish ta yi ta ce"ke matar nan kin yi wani irin
kyau wlh" dariya Jidda ta yi ta ce"da gaske?, ki ce zan tashi kan mijina"
tuntsirewa da dariya Raheena ta yi ta ce"ba dole ba, ai kedai ki bar komai a
hannuna, wlh sai kin mallakeshi a tafin hannunki, babu boka babu malam" numfasawa
Jidda ta yi sai kuma ta ce"nikam ina tsoro wlh, saboda malamin da muke zuwa wajensa
ya ce yanada riƙon addini kuma asiri zai wahala ya ci shi" taɓe baki Xahra ta yi ta
ce"ni banga wanda asiri ba ya ci ba, kawai dai ba zai iya bane, ki bari sai bayan
auren akwai wajen wanda zamu je wlh duk taurin kan namiji sai ya dawo ɗan boyi-
boyin ki. Ke duk rashin mutunci irin na Abbas sai da aka ladabtar min dashi, yanzu
ko tsinke na ajiye na ce kar ya tsallake wlh ba zai iya tsallakawa ba, kuma ni ke
juya dukiyarsa" ajiyar zuciya Jidda ta sauke kafin ta kalleta ta ce"ni fa ba wai
inason na dinga juya dukiyarsa ba ne ko wani abun, kawai ni ya so ni, ya fifitani
akan komai nasa, mu yi zama na lafiya da soyyaya wlh ni shine kaɗai burina"
Saurin dafe ƙirjinta ta yi, lokaci ɗaya Imara ta faɗo mata arai, girgiza kanta ta
yi tana kallon Xahra ta ce"Allah ya kiyaye, ni wai ina Munceey ta shiga ne?" tsaki
Amrish ta yi ta ce"daga cewa fa gatanan kinga har mun gama abin da muke bata dawo
ba, kawai mu tafi wlh"
"To mu je ina?, ai sai ango ya zo da motoci ya ɗauki amarya ko?" Girgiza kai Jidda
ta yi ta ce"a'a bari dai mu jira su, ai kinga bai san mun gama ba inaga"
****Fitowa ta yi daga kitchen hannunta riƙe da ɗan ƙaramin tea flask wanda Mamah ta
bata, Jadda dake zaune kan kujera ta shiga bin ta da kallo kafin ta ce"ni ko wa
nake gani haka kamar Imara?" a sanyaye ta ce"ni ce Jadda"
"Muhammadu Rasulullahi, ina wajen bikin?, ko ke ba ki je ba?, nima kinga jira nake
angon ya fito mu tafi tare" girgiza kai Imara ta yi ta ce"ban shirya bane Jadda"
"Sallamammen yaro mai halin uwarsa, nan fa na zauna ina jiran yaron nan sai cemin
ya yi wai mota zai kai a sakowa fetur, shine ya yimin zamba cikin aminci ya gudu"
ba Khalil ba hatta Imara dake tsaye sai da ta yi dariya, ya kalleta ya ce"Tom Jadda
ni zan kai ki karki damu, Imara je ki shirya" da idamu kawai Imara ta bishi dan
tama rasa abin da za ta ce masa dan kuwa ba zuwa za tayi ba.
****Tura kofar ɗakin tayi a hankali, babu kowa a parlon hakan yasa ta shiga ta
ajiye flask ɗin, tana shirin fita ta ji wayarsa tana ƙara, kallon ƙofar bedroom ɗin
ta yi sai kuma ta kalli screen ɗin wayar, babu suna hakan yasa ta ɗauki wayar ta
ɗaga ta kai kunne.
Saurin ajiye wayar ta yi ba tare da kashe ba, da idanu kawai Abaan ya bita ya
ƙaraso wajen, ɗaukar wayar ya yi ya kai kunnensa, bai sake kallonta ba ya shige
kitchen. Da idanu kawai Imara ta bi shi sai kuma ta tashi tsaye tana shirin fita.
Cak ta tsaya sai kuma ta juyo ta kalleshi da idanunta wanda ruwa yake kwance a
cikinsu. Bai mata magana ba ya zauna kan kujera ya haɗa tea ɗinsa, gajiya ta yi da
tsaiwar ta nemi waje ta zauna a ƙasa ta kifa kanta akan gwuiwarta, sai da ya shanye
shayin sannan ya ɗago ya kalleta, numfasawa ya yi kafin ya ce"mene dalilin rashin
zuwan?" ɗago kanta ta yi a hankali bayan ta goge hawayen da suka zubo mata ta ce"ni
kawai bana son zuwa" gyara zamansa ya yi yana kallonta sosai ya ce"saboda akwai
abin da ke cikin ranki?, Imara kar ki koyawa kan ki wata ɗabi'a wadda ba taki ba,
ki daina wannan abun da ki ke, kar na sake ji ko kuma ganin irin wannan dabi'ar,
banason a sake kawomin ƙararki kin ji abin da nace?" Saurin gyaɗa masa kai ta yi
tana ƙoƙarin ɓoye kukan dake shirin kwace mata. Tashi tsaye ya yi ya ce"ki tashi ki
je ki shirya, Khalil zai tafi ya tafi dake, kuma ina sake faɗa miki kar a sake
kawon ƙararki daga yau har ranar da za'a gama bikin nan" daga haka ya fice daga
ɗakin ya barta zaune.
Duk wani taku da Abaan ke yi masifa ce a gurin Imara, tana jin kamar yana tafiya da
rayuwarta, duk yanda take ƙoƙarin cire son shi daga cikin zuciyarta abun ya gagara,
burinta bai shige ta ganta zaune kusa da shi ba, idan dare ya yi har Allah Allah
take gari ya waye domin tayi ido biyu da shi, amma da alama duk abubuwan da take a
banza suke tafiya, da alama Abaan bai lura da halin da take ciki ba ballantana tayi
tunanin samun abin da take so daga gare shi.
****Around 7pm suka yi parking a wajen event ɗin, kallonta Khalil ya yi ganin yanda
ta yi shiru ya ce"sannu, kan ne har yanzu?, ko dai mu fara zuwa mu siyo maganin?"
girgiza masa kai tayi cikin sanyin murya ta ce"naji sauƙi sosai" girgiza kansa ya
yi ya ce"a'a Imara, idan da kin ji sauki ba haka za ki yi ba, bari a tashi sai muje
koda su Umaima ne a siya miki magani kinji" gyaɗa masa kai kawai tayi, sannan ta
sauka daga motar. Yana sauka ya haɗu da su Kamal hakan yasa ya kalleta ya ce"maza
je ki shiga Imara" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta fara tafiya. Tana shiga hall ɗin
ta hangeta can saman stage sanye da fararen kaya, yayinda duk wata budurwa dake
wajen ta saka baƙar riga, hakan yasa suka yi kyau ba ƙarami ba. Kallo ɗaya ta yiwa
Abaan dake zaune kusa da ita yana sanye da suit farare gashin kansa wanda ya sha
gyara sai sheƙi yake, dafe ƙirjinta ta yi sai kuma ta nemi kujera acan bayan ta yi
zamanta. Tana zaune aka dinga tashi ana zuwa rawa da amarya, Jidda ba zaka ce
bikinta ake ba dan sakar jikinta ta yi tana rawarta hankali kwance. Tana kallon
sanda su Umaima suka je kan stage aka dinga liƙa kuɗi kamar ba'a san zafinsu ba,
tashi Imara ta yi ta fita daga hall ɗin ta nemi can wani dandamali ta zauna.
Sai wajen ƙarfe 9pm sannan aka fara fitowa daga wajen, har sannan tana zaune a
wajen, ta dunƙule jikinta saboda wani zazzaɓi da ya rufe ta. Har sun shiga mota
Khalil ya ƙaraso wajen yana kallonsu ya ce"ina Imara?" Da mamaki Umaima ta ce"Imara
kuma?, ai ba ta zo ba" zaro ido Khalil ya yi ya ce"wane irin bata zo ba, ni ne nan
na kawota wajen nan, na ce ta shiga ciki, kuma akan ido ta shiga ciki yanzu kuma ku
ce bata zo ba" girgiza kai Nana ta yi ta ce"wlh to Yaya bamu ganta ba, mu muna tare
da yaya Adeel" jinjina kai Adeel ya yi ya ce"gaskiya bata zo inda suke ba, koma ta
shigo ɗin" da sauri Khalil ya bar wajen ya shiga dubata sai dai iya dubansa ban
ganta ba. Can ya hangi su Abaan tsaye suna magana da Kamal, ƙarasawa ya yi yana
kallonsu, ganin irin yanda yake kallonsu ya sanya Kamal ya ce"Khalil lafiya dai?,
meya faru?" girgiza kai ya yi ya ce
"IMARA!"
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*Sauran posting 1 na kammala book one, ƴar uwa har yanzu ba ki yi payment ba??,
kina son ganin yanda abun zai kasance kuwa?, da a baki labari ai gara ki bayar
saboda haka maza-maza ki yi payment ta wannan account ɗin 7041901078 Hauwa Adamu
lawan opay, sai ki turon shaidar biya ta lambata 08106608363, ₦500 kacal, karki
bari ayi babu ke, daga gobe ne💃💃, taku har kullum Nanameera**IMARA 💋💋*
49&50.
End of book 1
Mikiya writers asso...
Babu irin neman da ba'a yiwa Imara ba amma basu sameta ba, zuwa lokacin hankalinsu
ya yi matuƙar tashi. Tsaye Abaan yake jikin mota sai bin su yake da kallo, koda
wasa bai ɗaga ƙafarsa daga inda yake ba, Kamal ne ya ƙaraso yana kallonsa ya ce"wai
ya na ganka a tsaye?, ba fa aga yarinyar nan ba" gajiyayyun idanunsa ya zuba masa
ba tare da ya ce komai ba. Tsaki Kamal ya yi sanin halinsa ya ce"wai mene haka?,
idan kasan inda yarinyar nan take dan Allah ka faɗa"
Girgiza kai Kamal ya yi ya ce"ba haka nake nufi ba, anyway kai ma ka shigo a nemeta
da kai mana" ɗauke idanunsa ya yi yana kallon gefe, can kusa ya zura wayarsa a
aljihu ya yi gaba ya bar Kamal a wajen. Girgiza kai kawai Kamal ya yi sannan ya bi
bayansa.
A hankali yake tafiya toward direction ɗin flowers ɗin, Kamal ne ya biyo bayansa
yana kallon inda yake shiga ya ce"haba malam, me zai kai mutum nan wajen?, ka zo
muje wani wajen dan Allah" tamkar wanda yake magana da dutse haka Abaan ya yi masa
banza ya cigaba da tafiya. Bin bayansa Kamal ya yi gudun kada wani abun ya same
shi. Shassheƙar kukanta ya juyo hakan yasa ya ƙarasa inda take tsugune, wata
ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta, waro idanu Kamal ya yi sai kuma ya
ce"Imara" a firgice ta ɗago ganin mutane akanta ya sanya ta tashi tsaye ta shiga
goge idanunta.
Buɗe baki ta yi za ta yi magana ta ji an sauke mata wasu lafiyayyun maruka har guda
biyu. Ba Imara ba hatta Kamal sai da ya dafe kuncinsa saboda yanda ya ji ƙarar
marin, Abaan bai sake kallon kowa ba ya juya ya bar wajen. Tafiya tayi luu zata
faɗi Kamal ya yi saurin tare ta, ta faɗo hannunsa sumammiya. Ƙarasowa wajen Khalil
ya yi ya kalleta sai kuma ya kalli Kamal a rikice ya ce "lafiya dai?, me ya
sameta?" girgiza kai kawai Kamal ya yi ya ɗauketa suka bar wajen. Koda suka je basu
tarar da Abaan ba da alama tafiyarsa ya yi ba tare da ya jira koda amaryar ba.
****Turo ƙofar ɗakin ya yi ya shigo, tsaye ya samu Mamah sai kai da komo take a
cikin ɗakin, ya ƙarasa ya tsaya kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"lafiya dai
Mamah?"
Tunda ta fara magana Abaan ke kallonta, rabon da Mamah ta yi masa faɗa irin haka
tun yana ɗan shekara goma sai gashi yau ta sake masa irin sa akan IMARA. Bai ce
mata komai ba ya juya ya bar ɗakin, da idanu kawai ta bi shi sai kuma ta nemi waje
ta zauna jin jiri na neman ɗibanta. Abaan na fitowa kai tsaye ɗakinsa ya shige,
yana zuwa ya faɗa kan gado ya yi ruf da ciki, a hankali wasu zafafan hawaye suka
fara sauka akan fuskarsa abin da ya daɗe bai yi ba cikin rayuwarsa, domin ko da
yana yaro shi ba ma'abocin kuka bane. Gajiya ya yi da kwanciyar hakan yasa ya tashi
zaune, drawer dake gefen gadon ya buɗe ya ciro pictures ɗin dake ciki. Ɗaya bayan
ɗaya ya shiga kallonsu, wani hoto ya ciro yana zaune akan cinyar wani babban mutum,
gefensa kuma wata kyakkyawar budurwa ce tayi dariya. Shafa fuskarta ya yi hawaye na
zubowa daga idanunsa cikin rawar murya ya ce
"I'm sorry, double sorry Janan, na gaza, ba zan iya ba, nagaza cika alƙawarin dana
ɗauka. Ki hukunta Janan, dan Allah Janan"
Yanda yake kuka kamar ƙaramin yaro zai tabbatar maka da halin da yake ciki, tabbas
akwai wani ɓoyyayen abu wanda yake damunsa, rungume hoton ya yi yana cigaba da
kuka.
****A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda suka mata wani irin nauyi, tashi zaune
tayi tana ƙarewa ɗakin da take kallo, tunanin wanda ya dawo da ita gida ta shiga
yi, wani irin raɗaɗi taji fuskarta na yi mata hakan yasa ta tashi da sauri ta shiga
toilet ta zuba ruwa a fuskar, hannunta ta kai fuskar ta ji wani irin abu, da sauri
ta kalli mudubi, shatin yatsunsa ne kwance akan fuskarta. Gaba ɗaya fuskar tayi
wani irin jaa kasancewarta fara, sai a sannan ta tuna da marukan da Abaan ya yi
mata. Wasu zafafan hawayene suka zubo akan fuskarta, fitowa tayi daga toilet ɗin ta
dawo ta zauna gefen gado har sannan hannunta na maƙale kan fuskarta. Turo ƙofar
ɗakin a kayi ta juya ta kalleta, sanye take da sleeping dress fara ta ɗaure gashin
kanta, ƙarasowa Nana ta yi ta zauna kan bedside drawer tana kallonta, tausayi Imara
ta bata hakan yasa ta girgiza kai cikin ƙasa da murya ta ce"Imara Inason zan yi
magana dake"
Kallonta kawai Imara ta yi bata ce mata komai ba, amma yanda ta maida idanunta
kanta ya nuna tana saurarenta. Numfasawa Nana ta yi cikin sanyin murya ta fara
magana
"Imara inason ki fita a harkar yaya Abaan dan girman Allah, ki kalli abin da yake
gabanki, kinga dai abin da ya faru dake yau, na faɗa miki wani abu?, yaya Abaan
baya ƙaunarki, ke babu wani alamu dake nuna yana sonki, bayan haka ma bai damu dake
ba. A sanda kowa yake ƙoƙarin nemanki ɗazu shi tsayawa ya yi yana danna waya, sai
da kowa ya gaza nemanki sannan Yaya Kamal ya yi masa magana. Saboda haka ki dawo
daga wannan duniyar da ki ka shiga, ki fuskanci abin da yake gabanki, ki riƙe
maraicinki Imara, ki maida hankali akan abin da zai amfani rayuwarki. Bari na faɗa
miki gaskiya wlh! Wlh! Abaan ba zai aureki ba, saboda shi kwata-kwata mata basa
burgesa, ke hatta Jidda saboda furucin Jadda ya yarda da auren ba wai saboda yana
sonta ba, kuma kema shaida ce na yanda yake yi mata. Ki cire kan ki daga cikin
al'amuran rayuwarsa, tun kafin wani ya gane halin da ki ke ciki ya kamata ki dakata
haka. Ki daina baƙin ciki ko kishi dan zai yi aure, ki shiga a yi komai dake, ki
sani ba za ki taɓa auren mijin da ba naki ba, dole mijinki shi za ki aura. Dan
Allah ki ɗauki shawarata ki saki ranki a ƙarasa bikin nan lafiya ki cigaba da
karatun ki, ki ka san abin da Allah ya tsara miki?"
Goge hawayen da suka zubo mata tayi, ta kalli Nana cikin shassheƙar kuka ta
ce"Nagode sosai da shawarwarin ki Nana, Nagode sosai, zan yi amfani da abin da ki
ka ce in sha Allah, zan yi gwagwarmaya domin na samarwa da kaina kyakkyawar rayuwa,
ba zan sake shashancin son wani a zuciyata ba, na yadda kowa baya sona, kowa guduna
yake, zan rayu ni kaɗai in sha Allah, ba zan sake creating wata matsalar a cikin
ahalin nan ba"
Shiru Nana tayi tana kallonta sai kuma ta kamo hannunta ta ce"ba haka nake nufi ba
Imara, ya za'ayi ki ce babu wanda yake sonki, how comes?, dole ki sami wanda yake
sonki domin ba kida mugun hali, kar ki yiwa maganata mummunar fahimta dan Allah"
Murmushi tayi duk da hawayen dake kan fuskarta ta ce"ko kaɗan wlh Nana ban yi miki
mummunar fahimta ba, na san gaskiya ki ke faɗamin, kuma na yarda dake" ajiyar
zuciya ta sauke ta ce"tom Nagode sosai, ki tashi muje ɗakina mu kwana, gobe akwai
dinner kuma za ki je" gyaɗa mata kai kawai Imara ta yi sannan ta tashi, duk da
yanda kanta ke mata ciwo hakan bai hanata bin Nana ba.
Zaune suka sami wasu yan mata su biyu suna hira, da idanu kawai Imara ta bisu,
ƙarasawa Nana ta yi tana murmushi ta ce"yau kwanan hira zamu yi, ga Imara a gidan
nan take. Imara ga Maimoon ga Fadeela cousins ɗina ne ya'yan ƙanwar Mamah ne" ɗan
murmushi Imara ta yi ta ce"sannunku" murmushin suma suka mayar mata sannan suka
gaisa. Ita dai ta nemi waje ta zauna tana jin yanda suke hira gwanin ban sha'awa.
Washegari da wuri suka tashi saboda aikin da ake a gidan, sosai aka taru dan duk
yan uwan Mamah sun zo, kowa sai harkarsa yake, rashin sabo irin na Imara ya sanya
ta koma ɗakinta ta yi zamanta dan ita ba gwanar surutu ba ce. Tana nan zaune har
aka yi sallar azahar Nana ta shigo tana kallonta ta ce"wai ke mene haka?, kin wani
dawo ɗaki kin zauna. Ki tashi to kiyi wanka zamu tafi gidan make-up ance mu je da
wuri saboda muna da yawa" a sanyaye Imara ta ce"make-up kuma?, ni banason makeup
wlh" wani kallo Nana ta yi mata sai kuma ta ce"to ba faɗata ba ce, Mamah ce ta saka
saboda haka sai ki je ki sameta ki faɗa mata ke bakya so" langwaɓar da kai Imara ta
yi ta ce"ayyah Nana, dan Allah karki faɗa mata" ba ta ce mata komai ba ta fice daga
ɗakin bayan ta ɗauki abin da ya kawota. Tashi Imara ta yi ta shige toilet ba dan
ranta yana so ba.
****Ƙarfe 7:50pm suka fito daga gidan kwalliyar, gaba ɗayansu aka yi musu kwalliyar
har da Imara, sun saka wani uban su lace mai kyau, kai kana gani kasan da kuɗi aka
siya lace ɗin, Imara dake ta ƙoƙarin gyara rigar jikinta Nana ta kalleta ta ce"wai
me ki ke haka?" Kamar za ta yi kuka ta ce"ni wlh banaso, duk na matsu" tuntsirewa
da dariya suka yi gaba ɗayansu Maimoon ta ce"lailaima ke ɗin nan, wannan kayan ne
kin matsu?, baki san kayan da ake matsuwa ba ma" turo baki Imara ta yi ta ce"wlh ni
dai sun isheni, kuma wannan mayafin ya yi ƙarami" waro idanu Nana ta yi ta ce"to
malama sannunki, to bari ki ji koma me suka yi a haka za ki saka su" ɗauke kanta ta
yi tana kallon gefe. Dafata Umaima ta yi ta ce"kinga Imara mu je ki rabu dasu"gyaɗa
mata kai tayi suka shiga motar sannan sauran ma suka shiga.
A bakin ƙofar shiga suka tsaya saboda sune masu shiga da amarya, bayan amarya ta
fito da ƙawayenta wanda suma suka sanya lace irin nasu Nana wanda ke nuni da ankon
lace ɗin aka yi, tsara su aka yi yanda ya kamata sannan suka shiga da amarya. Banda
Imara wadda ana shiga ta zame ta fita daga layin, cika sosai aka yi a wajen dan
kusan kowa na dangi ya zo bikin, sai liƙa kudaɗe ake kamar ba gobe. Suna nan zaune
har aka kira yan cikin gidan domin su zo su yiwa amarya da ango liƙi, tashi suka yi
Nana ta kalleta ganin tana zaune ta ce"nan ɗin ma ba za ki taso ba?" langwaɓar da
kai Imara ta yi ta ce"dan Allah Nana ku je kawai, ni banason shiga wlh" tsaki Nana
tayi ta ja hannunta suka ƙarasa wajen. Khalil ne ya miƙo musu wrapper na yan dubu-
dubu, aka saka musu kiɗa suka fara liƙi, Imara kasa motsi ta yi dan ta rasa wanda
za ta liƙawa kuɗin, dan Jidda na ganinta ta haɗe rai, haka kuma ba zata iya zuwa
inda Abaan yake ba dan ta yiwa kanta katanga dashi. Tunda ta tsaya yake kallonta
hakan yasa ya tako har inda take ya riƙo hannunta, wrapper dollars ya zaro a
aljihunsa ya buɗe ya shiga liƙa mata. Da idanu kawai Jidda ta shiga bin su, ganin
ita ko biyar bai liƙa mata ba, tasowa abokansa suka yi dasu Khalil suka zo inda
yake tsaye suka shiga yi musu liƙe, ganin haka ya sanya suma su Umaima suka dawo
inda ake liƙin, gaba ɗaya sai kallo ya koma wajen, ya rage sai Jidda tsaye ita
kaɗai tana binsu da kallo. Amrish ce ta taso ta zo ta riƙe hannunta ganin tana
shirin kuka yasa ta yi mata magana can ƙasa ta ce"karki kuskura ki zubar da
mutuncinki, ki bari a koma gida" jinjina kai Jidda tayi tana sauke ajiyar zuciya.
Har aka tashi daga wajen ba ta sake koda dariya ba, suna fitowa ta shiga motar
Amrish suka bar wajen domin tasan ba Abaan ne zai kai su gida ba.
Amrish na parking ɗin motar ta fita daga gudu kai tsaye kuma apartment ɗin Jadda na
da ta shiga, biyo bayanta Amrish ta yi tana zuwa ta sameta kwance kan gado sai rusa
kuka take. Zama tayi gefenta tana rarrashinta amma ko saurarenta Jidda ba tayi ba,
shigowa sauran su kayi, Munceey ta ƙaraso inda take tana murmushi ta ce "ki kwantar
da hankalinki, yau dai ranki ya ɓaci, amma gobe ranta ne zai ɓaci, irin ɓacin ran
da zata ji kamar ta kashe kanta. Irin ɓacin ransa da zai yi sanadiyyar barinta
gidan nan, na rigada nagama shirya komai saboda haka ki kwantar da hankalinki ki
kuma goge hawayenki. Keda kuka sai na farin ciki Jiddo" ɗago kanta tayi tana
kallonta ta ce "kina fa kalla, kina fa kallan abin da aka yimin, wlh saidai idan
akwai abin da Abaan yake ɓoyewa akan yarinyar nan, idan badan haka ba wlh ko
kallonta ba zai dinga yi ba, ni daman tunda ya kawota ban yarda da ita ba" dafata
Xahra tayi ta ce"to ba gashi za'a yi maganinta ba, koma wani abun ne ai ya zo
ƙarshe, ki daina wani damun kan ki. Kina da masu share miki hawaye" goge idanunta
tayi sannan ta saki ranta.
Ranar kusan kwanan zaune suka yi suna hira, Imara ta saki jikinta duk da ba sosai
take maganar ba amma idan akayi abun dariya za tayi. Sai da aka kusa sallahr asuba
sannan suka kwanta, ita kuwa ta tashi ta ɗauro alwala ta zo ta fara gabatar da
sallah. Da safe gidan ya cika sosai da mutane, dangi da abokan arziki kowa ya zo,
ƙarfe 10:30am aka ɗaura auren Jidda da Abaan a masallacin dake gidan, daga nan kuma
duk mazan suka shige reception. Sai wajen ƙarfe 12pm sannan suka dawo, sanye duk
suke da fararen shadda wadda ita ce aka yi ankon ɗaurin auren. Kamar za tayi kuka
ta kalli Nana wadda ke janta ta ce"dan Allah ki cikani ni wlh banason hoton" ko
saurarenta Nana ba tayi ba ta cigaba da janta har compound ɗin gidan. Taron jama'ar
da ta gani ya sanya Imara sunkuyar da kanta, ita a rayuwarta bata iya shiga cikin
jama'a ba. Murmushi Umaima tayi ta ce"sai wani sunkuyar da kai ki ke kamar ke ce
amaryar" turo baki ta yi ta ce"ayyah ni wlh nagaji kaina ciwo yake" dariya Nana ta
yi ta ce"ki bari a yi mana hotuna da amarya sai ki tafi" da sauri ta kalli Nana
kamar za tayi magana sai kuma ta yi shiru. Ƙarasowa gabansu ya yi yana murmushi ya
ce"kaga ƙannen ango kuma ƙannen amarya" dariya suka yi banda Imara, Nana ta ce"ai
Yaya wani shagalin sai ranar bikinka" murmushi Kamal ya yi ya ce"kedai bari
mutuniyar, ku zo muje ayi hotuna daku mana" toh suka ce sannan suka bi bayansa har
inda ake hotunan, kallo ɗaya Imara ta yiwa Jidda wadda ke wani shishshigewa Abaan,
tana sanye da farin lace mai adon golden ta yafa mayafi golden akanta tayi kyau
Masha Allah. Ƙarasawa suka yi Imara ta tsaya daga can baya dan ko da wasa bata zuwa
inda Abaan yake, hotuna aka shiga ɗaukansu banda ita dan tana tsaye daga can gefe.
Kallo ɗaya Abaan ya yi mata sai kuma ya ɗauke kansa, kamar wanda aka yiwa dole haka
ya ƙarasa inda take ya jawo hannunta, a kusada shi ya tsayar da ita hannunta na
cikin nasa aka ɗaukesu hoto, Jidda fita tayi daga hoton ganin yanda ake ɗaukarsu
kamar ita ce matar tasa, juyawa tayi ta bar wajen kamar za ta tashi sama.
****Tunda Imara ta shiga ɗaki bata sake fitowa ba har aka yi sallar la'asar, Nana
ce ta shigo ta sameta a kwance, tashinta tayi ta ce"ki tashi ki yi wanka an fara
shirin kai amarya har ƙarfe 6pm" dafe kanta tayi kamar za tayi kuka ta ce"kaina
ciwo yake Nana, ni ba zan iya fita ba" dafa kanta tayi taji zafi sosai hakan yasa
ta ce"sannu to, ki yi zamanki idan zamu koma sai ki je, mu mun tafi" gyaɗa mata kai
kawai Imara tayi sannan ta koma ta kwanta. Kiran sallar magrib da ta ji ya sanya ta
tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala. Sallah tayi sannan ta fito daga ɗakin, bata
sami kowa a main parlon ba, da alama duk an tafi kai amarya. Fitowa compound ɗin
gidan tayi tana leƙe ko zata samu wani.
"Imara!"
A ɗan firgice ta juya, Jidda ta gani tsaye a bayanta, murya can ƙasa ta ce"na'am"
murmushi Jidda ta yi ta ce"dan Allah muje zan baki tea ki kai wa Yaya Khalil, ya ce
a kai masa to ni kuma tafiya zan yi" kamar ba za tai magana sai kuma ta ce to,
Jidda tayi gaba ita kuma ta bi bayanta. A bakin ƙofa Imara ta tsaya tana kalle-
kalle, lokacin gari ya yi duhu dan har an kusa fara kiran sallar isha'i, fitowa
Jidda tayi hannunta riƙe da wani ɗan ƙaramin tea flask, tana murmushi ta miƙa mata,
amsa Imara ta yi, ta ce"yawwa dan Allah idan kin je sai ki saka masa cup akai, If
possible ki tsaya ya shanye please" toh kawai Imara ta ce sannan ta juya ta bar
wajen, murmushi kawai Jidda ta yi sannan ta koma ciki.
Babu inda Imara ba ta duba a ɗakinsa ba amma baya nan babu ma alamar akwai mutum a
ɗakin, fitowa tayi hannunta riƙe da flask ɗin tana shirin sauka ta ga wata maid ta
hawo, a sanyaye ta ce"dan Allah ina Mama take?, da Yaya Khalil?" cike da girmamawa
ta ce"Hajiya Mamah ta fita, shi kuma Khalil yana ɗakin babban yaya ɗazu" jinjina
kai kawai Imara tayi sannan tayi hanyar ɗakin Abaan. Tura ƙofar tayi ta shiga, babu
kowa a parlon sai tv dake faman aiki ita ɗaya, ƙarasawa tayi ta ajye flask ɗin akan
table ta tsaya tana haki. Tunowa ta yi da hotunan rannan hakan yasa ta tayi hanyar
bedroom ɗinsa da gudu. Tana shiga Abaan ya fito daga kitchen yana sanye da armless
milk da alama bai daɗe da fitowa daga wanka ba. Tea flask ɗin ya gani hakan yasa ya
ƙarasa, dan ya yi tunanin Mamah ta manta dashi ma. Cup ya ɗauka ya tsiyayi shayin
sannan ya fara sha. Tsayawa ta yi ta rike ƙugunta kamar za tayi kuka, dan babu inda
ba ta duba ba amma bata samu hotunan ba. Turo baki tayi ta juya zata fita ta hangi
wata jaka akan mirror, ƙarasawa tayi ta buɗe jakar, wata ajiyar zuciya ta sauke ta
zaro envelope ɗin, murmushi ta yi ganin hotunan ne, ta yi zaman dirshan a wajen ta
cigaba da buɗe hotunan. Wata mata ta gani tsaye a kusada Abaan lokacin bai fi
shekara 18 ba, waro idanu Imara tayi ganin matar tana tsananin kama da ita, sake
ɗaukan wani hoton tayi nan ma taga matar ce tsaye sai Abaan gefensu kuma wata yar
ƙaramar yarinya.
"Joda!"
Imara ta faɗa cikin tashin hankali da mamaki, tabbas wannan Joda ce, koda basa ga
maciji da ita amma tagane kamarta, baza hotunan tayi a ƙasa ta shiga zarowa tana
kallo, a firgice Imara ta tashi tsaye tana girgiza kanta bakinta na rawa ta shiga
furta
"A'a, no ba shi bane, ba Ameer bane!, me hoton Ameer yake a gidan nan?" Tamkar wata
zararriya haka take magana, wani hoton ta ɗauko wanda ya sanya ta yi baya tana
shirin faɗuwa, gabaɗaya mutanen cikin masarautar Udaid sune a cikin hoton, idanunta
ya sauka kan Maheer wanda ke tsaye kusada Abaan, runtse idanunta tayi abubuwan da
suka faru suka shiga dawo mata ɗaya bayan ɗaya, saurin yada hoton ta yi, ta fice
daga ɗakin da sauri za tayi waje. Tsaye ta same shi a parlon idanunsa a lumshe.
Gabaɗaya jikinta rawa yake cikin rawar murya ta fara magana
"Waww...wane kai?, ka faɗa min gaskiya, a ina kasan Ameer?, daman turoka suka yi ka
kasheni?, wlh ba ni ce na kashe Ameer!, ban kashe shi ba!, bani ba ce!, kar ka
cutar dani, zan bar gidan nan yanzu dan Annabi!"
Ɗago idanunsa ya yi ya zuba mata yana kallonta, saurin ja da baya Imara tayi ganin
yanda idanunsa suka yi wani irin Jaa jijiyoyin kansa suka tashi, a hankali ya fara
takowa zuwa inda take tsaye. Baya Imara ta fara yi har sai da taje jikin ƙofa hakan
yasa ta maƙale a jikin ƙofar cikin tashin hankali take faɗin
"Mene haka?, ka matsa daga kusadani, ni tafiya zan yi, wlh ba ni ce na kashe shi
ba!, zan yi maka bayani kar ka cutar dani" runtse idanu Abaan ya yi ba tayi aune ba
ta ji ya ja hannunta, kai tsaye kuma ɗakinsa ya shiga da ita, bai lura da tarin
hotunan dake zube akan carpet ba ya cillata kan gado jikinsa na wani irin rawa, sai
haɗa gumi yake, Imara ta kasa gane abin da yake nufi, gabaɗaya tunanin ya tsaya
cak, me Abaan ke shirin aikata mata?, me ya sameshi haka har ya fita daga cikin
hayyacinsa?. Fashewa tayi da kuka ta tashi da niyyar guduwa, sake hankaɗata kan
gadon ya yi sannan ya bi ya danneta, zuwa sannan ko numfashi ƙwakwakwara bata iya
wa, ganin yanda yake abu a gaggauce ya sanya ta runtse idanunta, duk yanda ta so ta
kwaci kanta a wajen Abaan kasawa tayi, tana ji tana gani ya rabata da kimarta ta ya
mace wadda ko mijin daya aureta bai aikata hakan a gareta ba.
A hankali ya buɗe idanunsa ya zuba mata yana kallonta, gabaɗaya bata cikin
hankalinta dan ko numfashi bata yi. Dakyar ya iya tashi daga kwancen da yake ya ja
jikinsa zuwa inda take, bugar ƙofar da yaji an yi yasa ya ɗago yana kallon ƙofar
cikin tashin hankali
"Mamah!??"
*Duka wadannan amsoshin suna nan cikin littafin IMARA book 2, wanda kuma ba Free
bane, za ki biya ₦500 ta wannan account ɗin 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay sai a
tura shaidar biya ta lambata 08106608363, zamu cigaba da book 2 ranar Monday in sha
Allah, kafin nan duk wanda bai biya ba sai ya yi ƙoƙari ya biya, taku har kullum
Nanameera.*