Baqar Inuwa..Billy
Baqar Inuwa..Billy
*_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_*
*_Ya rabbi ina roƙonka da sunayenka ƙyawawa masu tsarki, ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni ni
da al'umma. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar dani da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Yanda muka
fara lafiya ALLAH yasa mu kammala cikin farin ciki da kwanciyar hankali🙏🏻_*.
*_Ya rabbi ka gafartama mahaifina, ka ƙarama iyayena biyu mata da suka rage lafiya mai amfani.😭🙏🏻_*
_Littafin *BAƘAR INUWA* ƙirƙirarran labarine da baida alaƙa da kowa da komai. An yisane domin
faɗakarwa, nishaɗi, ilimantarwa, harma da ban haushi ta wani sashe. Dan haka a wannan gaɓar ina son
jan hankalin mai karatu, yayma kansa adalci yayma marubuci adalci._
*_A duk lokacin da mai rubutu ya kafa alƙalaminsa akan takarda ba yana nufin dole zai rubuta irin
RAYUWARSA bane, ko irin RAYUWARKU. Malami yakan faɗakar ya tsoratar akan abinda ya dace. Haka
shima marubuci yakanyi rubutu domin faɗakarwa ko nishaɗantarwa akan abinda rubutunsa yazo dashi.
Idan yasa ƙyaƙyƙyawa, ba dole sai yanada irin wannan ƙyawun bane, domin kuwa kowa yasan a duniya
akwai ƙyawawa. Idan yasa mai ƙarancin ƙyau (domin UBANGIJI bai halicci mummuna ba, kowa da irin
ƙyawun da yay masa na halitta), ba dole sai yana a cikin wannan jinsin bane, sai dan rubutunsa a haka
yazo. Idan yasa mai arziƙi, badan dole sai shima yanada arziƙin ba. idan yasa mai mulki, ba dole sai ya
kasance jinin mulki ba. Idan yasa talaka, ba dole sai ya kasance talaka ba. Abinda kawai nasani alƙalamin
marubuci zai iya taɓa kowa. Mai kuɗi, talaka, mai mulki, ɗan ƙauye, ɗan birni, musaki, mai ilimi, jahili,
ƙyaƙyƙyawa, mai ƙarancin ƙyawu. Mai ƙyawun hali, mugu dama kowa da kowa. Duk kuma abinda ya
taɓo idan zaka nutsu wajen zagaye cikin duniya koda ace da tunani ne sai ka samu mai kamanceceniya
da LABARIN. Shiyyasa kuskure ne mai KARATU ya tsuke tunaninsa akan dole sai abinda ya sani
MARUBUCI zai wallafa ko ya faɗa. Idan akasin hakan yazo kuma shi a gurinsa marubuci baiyi dai-dai ba.
Karka manta ALLAH ya haliccemune yaruka daban-daban, jinsi daban-daban, yanki daban-daban, launi
daban-daban, addinai daban-daban, yaruka daban-daban. Bai zama lallai sai abinda kai ka sani ko kake
gani zai rubuta ba. MARUBUTA da yawa sun sha rubuta LABARANSU ko RAYUWARSU a littatafai daban-
daban batare da kunsan nasu bane ba. Saboda basu fito sun sanarma duniya nasun bane ba. Dan haka
ina roƙonku idan LITTAFI yazo muku, ku karanta kawai badan lallai sai yazama RAYUWAR wanda ya
rubuta ɗin tazam dai-dai da abinda ke ciki ba. Kawai kadai duba darasin dake ciki ka amfana, akasinsa
watsar, yi farin ciki da farin cikin da yazo dashi, dan wani abun akan rubutashine kawai domin ƙawata
labari ko nishaɗantar da mai karatu wajen cire masa wata keɓantacciyar damuwarsa. Ina fatan za'a
fahimceni_*
_Banyi wancan dogon bayanin bane dan na canja kowa, nayi ne kawai dan ya zama dai-dai da fahimtar
ka a ƙwaƙwalwarka da tuntar da kai wanene MARUBUCI a taƙaice. Domin kuwa KOWA masoyin Bilyn
Abdull ne, amma bai zama kallai ita ta zama abin SON kowa ba._☺️
*_Alhamdulillahi ZAFAFA BIYAR sun sake dawowa gareku da sabbin salo daban-daban. Muna fata ALLAH
ya baibayemu da alkairinsa mu da ku dake tare da mu. Sannan muna roƙon wanda ma basu tare damu,
kodan sauke haƙƙi kuzo dan ALLAH ku saya da kuɗinku badan zamu iya furta kalma mara daɗi gareku ba.
Dan kuwa koda wasa bama fatan jifan wani ɗan uwanmu musulmi da kalmar (ALLAH ya isa akan littafi).
Masu saya ku fitar, dan girman ALLAH kuji tsoron ALLAH. Badan mu ba, badan mun isa ba. Kuyi haƙuri ku
daina aikata mana hakan, domin UBANGIJI ya hana zalunci a tsakaninmu._*
_Masoya kumuje zuwa, domin kuwa yanzu za'a far share filin wasan, dan wannan karon tafiyar ZAFAFA
ta dabance_.
_____________________
*_Episode 1_*
.............Tafe yake tamkar iska zata kwasheshi ya faɗi dan sauri. Yayinda yake ƙananun surutai kai kace
sabon kamune a hauka. Ya sake cin tuntuɓe a karo na biyu, sai dai cikin sa'a ya dafe bangon
gwaguyayyen gidansa saɓanin ɗazun da sai da ya kai ƙasa. Dogon tsaki yaja zuciyarsa na sake hasala da
kumbura har cikin maƙogwaro. Cikin son huce haushinsa da takaici yasa ƙafa ya daki murfin gidan na sa
da duk ya cinye da tsatsa tsabar daɗewar da yay, dan tunda aka gina gidan banajin an taɓa sauya
ƙyauran saboda koɗewa da ciccinyewar da yay na tsatsa tamkar tsohon drom ɗin ƙarfe.
Ball ya fara da butar da ke a farkon shigowa, inda alamu suka nuna toilet ɗinsu ne a wajen. Ta tafi ta
daki ƙarshen bango, murfin yay gefe itama tai gefe.
Baba Nafi da ke alwalar magrib ta ɗago kai cike da nutsuwa da sanyinta ta dubesa. Sai kuma ta
maida kanta ƙasa saboda uwar hararar daya zuba mata kai kace idanun nasa zasu zubo ƙasa ne.
“Kowanne shege da ke gidan nan ya fito!!”. Ya faɗa a kausashe yana dukan langa-langan da aka
zagaye saitin inda yake tsaye matsayin kitchen ɗin girkinsu.
Cikin takaici da haushi aka bankaɗe labulen ɗakin tsakkiya, “Kai ko malam ka dinga sassauta ma
zuciyarka mana dan ALLAH!, da wannan farar magriban da kowa ke ƙoƙarin kai abincin buɗa baki
bakinsa maimakon a ganka bayan liman kana shirin gaida UBANGIJI sai ka lalace da neman masifa da
tijarar hana iyalanka su susha ruwa cikin salama kamar yanda ka hana kanka?”.
Fici-fici yay da ido yana duban ta cikin ɓacin rai. Ya tattaro duka takaicinsa da damuwa zuwa cikin
baki. Nunata yay da ɗan yatsa yana karkaɗa hannu cikin gargaɗi. “Larai ina rabaki da tararmun numfashi
idan ina magana amma baƙya kiyayata. Na rantse miki da ALLAH idan ban sauke dukanin abinda na
kwaso bisa kanki ba kice ba sunana DAUDA jikam mai ɗan-wake ba.”
Baki ta taɓe da sakin labulen, sai dai bakinta bai mutuba. Da ga cikin ɗakin take faɗin, “Can kaji da
fitinarka ba'a kaina ba. Baka sauke haƙƙin bani abinda zanci a cikin wata mai falala ba bazaka sauken
gangar ɗan bazakuɗa ba. Kai da ka kwaso abarka can ta ƙare maka ba Larai ba.”
Duk da ya jiyota sai bai tanka ba, ya cigaba da ƙwala shelar kiran kowa yazo gabansa. Shiru babu
wanda yay tari tamkar kowa ya mutu a gidan. Wani ƙududun takaicin baƙin ciki daya taso masa daga
tsakkiyar zuciya ya jawo da ƙyar zuwa maƙoshi ya fesar ta baki.
“Eh lallai ta tabbata an gama maidani ɗan iskan ƙasan gada, yo banda ana ɗaukata girman fadar
karuwai harni dake amsa sunan maigida a gidan nan zanzo ina magana ku barni ina ɓaɓatu ga ƙwalon
shege haihuwar tasha ko?..”
“Kayi haƙuri malam mudai salla muke wlhy, suma kuma nasan.....”
Wuff Larai tayo waje tana gyara zaninta dake neman ɓallewa saboda tsabar sauri, cikin harziƙowa ta
tare numfashin baba Nafi mai maganar cikin sanyi da rashin son hayaniyarta “To annamimatu kinsan
me? To muma sallar muke sai a maida sherin da ake son ƙulla mana cikin ciki ko?”.
“ALLAH sarki Larai nima ai abinda zance masa kenan bawai wani abu daban ba”. Baba Nafi ta sake
faɗa a sanyaye.
Baki larai ta taɓe da juya ƙeya ta tura kallabinta disko gaban goshi, daddagaggiyar ƙeyarta ta bayyana.
Murmushi kawai Baba Nafi tai da girgiza kanta ta ɗauke idonta gareta.
Duk abinda suke yana tsaye sai faman kumbura yake da harar ɗakin ƙarshe da ke jerin nasu baba
Nafin. Sai dai baice uffan ba. Kusan mintuna biyar aka ɗaga labulen ɗakin aka fito. Mace ce ƙyaƙyƙyawa
da bazata gaza shekaru talatin da biyar ba zuwa da bakwai. Daka ganta kaga ƴar duniya bugun farko.
Sheƙeƙe ta dubesa shi da matan nasa ta watsar tana taunar chewing gum tamkar ba azumi aka kai ba
yanzun nan.
“Wai Lafiya kaketa faman shela da farar magriba ko ruwa bamu kai bakinmu ba? Haba yadai
kamata asan da da yanzu akwai banbanci, dan da kana juyamune muna haƙuri da tujaranka saboda
kanada uwar kuɗinka a ƙugu, amma yanzu baka barinmu da cikinmu da hidimar ƴaƴanmu ka kuma haɗa
mana da tijara da gadara *BAƘAR INUWA......”*
Wata shegen dariya Larai ta bushe da shi, ta callara guɗa tana duban Asabe. “Kina birgeni amarya,
idan mu latsamu a tauna baida wahala ke ai kin wuce kanwar lasa”.
Baki Asabe ta taɓe ta ɗauke kanta gefe. Wani irin ƙududun baƙin ciki ya sake kume Malam Dauda. Ya
nisa tamkar bajimin sa dake a ganiyar tozon girma yana ballama Asabe ƙarfen ƙafarsa harara. Shikam ai
auren bariki bai masa rana ba. Fuska ya sake tsukewa yana kai hannu ya kaɗo mutsiyar tuƙin tuwonsu
dake rataye jikin kwanon kitchen ɗin.
“Matsalar mutum ce wannan kuma. Ina son naji wane shege ne tambaɗaɗɗe yaje wajen Jabiru mai
shago ya amso lemon kwalba da cin-cin ɗin da matarsa keyi yace injini?”.
Kallon-kallo Nafi da Larai suka shigayi, sai dai komai babu wadda tace tunda sunsan shima yasan
wadda zata iya wannan aika-aikar ai. Kuma shine ya bata wannan dama ɗin tun tana amarya, gashi
yanzu tsahon shekaru goma sha bakwai har ƴan matanta na yawo galla-galla a gidan harsu huɗu komai
ya gagara canjawa......
“Wai ba magana nake ba ne? Ko sai na maida ƙasan gidan nan zuwa sama ne!!?”.
Malam Dauda ya faɗa a matuƙar tsawace tsabar hasalar da zuciyarsa ke sake masa na baƙin cikin
bashin da aka cimasa bayan baida ko sisi dana sharesan da akai yana magana. Nanma babu wadda ta
tanka sai ƙarar taunar chewing gum ɗin Asabe kawai dake tashi ɗas-ɗas...
Matashiyar budurwa da zata iya kaiwa shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai a duniya ta fito da
ga ɗakin da Asabe ta fito ɗazun. Sanye take da dogon jijjab har ƙasa alamar salla tayi. Tana tsananin
kamanni da Asabe tamkar tayi kaki ta ajiye. Cikin ladabi da nutsuwa takai duƙe tana faɗin “Abbanmu
barka da dawowa? Ansha ruwa lafiya?”.
Ƙasa tai da kanta ƙwalla na ciko mata ido, dan tanada zuciya matuƙa, sai dai tana da ƙoƙarin
dannewa musamman akan mahaifanta guda biyu da halinsu baida maraba da girman haihuwar ƙasan
gada.
“Kayi haƙuri Abbanmu, dama zance maka nice na amso lemon a wajen jabiru”.
“Buhun bu*a'uban nan kayyasa (). E lallai na zama ɗan iska haihuwar ƙasan gada kuwa da gaske. To
ubanwaye ya aike ki!!?”.
Yanda yay maganar a tsawace ya sata runtse idanunta da ƙarfi tana haɗe kukan dake neman taso
mata. “Kayi haƙuri Abbanmu, babu wanda ya aike ni. Babu abinda zamuyi buɗa baki ne da shi shiyyasa
na amso mana, nace masa kaine ka aikoni dan inba hakaba bazai bani ba”.
Sake maƙurewa yay jikin bango tamkar tsohon ƙadangaren da ciwon sanyi ya buge yake shaƙo
ƙamshin mutuwa.
“Ni DAUDA naga haihuwar jaraba jinin ladin ƙasan gada. Niko wai yaushe lalacewata takai har
hakane a gidan nan ne wai? K dan uban uwarki har ni zaki laƙawa sheri ina fama da ƙishirwar azumi na?
To wlhy ki rubuta ki ajiye sai kinyi nadamar hakan daga ke har uwar taki, dan nasan itace ta aike kin ta
noƙe......”
“Kai Dauda sauraramin. To kodai dama dani ɗin kake bada itan ba da ka haifa? To wlhy ahir ɗinka
wahainiyarka ta kiyayi ramata, inba hakaba kaima kasan na fika tsiya da tujara. Ka buga ƙafa kamar na
karen mafarauta ka barmu cikin yunwa ga ruwa za'a sha saboda kafi kowa iya babbaku da tujara dan
kawai an anso abin nera dubu guda injika shine zakazo tsakar gida gaban magauta da ƴan bani na iya
kana zazzage min. To wlhy ina dai-dai da kai”.
“Tsssss!!!!”
Kakeji wani irin gigitaccen mari mai ƙara da alamar zaiyi ɗan karen zafi ya sauka bisa kumatun budurwar
nan dake tsugunne ranta a matuƙar jagule, ta amshi laifin ne dama dan gudun karsu raba halin da suka
saba a gaban kishiyoyin mahaifiyar tasu. Amma sai gashi dabarar tata batai ba.
Ta dafe kuncin jikinta na rawa. “Wannan marin na hanani zaman buɗa baki wajen Jabirunne da
kikayi ke kuma. Saura na ƙaryar da kikaimun itama. Ke kuma Asabe yanzu banda lokacin mai lokacinki,
amma ina nan tafe kanki..” ya ƙare maganar yana nuna Asaben.
Caraf Asabe tasha gabansa tana mazurai. “Wlhy ka sake taɓamin yarinya sai na rama mata. Kai barfa
ganin uwa ban son ta, son kayana nake ras, idan kuma kaji ƙarya sake taɓata dai-dai nake da kai, danni a
yanzu nake da naka lokacin. Banda kai dai kana cikin mazan da sai an tsoma kansu a wuta an ɗauraye
musu zunibi ka fita baka ko bamu geron kunu ba dan mun samawa kammu mafita kazo har kana tara
jijiyar wuya. To bara kaji ni ba matanka bane daka maida sakarkaru, idan kaji ƙarya kuma sake gwada
bugunta ka gani, kaima kasan wacece Asabe autar hajiyar birni shalelen bahago dan mai.......”
Sai kuma taƙi ƙarasawa ta balla masa harara, ganin ya juya fuuuu zai sake ficewa. Taja tsaki da faɗin,
“Da ka tsaya mana kaji ko zaka iya latsawa ka kwana lafiya ɗan gidan abun kwari mai yawo da tsinuwar
uwa bisa kai”.
Wani irin kuka budurwar nan da har yau ke duƙe ta fashe da shi. Cikin masifa Asabe ta juyo kanta
takai mata shiru dan tasan minene dalilin kuka. “Dan ubanki tashi anan kona huce kaf haushinsa a kanki
mara mutunci. Ko dan dai nice jinin asara sai na zauna yana cin zarafina gaban kishiyoyi na masa shiru
saboda ga jikar ta-salla wadda ta haɗiyi ƙur'ani dan haƙuri. K nifa bar ganina haka zan iya kakkaɓar daku
nai gaba dama tausayinku ne yasa nake zaune a wannan gidan da tsiya taima katutu abincima sai anyi
kwarakarsa a maƙwafta dan lalacewa”............✍️
*Tofa jama'a bana ina mukazo haka? Ina alƙalamin namu ya kwasomu ya kawo😹😹?.*
_A cikakken Littafin BAƘAR INUWA kawai zamu samu wannan amsoshin. Naira ɗari uku me kacal, tare da
duk zafafa biyar naira dubu ɗaya ne kacal. Karku bari ayi babu ku. Dan bakuga komai ba. Yanzu aka fara
sharar filin wasan. Cakwakiyar sai wasan ya kankama😉. Dan duk wanda akayi babu shi ALLAH yayi
missing🥺._
Taku
___________________________
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
________________________
*_BAƘAR INUWA..._*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form din kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_*
_“Kamar yanda na faɗa tun farko labarin, Littafin BAƘAR INUWA ƙirƙiraren labari ne, dan haka duk wani
sunan gari da zai iya zuwa cikin labarin shima ƙirƙirarsa akayi, komai ma da zai iya shigowa cikin labarin
ƙirƙirarsa akayi. Baida alaƙa da wata ƙasa ko wasu mutane. Koda kuwa kaji abinda ya shafeka ko yay
kamanceceniya da kai to ka ɗauka kamarce kawai yayi bawai yana da alaƙa da kai bane ba. Dan Bilyn
Abdull bata sanki/ka ba balle ta dasa alkalaminta akan ka. Rubutu ne kawai nayi dan nishaɗi, faɗakarwa,
ilimantarwa, harma wani abun zai iya zuwa muku da ban haushi saboda wannan karon ma a haka
alƙalamin nata yazo.😅🙏🏻_
________________
*_Episode 2_*
*_ƘASAR NAYA_*
.........*_(DALLO STATE): HUTAWA L.G.A._* Da gudu budurwar ta miƙe ta shige ɗaki tana cigaba da kuka,
ganin a yanda ta shigo ta wuce tana kuka, ƴammata biyu da za'a iya kira tagwaye kuma yayunta suka
kwashe da dariya suna faman taɓe baki da ɗaga kwalbar lemonsu suna ɗaɗɗaka hankali kwance.
Sai kuma suka maida dubansu akan Asabe data shigo tana cigaba da zazzaga ruwan tujara.
Ƴammatan suka faɗa suna mata jinjina da kwashewa da dariya a karo na biyu. Zama tai kusa da su taja
kwalbar lemo guda tasa haƙori ta ɓalle murfin tana huci. Batare data cema ƴammatan komaiba ta ɗaga
tasa a baki, kamar ƙiftawar ido sai gashi ta zuƙi kusan rabi sannan ta dire tana sauke ajiyar zuciya.
Wadda tafi hasken sosai dake kallon kwalbar lemon ta ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Mommy sunan
wannan shan lemon naki shan huce takaici”.
Tsaki tayi tana gyara zama da ɗaukar tsokar nama dake gabansu ta danna a bakinta. “Yo wannan uban
naku inba shan huce takaicin kakema ni'imar da ALLAH yay maka ba ai tuni yake tsotse maka ruwan jiki,
ga waccan mara mutuncin dake abu uwa ba jinina ba.”
“Yo Mommy bayan kamanin da take dake ai sai muce muma ko'an canja miki ita ne a asibiti? Muda
yakamata muyo kamanin naki hegiyar mai taurin kan tsiya da kicifi duk an haɗa ita an bata.”
Duk abinda suke budurwar nan na jiyosu daga uwar ɗaka. Dan haka ta sake fashewa da kuka
zuciyarta na mata ƙuna da raɗaɗin halin iyayen nata da ƴan uwanta. Tun tana ƴar ƙaramarta takejin ana
zagi da la'antar halin mahaifanta a cikin layinsu, har gashi yau tsahon shekara goma sha bakwai bataji
komai ya canjaba sai ma abinda ya ƙaru a dalilin ƴan uwanta guda biyu da kullum cikin janyo masu wata
sabuwar maganar suke. Duk da dai itama ta fara rashin ji mai kama da nasu ALLAH ya tarota ta nutsu
sanadin malamin islamiyarsu sayyadi Abubakar.
Hannu tasa ta share hawayenta da gyara kwanciyarta zuwa rufda ciki, duk da yunwa dake cinta
saboda azumin data kai hakan bai dameta ba, ta lumshe ƙyawawan idanunta data gada wajen
mahaifiyarsu Asabe a hankali Murmushi na suɓuce mata mai haɗe da hawayen tausayin kanta na rasa
Abubakar. Tabbas zuwa yanzu ta yarda ta rasashi, ya tafi har abada bazai sake dawowa gareta ba kamar
yanda iyayensa suka faɗa. Wannan ciwone a rayuwarta mafi muni da har abada bata tunanin
warkewarsa, dan ya zama gyambo a ƙirjinta. A tsaye take da sunanta, amma a zuciya ta jima da mutuwa
tun sanda iyayen abubakar suka saka ya fita a rayuwata.
Sunanta shine *_AMINATU_* sai dai ana kirana da *_RAUDHA_* sakamakon sunan kakarta da taci
wadda ta haifi mahaifinta. Kamar yanda kukaji a bakin mahaifiyarta sunan mahaifinsu DAUDA, sai dai
ana kiransa ɗan-azumi. Tun a ƙuruciyar mahaifinsu mutum ne marajin magana. Al'amarin nasa ya sake
turewa a lokacin daya fara bin wani ɗan anguwarsu driver matsayin karen mota. Kamar yanda kakarsu ta
taɓa basu labari tarbiyyar Abbansu da rayuwarsa ta sake gurɓacewa a dalin wannan bin mota, dan bai
rufa shekara ba a hanun uban gidansa sai shima ga tashi motar. Tun yana jan ƙaramar mota harya koma
babba irin ta company ɗin nan da ake ɗaukar kaya trailer. Fara jan motar trailer yasa albarka a hanunsa,
dan babu wani tazara da hakan kuɗi suka fara zauna masa. Da ƙyar ya yarda ya auri matarsa ta farko
Nafisa, wadda ɗiyar ƴar uwace ga kakarsu. Nafisa tanada matuƙar haƙuri, hakan yasa bata taɓa kai karan
ɗan-azumi ba a duk gallazawa rayuwarta da yakeyi. Basu rufa shekara da aure ba ya auro sabuwar
amarya mai suna Larai. Larai fitinanniyar mace ce mai kauɗi da rashin barin kota kwana. Yanda ta hana
Nafi zaman lafiya haka ta hana Mal. Ɗan-azumi. Mahaifiyarsa tayi-tayi ya saketa yaƙi. Babu jimawa da
auren Larai Nafi ta haihu, itama Laran bata cika shekara ba a gidan ta haihu. Zamansu ya cigaba da
kasancewa babu wani daɗi, yayinda Mla. Ɗan-azumi ya cigaba da sake kutsa kai a yawon tazubar. Dan
kuwa a kaso biyu bisa ukun kuɗin da yake samu suna tafiyane ga neman mata da ashararancinsa. Sune
manyan ƴan duniyar duk wani gari na baɗala da ire-iren gurare na ashararanci da akasan direbobi na
kakkaɓe dukiyarsu a wancan zamanin.
Nafi ce kawai ke damuwa da halin banza na maigidan nasu, Larai ko ko'a kwalar rigarta tunda akwai
kuɗi, dan ita kam dama sune matsalar rayuwarta tunda itama acan ya kwasota a tashar ƴan tazubar ɗin.
Suna da haihuwa hurhuɗu Nafi da cikin na biyar Ɗan-azumi ya sake sabon aure daga birinin Loss. Ba
kowa ya auroba kuwa sai Asabe ɗiyar *Ɗahare (Hajiyar birni)* mai tuwo-tuwo a ƙarƙashin gada.
Ɗahare mace ce mara mutunci da duk wani shege daka sani ɗan yankin nan dake zaman tazubar a
Loss ya san da zamanta. Asalinta a ƙasar saudia take tana TIKARI tsahon shekaru, a wani yaya da akayo
alƙawarin ALLAH ya cika aka yayota zuwa ƙasar Ghana. Kasancewarta shaharriya acan ɗin ma yasata ko
NAYA bata dawo ba ta sake komawa. Dan kuwa yaranta nacan su huɗu wanda ta haifa da wasu larabawa
biyu, sai dai dukansu aure tai da su. Na farko rasuwa yay ya barta da yara biyu mata *Samiha da
Hannah*, na biyu kuwa rabuwa sukai saboda Ɗahare ta wuce dukan tunanin mai tunani. Kwasotan ma
da akai shine yay shunenta dan yana so ya sace yaransa dake hanunta su biyu. Sai dai kuma ta koma
domin tanada hanya sosai. Komawar Ɗahare da biyu ne. Na farko da ƙudirin ɗaiɗaita rayuwar balaraben
nan ne uban ƴaƴanta guda biyu, *Halima da Nasiba (Asabe)*. Na biyu ƙudirin rabo ƴaƴanta biyu daga
hanunsa ne, dan labari yazo mata tana barin ƙasar yana zuwa ya kwashesu yabar wanda ta haifa da
mijinta na farko. Kamar yanda ta tsara kuwa hakance ta kasance, dan kuwa dai duk da balaraben nan
bawani mai shaharren arziƙi bane, dan kuwa baƙauyene ma. Sai dai yana da arziƙin dabbobi matuƙa na
kiwo dana tatsar madara. Duk irin makircin da Ɗahare ta ƙware sai da tabi wajen ganin ta rabashi da
wannan dukiyar, jin ana bincikenta a kama yasata tattaro duka ƴaƴanta huɗu ta baro saudia bisa
taimakon wasu mutanenmu dake can masu ɗaure musu ƙugu. Koda ta dawo gida kuma babu inda ta
yada zango sai tsakkiyar birnin jihar Loss. Inda ta fara tuwo-tuwo yaranta huɗu ƴammata zagaɗa-zagaɗa
na taimaka mata.
Game da ƴaƴan nata tamkar kumbo kamar kafinta ne. Dan kuwa a kaf halayyarta babu wacce suka
bari musamman ma Asabe mafi ƙyawun fuska da ƙyan sura a cikinsu. Dan kuwa ƙyaƙyƙyawar
balarabiyace da kallo guda bai isar mai dubanta. Dan-danan alhazan birni suka fara wawarsu da
sheɗanci, dan kuwa inma kace da aure kazo garesu to tabbas kuwa Ɗahare da sunanta ya koma Hajiyar
birni ba daga maka kafa zatai ba. Zatai maka wankin babban bargo tace bata gama more wahalarta ba
za'a tura mata ƴa cikin ɗaki, sam bata yarda ba.
Ko'a jikin ƴaƴan, dan suma basu buƙatar auren sai harkar neman kuɗin kawai, sai dai banda Asabe.
Dan duk kauɗi da rashin mutuncin Asabe ita dai tafi buƙatar aure sama da rayuwar barikin. Bawai batayi
bane, a'a bata cika sakin jiki tayi ɗin bane tamkar wata karya. A wannan halin ALLAH ya haɗata da Mal.
Dauda ɗan-azumi, wanda yake tsaka da tashen kuɗi. Gashi shima masha ALLAH ƙyaƙyƙyawan bakatsine
bafulatani. Dandanan ya fara sakar mata kuɗi na hauka, tare da zazzafar soyayya dan kwashi dai tunda
ya ɗana sau ɗaya yaji bazai iya haƙuri yabarta ba sai ya aureta. Duk wani shigi da fici irin na ƴan bariki
kwararru ɗan-azumi yayi ga malamsa na masa aiki, cikin ƙanƙanin lokaci ya rikita zuciyar Asabe tace inba
shiba sai rijiya mai gaba dubu. Hankalin uwarta ya matuƙar tashi dan tafi kallon sa'arta jikin Asabe fiye da
sausan ƴaƴanta saboda ƙyawu da ALLAH ya bata na larabawan asali da ko'a cikin ƙasar saudiyar abin
kallo ce. Ganin Hajiyar birni zata bashi matsala itama ya rufe mata baki ruf. Babu ɓata lokaci aka shiga
hidimar bikin daya bama kowa mamaki.
An ɗaura auren Asabe da Dauda, aka ɗakko amarya zuwa garin hutawa dake a jihar Ɗillo inda Dauda
ke zaune da iyalansa. Ƙyawun Asabe yasa ake layin zuwa ganinta har wasu na faɗin ɗan-azumi ya auro
aljana wadda zatai maganin sheɗancinsa. A zahiri ba aljanar bace, amma bakin mutane kam ya bisa dan
Asabe ta zame masa *BAƘAR INUWAR..* daya gwammaci aljanar ya aura. Asabe ta take Larai rashin
mutunci ta shanye. Dan ita ko kusa ko alama bata shakka ko kunyar tsige Dauda tas a bainar nasi ko
gaban ƴaƴansa balle uwarsa. Inhar zai faɗa mata cuta saita mayar masa da mutuwa koda zata kaisu da
dambe a tsakar anguwane. A haka ta samu ciki, inda ALLAH ya azurtata da haihuwar ƴaƴanta mata ƴan
biyu masu tsananin kamanni da DAUDA. dan ko kaɗan basu biyo Asabe ba sai dai ace ko na jini dole ka
gani a fisge. Ko kaɗan bata damuba, dan kuwa ƴaƴan soyayya ma take kiran ƴan biyun nata mata da
sukaci sunan Faɗima da Fatisa. Bayan haihuwar su Fatisa ko wata uku bataiba ALLAH ya sake bata wani
cikin, wanda shima ta sulluɓo ƴarta mace mai tsananin kamanni da ita a wannan karon. Dan kuwa ƴar
nan duk da jinjirace duk wanda ya kalleta sai ya sake duba. Dan ta wani fannin za'ace ta hado ƙyawune
na uwa da uba. Saboda ta ɗakko ɗan duhun fatar Dauda da hasken mahaifiyarta. Idan ka kalleta kai
tsaye zaka kirata half cast kawai. Itako taci suna *Aminatu* asalin sunan inna kenan mahaifiyar dan-
azumi. Sai dai kuma Asabe tace ana ce mata *Raudah* dan duk kishiyar data faɗar mata sunan uwar miji
a gidan ranar za'aga ƙarshen bala'i da jidali. Bayan haihuwar Rauda Asabe ta sake haihuwar mace itama
mai suna Yasmin. Itama dai kamanni biyu ta ɗakko na Asabe da Dauda. Sai dai itama baƙace sosai ba
kamar Rauda ba.
Basai an faɗa makaba, dan kuwa batun tarbiyyar babu ita ga ƴaƴan Asabe a gidan, tasu ta fita
daban data saura. (Ƴaƴanmu kan fara koyon ilimine daga ɗabi'unmu iyaye, dan haka sai mu kula dan
ALLAH kodan gaba da zasu kai girma su gallabemu). Sam ƴaƴan Asabe ƴaƴane na rashin ƙwaɓo a gidan,
duk taɓararsu babu ubanda ya isa nuna musu yatsa har a wajen Dauda. Dan har gori yakema sauran
matansa akan basu taɓa haifa masa ƙyawawan yara ba balle mai kama da shi, dan su kam ƴaƴansu
tamkar haɗin baki duk kamanninsu suka kwaso. Ko aike babu wanda ya isa aiken ƴaƴan Asabe sai ita, ita
ɗin ma sai sun gadama suke zuwa. Hakan kuma bazaisa ta nuna ta damu ba. Hatta da Raudha ma haka ta
taso a cikin nasu sai a hankali, dan itamadai halin ƴan uwan natane tsaf sai dai ma ace ta ɗarasu da
shegen miskilanci da baƙar zuciyar tsiya da jan magana, dan kullum cikin faɗa take da yara harma da
manyan. Sai dai kuma tanada ɗan sauƙin kai ta wani fannin kaɗan idan taso, ba komai ya jawo rashin jin
Raudha fin na sauran ƴaƴan Asabe ba sai gatan da Mal ɗan-azumi ke mata a gidan fiye da kowa dan tana
da sunan mahaifiyarsa.........
😉karfa ku bari ayi babu ku, dan ba'a far komai ba har yanzun😎🤙🏻.
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form din kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_*
_Irin wannan katoɓara haka🤭, inda nasa *(Bakatsinen bafulatani episode 2)* an samu mishkilane ba
haka bane. Dan babu sunan wannan jihar a ƙasar NAYA. ku ɗauka matsayin mistake Please🙏🏻😹_.
________________
*_Episode 3_*
..........Shigarsu secondary school ya ɗan fara canja wasu da ga halayen Raudha, taɗan fara rage
kwaikwayon halaye irin na mahaifiyarsu. Bata da yawan magana, bakuma tason taga iyayen nata na faɗa
tamkar karnuka a tsakar anguwa kowa na kallonsu yana ALLAH wadai. Hakan kuma ya farune sakamakon
ƙulluwar soyayya tsakaninta da malamin islamiyyarsu sayyadi Abubakar. Tun tana zama taita kuka idan
suna raba hali harta koma tana nuna musu fushinta. A lokacin da suke ss1 farkon shigarsu wani faɗa da
iyayen nata suka tafka har takaisu ga police station sakamakon yanzu Abbansu talauci ya masa katutu,
takai ma nauyin gidan iyayen nasu mata ne ke ɗauka. Dan tunda kamfani ya kamashi akan satar kayan
da yake jigila suka kafa masa kahon zuƙa, da yaga asirinsa zai tonu asabe ta zugeshi ya kwance tayoyin
motar ya saida, motar takai shekara a ajiye, sai da komai ya lafa ya saidama ƴan gwangwan ita ya kawo
kuɗin gida suka hau kai shi da Asabe da ƴaƴanta suka dinga cin daɗi sai ɗan abinda ake samma su baba
nafi wataran. Acan kamfani kuma akace ya mutu. Ko shekara kuɗin basu ƙullaba komai ya ƙare, dan
kuwa dai a ashararancin ɗan-azumi babu abinda ya canja na neman mata da busa sigari da caca. Tunda
kuɗi suka ƙare zaman lafiya tsakanin Asabe da Dauda ya ƙaura. Kullum sune faɗa kamar kaji, taje ta
nafko masa bashi dolensa ya biya ko bai ƙaunar ALLAH, idan yaƙi biya su tumu sama dan bala'i su dire
bisa ƙasa. Dan kullum zancenta shine ya saketa bata halaka rayuwarta da ƙuruciyarta a ƙarƙashin runfar
talauci. Shiko yace bata isaba tunda ta shigo ta shigo kenan. A randa taje ta cicciɓo masa wani bahagon
bashi da har akazo aka saka wani filinsa kasuwa da yake ta burin gina mata aljannar duniya ta koma tun
tana amarya ALLAH baiyiba ya sakasu yin faɗa na tashin hankali harda jima juna ciwo, shine aka
kwashesu zuwa ofishin ƴan sanda daya saka Raudha tsananin baƙin ciki. musamman akan habaici da
zagin da akema iyayen nasu akan sunyi dai-dai da juna kowa ɗan barikine ai, tunda dama a zauren dandi
suka haɗu, wama ya sani koba zaman auren suke ba.
Wannan ƙananun magana sun matuƙar ƙona ran Raudha harta kaita da kasa kuka saboda bushewar
zuciya. Kowa baije yay beilingn su ba, sai ita taje duk da ƙarancin shekarunta. Ƙyawunta da ganin
ƙarancin shekarunta yasa d.p.o ɗin sonyin amfani da mutuncinta sannan ya sakar mata iyayenta. Da
farko taso tai masa zagin ƙare dangi, sai kuma ta fasa saboda wani abu daya zo mata rai. A take ta
amince masa akan ya sakar mata iyayen bayan kwanaki biyu zata kawo masa kanta. A tunaninsa bata da
wayo, musamman da yay dubi da halin iyayenta na ƴan bariki. Kai tsaye ya sake su, tana ganin an
fiddosu tai wucewarta gida ta barsu duk da magana da suka dinga mata. Ta rigasu zuwa gidan, dan haka
kowa bai san itane taje ta fiddosu ba. Dama kuma tun a hanya suka taho suna hirarsu ta arziƙi tamkar
basune aka amso hanun hukuma ba saboda tazubar ɗinsu.
Koda suka dawo gidanma sun kaɗa sun raya Raudha taƙi tanka musu, taƙi cin abinci ta kuma daina
shiga harkar kowa a gidan. Tun suna ɗaukar al'amarin nata wasa harya fara cin ƙarfinsu, da ga ƙarshe dai
suka haɗa baki da wani malamin islamiyyar su Raudha ɗin da suke yawan jin sunansa a bakinta da ganin
tana tsananin girmamashi dan yana ɗaya daga cikin wanda suka gyara tarbiyyarta dake a bauɗe tunda
farko sannan Raudha ta sakko harta nema gafarar iyayen nata (Sayyadi Abubakar). Dan Ya sayyadi
Abubakar ya sanar mata su iyaye ba'a fushi dasu, ko wanne irin hali garesu lallaɓasu ake da ƙyaƙyƙyawan
kalami. koda anji ciwo akan kuskurensu shanyewa akeyi ayi haƙuri. Saɓawa ALLAH ne kawai ba'a yarda
kamusu biyayya akansa ba wannan haramunne.
Raudha taji wannan nasiha hartazo ta bama iyayenta haƙuri. Daga lokacin kuma ta dinga taka
tsantsan da harshenta a kansu da fushinta. Idan ma taga abu zai basu saɓani ta gwammace ta amshi
laifin ita koda zasu mata hukunci ne. Idan batasan tushen rikicin nasu ba kuma zatabi duk hanyar data
dace ta sasantasu cikin hikima. Sai dai kuma kuka ya zame mata tamkar abokin rayuwa, dan sam bata
ƙaunar halin mahaifan nata guda biyu ko kaɗan.
A yanzu haka Raudha da sauran ƴan uwanta na sauran ƴaƴan ɗakunan biyu sa'anninta suna akan
zana jarabawar gama secondary school ne. A ƙalla shekarunsu Fatisa goma sha takwas, Raudha kuwa
sha bakwai ita da Iklima da Binta. Kasancewar babu wani batun Noziri a karatun nasu yasa suka kammala
da ƙarancin shekaru, musamman ma ita dasu Binta duk sun girme mata.
Halin talauci da fataran da suke ciki ga shegen son kuɗi na Asabe ya saka ƴaƴanta su Fatisa fara
kaucewa hanya wajen biyema samari. Duk da kuɗin da yaran ke shigowa dasu na ban mamaki da kayan
kwalliya basu sana'ar ko asi bai taɓa saka Asabe nuna damuwa ba balle tuhumarsu. Sai dai ma ta baje
suci su sha mai daɗi tana kiransu masu farin jini. Tabbas *ZINA* tamkar sharri take, dan ƴar aikece
komin daren daɗewa saita dawo cikin zuri'arka. Hakanne ya faru akan su Fatisa dama wasu a ƴaƴan mal
ɗan azumi na sauran ɗakunan, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci rayuwarsu ta ɗakko hanyar lalacewa
Dauda naji na gani babu halin magana, duk da abun na ƙona masa rai da soya zuciyarsa. Dan ko yayi
magana Asabe ta taresa da masifar cewar yanama ƴaƴanta sheri saboda shima aikinsane zina. Maƙiya
masu baƙin ciki da hassada wa farin jinin ƴaƴanta na ɓoyewa bayan ƙofa suna musu dariya. Sai dai
abinda Asabe bata sani ba na ƴaƴan ɗakintane ya fito, amma itama Larai nada Kangararru irin su Fatisa
har su uku. Wani lokacin duk da gogewar ɗan-azumi a bariki, Asabe ta fisa bala'i, shiyyasa idan taja yaja
sai ya sakar mata dan zuwa yanzu girma yaɗan fara kamashi, ga ciwo dake cinsa a tsaye na hawan jini
wanda ko ba'a faɗaba asabe ce silarsa, gefe ɗaya taba ta gama cinye masa naman jiki sai ƙashi da jijiya
da fata.
Halayyar su Fatisa na matuƙar ƙona ran Raudha, sai dai babu yanda zatayi dan ko tayi nasihar basaji.
Ita kanta samarin na yawan kawoma rayuwarta hari, musamman daya kasance ta fisu ƙyau nesa ba kusa
ba. Hankalinta yakan tashi matuƙa, shiyyasa akoda yaushe cikin suturta jikinta take da kayan mutunci
harma da niƙab wani lokacin. Takan yawaita neman tsarin ALLAH daga ƙaddarar zina a gareta.
Rashin samo kuɗi da batayi yasa Asabe tsangwamarta a ɗakin fiye da kowa. Dan hatta Yasmin ta fita
daraja duk da kuwa Asaben tafi son Raudha fiye da kowa acikin ƴaƴan nata. Sai dai lallaɓa da lallashin da
take mata akan ta dinga kula samarin sai tafi su Fatisa samo kuɗi, amma Raudhan na bijirewa yasa ta
ɗauka karan tsana ta ɗaura mata ita da su Fatiman. Kullum cikin caccakarta suke da magana mara daɗi.
Da yake miskilace kuma bauɗaɗɗiya ko kulasu batayi ma balle ta nuna ta damu, fatanta kawai tai
aurenta tana gama secondary school da ya-sayyadinta Abubakar da kowa yasan suna soyayya zuwa
yanzun.
A ɓangaren sayyadi Abubakar shima babban burinsa mallakar Raudha matsayin mata. Dan haka
suna fara exam ya sanarma iyayensa akai kuɗi. Sunyi farin ciki da farko dan basusan ƴar waye ba a
Hutawa. Dan haka suka tambayesa acewar mahaifinsa sai sun fara bincike tukunna. Abubakar ya shiga
fargaba, amma sanin Raudha yarinyar ƙwaraice mai kamun kai, kuma da ita zai zauna yasashi jin ƙwarin
gwiwa.
Bayan kwana biyu mahaifinsa ya kirasa shida ƙanensa sukai masa wankin babban bargo, tare da
gargaɗinsa ya fita sabgar Raudha bata fito cikin gidan arziƙi da mutunci ba, su bazasu haɗa zuri'a da ɗan-
azumi ba. Idan ma ƙyawun yarinyar ke ɗiɓarsa yaje akwai ƙyawawa da suka fita ya nemo. Idan kuma ya
sake koda yima Raudha magana ne ALLAH ya isa basu yafe ba. Itama sunje har gida sun gargaɗi ubanta
akan ta fita hanyarsa. Daga karshe suka hanashi cigaba da koyarwa a islamiyyar su Raudha ɗin baki ɗaya.
Sukama maida rayuwarsa can cikin birinin Ɗillo wajen wani ƙanin baban nasa dake can da iyalansa.
Wannan shine sanadin raba Raudha da Sayyadi Abubakar. Tayi kuka kamar yanda shima yayi nasa.
Kusan dukansu sai da suka kwanta a asibiti dan ba karamar shakuwace a tsakaninsu ba. Halin data shiga
yasa ɗan-azumi da Asabe zuwa har gida sukaima iyayen sayyadi Abubakar tas. Wannan ya ƙara
harzukasu suka kara jin tsanar tushen Raudha da ƙyamar haɗa zuri'a da su.
Sosai wannan lalacewar aure taima Larai daɗi, dan kuwa tana ɗaya daga mutanen da suka sake lalata
zancen auren, mahaifin Sayyadi Abubakar nada ɗan hali, shiyyasa tun yana zuwa wajen Raudha takeji
baƙin ciki da hassadar hakan. Sai dai tabi duk wata hanyar rabasu hakan bai samu ba, sai gashi cikin sauƙi
komai ya lalace. Da wannan damar tai amfani wajen zuwa har gida ta sakema Asabe da ɗan-azumi
batanci fiye da wanda iyayen Sayyadi Abubakar suka jiyo ga wasu mutanen. Sai ka rantse ɗan-azumin ba
mijinta bane.
Raudha ta ɗanɗana azabar rashin Ya sayyadi Abubakar har batasan mi take rubutawa a jarabawa ba
har suka kammala. Bayan kammalawar tasu ta sake dawowa gida zaman sabuwar jiyya, a dalilin hakan
ciwon Asthma ɗinta da bai cika karfi ba ya sake ƙarfi har takai yana yawaita tashi yanzu. Gefe kuma ga
azababben ciwon mara idan zatai period har suma take wani lokacin. Dama dalilin ciwon marar natane
sayyadi Abubakar ya yanke shawarar data kammala secondary school suyi aure kawai, sai ta cigaba da
karatunta a gidansa. Sanda suna tare saboda tsabar kiyaye yanayin nata da wata ya kama zai kawo mata
magunguna da allura ta ajiye, da abin ya fara mata za'a nemo wani yaron makwafcinsu dake da kyamis
yay mata allurar. Ta hakane take samun sassauci sai abun yazo da sauƙi..
_Wannan kenan😚👌🏼._
Kiran sallar isha'i ne ya sata miƙewa da ga kwanciyar kukan da tayi, ta fito daga ɗakin baki ɗaya batare
data ko kalli inda su Fatisa ke zaune suna hira da shewa ba su da Mommynsu. Sai ma Yasmin ce data
miƙe zumbur tana ƙwala mata kira da faɗin, “Aunty R zanje”. Dan tasan massallaci zataje sallar asham.
Bata tanka mata ba, dan ƴan miskilancin na kusa ne, sai dai ta mata alamar tai alwala. Itama kuma ta
ɗauka buta ta ƙarasa inda sukeyin duk wani hidimarsu na harkar ruwa a gidan tai alwalar sannan suka
fice..........✍
*_Humm Sayyadu Abubakar Abubakar ya tafi, wa kuma zaizo? Ta ina zaizo? Yaushe zaizo AMINATU
Raudha?. Dukkan amsarku na cikin BAƘAR INUWA ne, dan bazan gaji da faɗaba ba'a fara komaiba har
yanzun masu karatu. Kar dai ku bari a baku labari._*
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form din kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_*
*_Episode 4_*
..........Ruwa kawai tasha tunda aka kai azimin na yau na kusan ashirin da ɗaya, sai dai hakan baisa ta
damu ba, duk da yunwa dake cin hanjinta dan koda asuba ma batai sahur ɗin kirki ba kasancewar tuwo
sukai na sahur, itako a rayuwarta sam bata shiri da tuwo musamman miyan kuɓewa ɗanye. Sau da
yawama idan taci gudawa yake sakata shi da shinkafa. Kai duk ma wani abu irinsu basu ciga damun
Raudha ba. Tafi so da buƙatar abinci mai ruwa-ruwa irinsu fura, kunu, koko da sauransu. Suna fita
Yasmin ta fiddo goran ruwa madaidaiciya dake ɗauke da kunu ta miƙama Raudha. “Aunty R gashi kisha”.
Cak Raudha ta dakata daga tafiyar da takeyi ta dubi Yasmin ɗin, ganin abu a leda yasata daka mata
tsawa dan sam bata fatan abinda zai lalata rayuwar Yasmin ɗin itama. Cikin ruɗewa Yasmin ta fara
rantsuwa. “Aunty R wlhy bani akayi, baba ce ta bani (Baba Nafi) sanda naje mata aika gidan kawu Rabi'u
(Ƙanin Baba Nafi) na amso mata kunun batare da Mommy ta sani ba. Niko kinga banyi azumi ba shiyyasa
na ɓoye miki shi dan karsu aunty Fatisa su gani su shanye ko Mommy”.
Ajiyar zuciya Raudha ta sauke da kamo yarinyar ta rungume a jikinta hawaye na ciko mata idanu. “I'm
so sorry my little girl, bana son ki fara koyon hali irin nasu Aunty Fatisa ne shiyyasa. Dan ALLAH ki kiyaye
karki bari wani ya yaudareki da abinda bamu da shi ya lalatamin rayuwarki kinji”.
Yasmin ta faɗa duk da ba komai take fahimta ba da ga gargaɗin ƴar uwar tata kai tsaye, saboda
ƙarancin shekarunta. Dan Raudha ta bata kusan shekara shida a duniya, bayan haihuwarta Asabe ta jima
kafin ta samu ciki, harma ta ɗauka haihuwar ta kare sai kuma ga cikin Yasmin ɗin..
Kama hanunta tai suka ƙarasa massallacin batare data amshi kunun ba, can gefe ta samu ta saka
musu abin salla inda bazasu takura ba, dan sam bata ƙaunar zafi ita, sanyi ma idan yay yawa yana taɓa
rayuwarta.
An gabatar da sallar isha'i da asham, bayan addu'oi da malam yayi tamkar yanda ya saba kowa yay
ƙoƙarin kama gabansa. Raudha bata tashi ba, sai roban kunun da Yasmin ta ajiye a gabansu ta ɗauka ta
buɗe murfin, duk da ya huce haka tasha kusan rabi ta miƙama Yasmin dake gyangyaɗin barci sauran dan
tasha itama. Amma sai Yasmin ɗin tace mata ta ƙoshi. Sanin kunu bai damu Yasmin ɗin ba sosai yasa
Raudha ƙarasa shanyewa sannan suka miƙe.
Sai da ta gama tattare musu kayansu sannan ta duƙa Yasmin tahau bayanta danta lura barci takeji.
Yarinyar ta saki sassanyar ajiyar zuciya tamkar yanda Raudhan tayi itama. Koda suka iso gidan a tsakar
gida suka iske kusan kowa a ƙofar ɗakinsa. Yaran nata hayaniyar surutu iyayen kowa na sabgar gabansa.
Sannu kawai tai musu bayan sallama ta shige ta kai Yasmin ɗin ɗakin barcinsu da gaba ɗaya ƴammatan
gidan kan kwana musamman idan ranar Babansu a ɗakin mamanka yake. Idan ɗakin wata yake daban
zaka iya kwana a ɗakin mamanka ɗin. Fitowa tai tai ɗan uzirorinta batare data tankama kowa ba ta sake
shigewa tai kwanciyarta dan su Fatisa a ƙofar gida ta barsu suna hira.
*_WASHE GARI_* Raudha ta tashi da ciwon mara mai tsanani tamkar yanda takeyi duk wata. dama tun
kusan jiya takejin alamarsa kaɗan-kaɗan, batai wani yunƙuri ba dan maganin da take sha ya ƙare. dama
Ya-sayyadi ne ke saya mata shi kasancewar yasan lalurar tata. Idan har zatai period sai kowa ya sani. ba
ƙaramar azaba take sha ba na ciwon mara dana ƙafa. Daga ƙarshe taita kwara amai. Idan ka ganta a irin
wannan halin ma saika ɗauka yaron ciki ne da ita. Dan a farkon fara hakan tana jss1 secondary kowa a
gidansu dama makaranta sun ɗauka ciki ne da ita, duk da lokacin batafi sa'ar Yasmin ƴar shekara goma
sha ɗaya ba. Sai da aka dubata likita yace period zata fara sannan hankalin malaman ya kwanta har
sukazo da ita gida akaima iyayenta bayani.
Duk murƙususun azabar da takeyi a ɗakin babu wanda ya sani, dan gidan shiru alamar yaran duk sun
fice sabgogin gabansu, manyan kuma kowa barcinsa yakeyi. Sosai take cin azaba, dan tun tana kuka ma
har kukan ya gagara, tsanani yay tsanani har takai Raudha da suma.
Kamar yanda ya saba shigowa gidan fagan-fagan babu ko sallama yauma haka ya shigo, dan tun
fitarsa sallar asuba bai sake shigowa ba yana rumfar ƴan gulma kamar yanda ake kiran majalisarsu. Jin
gidan shiru ya sashi fara ƙwala kiran Raudha, dan a rin wannan lokacin ita kaɗai zaka iya samu a gidan
tana bautar gyarawa, data gama take wucewarta wajen tafsir sai sha biyu ta dawo.
Shiru babu wanda ya amsa masa, yabi gidan da kallo a harzuƙe, ko'ina kaca-kaca da kwanika da
tulin tsummokaran kayansu kusufi-kusufi. Tsaki yaja yana nufar ƙofar ɗakin Asabe. “Asabe! Asabe!!” ya
shiga ƙwala mata kira, dan har yanzu haushinta na jiya bai bar ransaba, musamman daya kasance yanzun
nan jabiru mai shago ya sake masa maganar kuɗinsa, shine ma dalilin shigowa gidan da yay.
Cikin barci Asabe taji muryarsa bisa kai, ta miƙe a zabure tana yaye labulen daya saya falon nata
matsakaici, komai babu a cikinsa sai ledar ƙasa dan duk ta siyar sun cinye kuɗin a ciki ita da ƴaƴan.
“Wai wane kalar jidaline kuma haka da wannan farar safiyar? bazaka barni nai barcin dana gagarayi
ba da asubahi!”.
Tsaki yaja yana turo kai cikin falon, yaci tuntuɓe da ƙafar Fatisa dake barci a gefenta itama, da sauri
Asabe ta tarosa. “Gashi nan wajen gargajigarka ta masifa zakaima kanka lahani a banza, wai nikam mike
faruwa ne?”.
Numfashi yaja da ƙarfi, batare daya amsa mata ba ya kai zaune a tsakar falon yana godema ALLAH a
zuciyarsa da bai faɗi ba. “Asabe ina Raudha!?”.
“Raudha kuma? Wani laifin ta ƙara maka ne?”.
Kansa ya jinjina mata cikin tausasa murya tamkar bashine ya shigo da bala'i ba yace, “Laifi kam tana
da shi a gareni kema kin sani, to amma abinda ya fara kaɗoni gida yasani yafe mata zan ma biya jafarun
kuɗinsa insha ALLAH. Ina Alhaji Maude Dallatu uban gidan falalu mai shagon kayan ƙwalam ɗin can na
bakin titi?”.
“Eh na gane!”.
Asabe ta faɗa da sauri cikin ƙaguwar son jin inda zancen ya nufa. Fahimtar hakan ce ta sakashi cigaba da
faɗin, “Wai shine fa ya aiko Falalu ɗin akan ya sameni ya faɗamin zaizo akan Raudha wajena.....”
“Ni bangane ina zancenka ya dosa ba wlhy ɗan-azumi, fito fili ka faɗamin kasan bana son wani
kwana-kwana.”
Baki ya washe sosai cikin raɗa yace, “Inagafa cazai na bashi aurenta, idan ko haka ta kasance Asabe ai
mun haye wlhy. Shiyyasa a koda yaushe bana gajiya da alfahari da ƴaƴanki ƙyawawa”.
Itama tuni fara'a ta baibaye fuskarta, nan fa suka shiga ƙus-ƙus akan batun wai kada magauta su
jiyosu. Tun ma kan suji ta bakin Alhajin harsun gama yanke hukuncin tsaida ranar biki. Bisaga wannan
shawara da suka tsaida cike da zumuɗi Asabe ta miƙe kiran Raudha.
Da sauri Larai dake laɓe tanajin komai ta afka ɗakinta har tana neman faɗuwa. Asabe kuwa da bata
lura da itaba ta nufi ɗakin su Raudha.
Kururuwar ihun Asabe ne ya saka kowa fitowa a gidan har masu barci da Larai daketa faman kai kawo
a ɗakinta ranta a dugunzume da zancen da taji.
Suna ƙoƙarin jin dalilin ihun nata suka hango Raudha a sanƙame tana girgizawa. A tsorace duk suka
afka ɗakin, Baba Nafi tai dabarar ɗakko ruwa ta shafama Raudha ɗin. Sai gashi ta kawo wani nannauyan
numfashi. Sai kuma ta ƙudundune jikinta tana ƙanƙame Asabe da sakin wani kuka maiban tausayi dako
sautinsa baya fita saboda azabar da taci.
Kawai take iya furtawa da ƙyar tana sake ƙanƙame Asabe da itama tarasa ina zata saka kanta taji sanyi,
dan sun fahimci ciwonta na marane ya motsa. Fatisa ce ta bada shawaran a kaita asibiti ko za'a iske
Doctor Rufa'i abokin ya-sayyadi da wani lokacin shike kawoma Raudha magungunan da ga ya sayyadi
Abubakar. Amma sai ɗan-azumi ya daka mata tsawa da faɗin, “A gidan ubanwa wani keda kuɗin asibiti
anan gidan?, banda jangwaloma mutane masifa a samu ɗan libiya a jiƙa a bata tasha zai faɗa mata
yanzun nan, sanin kanku ne maganin da yaron can ke saya mata Sule yasha faɗa mana tsadarsa ai.
Sannan ba ko'ina ake iya samunsa ba ma a garin nan. Shima yana sayo mata ne a Ɗillo”.
Fatima tai saurin cewa “Abba bafa ciwon ciki bane ba, kuma kasan kaima sai an bata maganin nan ko
allura kawai take samun nutsuwa. Sai kuma last time da Doctor Rufa'in yay mata kalar sabuwar alluran
nan shima da wuri ya daina mata”.
Zai fara hayayyaƙo mata itama tai saurin katsesa da faɗin, “Abba ni akaita ina da kuɗi”.
Jin haka yasa Mommy (Asabe) haɗiye maganar da take tattarowa domin fara zuba masa tujara.
Amma duk da haka bawai ta barsa bane, zata dai jira taga lafiyar yarinyarta ta samu sannan ta cashe
masa...........
_😂Asabe ya Asabe, ɗan-azumi ya ɗan azumi. Wannan tujara da ƙauna sai ALLAH😆😹_.
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_*
________________
*_Episode 5_*
..........Bada son ran ɗan-azumi ba aka kwashi Raudha zuwa asibiti. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso, inda
aka amshi Raudha dake a jigace har batasan inama kanta yake ba zuwa yanzun. Ko sisi Fatima bata da
shi, tayi ƙarya ne kawai dan Abbansu ya bari a kawo Raudha asibiti. Tana ganin an amshi Raudha ɗin ta
fito ta nufi ofishin Doctor Rufa'i, sai dai anyi rashin sa'a wai baya nan yamaje Ɗillo tun jiya. Dawowa tai
inda Mommy da Abban ke tsaye a ƙofar ɗakin da aka shiga da Raudha ɗin. Zama tai itama tabi ayarin
ƴan tagumi, a haka har doctor ɗin ya fito yana mai kwantar musu da hankali akan karsu damu komai zai
dai-daita, dan zai rubuta musu wasu allurai da zasu sayo, da zaran anma Raudha ɗin inssa ALLAH zata
samu nutsuwa. Cikin gamsuwa da rashin damuwa aljihunsa zaiyi tsuwwa ya miƙe yabi doctor ɗin, har
yaje ya dawo mommy da Fatisa da Fatima bakinsu bai saɓa ba. Sai da ya dawo da takardar ya mikama
Fatisa ɗinne ta ce, “Abba ya zaka bani kuma? Ba cayay a sayo ba?”.
Wani shegen kallo ya watsa mata ita da Fatima fuska a ƙwaɓe. “Kunci bu*a'ubaku, ƴan bu*a'uban
yara da basa ko ganin mutuncina. Ni kikema magana haka kamar kina a gaban tsohon kwarto”.
Fuska Fatisa ta ƙwaɓe tana ƙunƙuni, zai sake magana Asabe ta katsesu.
“Wai nikam maganin zaku sayo a cetomin yarinya ko tazubar ɗinne ya motsa muku a bainar nasi?.
Kai kullum bazaka ja girmanka ga yaran nan ba balle tauna harshenka da baiko da linzami wajen sakin
magana”.
“Kar yayi linzamin mana. Banda shegantaka irin tata ba itace tace tanada kuɗi ba shine zata wani
tsareni da idanu na rashin ta'ido. ai sai da nace ku bata ɗan libiya amma tace tanada kuɗi ko......”
“Mommy nifa wlhy banda ko sisi anan. Nace inada sune danya yarda akawota asibiti. Dan haka sai yaje
ya nemo inma baida su, dansu dai likitocin nan bawai batun lamuni suka sani b.....”
Hannu yakai zai kwaɗa mata mari ta tashi ta fita a guje Fatima na take mata baya. Babu ko kunya ya
rufa musu baya shima duk da kuwa tsufa ta fara kamashi, ga sigari duk ta gama cinyesa a tsayee....
Cak yaja ya tsaya yana huci saboda jin an ambaci sunansa. Sai kuma duk ya diririce ganin Falalu mai
shago tare da Alhaji Maude Dallatu, ya ɗan tura hularsa baya yana ƙaƙaro murmushi. “A'a Falalu kune
anan? Ince dai lafiya ko?”.
Cewar Alhaji Maude duk da kuwa zai iya girmar ɗan-azumin ko suyi sa'anni.
Fuska ya marairaice kamar zaiyi kuka, saboda hangen damar dake garesa ta ƙarshe da mafita
kenan. “Alhaji wlhy Raudha ce babu lafiya muka kawo asibiti. Shine waccan ja'irar na bata ta sayo
magani take shirin min ƙyuya irin nasu na yaran zamani”.
Fatisa tai saurin waro ido waje suna kallon juna ita da Fatima da gumtse bakunan su jin dariya nason
kufce musu.
Alhaji Maude ya sake faɗa a ladabce yana miƙa hannu ya amshi takardar hannun Abban. Kamar bazai
bashi ba dai yana ɗan nannoƙewa sai kuma ya miƙa masa. Koda Alhaji Maude ya amsa bai wani tsaya
dubawa ba ya kalli Falalu dake ɗauke da kaya niƙi-niƙi alamar duba wani mara lafiyan sukazo ko
makamancin hakan. “Falalu ƙarasa ciki ina zuwa”.
“To ranka ya daɗe, amma daka kawo ni sai naje zai fi”.
“Baba ka jirani nan kaima ina zuwa”. Alhaji Maude ya sake faɗa yana tafiya da kallon mal. Ɗan-
azumi. Kafinma yace masa wani abu har yayi nisa. Hannu ɗan-azumi ya ɗaga sama yana godema ALLAH
daya kawo masa Alhaji Maude a lokacin daya dace, sai dai a ransa kuma ya ƙudira dolene kuɗin da duk
zai biya na maganin sai Fatisa tayi kashinsu. Yana nan tsaye ko mintuna goma ba'aiba sai ga Alhaji ya
dawo, da taimakon sa sukaje inda aka kwantar da Raudha ɗin. Babu ɓata lokaci doctor ya amsa dan
dama su kawai yake jira.
Alhaji Maude na nane da su har kusan awa uku, dan sai da Raudha ta farfaɗo ta koma normal barci
da allurar ta sakata sannan yace musu zaije ya dawo zuwa anjima. Godiya suka dinga masa kamar zasu
gurfana ƙasa. Yana juya baya Asabe ta warce kuɗin daya mikama Baba tana faɗin. “Ɗan cin rabo, kaci
naka zaka hau kan haƙƙina”.
Hannu yakai zai damƙota a fusace. “A gidan wane shege akace rabonki ne? Asabe anya zakiga
ANNABI kuwa?”.
“Ai tare da kai zamu gagara ganinsa kwantar da hankalinka jemage maƙi jinin ƙasa sai samaniya..”
Cikin takaicinsu Fatisa tace, “Asibitine fa Mommy. Yanzu dan ALLAH idan ya dawo ya jiku kuma fa?
Mudai wlhy kuna zubar mana da mutuncinmu”.
Baki Asabe ta ƙyaɓe. Batare data tanka ba ta zari dubu biyu ta miƙawa baba ta saƙe sauran a zane.
Ƙin amsa yayi, sai dubanta da yakeyi cikin takaici da ɓacin rai. “Mikike nufi?”.
“Babu abinda nake Nufi sai haƙƙinka dana baka gashi nan. Tunda ALLAH kaɗai yasan abinda kaci
kaima”.
Wata dariyar takaici da tafi kuka ciwo yayi ya ɗauke kansa. “Asabe kina wasa da lamarina wlhy. Ince
dai nine silar haɗa auren ko? To wabilahillazi zan iya rusashi a gabanki kuma na bashi wata sai dai ki
hangi arziƙin”.
Duk da taji tsoron zancen nasa dan tasan zai iya sai ta balla masa harara. Zatai magana likita daya
ƙaraso ya katseta. “Baba zaku iya tafiya da ita babu damuwa”.
Gaba ɗayansu suka juya gareshi, kafinma suce wani abu Fatima da bata tanka musu ba tunda suka
fara ta afka ɗakin da Raudhan take Fatisa biye da ita. Asabe ma ɗakin ta juya da niyyar shiga mal. Ɗan-
azumi ya samu damar warce kuɗin data saƙe a cikin zani. A wani irin muguwar zabura ta juyo, sai dai
kamar walƙiya ya ɓacema idanunta. Ranta yayi ƙololuwar ɓacin da har ma ta kasa bin bayansa balle yin
magana har Fatisa da Fatima suka fito riƙe da Raudha. Yini guda harta sake ramewa, sai idanu zuru-zuru
ga allurar da akai mata yasa barcin bai gama sakinta ba.
Raudha ta faɗa a hankali idonta akan Asabe. Ƙwafa Asaben tayi tana magana cikin ɓacin rai, “Minene
kuwa zai dameni idan ba ubanku ba, wanda ƙaddarar rabonku ta zama silar haɗuwata da shi. Wlhy a
wannan gaɓar kuwa lallai zan shayar da Dauda zumar mamaki. Yanda yake jinsa tantiri nima tantiriyarce
ta gaske, kuma zan tabbatar masa da hakan yau basai gobe ba”.
Dariya Fatima ta ɗanyi dan ita ko'a jikinta. Raudha kam hawayen da suka ciko mata idanu ne suka
silalo a hankali. Hannu ta kai ta share da ɗan cije baki saboda kanta dake sara mata.
A haka suka hau mashin ko sisi babu a jikinsu. Sai da sukazo gida Asabe ta shiga ta kawoma mai
napep ɗin masifa fal ranta..
Har aka sha ruwa Malam ɗan-azumi bai yarda ya dawo gidansa ba, dan yasan halin Asabe sarai. Ya
tabbatar yau duk da azumin dake a bakunansu sai sun tara ƴan kallo a cikin anguwa, shi kuma baya
buƙatar hakan tunda yasan shine mara gaskiya, shiyyasa ya zaɓi ƙin dawowa gidan har aka sha ruwa.
Yadai samu gasashen naman kazarsa da fura mai sanyi yaci yay ƙat. Ya kuma ɗora da indomie da ƙwai da
shayi wajen Bello mai shayi. Sannan ya ɗan zuƙa sigarinsa kara uku.
Sai wajen sha ɗaya na dare ya lallaɓo a tunaninsa kowa yayi barci. Sai dai yayi rashin sa'ar cin karo da
Asabe dake zaune dakaka tana zaman jiran shigowar tasa. Yanako shigowa tai caraf da rigarsa taci
kwalarsa. Tun sunayi iya su har kowa na gidan ya farka. Dama Larai na laɓe tana kallon komai tun farko
tana kwasar dariya, tunda taga Asabe zaune taƙi shigewa tasan akwai wata a ƙasa dama, balle itama
akwai tsiyar data harbo, dan tun maganar da taji a ɗazun game da Alhaji Maude Dallatu mai son Raudha
hankalinta bai kwanta ba, suna fita a gidan itama ta fice.
Rigimace sosai ta harƙume a tsakaninsu harda doke-doke. Dan sai da maƙwafta suka shigo aka
rabasu da ƙyar. Kuka sosai Raudha keyi tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta. Dan ko leƙe bata leƙo
ba dama tunda aka fara faɗan tana ɗaki kwance.
Abu kamar wasa har gabannin asuba wannan faɗa yaƙi rabuwa. Mutane har sun gaji sun koma
gidajensu sun barsu. Ƴan gidan kam har yara sun farka dan kowa ya gagara barci. Duk suna a tsakar gida,
Raudha ce kawai batako leƙo ba tana lafe a ɗaki tana faman dirzar kuka. Ko sahur ɗin kirki ranar babu
wanda yayi a gidan. Kiran sallar asuba yasa Baba Nafi fara roƙona malam Dauda akan ya fita massallaci
shi dan ALLAH ko hakan zai kawo masalaha. Shawararta yasa shi fitar yana faman huci, duk da ba yaune
karon farko da suke irin wannan faɗan ba, sai yakejin zafin Asabe a yau fiye da koyaushe. Ji yake tamkar
ya saketa ya hutama ransa.
Koda aka idar da salla maimakon yaƙi dawowa gidan sai shaiɗan ya dinga tunzurasa akan ya shigo
yaga ƙarshen haukan Asaben. Yaran kawai ya samu suna kiciniyar alwala a tsakar gida. Dan Baba Nafi da
su Fatisa sun lallaɓa Asabe da ƙyar ta shiga ɗaki itama bayan tayi alwala. Tana ɗaki zaune tana rusar kuka
ya dawo, dan ko sallar ma haka tayita tana kuka. Wani irin ɗaci da zafin Malam Dauda takeji yau fiye da
ko yaushe a rayuwarta.
“Haba Malam mi kuma ya dawo da kai gidan nan a yanzu?”. Baba Nafi dake tattare kayan wanke-
wanke ta faɗa lokacin da malam Ɗan-azumi ke shigowa gidan zuciyarsa tamkar zata kama da wuta.
Zuciyar tasa dama a kusa take, dan haka cikin masifa yace, “Na dawone dan naga ƙarshen isakancin
Asabe yau a gidan nan!!”..
“Kai ɗin banza daka isa kaga ƙarshen iskancina Dauda. Kaima kasan ni nafi ƙarfin kanwar lasarka, dan
ina dai-dai da wandama ya fika balle kai ɗin ƙaramin shegen bariki”.
Da wani irin rawar jiki malam Dauda ya cacimi taɓaryarsu ta daka yayi kan Asabe gadan-gadan. “Aiko
yau zan tabbatar miki da ni babban Shege ne....!”
Baba Nafi datai saurin shan gabansa ta riƙe taɓaryar da sauri. “Haba Malam waini kam mike
damunku yau haka ne? Yanzu akan ƙaramin abu dabai taka kara ya karya ba zance yaƙici yaƙi cinyewa
domin ALLAH!”.
Hankaɗe Baba Nafi yayi, cikin matuƙar sake harzuƙa ya fisgi taɓaryar yana ƙoƙarin sake nufar Asabe
da itama ta rarumo kujerarsu ƴar tsugunno ta nufosa, su Fatima suka riƙeta. Sake riƙesa Baba Nafi tayi
dan taba duk ta gama cinyesa a tsaye ba wani ƙarfin kirkine da shi ba. Cikin matuƙar sake harzuƙa yake
nuna Asabe da ɗan yatsa yana faɗin,
*_“Kije na sakeki Asabe. Na sakeki saki biyun daya rage tsakanina da ke!!_* Bana son sake ganin
fuskarki, Idan ba hakaba wlhy yau sai na kasheki a gidan nan da hannuna”.
Da sauri Larai ta shige ɗaki wani irin ɗan karen daɗi na saukar mata a rai da zuciya, har ji take tamkar
ta daka tsalle ta dire dan yau burinta ya cika. Itako babu abinda zatace da malam ɗan-kande sai godiya.
Gashi ya mata aikin da taketa kashe kuɗi tsahon shekaru a cikin ƙanƙanin lokaci. Gwatsar wayarta da
tasha ɗaurin ƙyauraye ta ɗauka ta shiga laluben ƙanwarta Haƙila danta guntsa mata wannan daddaɗan
labari haka da farar safiyar nan ta juma'a.
A tsakar gida kuwa duk yanda Baba Nafi take ƙoƙarin ƙwaɓar Malam ɗan-azumi yaƙi saurarenta sai
sake maimaita kalmar saki yake ga Asabe da gaba ɗaya jikinta yay sanyi kuma a lokaci guda. Dan yana
ambaton ya saketa duk zafinsa da takeji kuma sai taji ya kau baki ɗaya. Da wani irin sanyin jiki ta saki
kujerar hannunta jin hajijiya na neman kadata ƙasa. Riƙota su Fatisa sukayi suma jikin nasu na rawa.
Raudha dake cikin ɗaki zaune tana karatun Al-qur'ani tai saurin miƙewa tana dafe ƙirji, dan kalmar
sakin nan tajita tamkar sukar mashi a ƙahon zuciya. Tuni ta nema kukan da takeyi ta rasa. Da gudu ta fito
tsakar gidan, taje gaban Mahaifin nasu ta zube gwiwa a ƙasa tan roƙonsa akan yayi haƙuri karya saki
Mommyn su dan ALLAH. Duk hukuncin da yakejin zai mata ita yayi matashi dan ALLAH duk zafinsa zata
ɗauka.
Hankaɗeta yayi cikin rufewar ido yay waje yana cigaba da kunfar baki. Raudha ta miƙe da gudu ta bisa
tana kuka amma ko waiwayenta baiyiba.........
*_Tofa yau dai da alama auren zobe ya ɓalle? Ko asabe zata yarda tabar gidane? Duk da kuwa saki uku
ne a kanta idan aka tara da guda ɗaya na baya. Shin auren Raudha da Alhaji Maude Dallatu zai yuwu
kuwa?. To minenen ma ma'anar BAƘAR INUWAr? Suwaye BAƘAR INUWAr? Mizai biyo baya a gundarin
labarin BAƘAR INUWA? Dukan amsoshinku na cikin Littafin BAƘAR INUWA da nakeda tabbacin ya taɓo
muku inda ke muku ƙaiƙayi. Karku ɗauka a gidan su Raudha kaɗai cakwakiyar zata ƙare. Sam ba haka
bane, akwai wasu rikicin da gidajen a gaba. Sanin alaƙarsu da Littafin BAƘAR INUWA sai ka mallaki naka
ankai har ƙarshe da kai. Masoya ba'a fara komai ba, dan kuwa a paidpages ne kawai zaku san minene
gundarin labarin BAƘAR INUWA_*
_Ku kasance da ZAFAFA BIYAR domin karanta daɗaɗan labaransu guda biyar dake tafe da salo na
musamman masu ƙayatarwa_.
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
6*_Typing📲_*
*____________________*
*_____________________*
*_Huuuuuum! Idan kaji hanci a sama yayin gittawar mata ƴan ƙwalisa ko shiga gidajensu kasan maganar
ta ƙamshi ce_*
*_Ina magana ne aka kayan ƙamshi ƴan gaske ba saka iska ta hure maka ba_*
*_Ina mata ƴan ƙwalisa ma'abota so da ƙaunar ingantattun haɗin turaruka ƴan gaske? To kuzo maza ga
dama a tafin hanunku cikin sauƙi da sauƙaƙawa._*
*_Ana siyarda Turarukan Wuta na yan Maiduguri Set na amare. Ana bada sari kuma._*
*_Sannan akwai kayan gyaran jiki. Akwai zumar qiba result cikin 1 week. Turaren daki, jiki, kaya,
tsuguno, humra, colacca, turaren wanka, mopping scents, air freshener._*
*Sai kunzo🤳🏻*
*________________________*
*_Episode 6_*
...........Da ga Asabe har ƴaƴanta hankalinsu a matuƙar tashe yake. Hakama Baba Nafi, duk da Asabe
kishiyace a gareta aurota da akai a gidan ba ƙaramin alkairi ya zame musu ba ta wani ɓangaren. Dan
koba komai Asabe kansaka Malam ɗan-azumi ya sauke haƙƙoƙin su dake kansa koda baiyi niyyar hakan
ba. Dan kafin ya aurota sai ya gadama yakeyi, ya gwammaci yaje yay caca ko neman mata. Sannan duk
jarabarnan tata da wahala kaga tana faɗa da kishiya, wani lokacin Larai kanso suyi, amma Asabe sai taƙi
kulata. Mal. Dan-azumin ne dai ita da shi kamar suna kallon hanjin juna. Hatta da sauran yaran gidan duk
sun zama sukuku, musamman ma da Inna mahaifiyar malam Dauda ɗin tazo ta sake zazzaga tata masifar
ga Asabe saboda Larai taje ta sanar mata ƙarya da gaskiya, duk da kuwa ba ƙaunar laran take ba. Babu
wanda ya tanka mata sai larain, dan harda kawoma Innar ruwa saboda tsugudidi. Saida ta gama zazzage
masifarta tsaf da gorin Asabe tabar mata gidan ɗanta sannan tabar gidan, Asabe dai na ɗaki ita da
yaranta duka cikin matsananciyar damuwa. Dan har Inna tayi ta gama babu wanda ya leƙo.
Gaba ɗaya wannan yini dai anyisa a gidan cikin rashin daɗin rai ga azumi. Idan ka cire Larai dakejin
tamkar ta ciji sama dan farin ciki. Malam Dauda bai sake dawowa gidan ba sai dare bayan sallar isha'i.
Tsabar jinsa yau a sama da sigari ya shigo gidan yana busawa, wayarsa mai shegen ƙara tana raira waƙar
(marigayi Ali makaho)
Galala Baba Nafi tai tana kallonsa, dan duk iskancinsa bai taɓa shigowa gidansa yana shan sigari ba
tunma yanaji da ƙuruciya a iskancin. Amma abin mamaki sai gashi a yau cikin watan azumin ramadana, a
kwanakin goman ƙarshe da kowa ke dagewa da ibadar ALLAH, ya shigo gidansa dake cike da ƴaƴa a
wannan yanayi.
Tsakar gida ya zauna akan rijiyarsu yana kaɗa ƙafa da kai yana zuƙar sigari da ƙwala kiran sunan
Asabe tamkar zai tsaga bangon gidan. Ko tari bataiba ballantana ƴaƴanta, jin taƙi tankawar ya sakashi
fara zazzaga ruwan masifa da jaddada mata ta bar masa gidansa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu
baisan sake ganinta. Kuma ko Yasmin bai yarda ta ɗauka ba idan zata wuce, ta bar masa abarsa.
Nan ma ko tari babu wanda yayi sai Larai data fito daga ɗakinta ɗauke da tire ta jero kwanika. Dan
duk da bai bada kuɗin cefane ba, ba kuma aikinta ba yau kuɗinta ta saka tai girki iya ita da ƴaƴanta da
shi. Wani irin washe baki yayi yana gyara zama a lokacin data kai tsugunne gabansa tana dire tray ɗin.
Cikin jin daɗin sunan daya kirata da shi ta buɗe tsohuwar kular dake sama, wadda ke cike da taliya da
miyar kifi, sai kunun tsamiya a kofi da ƙosai data sayo masa a ƙaramin kwano. Albarka ya shiga kwarara
mata da gyara zama ko kunya babu da tunanin bashi yay cefanen ba. Baba Nafi kuwa dake kallonsu tuni
zuciyarta ta harba. Dan zuwa yanzu ta fara zargin Larai akan wannan fitinar dake faruwa tsakanin mijin
nasu da Asabe. Dan lallai akwai wani abu a ƙasa gaskiya.
Cikin farin ciki Malam Dauda ya kwashi girki yana kwararama Larai kirari tamkar wani jikan maroƙa.
Itako sai wangale baki take.
★★★
Washe gari sabuwar fitina ta sake tashi tsakanin Asabe da malam ɗan-azumi. Dan ya tabbatar mata
sai ta bar masa gida a yau. Kuma bazata tafi masa da yaransa ko'ina ba. Ta bashi haƙuri sosai tana kuka
amma yaƙi saurarenta, saima yi yake tamkar tana zugashi. Dan gaba ɗaya ya sake birkicewa, har
mamakinsa mutane keyi musamman yanda aka san yana bala'in son Asabe, ba kuma yaune karon farko
da suke irin wannan fitinarba a cikin anguwar, harma wadda tafi haka sunayi kuma su shirya. Ana tsaka
da hakan kuma sai ga Inna yau ma. Komai sake rincaɓewa yayi har maƙwafta da suka taru domin bashi
haƙuri akan ya maida Asabe kodan ƴaƴansa sai da ta shafesu. Dan Inna tas ta zagesu ta sake saka malam
ɗan-azumi ƙarama Asaben saki ɗaya daya saura a tsakaninsu wanda ya mantama yayisa tun shekarun
baya.
Wannan abu yayima su Fatisa zafi matuƙa. Dan haka suka shiga haɗa kayansu masu muhimmanci
dana mahaifiyarsu. Cikin ɓacin rai Fatima taje ta jawo hannun Raudha da Asabe dake gurfane suna basa
haƙuri, dan itama Asaben ta zama tamkar ba itaba yau duk masifarnan babu ita.
“Mommy dan girman ALLAH in har ba Abbanmu ne autan maza ba a duniya ki barsa kizo mu wuce
tunda kema kina da dangi ba'a bola ya tsintoki ba, dan ALLAH idan ya tashi ya auri Innar dake zugashi
ɗin...”
“K! fitsararriya!!”.
Inna ta faɗa a tsawace. Ko kallonta Fatima batayiba taja hannun Raudha da Asabe suka nufi ɗaki.
Abinda Fatiman tayi ya sake hargitse gidan, Malam Dan-azumi da kansa ya shiga har cikin ɗaki ya
fisgo Asabe ya kaita har ƙofar gida yana faɗin tabar masa gidansa, baya son ganinta ya tsaneta. Cikar da
ƙofar gidan ta sakeyi ne yasa harsu Raudha suka fito da kaya malam Dan-azumi da Inna basu lura ba.
Hakama Baba Nafi. Larai kuwa sarai ta gansu dan tana gefe tanata kwasar dariyarta.
Mota ƙarama suka fara samu da zata kaisu har jihar Bina shata, kafin wata makwafciyarsu da suke
ƙawance da Asaben taje ta kamo hannunta ta kawota har wajen motar, dan itace ta hana su Fatisa
komawa wajen gudun kar Malam Dan-azumi ya gansu ya hanasu bin Asaben. Itako bata fatan Asabe ta
tafi tabar ƴaƴanta, gara duk rintsi ta tafi da abinta kafin abun yay sauƙi, dan da gani kasan malam dauda
baya cikin hankalinsa sam. Tafiyar Asabe yasa akaɗan samu sauƙin hayaniyar. Sai mutane daketa yima
Malam Dan-azumi ɗin ALLAH wadai da koran Asaben da yayi batare da wani ƙwaƙwƙwaran laifi ba, dan
koda aka tambayesa ya rasa mi zaice tayi masa sai babbotan borin kunya yakeyi shida Inna da dama
kowa yasan batan ƙaunar Asabe dama duk surukan nata sai baba nafi kawai, ita kanta wani lokacin baba
Nafin baji da dadi take hannun innar ba. Na Larai da Asabe yafi zafi ne kawai dai dan ta kasa tanƙwara
Malam Dauda ɗinne ya sakesu dole ta haƙura. Yanzu ko data samu dama shiyyasa tai tsayuwar daka
wajen ganin ƙarshen Asaben da take kallo matsayin wani miki ga ɗan nata....
★A Bina su Asabe suka yada zango gidan yayarta Halima da take aure anan. Sai dai kuma sunyi
rashin sa'a bata nan wai tana jihar Loss kusan wata guda kenan ita da ƴaƴanta duka da mijinta. Sam
Asabe bataso haka ba. Dan bata buƙatar zuwa babban birinin ƙasar Bingo dasu Fatisa wajen Gwaggo
(Mahaifiyarsu hajiyar birni). Saboda ta tabbata idon hajiyar birni idon su Raudha to akwai matsala.
Cikin damuwa da sanyin murya Raudha ta kalli Asabe da sauran ƴan uwanta da duk suka jigata
saboda azumi, ita kanta daba azumin takeba a jigace take dan babu abinda taci tun jiya da rana sai ruwa.
Hawayen dake a idanunta ta share da faɗin, “Mommy nikam a ganina mizai hana mu wuce Bingo wajen
su Gwaggo direct mana. Babu amfanin wani raɓe-raɓe a gareki damu a yanzu. Na tabbata Gwaggo ta
canja zuwa yanzu, sannan zata amsheki hannu biyu tunda daman zamanki da Abbanmu ne bata so.”
Shiru asabe batace komaiba. Tasan maganar Raudha gaskiyane, sai dai tana fargabar zuwa dasu
Bingo su lalace kuma. Su Fatisa basa jin magana tabbas, amma rashin jinsu bai kai inda masu karatu ke
hasashe ba, sai dai ta tabbatar kusantasu da hajiyar birni a yanzu komai zai iya faruwa, saboda masifar
son kuɗinta. Suma ƴaƴanta ta ɗorasu a hanyar banza dan kawai ta samu kuɗi, balle su kuma jikoki gasu
kuma yaranta dukansu masha ALLAH, ba duk namiji zai kalla ya iya kauda kai ba......
“Mommy gaskiyafa Raudha ta faɗa wlhy, gara kawai mu tafi Bingo ɗin”.
Numfashi asaben taja mai nauyi, “Banƙi ta taku ba, sai dai nima akwai abinda nake lissafawa. Amma
kuma banida wata mafita saita tafiya Bingo ɗin a yanzu. Matsalar kawai dai itace bamu da isassun kuɗin
motar da zasu kaimu ne mu duka”.
A tare duk suka dubi Raudha datai maganar cikin mamaki. Cikin rashin damuwa da kallon da suke
matan ta zaro kuɗi a cikin zani sabbi ƙal ƴan ɗari biyu ta miƙama Asabe. “Mommy jiya mutumin nan da
yazo dubani a asibiti ya bani su. Nayi niyyar bakine dama idan munzo gida danki fara sana'a. Amma
yanzu na tabbatar insha ALLAH zasu kaimu duk inda zamuje ko?”.
Hawaye ne suka ciko idon asabe. Dan bata taɓa tunanin Raudha haka ba. Ganin yanda take musu
nuni dasu gyara yasa take tunanin sam Raudha bata ƙaunarta matsayin mahaifiya. Ashe ba haka bane
ba. “ALLAH yayi muku albarka, ya kare min ku”.
Ta faɗa gawaye na silalo mata na nadamar sakaci da tasoyi akan tarbiyyar ƴaƴanta saboda ruɗin
shaiɗan da son zuciya. Hannu Yasmin dake jikinta tasa ta share mata hawayen. “Mommy ki daina kuka,
banason naga kina kuka kamar irin na Aunty R”.
Asabe ta rungume Yasmin tana murmushi da share sauran hawayen. “Na bari auta, itama bazata
sake yin kukaba insha ALLAHU. Da ga yau zan tsaya akanku da inganta tarbiyyarku da muku addu'ar miji
nagari ba irin mahaifinku ba da ni.”
Ba Raudha da ɗabi'ar iyayensu ke damunta a rai ba, hatta su Fatisa yau duk sai jikinsu yay sanyi ƙalau.
Bayan asabe ta kira ƙawarta dake hutuwa sukai magana sai suka ɗunguma tasha duk da yamma tayi liƙis.
Basu damuba dan tafiyar daren ma sai tafi musu kwanciyar hankali. Anan tasha sukasha ruwa dayin
sallar magriba. Kafin motarsu ta tashi zuwa birnin Bingo. (Babban birnin ƙasar NAYA kenan. Dan yanzu
hajiyar birni tana nan da zama ta baro jihar loss).
★★★
Ko bayan tafiyar Asabe Malam Dan-azumi bai farga da rashin su Raudha a gidan ba har yamma. Dan
bayan lafawar komai sai zuciyarsa kuma ta sake shiga ƙuntata fiye da farko. Rasa mike masa daɗi yayi
dan haka yabi Inna data jashi zuwa can asalin gidansu na gado. Barci ya kwanta yayi sosai dan har gab da
magrib sannan ya tashi. Sai da ya fara shiga massallaci yay ramuwar sallar azhar da la'asar sannan yay
zaman jiran magrib zuciyarsa duk babu daɗi. Koda aka idar da sallar magriba yau bai zauna shan kunun
sadaka ba yayo gida fagan-fagan tamkar zai kifa ƙasa dan sauri. Da akuyar Larai dake bakin kwata ya fara
bal. ta saki wani marayan kuka daya saka duk jama'ar fitowa daga ɗakunansu.
Larai ta faɗa tana hararsa da nufar akuyarta dake kwance ta kasa tashi dan azaba. Bai tanka mataba, sai
nufar ɗakin da yara ke kwana yayi ya leƙa, duk da kuwa duk sauran yaran gidan sun fito suma. Cikin sauri
ya afka ɗakin ya hau leƙe-leƙe duk da babu wani lungu da zai iya ɓoye mutum a ciki. A zabure ya sake yo
waje, nan ma bai kula sauran yaran dake masa barka da shan ruwaba ya nufi ɗakin Asabe dake garƙame
da ƙwaɗo.
Wata muguwar ashariya ya lailayo ya dire yana duban Baba Nafi. “Ina yarana?”.
Duk da sarai tasan su Raudha yake nufi sai ta haɗe rai itama. A ɗan zafafe tace, “Gasu nan tsaitsaye
ai”.
Yanda yay maganar a tsawace ya saka kowa zabura banda Larai data laɓe baki tana hura hanci. Cikin
jin zafin yanda ya nuna damuwa da rashin ganin ƴaƴan na Asabe ta ce, “Tunda ka kori uwarsu mi zasu
zauna kuma su mana anan muma. Kaima kasan sun bita”.
Wata muguwar shaƙa ya kaima Larai ido a rufe, ya maƙureta jikin bango, “Ubanwa yace ta tafimini da
ƴaƴa kuna gani kuka barta!!?”.
Cikin fisge-fisgen azaba Larai ta turesa tana kakarin shaƙa. Kafinma wani yay magana ya nufi hanyar
fita ƙofar gida da sauri.
Kai tsaye gidan Malam Gambo amininsa ya nufa. Cikin sa'a kuwa yaci karo da shi a ƙofar gidansa. Ko
sallama babu ya zube a tabarmar da Malam Gambo yake kai yana huci.
Malam Gambo dake dubansa yana murmushin ƙeta yace, “Mutumina lafiya dai ko? Badai Asaben
bace ta sake dawowa kuma?”.
Harara ya zuba masa yana sake ƙwaɓe fuska. “Gambo gaba ɗaya shawararka ruguzani take nemanyi
ba gyarani ba. Kai kace naima Asabe saki ɗaya zakasa ta dawo gidanka da zama har sai na gama hidimar
auren Raudha da Alhaji Maude na jiƙu da kuɗi sannan na dawo da ita, amma har akaci aka tsire banma
ganka a wajen ba. Gashi daga ƙarshe tama sace su Raudhan ta wuce da su”.
M. Gambo dake gimtse dariya yay ƙoƙarin dai-daita kansa da ƙyar. Cikin nuna ɓacin ran ƙarya ya
miƙe zaune sosai. “Ya zakace banzo ba M. Dauda. Idonkane kai dai kawai ya rufe har bakaga sanda
naketa ƙoƙarin ganin na saka Inna ta huce bata sakaka yin saki ukun nan ba.....”
“Ni wannan duk bashi bane damuwata a yanzu M. Gambo. Babbar matsalata ta tafimin da yara.
Shirina duk ya zama na banza kenan?”.
“Kwantar da hankalinka bai zamaba M. Dauda. Ai mugu shine yasan makwantar mugu. Badai kasan
inda ka auro Asabe ba?”.
“Ya kake min wannan banzar tambayar. Idan ban sani ba daga sama akaimin wahayinta!”.
“ALLAH ya baka haƙuri ba haka nake nufi ba. Abinda nake nufi tunda kasan gidansu a loss mizai hana
muyi shiri muje mu amso ƴaƴanmu”.
“Kai bazai yuwuba. Mahaifiyarta da ƴan uwanta jarababbune na bugawa a filin idi. Gashi basa
ƙaunata ko kaɗan. Wannan ne yasa naje wajen malam na tsandu yay mata wani kafi da bata sake zuwa
loss ba tun Yasmin na shekara uku. Yanzu ma uwar tata tabar Loss tana birinin Bingo....”
“A lallai likafa taci gaba, Bingo? to basai mu satosu ba kawai. Ai shiyyasa na faɗa maka mugu shine
yasan makwantar mugu ai”.
Karan farko M. Dan-azumi ya saki murmushi dan gamsuwa da maganar M. Gambo. “Eh to kazo da
magana mai ƙyau kuwa. Inko hakane dole na tsara wani abu a wannan gaɓar ma kodan na samu ƴan
kuɗaɗe hanun Alhaji Maude Dallatu.”
“A wlhy ina bayanka M. Dauda. Tatsi ka more rabonka ɗan takarar ɗan-majalisa ba wasa bane. Kaga
idan ALLAH ya taimakemu akai auren nan kuma yaci ɗin nan aimu mun haye wlhy. Kakarmu ta yanke
saƙa rabajau zaka ganmu mutumina. Surukan ɗan-majalisa fa kenan, kai wlhy ƙilama ai maka Ministan
kuɗi kona man fetur ni kuma kwamishina...”
“Minister kuma? Kai fa M. Gambo wani zubin kamar haka-haka kake. Minista ba shugaban ƙasa keyi
ba?...”
“Af wlhy na shafa'a ne Dauda. Kasan maijin yunwa ko goruba aka bashi gani yake abinci ce”.
“Kai dai ka sani, ni kaga tafiyata shawararka ta faɗa. Zanje na ɓata daren yau wajen shirin yanda
komai zai tafi har tafiyarmu Bingo ɗin ma”.
“Af to babu damuwa sai na jika. Amma sai bayan salla ko? Tunda naga kwana shida sallar ta rage
kacal”.
M. Dauda ya faɗa yana barin wajen. Shaƙiyyar dariya M. Gambo ya saki yana kaiwa kishingiɗe. “M.
Dauda kenan inka san wata ai baka san wataba. Badai ni ka raba da Ladi dandi ba muna tsaka da more
duniyata. To kai gashi na rabaka da Asaben da kake ji da ita kuma zan koma ta bayan gida na aureta kai
dai kaini gidan nasu kaga ikon ALLAH. Dan ba wani dawo da yaranka zai kaini ba hhhhhh”...........✍
🤔Tofa, Larai ko M. gambo?. ALLAH dai ka tsaremu da abokai masu fiska biyu😥.
______________________
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
________________
*_Episode 7_*
...........*_BINGO CITY_*
Kasancewar tafiyar dare da sukayi a tasha suka ƙarasa kwana, sai da safe suka fito domin shiga cikin
garin Bingo. Duk da Asabe a tsorace take, hakan bai hanata tarar motar taxi suka shigaba. Kai tsaye
anguwar data san su hajiyar birni na zaune a yanzu suka nufa. Sai dai har cikin rai tana tsoron haɗuwa da
Gwaggon nata. Tana kuma tausayin ƴaƴanta akan tarbar da zasu samu ga mahaifiyar tata da sauran ƴan
uwanta. Amma sai ta danne dan kar ta tada hankalin ƴaƴan nata da sukai zugum-zugum musamman
Raudha.
Tun a farkon shigowa layin sukai tambayar gidan Hajiyan Birni (sunan da asabe tasan ake kiran
Gwaggo a ko ina). Sananniyace a anguwar kodan katafaren shagonta na abinci da duk kewayan babu
kamarsa a yanzu. Dan takai manya-manyan masu kuɗi da sanannun mutane ke zuwa wajen cin abinci da
shan giya wajenta. Ta iya abinci kala-kala na ƙawa, gashi tana tsaftacewa. Ta samu kuɗi matuƙa shiyyasa
ma ta baro geto ta dawo wannan anguwar da zama kodan customers nata ƴan ƙarya da sanannu wanda
basa buƙatar shiga kowane waje.
Basu Raudha ba, hatta da Asabe mamakin ganin ƙaton wajen kuma lafiyayye take, itadai tasan
Gwaggo bata da ƙarfin gina irin wannan wajen da sunan gidan abincinta. Kodai watace mai irin sunan
Gwaggo itama......
Yasmin ta katse ma Asabe tunaninta. Numfashi taja da ƙarfi tana ɗan waige-waige ko zataga inda Yasmin
ɗin zata tsugunna. “Kinga jeki bayan dustbin ɗin can kiyi”.
Da sauri Raudha ta ɗan girgizama Asabe kai tana riƙo hannun Yasmin dake ƙoƙarin tsillawa da gudu.
“A'a Mommy bai dace ba. Itafa mace ce, ya zata duƙa a titi yin fitsari? Mizai hana mu tambaya kodan
guje mata ɗaukan wani cutan”.
Fatisa ta ballama Raudha harara tana yamutse fuska, “Raudha bazaki bar dai iyayi ba a rayuwarki?
Miye idan tayi fitsari a can, duka shekarun Yasmin ɗin nawa a duniya da har za'a kirata mace”.
Kafin wani ya sake magana wata matashiyar budurwa sanye cikin wando baƙi da t-shirt pink alamun
Uniform ɗin wajen kenan ta fito a cikin wajen cin abincin, cikin gurɓatacciyar hausanta tana faɗin, “Kai
lafiya kuwa? Nan ba wajen tsayawa bane ba ku ƙara gaba”.
Fati zata fara magana cikin hasala Asabe ta dakatar da ita. “Yi haƙuri ƴammata ba haka nan muka
tsayaba muma, muna neman wata ne anan ɗin?”.
“Wata kuma?”
“Eh wata muke nema Hajiyar Birni. An kuma tabbatar mana tana anan wajen”.
Wani kallon banza budurwar ta sake musu sama da ƙasa. “Tabbas sunan mai wajen nan kenan. Sai
dai ku kuma sam bakuyi kala da masu alaƙa da ita ba, da har zaku nemi ganinta haka kai tsaye”.
Asabe da ƙwalla ya cikoma idanu tace, “Hakane yarinya. amma ki taimakemu ki sanar mata Asabe ce
da ga Hutawa”.
Kamar budurwarnan bazata motsaba tanata musu kallon banza. Sai kuma taja guntun tsaki. A yatsine
ta ce, “Kunga kuɗan koma daga can”.
Nan ma Fati zatai magana Asabe ta hanata. Sai da budurwar ta juya ciki Asabe ta dubesu. “Dan ALLAH
ku kwantar da hankalinku bana son wata fitina. Idan munga ba ita bace gaba zamuyi ai. Maida zance ga
kowa ba namu bane a yanzu”.
Badan hakan ya musu daɗi ba suka ɗaga mata kai alamar to.......
*★★★**★★**★★*
Kasancewar yau rana ce ta aiki kowanne ofishin gwamnati zaka samu ma'aikaci harma dana wanda
ba gwamnatin ba ma'abota ayyuka a cikinsu. Baka ganin komai sai kaiwa da komowar ma'aikata a dukan
ma'aikatu.
Sai dai a mafi yawan ma'aikatun gwamnati kamar yanda kowa ya sani ƴan siyasa ne mafi rinjaye a
cikin yankin ofisoshin da suka shafi gwamnati. Kamar dai a yankin gidan gwamnati na babban birnin
ƙasar NAYA (Bingo). Yawaitar ƴan siyasa a wajen yana da alaƙa da zaman taron meeting da shugaban
ƙasa yayi har kusan sau biyu a safiyar ta yau saboda gabatowar watannin zaɓe da muka shiga shekarar
ƙarshe na saukar duk wani mai mulki da ya ƙulla hawa biyu akan karagarsa.
A yanda alama ta nuna taron baima wasu daɗi ba. Dan lokacin tashi ma baiyiba shugaban ƙasa ya fita
a wajen taro na biyu da aka zauna da wasu manyan dattijan jam'iyyar masu faɗa aji da mafi yawansu
suka kasance masu sakawa da hanawa na wannan jam'iyya ne. Sai dai kuma bayan fitar shugaban ƙasa
daga wajen taron da kamar mintuna goma sha biyar labari ya shigo kunnensu ya sake zama na
musamman da ƙasaitaccen dattijon mai arziƙin nan kuma tsohon alƙali da kowa yakejin sunansa a ƙasar
dama wajen ƙasar, har zamu iya cewa a yanzu ya zama tamkar wani shugaba dan ko masu mulkin babu
abinda zasu layance masa na gwagwarmayar rayuwa da sanin muhimmancin talaka.
Kamar yanda basu fasa cigaba da ƙananun magana irin wadda akasan ƴan siyasa da itaba, haka ma
shugaban ƙasa bai fasa ganawar sirrinsa da *_Alhaji Hameed Harith Taura_* ba.
Kallo ɗaya zakaima ƙyaƙyƙyawar fuskar dattijo Alhaji Hameed Taura dake ɗauke da ƙasaitaccen
murmushin manya ka fahimci ɗunbin kamala da dattako tattare da shi. Yana zaune cikin luntsumemiyar
kujerar da ke a ƙayataccen katafaren falon hutawa na shugaban ƙasa mai zaman mutum uku (three
sitter). Zama ne irin na ƙasaita da dattijan taka, yana sanye cikin ɗanyar farar shadda harda malun-malun
da suka ƙawatu da aikin surfani na maƙudan kuɗi. Ƙyaƙyƙyawane, duk da tsufa na farin gashi yama
fuskar tasa shinge. Sai dai maimakon ya ɓata ta sai ya sake ƙawatata da kamala. Gefensa kaɗan
shugaban ƙasa ne zaune shima cikin tasa ƙasaitar irin ta masu mulki. ba zasu iya zama shekaru ɗaya ba,
sai dai yanayin jiki yasa Shugaban ƙasa yafi Alhaji Hameed ƙiba. Amma kuma kasantuwarsu cikin jin daɗi
ya zaftare kaso mafi yawa na tsufan nasu gamai kallo.
Shugaban ƙasa dake magana cikin tsantsar damuwa ya sake gyara zamansa fuskarsa na nuna
tsantsar damuwa da taraddadi. Cikin harshen turanci yake cigaba da faɗin, “Alhaji Hameed a wannan
gaɓar da gaske nake bana buƙatar mulkin nan yabar hannunmu, dan na tabbatar maƙiyanmu na amsa
tamkar mun bada sandunan rusa dukan tanadinmu ne a zahiri. Kai shaidane akan faɗi tashin da
mukaitayi na ganin nayi shekaru goma bisa mulkin nan kafin yau. Miyasa bazaka amsa shawarata ba na
fitowa takara kaima. Dan ni kai kaɗai idanuna ke iya hangomin zaka kawo kujerarnan a yanzun....”
Alhaji Haneed dake kallon shugaban ƙasa fuska ɗauke da murmushi na dattijantaka ya ɗan muskuta.
Shima cikin harshen turancin ya fara magana da sigar rashin muhimmancin maganar ta shugaban ƙasa
da rangwamen tasirinta a garesa. “Your Excellency badan a bakinka zancen nan ya fitoba dana kirasa da
tarin wauta ƙwarai da gaske. Karka bari daɗin mulki ya kasa barinka ka dinga hango cewar ni Abdul-
Hameed zan iya. Excellency ni sam bani da sha'awar mulki a ƙasarnan sam. Na zuri'ata da harkokin
kasuwancina ma ya isheni gayya da takura. Sanin kankane dan na huta na tattara ayyukana na damƙa a
hannun yarona tsahon shekaru goma kenan, iyakata a yanzu na taimaka masa da abinda bazan takura ba
da ga gida. Ka ajiye maganata a gefe muyi mai muhimmanci. Kaine ka tilastani shiga siyasa saboda wasu
abubuwa da muke iya hangowa zamu gyara koda bata hanyar mulki ba. Amma daka nuna sha'awar
zakayi mulkin kai sai na baka goyon baya nima saboda nasan zaka iya. Kuma Alhmdllhi kayi ɗin an yaba.
Ni yanzu inada shawara guda ɗaya zuwa biyu Excellency. Mizai hana mu duba a cikin yaran nan dake
biye da kai ƙafa da ƙafa mu ɗora mai nagarta akan hanyar da mukeso, mu tallafa masa da taimakon
UBANGIJI idan ya amince sai ya bashi mulkin tamkar yanda ya baka...”
Wani numfashi mai ƙarfi daya dakatar da Alhaji Hameed a magana Shugaban ƙasa yaja, cikin jin
ɗaci da sukar da kalaman Alhaji Hameed ke masa a zuciya, ya haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi da
ƙyar yana ƙaƙaro murmushi a saman fuskarsa. “Am sorry to say bana katseka bane ba Alhaji Hameed.
Maganarkace tazo dai-dai gaɓar dataimin daɗi matuƙa. Harma a dalilinta wani tunani ya faɗomin a rai
nima.”
Alhaji Hameed ya faɗa cike da yardar daya bama shugaban ƙasa matsayinsa na amini garesa shekaru
aru-aru.
Shugaban ƙasa dake jin tamkar ya sokama Alhaji Hameed wuƙa ya sake ƙawata fuskarsa da
murmushi. “Na yarda mu sami wani da muke ganin zai ɗora aikinsa bisa namu ɗin, sai dai a duk yaran
dake tare da ni ɗin ban hango wannan nagartar ga kowa ba sai ga ɗanmu....”
“Yes ɗanmu Alhaji Hameed. Basheer shi kaɗaine zai iya mana yanda mukeso batare da ya rusamu
ba. Zamu tallata Basheer kuma inaji a jikina zai zama mai nasara insha ALLAH”.
(Dariya) karo na farko Alhaji Hameed yay dariya mai faɗi har haƙoransa na bayyana sosai.
“Excellency baka rabo da wasa kai sam a rayuwarka. Banda ma dai iskar ac na busaka ta yaya kake
tunanin Basheer zai iya siyasa harma takaisa ga mulki?. Idan ka manta bara na tuna maka. Bazan iya
sakacin da Basheer zai ajiye harkokinmu ya dawo harkar siyasa ba, dan haka mubarma maganarnan
Please, dan nasan bashi da interest akan hakan shi kansa....”
“Kash! Banso kai wannan zancen ba sam excellency, kaima ka sani kai ɗin mai iya zartar da hukuncine
akan dukkan zuri'a ta. Sai dai kai baka hango ni abinda nake hangowa a wannan gaɓar. Dan haka ka sake
shawara badai wannan ba”.
A take ɓacin rai ya gauraye fuskar shugaban ƙasa. Dan kuwa wannan itace dama ta ƙarshe da suke
da ita akan Alhaji Hameed ɗin a wannan karon ma kamar yanda suke gani. Sun ɗauka tsahon shekaru
suna shiryama Alhaji Hameed Taura tuggu iri daban-daban, amma yana tsallakewa, sai dai a wannan
karon sun ɗauka alwashin bazasu taɓa bari damarsu ta suɓuce musu ba. Dole ne Alhaji Hameed ya
amince da buƙatarsu ko yana so ko baya so......
Miƙewar da yay cikin fushi ya saka Alhaji Hameed riƙosa da hanzari. “Wai badai fushi kayi ba?”.
Cikin pretending shugaban ƙasa ya sake tsuke fuska yana son ƙwace jikinsa. “Mizaisa raina ya ɓaci
tunda ka nunamin ban isa da jininka ba. Niko kaga komi ka zartar akan yarana ko tari bazanyiba balle ma
na nuna maka inada alaƙa da sawarka ko hanawarka a kansu”.
Murmushi Alhaji Hameed yay yana girgiza kansa. “To naji zauna muyi magana. Dan nima ba ina nufin
baka isa baneba. kawai dai akwai ƙurar da nake hangowa da tasowarta na dai-dai da guguwar da babu
abinda zai iya tareta yayinda ta keto tsakkiyar birnin Bingo dama NAYA baki ɗaya”.
“Wannan hausan naka yayi girma da yawa ban fahimci komai ba”.
“Zaka fahimta ai”. Cewar Alhaji Hameed Harith Taura yana dariya.......
★★★*****★★★
Rai ɓace dattijuwar tsohuwar ta fito sanye cikin kaya na alfarma. Leshi ne daya amsa sunansa leshi
mai tsadar gaske irin na jama'ar wannan yanki (masu hannu da shuni). Sai dai tana buɗe baki zatayi
magana idanunta suka sauka akan su Asabe dake tsaye gefe har yanzu cikin alamun gajiya da buƙatar
hutu. Turus ta ɗanyi a tsaye, sai dai fuskarta ta shanye tsoro da mamakinta. Asabe da jikinta keɗan rawa
tun fitowar mahaifiyar tata ta fara takowa a hankali zuwa gareta hawaye na ƙoƙarin cika mata ido. Batun
yanzu ba tasan mahaifiyar tasu ƴar gayu ce, sannan takowace hanya bi take domin neman kuɗi, tun
ƙuruciya burinta tara manyan kuɗi ne, sai dai kota fara tarawar sukan rushe ne. Amma a bin mamaki a
yau sai gata cikin yanayin da mai kallo kawai ya isa shaida lallai ta tara ɗin.....
Muryar Hajiyar birni ta katse tunanin Asabe da bata san ma ta iso gareta ba. A firgice ta ɗaga kai ta dubi
mahaifiyar tasu hawayen da take maƙalewa na sakko mata a guje.
Baki Hajiyar birni taɗan taɓe kamar zata juya. Da sauri Asabe ta riƙo hannunta tana sake fashewa da
kuka. Sanin halin Asabe da abinda zata iya yasa Hajiyar Birni juyowa a tsawace tace, “Sakarmin hannu.
Danni tuni nama fiddaki a cikin ƴaƴana. Na barma Dauda dandi dan na kula ya fini kima da mutunci a
idonki ai.”
“Wlhy baiko kamo yatsan ƙafarkiba Gwaggo. Na tuba nabi ALLAH na biki dan ALLAH kimin rai. Kece
komaina gwaggo, dan ALLAH ki tausayamin ni da yarana dan ke kaɗaice dolenmu sai ƴan uwana”.
Kamar hajiyar birni zata sake cewa wani abu sai kuma ta fasa saboda sanin a inda take, yanzu ko gab
ma'aikata suke da fitowa cin abinci, bata fatan abinda zai ɓata mata rai. Gaba tai tanama matashiyar
budurwar ɗazun magana da ido tai shigewarta ciki tabar Asabe nan tsugunne da su Raudha dake a tsaye
cirko-cirko ransu a dagule matuƙa, duk da sun fahimci hamshaƙiyar matar data fito Gwaggo ce
mahaifiyar Mommynsu. Dan rabonsu da ita tun suna ƙanana sosai.
★
Gida ne matsakaici mai rangwamen girma da ƙyawu budurwar nan ta kawosu. Wadda alama ta
nuna umarnin hajiyar birni tabi. Basu sami kowaba a gidan, sai dai a kallo guda zaka fahimci mazauna
cikinsa ya wuce mutum ɗaya kacal. Duk da budurwar tasan lokacin azumine hakan bai hanata ajiye musu
abincin data taho da shi ba daga restaurant ɗin. Daga haka ta juya inda ta fito.
Asabe data fahimci nanne gidan mahaifiyar tasu saita bama yaran nata umarnin tashi su fara gyara
jikinsu, musamman ma Raudha dake a yanayin buƙatar hakan matuƙa. Duk basuyi musun hakan ba, dan
dama sunada buƙata suma.
Ɗaya bayan ɗaya suka dinga wanka a toilet ɗin dake a tsakar gidan bayan Raudha ta tsaftace sa, suna
kammalawa Yasmin tai zaman cin abinci, Raudha ma ta ɗan tsakura tasha magani ta kwanta. Ganin
Asabe ma ta kwanta Fatisa da Fatima suka faki idanunta sukacinye sauran abincin da Yasmin ta rage. A
taƙaice dai suka karya azumin dake a bakunansu. Suma kwanciyar sukai suna sauke ajiyar zuciyoyi najin
nutsuwar abincin da sukaci.....
*_____________________________*
*_FRIDAY EVERNING_*
DAREN juma'ar data kasance dai-dai da kwanaki biyar na wanzuwar wasu al'amura a ɓangarori
biyar. Ya kumayi dai-dai da jajibirin sallar ƙarama da kowa ke saka ran kasantuwar ta lahadi insha ALLAH.
*_ANGUWAR SOBIA_*, Anguwace da ke ɗauke da manyan gidaje na alfarma. Basai an tsaya dogon
bayani ba a kallo ɗaya ta isa mai buƙatar amsa cewar mazauna cikinta sun tara kodan hasken daya
gaurayeta tako ina da keda banbanci da rana kaɗan. A wannan anguwa gida mai lamba goma sha huɗu
shine mallakin dattijo Alhaji Hameed Harith Taura da zuri'arsa baki ɗaya. Katafaren gidane daya mallaki
komai najin daɗin duniya. Ɓangarorin da suka kasance daban-daban a cikinsa ke nuni da ba Alhaji
Hameed bane kaɗai ke rayuwa a cikinsa. Yana tare ne da dukkan zuri'arsa.
Kamar yanda anguwar ke ƙawace da hasken lantarki, hakama cikin gidan yake tarwai da hasken da
kake iya ganin shigi da fici na mutane ta kowanne sashe. Sai dai a kallo guda zaka fahimci masu yawan
kaiwa da komowar ma'aikatan gidanne ba masu gidan ba ko ƴaƴan gidan.........✍
________________________
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
*_Typing📲_*
*_Episode 8_*
............“Nikam dai nake ga kamar anzo gaɓar daya kamata ace nasan minene damuwarka?”.
Dattijuwar tsohuwa fara ƙal ta faɗa tana duban dattijon dake kishingiɗe a gefenta yana buɗe
kwanikan data ajiye masa masu ɗauke da tuƙaƙƙen tuwo dawa daketa tashin ƙamshin kanwa. Duk da jin
daɗi dake tattare da yanayinsu hakan bai hana bayyanar tsufanta ba ƙarara, sai dai jikinta nada ƙwarinsa
musamman daya haɗa da cikar kamala da nutsuwar dake tattare da ita. A fuska kawai zaka fahimci ita
ɗin bamai yawan wasa bace sam. Sai dai hakan bai hana kwarjininta bayyana akan fuskar ba.
Yanda ta tsatstsare sa da idanunta masu girma da haske duk da tsufan dake tattare da zagayen
fatarsune ya saka Alhaji Hameed sakin murmushi yana tashi zaune sosai.
“Nifa kibar hukuntani da idanun nan naki Jannatu, tunda ko kwanikan nan da kika ajiye shaidane
banyi wani laifi ba”.
Murmushi ta saki a karon farko tana girgiza kanta mai cike da furfurar gashi dake shan gyara. Ta gyara
zamanta tana gyara kwanikan tuwon data zuba masa a gabansa. “Nima ba hukuntaka nakeba Dattijo.
Kawai dai idaniyatace ta gaji matuƙa da ganin yanda kullum tunaninka keyin nisa da ni. Tun randa kukai
zama da shugaban ƙasa na fahimci ka kasa sukuni. Daka zauna ko wani ya gusa a jikinka zakai nisa da
duniyar mutane zuwa wata daban. Idan har ban shiga hurumin daba nawaba mizai hana na sani ko inada
abin cewa dazai kawo mafita dattijo”.
Komai baiceba. Sai dai yayi murmushi mai sanyi da cigaba da cin abincinsa da yakeji a duk duniya
babu abinda ya kaisa daɗi da nutsuwa a garesa. Itama ɗin bata sake cewa koman ba, dan ta fahimci
ma'ana da dalilin shirun nasa. Sai ma ta maida hankalinta ga television ɗin dake manne a ƙayataccen
bangon falon nasu kawai.
Alhaji Hameed ya faɗa dai-dai yana ture kwanikan abincin nasa alamar ya kammala. Hakan kuma
yayi dai-dai da juyowar matar tasa garesa tana gyaɗa masa kanta. “Babu wanda ya shigo, kasan yau
jajibirin salla, mafi yawansu suna can wajen gyaran jikin kwalliyar salla. Garama ja'irarnan Bilkisa data
shigo ɗazun da hantsi tacemin can zataje sallar juma'a wajen uwarta Asma'u”.
Kansa kawai ya jinjina mata tare da ɗaukar ruwa yasha. Sai da ya ajiye kofin dayin hamdala ga
UBANGIJI kafin ya gyara zamansa sosai da sake nutsuwa fiye da farko.
“Jannatu tabbas akwai abinda ke damuna, sai dai na barsane a iya ni da tunanin zan samo mafita mai
ɓullewa kafin ki sani k da Basheer. Kamar yanda kikayi tunani damuwata nada alaƙa da zuwa ofishin
shugaban ƙasa.” yaja numfashi, batare da ya bata damar cewa wani abuba ya cigaba da faɗin, “Ya buƙaci
na fito takarar shugabancin ƙasar NAYA saboda rikicin da aketa tafkawa akan wanda zasubama takarar a
wannan jam'iyyar. Dan kusan mutane biyar ne suka nuna sha'awar hakan, sannan dukansu sun cancanta
a fuskar gudunmawar da suka bama jam'iyya da shi Excellency ɗin. Kai kawon daketa wanzuwa ya
sakashi ganin duk su huta shi ya ɗora wanda yaga ya cancanci ɗorawa daga ayyukansa. Shine bai tunkari
kowaba sai ni”.
(Murmushi) ta saki murmushi mai faɗi tana sake fuskantarsa. “UHMM!! That's a salient point Dattijo.
Sai dai kai wace amsa ka bashi?”.
“Ban san dalilinki na jingina tatsuniyar tasa da muhimmiya ba. Sai dai na yarda dake wajen warware
matsaloli cikin sauƙi. Amsar dana basa ɗayace wadda nasan kema zakiyi tunanin hakan, shine ba
zanyiba, banga dalilin dazai sakani yin mulki a wannan shekarun nawa ba na tsufa. Kai ni bamma taɓa
sha'awar hakanba shima ya sani. Siyasar kanta ma sai da kukayi yaƙi sosai kafin na shiga domin bada
shawarwari badan tana cikin tsarina ba. Sai dai bijirewata baisa ya ƙyaleniba. Ya kawo dalilai masu yawa
da yake ganin Basheer ya cancanta....”
“Shima bai cancanta ba”.
“Miyasa kikace haka Jannatu?”. Ya tambaya cikin mamaki da taraddadi. “Dalilai masu yawa
dattijo. Sai dai ba kowa zai iya kallonsu a dalilan ba, amma nasan kaima zaka fahimci wasu a hakan”.
“A dalilin fahimtar wasunne ma yasa kai tsaye nace shima ɗin bazaiyiba Jannatu. Tayaya ma
excellency ke tunanin zanbarma duniya Basheer alhalin shine kawai inuwar hutuna a yanzun. Shine kaɗai
ɗan da muka haifa, a kuma wannan gaɓar dukkan wani kaiwa da komowa na abinda ALLAH ya azurtamu
da shi a hannunsa yake, hasalima bana tunanin yanada interest akan mulki shima”.
“Wannan gaskiyane dattijo. Naji daɗi da tunaninmu yazo iri ɗaya. Duk da dai ni da kai akwai
banbancin hange a tafiyar. Rashin cancantar Babangida ko kai a siyasa bashike nufin zamuƙi amsar
wannan damar ba da ALLAH ya matso da ita a tafin hannunmu, domin taimakon talakawa da ƙasarmu ta
NAYA.”
“Ban gane mikike nufi ba? Mizai amfanar damu a cikin amsa bayan munsan babu mai riƙewa to?”.
“Akwai!”.
“Akwai?! To wa kenan?”.
*_RAMADHAN!”_*
A take dukkan Murmushin da ke shimfiɗe a saman fuskarsa ya ɓace ɓat. Wani abu mai kama da fushi da
ɗaci ya bayyana. Kansa ya kauda gefe tamkar bazaice komai ba, dan ita kanta ma harta fidda rai da ga jin
wani abun a bakinsa.
★★★__________★★★
A lissafi yau kwankinsu biyar kenan cif da shigowa cikin birnin na Bingo, inda a cikin kwanaki biyar
ɗin nan Asabe tasha matuƙar fama wajen neman yafiyar mahaifiyarta data turje cewar bazata riƙe su
Raudha ɗin ba. A cewarta ita kaɗai ta haifa, ita kaɗaice dolenta da idan Dauda ya koro zata amsa. Amma
ƴaƴansa su shirya ta basu kuɗin mota su koma gidan ubansu suma.
Hankalin Asabe yayi matuƙar tashi harma dasu Fatisa, dan haka suka dage wajen roƙo da taya
Mommynsu magiyar ganin an barsu sun rayu a kusa da ita. Sai dai ga Raudha sam abin ba haka yakeba.
Dan gaba ɗaya zubin kakar tasu da ɗabi'unta basu mataba, domin tun ba'ai nisa ba ta auna ta ɗora
abubuwa da yawa na kakar tasu a mizani da ya cire mata sha'awar rayuwa anan ɗin. Duk lalacewa gara
gidan mahaifinta, tunda dai acan babu mai takura maka akan tilas sai kabi wata hanya mara tushe.
Abinda ya ƙara tada hankalin Raudha da zama cikin ƴan uwan mahaifiyar tata shine....
*Halayensu*, dan a kallo ɗaya idan kai musu da wahala ka ɗorasu a mizanin mutanen kirki kai tsaye.
Kamar yanda kukaji tun a farkon labarin su Asabe su huɗu ne a wajen hajiyar birni, Asabe kuma itace
auta, sannan itace ta fara bijirewa wajen ganin tayi aure. Sai dai bayan auren nata yayarta da suke uba
ɗaya wadda itace ta uku a gidan itama ta sake ɓallewa tai aurenta a birnin Bina. Yayinda hajiyar birni ta
cigaba da zama da sauran ƴaƴan nata biyu suna neman arziƙi ta kowacce irin hanya.
Sai dai kuma bayan shuɗawar wasu shekaru da adadinsu bai wuce uku zuwa huɗu ba itama babbar
yayarsu tai aure anan cikin Loss ɗin. Amma kuma sai aka samu matsala auren bai wani yi ƙarko ba ya
mutu sakamakon mijin data aura baisan haihuwa. Ta fito da ciki inda ta haifi ƴan biyu, suka kuma cigaba
da zama anan wajenta, dan duk bushewar zuciya irin na hajiyar birni bata amince ƴaƴanta suyi nesa da
itaba. Duk inda zaka kaje da rana ka dawo ka kwana a gida. Koda babbar yayar su Asabe ta yaye yaran
nata sai ta sake wani auren duk da hajiyar birni bata so. A wannan karon tayi auren ne a jihar Dokato,
inda shima auren bai kai ko'ina ba ya ƙare sakamakon jarababbiyar kishiya data samu. Nan ma ta fito da
yaro, duk da shi sai da akai kicimilli kafin ubansa yabar mata akan tilas. Bayan fitowar tata kuma
ƙanwarta mai bi mata itama ta auri wani ɗan siyasa mai faɗa aji anan Loss (Aunty Hannah), sai dai a nan
Bingo suka zauna.
Itakam ta zauna harda yarinyarta guda data haifa da shi, sai dai sheka guda kenan auren ya mutu ta
dawo gida da zama itama, ta kuma faɗa harkar siyasa dalilin sanin manyan mutane da tayi tun tana
gidan tsohon mijinta ya taimakama nasarorinta ƙwarai da gaske. Dan a yanzu haka tana kusa sosai da
matar shugaban kasa harma da shi shugaban kasa ɗin kansa, duk da dai bata fito da hakan a fili ga
mutane saboda tsohon mijinta. A taƙaice dai a yanzu haka hajiyar birni duk tana tare ne da yaran nata da
jikoki huɗu a wannan gida. Sai kuma ƴarta ta uku dake aure a Bina itama da yaranta uku. Sai Asabe mai
yara huɗu, kuma sune za'a kira kamar manya a jikokin na hajiyar birni duk da uwarsuce ƙarama.
Bayan magiya da roƙo da aka dinga mata tare da yayun Asabe biyu da suka kasa zaman aure suma sai
ta amince. Sai dai ta amince ne da sharaɗin zasu tashi su nema na kansu dan bazata iya ciyar dasu har su
huɗu ba. Kai tsaye Asabe ta amince bisa shawarar yayun nata da suka kwaɗaita mata wani abu daban ba
wanda zuciyarta take ƙyamata ba a yanzun.
To ayanzu dai haka gasu a zaune bisa sharaɗin neman nakan nasu, wanda a dalilinsa hajiyar birni tace
su Raudha su shirya bayan salla zasu fara mata aiki a restaurant ɗinta. Dan zasu iya samun wasu ayyukan
a dalilin zamansu wajen, tunda masu hannu da shuni ne ke dabdala akoda yaushe.
Kamar koda yaushe tunda suka zo garin yau ma ta buga uban tagumi bayan kammala aikin gidan da
a yanzu ya zame musu tamkar wajibi ita da sauran ƴan uwanta. Sai dai halinsu na rashin son moriya kesa
duka aikin ya dawo kanta sai abinda Yasmin taɗan iya tsakura a ciki ta rage mata. Duk da azumi ne haka
take dagewa ta gyara komai tsaf, hakan ya saka gidan canjawa cikin ƙanƙanin lokaci, da'alama dama
rashin zama a gyarashine ya sashi canja kamanni......
“Raudha!”.
Asabe ta kirayi sunanta da ɗan ƙarfi a karo na biyu. Firgigit ta juyo ta kalleta dan sam bataji na farko ba.
Hannu Asabe ta shiga tafawa na taraddadi tana salati. “Oh ni Asabe Raudha wai mi kike son maida
kanki ne? Duka shekarunki nawa da zaki jefa kanki cikin masifar tunane-tunane mike damunki?”.
“Mommy babu komai fa, kawai na zaunane naɗan huta Yasmin ta fito wanka nima na shiga”.
“Ƙarya kike Raudha, ki faɗamin gaskiyar abinda ke damunki tun kafin mu saɓa.”
Ajiyar zuciya Raudha taja da ɗan ƙarfi tana haɗiye ƙwallar data cika mata ido. Cikin yunƙurowar
dukan damuwar dake akan ƙirjinta ta fara magana. “Mommy so nake na koma islamiyya, kinga dai
rayuwa bazata tafi da ƙyau ba babu neman ilimi, tunda babu tabbacin samun cikar burin yin makarantar
gaba da sakandire (secondary) inaga ya dace ace mun maida hankali akan na addinin matuƙa, a ƙalla dai
mun mori wani yanki na arziƙin duniya dazai amfanar damu har a lahira. Amma idan na ɓata miki rai a
zancena kiyi haƙuri”.
Sosai zuciyar Asabe ta karye da tausayin ɗiyar tata. Ta sani duk cikin ƴaƴanta babu mai nutsuwar
Raudha. Yarinyace mai hankali da sanin yakamata. Ya rinyace abar alfaharin kowaɗanne irin iyaye. Sai
dai yarinyace mai murɗaɗɗen hali da wuyar sha'ani. Ba komai take kallo dai-dai da ra'ayin mutane ba, ta
rasa inda ta kwaso wannan bauɗaɗɗen halin nata da taurin zuciya. A ido zakai mata kallon mai sauƙin
kai, amma sam ba haka baneba, wanda ya nutsu ga fahimtar halin Raudha ɗinne kawai zai gane ra'ayinta
yasha banban dana mutane.......
Sassanyar muryarta ta katse tunanin Asabe. Guntun murmushi ta saki tana kaiwa zaune kusa da ita, tare
da kai hannu ta kamo nata. “Karki damu indai islamiyya ce zan sakaku Raudha, sai dai ki sani bazai zama
dai-dai da yanda kike zuwa ta gida ba har sau sama da uku. Saboda kinga nan zaku ringa zuwa wajen aiki,
kinga dai yanda sauran ƴan uwana ke tsaye bisa ƙafafunsu, babu wanda ke zaune yana dogaro da
Gwaggo. Kowa neman na kansa yake yi ta yanda nima bazai yuwu na zauna na zuba ido Gwaggo ta
cigaba da ɗawainiya damu ba”.
“Hakane Mommy, sai dai ina roƙon dan ALLAH komi zamuyi ya kasance bisa ƙyaƙyƙyawar hanyar
da bazamuyi dana sani ba watarana mu da ke. Bazan ɓoye mikiba Mommy wlhy sam rayuwar gidan nan
batamin daɗi, nafison hutawa....”
Harara Asabe ta dalla mata da ture hannayenta a cikin nata, rai ɓace tace, “Uban hutawa kikafi so
mara mutunci, Raudha bar ganin ina lallashinki wlhy zan ɓata miki rai. Duk da buhun wulaƙanci da
tozarci da ubanku yay min har kike iya kallon cikin idona kina faɗamin baƙya son nan kin fison Hutawa.
To dan ALLAH ga hanya nan koma Hutawar mtsoww mara mutunci kawai”.
Hayaniyar Asabe ce ta fito da Hajiya Mama babbar yayar su Asaben da yau bata fita ko'ina ba tana
gidan tana barci.
Ta faɗa a hasale tana harar Raudhan datai ƙasa da kanta hawaye na gangaro mata bisa kumatu. Cikin
ɓacin rai Asabe taima yayar tata bayani kamar ta rufe Raudha da duka dan taji zafin maganar datai sosai
a ranta. Itama Hajiya Maman faɗa tahau Raudhan da shi sosai har tana mata gorin ubansu bai iya
komaiba sai bin mata kamar tsohon bunsuru da busa sigari. Ba Raudha kaɗai ba, hatta su Fatisa wannan
furuci na Hajiya Mama ya zafesu a rai matuƙa. Ana tsaka da wannan kicimilli ɗayar yayar Asaben da suke
kira Aunty Hannah ta shigo gidan. Da alama fita tayi, dan sanye take da kaya na alfarma sai bula ƙamshi
take. Babu yanda za'ai mai kallo yace daga wannan gidan ta fito duk da shima gidan nada ƙyau
gwargwadon iko. Sai dai shigar tata tafi kama data hamshaƙan mata da duniya ke kan ganiyar ƙaunarsu
da rungumarsu a jikinta. Ta ajiye key ɗin motar ta bisa centre table ɗin falon tana kaiwa zaune.
“Nikam lafiya kuka rufe yarinya ƙarama da ihu tamkar wasu kishiyoyinta?”.
Sanin halinta na rashin son ganin ana takurama yara Hajiya mama tai saurin faɗin, “Hannah bar
wannan ba abar goyon baya baceba....” nan itama ta shiga zayyana mata abinda ya faru da Raudha ta
faɗa harya fusatasu.
Saɓanin su ita murmushi tayi tana gyara zama saboda wani abu daya cuɗanya tunaninta da zancen
Raudha ɗin cikin ƙanƙanin lokaci, har takai ƙwaƙwalwarta ta haska mata wani nasara a ƙananun daƙiƙu,
dan yanzu haka daga government house take.
Ta faɗa murmushinta na sake faɗaɗa tare da shafa kan Raudha a hankali. Su Asabe na buɗe baki da nufin
yin magana ta girgiza musu kanta tana miƙewa. Dukansu binta sukai da kallon mamaki harta shige cikin
ɗakin barcinta. Bawai amsa buƙatar Raudha ɗin bane abin mamaki a wajensu, dan sun san itaɗin mace
ce mai son yara sosai, sannan ma tun zuwan su Asabe gidan kowa ya fahimci irin son da take nunama
Raudha, dan ko abu zata saka ai mata kafin ta saka su Fatisa ta saka Raudha, sannan har zama take suyi
hira da Raudha ɗin. Abinda ya basu mamaki ta shigo a yanayin damuwa sosai, amma dagajin abinda suke
ɗauka laifi ga Raudhan sai saɓanin hakan ya bayyana a fuskarta, dan a zahiri tamkar abinda Raudhan tayi
ne ya warware dukan damuwar data shigo da shi cikin gidan.........✍
_Tofa minene a ran aunty Hannah da har yay dai-dai da burin Raudha kuma?🤔_
___________________
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_Episode 9_*
..............*_GOVERNMENT HOUSE_*
Sosai jam'iyya mai mulki ke shirin kamawa da wuta a wannan ɗan tsukun a dalilin shirun party
Chairman da shugaban ƙasa game da batun ɗan takara. Bakajin komai sai tsugunne-tsugunne da kace
nace. Dan a wannan gaɓar ba wai jinta bakin su party Chairman ne kawai keda amfani ga jamiyya ba.
Hatta manyan jam'iyar an zuba musu na muzurune game da kaiwa da kawowa da suketa famanyi cikin
duhun dare.
Wasu a cikinsu na goyon bayan shugaban ƙasa ne kai tsaye, yayinda wasu ke kaiwa da komowane
akan nasu ƴan takarar da suke fatan a tsaida domin cancanta ko wani burinsu na daban tamkar yanda
shima shugaban ƙasa keda tasa manufar shi da muƙarabbansa na bayan fage, harma da wanda suke a
cikin tafiyar mulkin tsundum.
*_01:32am_*
Agogo ya nuna a sirrintaccen falon dake fadar shugaban ƙasa ke ganawa da shaƙiƙansa na siyasa
masu faɗa aji a bayan fage dama a zahiri ga jam'iyyar. A zahiri su ɗin manyane na ƙasa da ko kwatancen
arziƙi sukai da kai idan da rabo sai ka haye. Da taimakonsu shugaban ƙasa ke mulki bayan UBANGIJI ya
ƙaddara hakan, duk da dai akwai wasu gwasaken ɓoyayyu. Inda yay biyayya ga dukan tsarinsu ya mora
suka mora. Daɗin hakan yasa basa buƙatar kuɓucewar mulkin a hannunsu, gudun kar wanda zai faɗa a
hannunsa ya gagara zama ƙarƙashin mulkin mallakarsu da faɗa aji. Hakan yasa su yanke shawarar sake
ɗora wanda zai iya binsu sau da ƙafa, sai dai sun hanga sun hango matsalolin dake cikin hakan ga dukkan
waɗanda suka hasaso ɗin kai tsaye. Da ga ƙarshe bayan wasu dalilai suka yanke shawarar bama tsohon
Alƙali kuma shahararren ɗan kasuwa Alhaji Hameed Taura takarar, da shirin bayan anyi komai an gama
mulki ya samu zasu salwantar da rayuwarsa wanda zasu bama mataimakinsa ya maye gurbinsa. Sunyi
wannan tunanin duk da cewa Alhaji Hameed Taura ɗayane da ga cikinsu, sai dai sam baisan akwai wata
alaƙa a tsakaninsu su huɗu da suka killace kansu da itaba wadda babu shi. Sannan baisan ɓoyayyar
manufarsu mummuna akansa ba tun shekaru masu yawa da sukasha auna rayuwarsa ba'a dace ba,
saboda kwanansa basu ƙareba dan a hannun ALLAH suke. Babban dalilin zaɓarsa domin sake kawo
kujerar shugaban ƙasa yanada alaƙa da farin jinin da ALLAH yay masa ga al'umma saboda ɗunbin
ƙyautatawarsa ga talaka. Bashi da ƙyashi balle wulaƙanci. Ya cicciɓa mutane da yawa talakawa da sukai
arziƙi a ƙarƙashin dukiyar da ALLAH ya mallaka masa. Bashi da girman kai, bashi da izza. Sannan baya
ɗaukar raini ga dukkan wani maiji da kansa koda ace ya fisa arziƙi ne. Bai taka kowa bai yarda a takashiba
shima.
Su kansu kusan kaso biyu bisa ukun dukiyoyinsu kaso biyu na Alhaji Hameed Taura ne. Wannan yana
ɗaya daga cikin manyan dalilan da yasa zukatansu suke jin tsoron kar wataran ya amsa su koma baya.
Shiyyasa suka sha auna halaka rayuwarsa amma ALLAH baisa sun dace ba. Hatta ɗansa *Basheer
Hameed Taura* sunsha kai masa hare-hare ALLAH na kareshi. Rashin nasarar hakan ta sakasu komawa
kan jikansa namiji tilo shima guda ɗaya a cikin ƴaƴa goma sha shidda da ɗan nasa Basheer Hameed
Taura ya haifa mai suna *_RAMADHAN B. HAMEED TAURA_*. Sun so tsunduma rayuwar Ramadhan a
harkar shaye-shaye tun yana secondary school ALLAH ya tsallakar dashi. Dan kuwa bai jima da farawaba
ALLAH ya fargar da Uwargida kuma amarya ga Alhaji Hameed Taura, *Hajiya Firdausi Amin Taura*
kenan. Mace ce jajirtacciya kuma tsayayya akan ahalinta. Sam bata da wasa koda akan fuskane. Mace ce
mai addini matuƙa da son taimako. A hannunta Ramadhan ya girma tun daga yaye, duk da kuwa suna
gida ɗaya mahaifiyarsa sam bataso hakan ba, musamman da taga bayanshi bata sake haihuwar wani ɗa
namijinba a cikin ƴaƴa shidda mata data sake haihuwa da Basheer Hameed Taura. Bama itaba kaf sauran
matan Alhaji Basheer Hameed Taura ɗin guda biyu duk basu da ƴaƴa maza sai mata. Sai dai babu yanda
ta'iya, dan sam Anne ba sakarar uwar miji bace da matar ɗa zata taka koda da kirsane. Babu ruwanta da
rayuwarsu bare harkarsu, dan bata taɓa sakama matan ɗan nata idoba balle damuwa da mi suke ciki.
Dan da ace ita ɗin sakaraice da tasha matuƙar wahala a hannun Gimbiya Su'adah.
Gimbiya Su'adah mace ce mai izza da tsananin taƙama kasancewarta ɗiyace ga sarkin jihar Bina.
Sannan ƴar gata kuma sangartacciya mai ji da mulkin gidansu. Mace ce mai shegen girman kai da ƙyamar
talaka, dan sam bata biyo ƙyawawan halayar mahaifinta ba. A ƙasar amuruka suka haɗu da Alhaji
Basheer Hameed Taura yayin karatu, inda soyayya mai ƙarfi ta ƙullu harta kaisu ga aure kasancewar su
ƴaƴan ƙwarya tabi ƙwarya.
Bayan ceto rayuwar Ramadhan da Anne tayi daga faɗawa shaye-shaye suka sake harar rayuwarsa
akan neman mata. Sai dai anan ALLAH ya karesa, dan baima saka matan a gabansaba balle su damesa.
Musamman daya kasance yanada ƙananun shekarune dama a wancan lokacin. Abokan banza suka
ƙirƙirar masa da sukaso fara jansa yawon dare, tunda ya farga da halayensu ya janye jikinsa. Dan
Ramadhan mutumne daya gado halayen iyayen nasa ta ɓangarori biyu. Akwai halin mulki na ɓangaren
mahaifiyarsa tattare dashi. Akwai kuma halin dattako na ɓangaren kakansa dake yawo a jikinsa. Hakanne
ya sakashi zama mai murɗaɗɗen hali tun daga yarinta har girma. Bazamu ce dashi miskili ba. sai dai
zamu kirasa mutum mai tsananin girman kai da ɗagawa. Ba komai yake so ba, ba komai ake saka yaso
ba, sai idan shine yaso a karan kansa. Da yawan lokuta Anne ce kawai ke iya tanƙwarashi ta ƙarfin tsiya
saboda itama tanada zafi sosai.
Su *Alhaji Wali Bajau* basu daina bibiyar rayuwar iyalan Alhaji Hameed Taura ba musamman
Ramadhan da suke kallo matsayin zuciyar gidan har yakai girma. Da tsiya-tsiya da makirci Alhaji Haladu
Gwandu ya ƙulla soyayyar ɗiyarsa da Ramadhan har takaisu ga aure a shekarar daya kammala karatunsa
akan lauya. *Amnah* yariyace ƙyaƙyƙyawa kuma ƴar gayu kamar yanda Ramadhan ke buƙata. A shekaru
kaɗan ya ɗarata hakan ma dai-dai da ra'ayinsa ne, dan sam baison auren yarinya ƙarama yace sun cika
shirme da ƙuruciya wa miji. Soyayya ce ta haɗa Amnah da Ramadhan a zahiri, a baɗini kuwa su Alhaji
Gwandu sun shirya hakanne da manufa, dan ta bayan fage suka dinga amfani da Amnah suna cutar da
Ramadhan. Burin Ramadhan aikinsa na lauya, tare da faɗaɗa karatunsa na Addini dan tun yana shekara
sha bakwai ya sauke alkur'ani mai girma ya fara hadda, saboda Anne bata da wasa, ga shi ALLAH ya bashi
ƙwalwar karatun shima. Sai dai burin mahaifiyar Ramadhan gimbiya Su'adah ba haka bane. Burinta duk
dukiyar Taura Family ta dawo hannun Ramadhan ne, dan haka taita ƙoƙarin jan hankalin mijinta harya
amince da jawo Ramadhan ɗin cikin babban kamfanin (company) na taura aka ɗaurasa matsayin oga
kwata-kwata. badan ya so ba ya amsa, dan shi hakan baya cikin burinsa. Amma nasihar tsoho Hameed
Taura ya sakashi amincewa akan tilas ya fara musu aiki. Lokaci-lokaci kuma yana taɓa aikinsa na lauyanci
a ɓoyo dan gudun ɓacin ran mahaifiyarsa mai zafin zuciya da son nuna gadara ga kowa.
Suna shekar ta uku da aure Amnah ta haihu ƴarta mace, sai dai kuma an haifeta sikila ne tamkar
uwar tata data kasance sikilar ce dama. Ko kusa hakan baisa ubanta ƙin son kayarsa ba duk da sam
gimbiya Su'adah basan auren takeba. Amma kasancewar itama uban Amnah ɗin ba koma baya bane
akan juya kuɗi ya sata ɓoye ƙiyayyar auren a ƙasan zuciyarta, sai idan abin nata ya motsane taita azabar
masifa.
Hawan Ramadhan MD a Taura company matsaloli sukaita faruwa na ɓatan kuɗaɗe da wasu asarori da
aka rasa musabbabinsu. Tun su Alhaji Hameed na kawaici hartakai shida mahaifin Ramadhan Alhaji
Basheer Taura sun zaunar dashi sun masa ƙorafi da tambayar mike faruwane haka company keta baya
maimakon gaban da suke fita da nasarori?.
Amsa ɗaya ce shima baida masaniya. Amma yana kan bincike da ƙoƙarin daƙile komai. Tun ana
tattaunawa iya su uku harta kai Anne ta shigo tafiyar, hakama sauran matan gidan sun sani. Kowa yana
ɗaura zarginsa akan Ramadhan da tunanin ko yana wata harkar banza ne ta kuɗi a ɓoye?.
A ranar da su Alhaji Balarabe Gizo suka shirya kai rayuwar Ramadhan ƙasa yayi dai-dai da ranar
birthday ɗin ƴarsa Haseenah ƴar shekara biyu cif a duniya. An shirya liyafa ta gani ta faɗa tare da gayyata
ta mutanen arziƙi Alhaji Haladu Gwandu ya baiwa Amnah ruwan addu'a da aka gauraya da guba akan ya
amso ma Ramadhan ɗinne saboda ciwonsa na diabetis, Ramadhan nada diabetis sakamakon ya zame
musu tamkar gado ne. Alhaji Hameed Taura nada shi, hakama Alhaji Basheer Taura, shima Ramadhan
ɗin haka da wasu daga cikin yara matan gidan. Sam Amnah batai tunanin mahaifinta zai iya cutar da
Ramadhan ɗinta ba. Dan haka ta ɗauka ruwan addu'a da ƙyaƙyƙyawar zuciya takai masa. Sai dai an samu
akasi bayan gama birthday party lafiya an watse ta buɗe fridge a gajiya ta ɗauka goran da ruwan addu'ar
yake da tunanin ruwa ne saboda fitilar kitchen dake a kashe saita falo data ɗan hasko kaɗan ta sha. Tana
sha Haseenah najan hannunta da mata gwarancin ruwa ruwa. Sai da tasha sosai sannan ta bata tasha
itama.
Wannan magani da Amnah tasha da ƴarsu Haseenah ya zama sanadin barinsu duniya. Dan kuwa
azababben ciwon ciki ne ya baibayesu ita da ɗiyar har sai da aka kaisu asibiti, inda tunkan suje ma
Haseenah ta rasu saboda ƙarfin gubar, Amnah kuwa sai kusan asuba itama tace ga garinku nan. Likita ya
tabbatar musu hanjinsu ya kakkatsene ita da ɗiyarta saboda ƙarfin gubar da suka sha.
Kwatanta irin tashin hankalin da Ramadhan ya shiga a wannan lokaci ɓata bakine. Bama shiba
kowama da ke da alaƙa dasu wannan al'amari ya taɓa masa zuciya. Dan kowa dai ya fahimci guba aka
ajiye musu. Sai dai ba'asan kowa ya ajiyeba saboda Amnah ita babanta yaba hannu da hannu batare da
kowa ya sani ba. Ya kuma jaddada mata maganin diabetis ne kar Ramadhan yasha sai randa yake aiki
musamman motsa jikinsa. Ita kuma ALLAH baisa ta bashi maganin ya sha da rana ba ta bari sai an tashi a
birthday ɗin Haseenah. Ashe da rabon ajalinsune a ciki.
Sosai Ramadhan ya fita a hayyacinsa. Dan yana mayuƙar son matarsa da ƴarsa duk da lalurar dake
tare da su ta sikila. Iya bincike anyi a gidan babu wani bakin zare da aka samu sai tunanin cikin masu
zuwa birthday ne suka ajiye gubar kawai. Tsabar yanda Ramadhan ya tada hankalinsa akan son gano
wanda ya aikata ya saka su Alhaji Haladu Gwandu da abin yay matuƙar taɓawa da tunzurawa sakawa aka
kai Ramadhan ƙasar Ukraine wai ganin likita. Sune suka tsarama likita ƙaryar da yace kar a sake yarda
Ramadhan yay zaman NAYA sai bayan wasu shekaru harya manta da abinda ya faru. Sunyi hakanne
domin su nisantashi daga bincike ko bibiyar ainahin gaskiyar lamarin da suka san reshe ya juye da
mujiyane. Dan haukane kawai Alhaji Haladu Gwandu baiyiba a dalilin rasuwar shalelensa data bar duniya
a dalilinsu.
Ƙura ta lafa, abubuwa sun canja, shekaru sunyi gudu har kusan biyar da faruwar komai. Ramadhan
yayi jiyyar zuciya data gangar jiki harya warke, amma anyi-anyi ya dawo NAYA yaƙi. An kaɗa dambu da
takiya yace shi da NAYA har abada. Babu irin roƙo da lallaɓa da basu masaba musamman gimbiya
Su'adah da take kasa ɓoye ɗunbin soyayyar da take masa koda a idanu ne amma ya kafe akan bakansa.
Da ga ƙarshe ma sai ya koma U.S da zama. Kafiyarsa da murɗin hali yasaka kakansa Alhaji Hameed Taura
yin fushi yace su barsa ya dawwama acan dan ALLAH karya dawo. Ya kuma saka sharaɗin koda wasa kar
wanda ya sake zuwa dubashi har Mahaifinsa da gimbiya Su'adahn. Inko ba hakaba zai saɓama mutum a
gidan.
Wannan shine dalilin da yasa Alhaji Hameed Taura baya son ko maganar Ramadhan ai masa a gidan,
duk da yana tsananin kewarsa a kusa da shi da begensa shima. Dan shi kaɗai ke zuwa dubashi a ɓoye
batare da shi kansa Ramadhan ɗin ya sani ba.
Yayinda Ramadhan kuma har yanzu zuciyarsa ke cike da burin binciko koma wanene da alhakin kashe
masa iyalinsa, dan haka a tsahon shekarun nan babu abinda yake saƙawa da kwancewa bayan
kasuwancinsa daya maida hankali dayi shi kaɗai sai hanyar dazai yi binciken yanda rayuwar matarsa da
ƴarsa ta salwanta. A cikin wannan halin kuma Anne ta kawo shawarar Ramadhan B. Hameed Taura ya
maye gurbin kakansa a kujerar shugaban ƙasa da akai masa tayi. Inda dudu shekarun Ramadhan B. Taura
36 a duniya. Ya rasa iyalansa yanada shekaru 31. Yanada ashirin da bakwai yay aure. A yanzu shekaru 5
cif da faruwar komai kuma.
A hasashe ba'a taɓa samun wani shugaban ƙasa mai adadin shekarunsa na ƙuruciya ba a ƙasar ta
*NAYA* ba sam.
“Kana nufin dole kenan mu amince da zancen Alhaji Hameed Taura indai muna buƙatar cikar
burinmu Your Excellency?”.
Shugaban ƙasa da Alhaji yaro glass suka kalli juna suna murmushi mai kama da takaici suma. Yayinda
Alhaji Haladu Gwandu ya dafa kafaɗar Monday Mazier ɗin yana faɗin. “Mr MM cool down abeg. Muma
duk irin zafin da kakeji munjisa a lokacin daya tabbatar mana ya amsa tayinmu, amma kuma jikansa ne
zaiyi bashi ba. Ƙwarai da gaske ya shammacemu, shammata maiban mamaki. Dan yayi hakane dan mu
janye buƙatarmu kodan kasancewar jikan nasa yaro, tunda yana ganin ba'a taɓa shugaban ƙasa mai
ƙarancin shekarunsa ba a wannan ƙasa ta NAYA. Sai dai kodana zauna nai zari sai banji komai ba, domin
Ramadhan baida maraba da hoton bango da kowa zaizo ya kalla ya wuce manne a falo batare daya
amfana masa komaiba. Shine surikina da yarinyata ta rasa ranta a dalilinsa, yana can U.S tsahon shekaru
biyar tamkar zararre. A ganina wannan damace a garemu mai sauƙi, duk da naji a raina Taura yayi
hakane danya dawo da hankalin yaron gida kamar yanda sukaita fata a shekarun baya yaƙi hakan. Amma
idan Taura yasan wata ai baisan wataba, Idan muka fitar da yaron matsayin ɗan takara zamu kawo wani
sabon abu a ƙasar nan da ba'a taɓa yiba, sannan matasa zasu yarda da gaske muna tare da su. Babu
tantama mulki zai cigaba da kasancewa a hannunmu ne”.
Alhaji Yaro glass ya gyara zama da faɗin, “Tabbas nima sai yanzu na fahimci manufar Taura na yarda
cikin sauƙi, kuma hakan yamin daɗi, dan mu idan bai saniba wata damace ta ɗaukar fansa sau biyu akan
abu guda. Ramadhan zai hau mulki na tsahon shekaru biyu kacal, sannan zai mutu sau biyu......”
Alhaji Yaro dake murmushi yace “Ƙwarai kuwa sau biyu, dan dole ne mu ɗauka fansar Amnah data
mutu dominsa, sannan mu kashesa adalilin taurin ran kakansa da ubansa. Na farko zai kasance cikin
nasararsa da jin daɗin mulki a shekarar farko, a shekara ta biyu zai fara ciwo a dalilin guba da zata zagaya
jininsa zuwa ɓargo da jiki. A shekara ta uku muyi bikin mutuwarsa da biznesa vice president ya hau
kujera ya shekara biyu biyar cif kenan. Shekar ta ƙarshe a sake sabon zaɓe wannan shine amsar mutuwa
biyu”.
Ya ƙare maganar yana ƙyalƙyalewa da dariya, suma sauran suna tayasa kamar wasu zararru. Sai da
sukai mai isarsu kafin suyi shiru suka koma shan shayi da cigaba da ƙulla tsiyatakunsu........✍
_Safiyya Huguma_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_Episode 10_*
.............*_WASHE GARI_* shugaban ƙasa yay waya da god father nasu na siyasa dake faɗa aji a ƙasar
baki ɗaya, sai dai a siyasance babu mai iya jin sunayensu. Ya sanar musu dukanin tsare-tsarensu. Sosai
nasu tsarin yay masa shima harya yaba musu, dan yasan komai sai dai suna bayan fagene, ya kuma
tabbatar musu komai zai tafi dai-dai dan Alhaji Hameed Taura a tafin hannunsu yake.
Cikin farin cikin yabon da shugaban ƙasa ya samu yace, “Na gode ranka ya daɗe. ALLAH ya ƙara girma
da ɗaukaka. Badan ku ba babu mai ganin koda hotonmu a ƙasar nan. Shiyyasa muke addu'ar tsahon rai a
gareku domin muyita cin karenmu babu babbaka”. (Ashe kasan shi mai mutuwane, rayuwarsa mai
ƙarewace excellency. Inhar kuwa zai mutu to bai isa amfana maka komaiba face wanda yazo cikin
ƙaddarar duk wanda kuka hara. ALLAH ka bamu shugabanni na gari🙏🏻🤦🏻).
Bayan ya gama masa kirari da yabon dake sake buɗa masa kai ya ɗora da bayanin...
“Ranka ya daɗe a yanzu haka mun gama yanke shawarar ganawa da shi yaron kawai muji ta bakinsa
shima”.
“Tunani mai ƙyau, sai naji ku”. Daga haka ya yanke wayar. Shugaban ƙasa ya cireta a kunnensa yana
jan kakkauran tsaki da ballama wayar harara. Cikin ƙunƙuni yace, “Mugu ƴan hana ruwa gudu, ALLAH dai
ya kusa kasheku muma mu babake ko'ina, daga sama har ƙasan ta zama tamu. Dan badan kuba da mune
taurarin duniya ta kowanne fanni.”
(Kai jama'a kamar bashi bane ya gama masa ƴar murya yanzun🤣, siyasa shegiya😂).
*_TAURA HOUSE_*
Kamar yanda al'adun ƙasashen da hausawa yake dama musulinci baki ɗaya, irin wannan lokacin ko
nace wannan ranar ranakune masu muhimmanci na shirye-shiryen bikin salla. Tamkar kowanne gida
dake shiri haka Taura family house ma keyi ƙwansu da kwarkwata. Danko duk ƴammatan gidan zaka
gansu da zanen lalle baƙi ko ja. Wasu sunyi kitso wasu gyaran gashi kawai. Hakama matan Alhaji Basheer
Hameed Taura babu koma baya dan duk ɗinsu ƴan gayu ne kuma ƴaƴan manya, dan kowacce tana
alfahari da irin gidan data fito ne.
Misalin ƙarfe tara na dare da yay dai-dai da sanarwar ganin jinjirin watan shawwal daga bakin mai
girma sarkin musulmi ƙararrawar dake sanar da taron meeting na iya manyan gidan ta kaɗa. Ba sabon
abu bane hakan a duk daren kowacce salla, sai dai a wannan karon taron meeting ɗin yazo da banbanci.
Sakamakon manyan gidan kawai ake buƙata banda yara.
Cikin tunani da taraddadin lafiya duka matan Alhaji Basheer Hameed Taura suka kimtsa kawunansu
zuwa sashen surukan nasu domin amsa kira. Sai tsoffi guda biyu da suka kasance ƙanne ga Alhaji
Hameed Taura da suma suke zaune a gidan a halin yanzun. Sai ƙanin Alhaji Hameed Taura ɗin autansu
da ya iso da iyalansa daga ƙasar Dubai a daren jiya domin halartar bikin salla da sukanzo a kowacce
shekara...
Duk wani wanda ake buƙatar gani a katafaren falon na alfarma da an tsarasane kawai domin gudar
da meeting na ahalin gidan ya iso. Kowa ka gani zaune yake cikin mutuntawa ga dattijo Alhaji Hameed
Taura da matarsa Anne. Dan dukan matan Alhaji Basheer kansu a ƙasa yake kasancewar suna gaban
surukai.
Bayan an buɗe taro da addu'a Alhaji Hameed Taura da ahalin gidan ke kira da suna Bappi yay gyaran
murya da tasaka kowa sake nutsuwa a wajen.
“Da farko dai ina tayamu murnar ganin wannan wata na shawwal da rai da lafiya. Ina roƙon UBANGIJI
ya amshi ibadunmu da mukayi, ya yafe mana kura-kuranmu. Yasa muna da rabon ganin na gaba da rai
da lafiya.”
Ya cigaba da faɗin, “Nasan zakuyi mamakin canzawar zaman meeting ɗin yau, dalilin hakan kuwa ya
dangantane ga Ramadhan kacokal”.
Da dauri Gimbiya Su'adah da yaran ke kira da (Maa) ta ɗago jin an ambaci sunan gudan jininta mafi
soyuwa. Yayinda firgici da taraddadi ya bayyana cikin ƙyawawan idanunta. Dan batason mi kuma ya
samu Ramadhan ɗin ba koya aikata. Tunda yau kusan satinsu biyu rabon da suyi waya sakamakon ta
masa maganar ya daure yazo musu salla gida......
.... ya katse mata tunani da cigaba da faɗin, “Wani babban al'amarine ya tasoma gidan nan, sai dai
mun ɗaukesa kacokan mun rataya ga shi Ramadhan saboda wasu dalilai. Na farko yin hakan zaisa ya
dawo kusa damu dole. Na biyu zaisa yazo shima yay aure. Na uku ya isar da abubuwan da muka kasa
isarwa ga sauran mutane bisa ga abinda ALLAH ya azurtamu da shi.”
Duk da a dunƙule yay dukan bayanin hakan bai hana farin ciki bayyana a fuskar Maa ba. Ji take tamkar
Bappi ya mata albishir ne da wani yanki na farin cikin samun ƙyaƙyƙyawar makoma. Tana matuƙar burin
ganin yaronta a kusa da ita. Tsabar jin daɗin hakan harta gama yanke masa matar aure a ranta. Dan
wannan karon tanason zaɓama yaron nata matar aure ko hakan zaisa ta sanadin matar ya dawo gareta
ba wajen Anne ba....”
Dogon tunanin da gimbiya Su'adah ta tafi yasa har Bappi ya kammala jawabinsa ma bata ƙarasaji
wasu abubuwan ba. Sai murmushi take wanda ya kasa ɓoyuwa bisa fuskarta.
Ana tashi da ga taron tun kan ta ƙarasa sashenta ta fara kiran wayar gimbiya Asma'u yayarta da suke
uwa ɗaya uba ɗaya (Adda Asmah). Su baƙwai mahaifiyarsu gimbiya Naja'atu da ake kira fulani ta haifa,
sai dai sauran duk mazane su biyune kacal mata, kuma sune manya. Hakan yasa musu wata shaƙuwa da
son juna na musamman dan sun tashine tamkar tagwaye. Kasancewar kuma irin gidansu gidane na
tsantsar ƙabilanci da ƴan ubanci yasa kowa da nasa yake shaƙuwa.
Dai-dai tana saka ƙafarta a ƙawataccen falonta na alfarma da yaji kayan more rayuwa har zaman
musaltashi zai iya zama ƙauyanci gimbiya Asma'u ta ɗaga wayan. Itama tayi aure tuni, anan cikin garin
Bingo ma take, rana ɗaya ma akai musu aure. Sai dai ita tayi kusan shekara biyar bayan aurensu kafin ta
samu haihuwa. Yaranta biyu kuma kawai. Mace da namiji.
Batare data dubi su Zuhrah dake zaune a falon kowa na harkar gabansaba ta shige tana mai zolayar
yayar tata da faɗin, “Haba ƙasa badai har kin fara barcin naki ba ko?”.
Amsar da aka bata daga can ta sata sakin ƴar dariya tana tura ƙofar glass na corridor ɗin bedrooms
ɗinta ta shiga. Ta kan wani tattausan carpet dake a tsakkiyar corridor ɗin ta taka zuwa ƙofar tsakkiya.
Ɗaki ne da musaltashi ɓata lokacine. Dan haka kowa ya musalta da kansa. Ƴar sarki matar Alhaji Basheer
Hameed Taura. Ta kai zaune tana sake ƙawata murmushin fuskarta da faɗin, “Amin Adda Asmah. Dama
albishir na kiraki nai miki”.
Tai dariya saboda zumuɗin Adda Asma daga can. “Oh god hajiyar ruɗu kwantar min da hankalinki.
Bafa wani abu bane yaronkine kawai zai dawo NAYA, dalilin kiran naki kuwa maganar aure da mulki da
ya sakko a ciki ne. Inaga lokaci yayi da zamu cika burinmu na haɗa auren Ramadhan da Aina'u tunda ta
kammala karatunta”.
Dariya ta kuma saki wadda inba Asma ɗin ba babu mai iya ganinta a saman fuskar Gimbiya Su'adah
saboda izzarta da girman kai. A take a wajen suka gama yanke hukunci komai game da auren ƴaƴan
nasu, batare da gimbiya Su'adah tayi wani dogon tunani ko bincike akan mike a ran Bappi ba.
Ita ɗin mace ce ƙyaƙyƙyawa kuma gogaggiya, inda a dalilin harkar barikinta ta haɗu da Alhaji Yaro
glass babban ɗan siyasa dake riƙe da babban muƙami a ƙasar ta NAYA. Tun a haɗuwarsu ta farko taji
sonsa a ranta, inda akai dace shima ya kamu. Dan haka sukai aure cikin ƙanƙanin lokaci. Sai dai abinda
bata saniba Alhaji Yaro glass a ƙarƙashin mulkin mace yake a cikin gidansa. Dukkan faɗa ajinsa iyakarta
waje ne. Daya taka gate ɗin gidansa sunansa mijin hajiya Fanta. Tabbas ta fuskanci ƙalubale kala-kala a
zamanta da Hajiya Fanta da bazasu musaltu ba, har takai sai da ta tsigeta a gidan hankalinta ya kwanta.
Ta kuma kauda hankalin Alhaji Yaro glass da ga gareta baki ɗaya, duk da ƙulafucin son komawa garesa da
takeyi musamman saboda ƴarsa ɗaya tilo da suka haifa tare dake wajenta. Tun farkon zuwanta gidan
suke ƙawance da Hajiya Bushira hamada, wadda sam bata shiri da Hajiya Fanta duk da kuwa mazajensu
abokaine shaƙiƙai. Koda yake ance ada ƙawayene suma na amana, sai dai ƙawancen ya watse ne a dalilin
ƴaƴansu. Mafari kenan Hajiya Bushira taita tunzura Alhaji Yaro glass ya ƙara aure, tun baya biye mata
har yaji sha'awar yin hakan lokacin daya haɗu da Aunty Hannah.
Bayan fitowarta a gidan hajiya Bushira tayi iya ƙoƙarinta na ganin Aunty Hannah ta koma gidan Alhaji
Yaro glass amma hakan ya gagara, har suka samu nasarar ɗarewa kujerar mulkin ƙasar ta NAYA. Inda
Prof... Usama D. Hamada ya samu nasarar zama shugaban ƙasa bisa ƙoƙarin su Alhaji Hameed Taura. Su
kuma su Alhaji Yaro glass suka koma gefe matsayin manya sunacin karensu babu babbaka. Dan ko
muƙami ɗaya basu amsaba a bayan fage suke nasu mulkin su.
Hankalin aunty Hannah ya sake tashi dan tana son Alhaji Yaro glass sosai, amma sai Hajiya Bushira
Hamada (First lady) ta kwantar mata da hankali akan karta damu, inhar tana raye sai ta koma aure gidan
Yaro glass. Aunty Hannah tana cikin manyan ƙawayen first lady da suke mata ayyuka a ɓoye, amma tana
ɓoye kantane saboda Alhaji Yaro glass.
A yau ma first lady ce ta buƙaci ganin aunty Hannah ɗin tun daren jiya akan wani aikin sirrinsu, a
hirarsu ne first lady keɗan tsoguntama aunty Hannah batun wanda su shugaban ƙasa suke son tsaidawa
takara, tare da burinsu na salwantar da rayuwarsa daga baya Alhaji Yaro glass ya maye gurbinsa, dan
shine sukeso ya zama mataimakinsa. Wannan al'amari ya matuƙar saka Aunty Hannah a farin ciki
matuƙa. Har takejin zata iya bada gudunmawarta akan wannan al'amari. Sai dai maganar data biyo
bayan hakan ce ta sakata a damuwa, dan kuwa first lady ta sanar mata sun tattauna da shugaban ƙasa
akan suna son samawa yaron matar auren da zata dinga musu aiki a kansa batare da sanin kowa ba,
amma suna tunanin ta yadda zasu ɓulloma Alhaji Hameed Taura game da hakan. Dan samawarwa
Ramadhan matar aure daga ɓangarensu ne kawai mafita da hangen nasararsu a tafiyar. Hakan yasa
tacema aunty Hannah taje ta tayata tunani da nazarin mafita dan tana son ita ta fara kawoma shugaban
ƙasa mafita koda ƙara samun ɗaukakarta na mata garesa, sannan ita kuma ta zama first lady kodan
cusama hajiya fanta baƙin ciki. Dan ba hawan Alhaji yaro glass bisa kujerar matamakin shugaban ƙasa ko
zama shugaban ƙasa bane matsalarta ita. Hajiya Fanta ta samu muƙami dai-dai da wanda ta taka shine
damuwarta kawai. shiyyasa take so ta shiga ta fita wajen ganin ta nakasa Hajiya Fanta kafin lokacin
Aunty Hannah ta koma gidan ta zama tauraruwa a mulkin da Alhaji yaro glass zaiyi.
Wannan shine dalilin shigowarta da damuwa gidan. Sai dai kuma abinda ta tarar na boran Raudha
ya kawo mata mafita cikin sauƙi da take tunanin first lady zatayi matuƙar farin ciki da ita har itama ta
samu cikar burinta na komawa gidan Alhaji Yaro glass matsayin matar vice president.
Ta saki murmushi mai ƙayatarwa tare da jawo hamshaƙiyar wayarta 1phone ta shiga sarrafata. Kai
tsaye number first lady ta laluba. Harta tsinke ba'a ɗaga ba, dan haka ta yanke shawarar sake kira dan
tasan saƙon da take shirin kaiwa mai matuƙar muhimmanci ne.
Cikin sa'a kuwa tana gab da tsinkewa first lady ta ɗauka. “Hannah am sorry ina amsa wani call ne. Ina
fatan har an samu mafitar ne da gaggawa haka?”.
“Sosai ma kuwa your excellency. Zumuɗin hakanne ma yasa na kasa haƙurin bari sai nazo nace bara
na kiraki”. Aunty Hannah ta faɗa cikin washe haƙora kamar tana gaban first lady. Itama daga can first
lady ta amsa ne cike da zumuɗin son jin yaya akai? Dan haka kai tsaye aunty Hannah ta fara jero mata
bayani....
“Akwai yarinyar ƙanwata dake aure acan jihar Ɗillo. Sai dai a wani ƙaramar hukuma suke mai suna
hutawa. Yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce son kowa ƙin wanda bai samu ba. Gata ƙarama sosai sweet 17. Tanada
yanayi irin na mutane masu haƙuri da komi zatai baza'a zargeta ba. Sannan inada yaƙinin zata shiga ran
Alhaji Hameed Harith Taura cikin ƙanƙanin lokaci. Kai harma da uban gayyar kansa dan da gaske yarinyar
ta haɗu your excellency......”
“Ban katsekiba Hannah, amma mu minene alaƙar shirinmu da ƙyawunta ko sanyin halinta? Mufa
wadda zatai mana aiki kawai muke buƙata batare da matsala ba”.
“Hakane your excellency amma bara na kaiki. Alhaji Hameed Taura mutum ne mai son mu'amula da
mutanen kirki, a dalilin hakane mazajenmu suka ɓoye masa ainahin fuskarsu suka aro ta mutuntaka suka
yafa ma kansu har takai abotarsu yin tsaho zuwa yanzun. Dan haka bazai yuwu mu samo yarinya mai
rawar kai ba akan wannan shirin. Dole ta kasance mai irin suffar Raudha, sannan ƙyaƙyƙyawa. Abu na
biyu dole ta kasance ɗiyar masu ƙaramin ƙarfi da basu da wata power ɗin zamtowar yarinyar mai
buɗaɗen kai da komai zata iya fahimta idan an sakata tayi, sannan kuma zamu iya juyata ita da iyayenta
yanda muke buƙata muma cikin sauƙi dan batasan komai ba sai abinda muka ɗorata a kai”.
First lady ta ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Kai Hannah shiyyasa nake bala'in sonki wlhy. Dan kuwa
kanki na ja matuƙa. Sai dai matsalar ɗaya zuwa biyu ce. Matar shugaban ƙasa ƴar 17years, kuma mai
kwalin secondary school kawai. kuma ɗiyar ƴar uwarki bayan kinsan shirinmu shine itama idan ta
kammala mana aiki rayuwarta zata iya salwanta”.
Aunty Hannah tai ɗan murmushi tana sake damƙe filo a jikinta. Dan ita inhar buƙatarta zata biya
salwantar rayuwar Raudha ba komai bane ba a gareta. “Your excellency matsala ta farko ba matsala
bace ba. Dubi da shima ɗin yaro ne matashi da zai zam na farko bisa kujerar mulkin ƙasar NAYA. Karatu
kuwa ko tana gidansa za'a iya sakata ta fara badan zai amfanemu ba sai dan kawai zai bada kariya ga
masu ƙorafin matar president iyakarta secondary. Na uku kuwa karki damu, dan mun rasa iyayenmu ma
munyi haƙuri balle ƴaƴa. Ko Samha ce zan iya sadaukar da ita domin samun cikar burinmu (ƴarta fa😱,
anya kuwa gsky aunty Hannah ke faɗa🤦🏻). Abinda kawai zamu maida hankali yanzun shine koya mata
rayuwar manyan mata da abubuwa.”
“Okay na gamsu da bayaninki, sai dai kuma taya zamu haɗa alaƙar su kuma?”.
*_Yaya kuke gani masu karatu? Shin Ramadhan zai amince ya amsa kiran Alhaji Hameed Taura kuwa
zuwa ƙasar NAYA? Harma da tayin zama shugaban ƙasa?? Kokuwa ƴan ƙasar ta NAYA zasu yarda da
wannan sabon al'amari na hawan matashi mai jini a jika irin *_Ramadhan B. Hameed Taura_* ne
matsayin shugaban ƙasarsu ne?. koba shekaru ba karku manta akwai matsalar sauran ƴan jam'iyya,
akwai ta shekaru, akwai!! Akwai akwai da yawan gsk. Muje zuwa donjin shin yaya zata kaya ne?🚶🏻_*
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_Episode 11_*
............*_SALLA BIKI ƊAYA RANA_*
A duk wanda ka duba yau inhar musulmi ne na ƙwarai zaka fuskanci farin cikin zagayowar wannan
rana ta salla bisa fuskarsa. Rana ce da mafi yawan al'umma suka ganta suka kuma sake ganinta. Sai dai
hakan baisa ta gunduresuba. A kowace shekara murnar zagayowarta ake yara da manya tamkar lokacin
suka fara riskarta.
Ƙarfe goma na safe tawagar ɗunbin al'ummar musulmi dake a sassa da dama na babban birnin ƙasar
Bingo da ke a NAYA suka kammala sallar Edi. Bakin kowa a washe yana gaida ɗan uwansa ko aboki.
Yayinda irin su Raudha baƙi a garin keta ƙoƙarin ganin sun fito da ga harabar babban masallaci idin
domin samun abun hawansu. Dan kuwa dai aunty Hannah ce da kanta ta kwaso ƙwai da kwarkwatar
yaran gidan ta taho dasu filin na idi.
Duk da a ƙurarren lokaci su Raudha sukazo Bingo tsaf Aunty Hannah ta haɗama kowansu kayan salla
na gani na faɗa. Wanda a zahirin gaskiya first lady ce ta bada maƙudan kuɗaɗe domin yin hakan. Su
dukansu matan sanye suke cikin baƙaƙen abayoyi ƙirar Egypt, sai dai ta kowa ta banbanta da kalar adon
da yafi buƙata. Kasancewarsu ƙyawawa jinin ƴaƴan larabawa duk da ba kowanne a cikinsu ya biyo iyayen
nasu ba sai gasu ɗas tamkar wasu ƴaƴan manyan mutane.
Tafe suke Yasmin da twins na surutu da bada labarin yaran da suka zauna kusa da su basu iya salla ba
su Fatisa na dariya. Sai Raudha da kusan ke ƙarshe a bayansu tana tafiya a nutse dan sam bata iya sauri
ko garaje ba. Kanta a ƙasa yake tana ɗan kallon yara daketa kaikawo cikin shigar malam bahaushe abin
sha'awa. Kamar ance ta dubi gefenta idanunta karaf akan wani matashin saurayi da kallonsa kawai baida
daɗin yi. Duk da ranar salla ce kuma shigar farar jallabiya yayi fara ƙal a jikinsa saita banbanta da jikin
nasa. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci baiyi kama da mutanen kirki ba.
Gabanta ya faɗi ganin yana gyara wata ƴar wuƙa dake a hannunsa sai ƙyalli takeyi. Abinda ke manne
a kunnensa ya kai hannu ya gyarama zama alamar magana yakeyi da wani, dan bakinsa sai motsi yake
yayinda idanunsa ke kallon saitin inda yake tunkara. Juyawa tai da ƙyau itama tana duban wajen.
Zuciyarta ta ɗan harba sabida yin tozali da wani kamilallen dattijon tsoho ƙyaƙyƙyawa. Duk da shekaru
sunja garesa hakan bai hana bayyanar cikar kamalarsa da jin daɗi ba. Tsaye yake akan ƙafafunsa cikin
ɗanyar shadda fara ƙal da ko ba'a faɗaba kasan an narka kuɗi wajen ɗinkata.
Ya sake damƙe hannun mutumin da suke tare fuskarsa na sake ƙawatuwa da murmushi alamar
gaisuwa sukeyi irin wadda take nuna an daɗe ba'a haɗu da mutum ba. Sake maido kallonta tai ga
saurayin nan daketa sake tunkararsu. A take jikinta ya fara rawa, tanaji a ranta akwai abinda saurayin ke
ƙullawa mara ƙyau a zuciyarsa game da kamilallen tsohon da takejin nutsuwa a zuciyarta game da shi.
Badan ta sansa kota taɓa ganinsaba sai ɗazun da suke shigowa massallacin idin da wani tsoho daya fisa
tsufa sosai ya kusa faɗuwa. Dakaga tsohon na ɗazun kasan talakane, amma sai ga wannan dattijo ya
zaburo har shima yana shirin faɗuwa ya tare tsohon a jikinsa yana masa sannu, kasa ɗauke ido tai a
kansu a ɗazun har suka shige cikin massallaci yana riƙe da shi. Kwarjininsa da cikar kamalarsa da
shekarunsa na girmane kawai sukaja hankalinta da zuciyarta nason taimakonsa, (sai dai ta yaya?). Ta
ambata a zuciyarta batare da tasan amsa ba. Farga da saurayin na gab da kaiwa garesa ga shi zai juya
baya ya sakata zabura ta nufesa. Kusan a tare suka ƙarasa ga dattijon ita da saurayin.
Cikin ƙwarewar aiki na iya kisa saurayin ya kaima Alhaji Hameed Harith Taura yanka da kakkaifar
wuƙar hannunsa gayama jini na wuce yanka ta gefen ciki. Inda ya tabbatar idan ya yanka sai ya mutu
kuma. Sai dai kash, wuƙar na gab da kaiwa kansa batare daya fargaba dan yayi kamar zai wucene Raudha
tazo ta tare yankan ya sameta a cinyarta sakamakon ɗan tsallen da tayi nason cimmasa.
Wata irin ƙara ta saki da damƙe cinyarta da hannu guda ɗayan kuma ta damƙo rigar jazuga dake son
sake kaima Alhaji Hameed Taura wani yankan ganin wannan Raudha ta tare. Kusan duk wanda ke a kusa
da su a wajen sai da ya juyo, a take kuma duk akayo kanta. Inda Alhaji Sammani yay azamar janye Alhaji
Hameed Taura dan bashi kariya daga yunƙurin saurayin a karo na biyu. Hakanne yasa saurayin fincike
rigarsa daga hannun Raudha datai ƙasa zata faɗi ya arta cikin na kare (gudu).
Da sauri Alhaji Hameed ya kai hannu ya riƙo Raudha jikinsa na rawa. Dan duk mai hankali ko ba'a
masa bayanin komaiba zai fahimci abinda yay shirin faruwar. Sai dai kafin ma kowa ya nema ba'asi wani
yaro da bazai gaza shekaru goma sha uku ba yake faɗin duk abinda ya gani. Dan kuwa akan idonsa
Raudha taima Alhaji Hameed Taura garkuwa daga suƙar wuƙar saurayin.
Cikin ƙanƙanin lokaci ahalin Alhaji Hameed Taura suka zagaye wajen, ga securitys da ƴan agaji suma
duk sun iso. Duk mai tausayi sai ya zubarma Raudha hawaye ganin irin mugun yankan da saurayin yay
mata a cinya, dan ma ansa abu an yane ƙafar dan har rigar ya tsarge. A sume take jikin Alhaji Hameed
Taura dake cikin matsanancin tashin hankali. Musamman yanda Yasmin tazo ta faɗa jikin Raudha tana
kuka da girgizata.
Isowar Ambulance ɗin da ake jirace tasa mutane darewa ma'aikatan asibitin suka iso wajen da keken
ɗaukar mara lafiya. Da taimakon Alhaji Basheer Hameed Taura da shima jikinsa ke rawar tashin hankalin
abinda yaso samun mahaifin nasa aka ɗora Raudha bisa keken har cikin Ambulance ɗin.
Daga ahalin gidan Taura har su aunty Hannah kaiwa da komowa kawai suke na tashin hankali a ƙofar
ƙayataccen asibin na musamman da aka kawota. Wanda tabbas badan dalili ba ko katangarsa bai zama
lallai Raudha ta taɓa taɓawa ba harta ƙare rayuwarta. Da farko ƴaran gidan Taura hankalinsu yafi tashine
akan jin kakansu aka kawoma harin ALLAH ya tsaresa. Sai da sukaga hankalin Pa ɗinsu da kakan nasu su
kuma akan Raudhan yake sannan suka ɗan koma jimantawa. Koda za'a kawo Raudha asibitin badan
securitys da ke biye dasu har nan ba da gida zasuyi wucewar su. Har mamakin yanda Bappi da Pa suke a
ruɗe sukeyi, sun san yarinyar tayi ƙoƙarin kodan jarumtar da tayi na tarar wannan azaba. Sai dai mafi
yawansu sunaji a ransu tayine dan neman suna ko kuɗi ko wani abu daban koma tare take da saurayin.
Dan sun san haka kawai dai mutum bazai tarema wani mutuwa ba babu dalili, ballema ƙaramar yarinya
irinta. Wasu ko a cikinsu gani suke koma bakin saurayin da Raudha ɗaya ne, maybe akasi aka samu
kawai, ko kuma ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya.
To koma dai miye Alhaji Hameed Taura da ɗansa Alhaji Basheer Hameed Taura su ba haka bane a
nasu zuciyar. Ɗunbin tausayine na Raudha da jinjinama ƙundunbalarta a ransu, sai fatan ALLAH ya bata
lafiya da taraddadin wanene ya aiko saurayin ga wannan aikin? Dan kuwa dai cikin hayaniyar mutane ya
ɓace ɓat, har suka baro wajen securitys na nemansa ne amma babu alamar zasu gansa.
Aunty Hannah da su Fatisa na rakuɓe a gefe suma rayukansu fal mamakin abinda ya faru. Dan sam
babu wanda ya kula da sanda Raudha ta tafi bama Taura kariya sai ƙararta sukaji, sai ko sauran bayani a
bakin mutane da suka tsinta. Yasmin dake kuka Alhaji Hameed Taura yazo ya durƙusa gabanta, duk da
tsufansa da matsayinsa bai dubaba. Yasa hannayensa biyu yana share mata hawayenta. Cikin lallashi
yace, “Minene sunanki?”.
“Yasmin!”.
“Oh mai sunan larabawa to kukan ya isa haka ok? Kima aunty addu'a zata tashi lafiya kinji!”.
Kanta ta jinjina masa tana jan tagwayen ajiyar zuciya. Tausayinta ya kamashi matuƙa. Ɗunbin
kamannin daya gani tsakaninta da mara lafiyar ya sashi hasashen ƴar uwartace. Hannunta yaja ya zaunar
a kusa da shi yana kai kallonsa ga Muneera data koma can gefe tana waya kamar bataso a jita, da alama
dai wani take sanarma abinda ya faru. Ya san kuma bazai wuce mamansu Gimbiya Su'adah ba. Dan tun
ɗazun yakejin kira na shigo masa waya ya tabbatar Anne ce amma bai ɗauka ba. Yasan dai zuwa yanzu
labarin abinda ya faru ya karaɗe kowacce kafar yaɗa labarai abinka da babban mutum.
Ko wane gidan tv ka kalla daga nuna sallar idi sai zancen an kaima Alhaji Hameed Harith Taura hari a
filin idi. Yayinda hoton Raudha na kwance cikin jini a hannunsa shima keta kai kawo.
Babu yanda Alhaji Basheer baiyi Bappi ya koma gida ba amma yaƙi, ya tabbatar masa bazai iya barin
wadda ta fansar da lafiyarta a gareshi cikin wannan halin ba ya iya komawa gida ya samu nutsuwa. Dole
ya ƙyalesa har lokacin da doctors ɗin dake tare da Raudha suka fito suna sanar musu Alhmdllh ta
farfaɗo. an kuma mata ɗinki a wajen tare da alluran kariya daga gujewa wasu cututtukan. Domin a
bincikensu sun gano jikin wuƙar akwai dafin maciji.
Wannan abu ya sake tayarma da Alhaji Hameed da zuri'arsa hankali. Dan tabbas da an samesa babu
makawa zai iya rasa ransa kodan yanayin jikin tsufa dake tare dashi..
*__________________________*
“Sai da nace maka yaron nan bazai iyaba Mr JK amma ka dage akan ƙwararrene ta hanyar wannan
aikin”.
Ɗan takarar shugaban ƙasar NAYA a jam'iyyar adawa ya faɗa cikin ɗunbin tashin hankali da ruɗani
yana nuna mutumin dake daura dashi a ƙayataccen falon na alfarma. A tsakkiyar falon kwanikane
barbaje na abincin salla, sai sauran mutane uku dake ta gefen hannun haggunsa suma bisa kujerun
rayukansu duk a ɓace.
Wanda aka kira Mr JK ya girgiza kansa cikin takaici shima yana faɗin, “Karkaga laifina Engineer. Ku
kanku kunsan badan yarinyar can data bashi kariyaba babu shakka sai aikin yaron ya tafi dai-dai, sai
yanzu na sake tabbatar da Alhaji Hameed Taura ya wuce ifiritu sai dai hatsabibi. Duk yanda muke
tunanin cimmasa cikin sauƙi abune mai wahala”.
Cikin sauran mutane ukun ɗaya ya amshe da faɗin, “Tabbas abune mai wahala, sai dai ya kamata
musan yarinyar nan ƴar uban wacece ne? Sannan minene dalilinta na bashi kariya?.”
“Wannan yanada muhimmanci Alhaji Sale Sukini, sai dai babban mai muhimmancin shine Alhaji
Hameed. Domin wannan abun daya faru babu abinda zai ƙara masa sai farin jini ga jama'a. Ka duba kaga
cikin ƙanƙanin lokaci kowacce kafar watsa labarai data yanar gizo ta ɗauka. yaya kuke tunani idan rana
tsaka ya fito da manufarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar NAYA kuma?”.
“Kuma gaskiya fa maganarka nakan hanya Alhaji Badamasi. Domin barin Alhaji Hameed Taura a
raye tamkar hana yuwuwar nasararmuce. Babu yanda zamu haɗa takara da shi a dubemu a ƙasarnan, su
kansu abinda suka fahimta kenan shiyyasa suka jawoshi ya hau kujerar dan sauran da suka nuna sha'awa
a jam'iyyar tasu duk ruɓaɓɓune, babu wanda zai iya kawo kujerar. Shiko duk da bawai siyasar ya bama
ƙarfi ba suna cewa gashi jama'a zasu amsa”.
Duk da ac dake aiki a falon hakan bai hana Engineer zame hularsa ya hau fifita ba, dan wata irin zufa
ce ta ruɗani ke karyoma duka sassan jikinsa. Ya tabbatar duk abinda abokan nasa suka faɗa shine
gaskiya. Shiko a yanzu babu abinda yake buri da fata sama da shugabancin ƙasar NAYA. yayi shekaru
goma cif yana mulkin bisa muƙamin gwamna. Yaji daɗi sosai ya koma a kujerar majalissa itama shekaru
biyar kenan, yanzu kuma burinsa yakai ga kujerar daga ke babu wata. A da hankalinsu kwance yake da
hangen nasara saboda waɗanda suke hasashen jam'iyyar mai mulki zata bama takara duk bazasuyi
armashi ba. Sai dai labarin daya zo musu sati kusan guda kenan akan zaman shugaban ƙasa da Alhaji
Hameed Taura da kowa ke tunanin takara sukeson bashi ya ɗaga musu hankali. Domin kuwa a majiya
mai ƙarfi sukaji hakan daga bakin wani munafikinsu dake cikin mulkin na shugaban ƙasa a yanzun. Sun
yarda da shine bisa dalilin ba yaune karo na farko daya kawo musu labariba kuma ta tabbata daga fadar
shugaban ƙasar na NAYA.
Zaman sake sabon ƙulli sukai akan Alhaji Hameed Taura da baisan sunayi ba ma....
*_Tofa maƙiya ta ko ina🤔_*
*_GOVERNMENT HOUSE_*
Kamar yanda abokan adawa kecan suna tattaunawa anan fadar ta shugaban ƙasar NAYA ma
hakanne. Dan kowannensu na kallon abinda ya farunne ta fuskar siyasa. Alhaji Hameed Taura mutumin
kirkine da kowa ke yabon halayensa tun ƙuruciya. Dan ko lokacin daya ɗan fara bayyana kansa a siyasa
mutane ƙalilanne suka soki hakan.
Su kansu rayuwar Alhaji Hameed Taura bawai damuwarsu bace. Sai dai basa buƙatar rasata a yanzu
har sai sun cimma nasu burin sannan. Dan haka zasu sake tsayawa tsayin daka wajen ganin sun bashi
kariya har su tsallake.
Duk da tare shugaban ƙasa yay salla da Alhaji Hameed Taura a babban masallaci kuma har abin ya
faru bai koma gidaba hakan bai hanashi sake sabon shiru shi da tawagarsa suka nufi asibitin da aka kai
Raudha ba. Dan labari ya samesu cewar Alhaji Hameed Taura na asibitin. Dolene suma suje su nuna
jimaminsu da bama al'amarin muhimmanci tunda shima ya ɗaukesa da girma.
Cikin ƙanƙanin lokaci asibitin ya ƙara samu tsatstsauran tsaro a dalilin isowar shugaban ƙasa da
tawagarsa. Hakan bai bama kowa mamaki ba saboda sanin amintakar dake tare da shugaban ƙasar da
Alhaji Hameed Taura. Dole aunty Hannah ta ɓuya dan bata buƙatar shugaban kasa yasan tanada alaƙa da
Raudha a yanzun.
Bayan sun duba Raudha dake cikin ƙyaƙyƙyawar kulawa shugaban ƙasa ya tilasta Alhaji Hameed fitowa
suka ɗunguma zuwa Taura house tunda jikin nata Alhmdllh. Da wannan damar suma sauran yaran duk
suka gudu gida tunda daman zaman kakansu sukeyi anan ɗin. Sai dai anbar Raudha cikin tsananin tsaro
da kulawa ta kowanne fanni. Ga ƙyaututtukan maƙudan kuɗaɗe da waɗanda suka rako shugaban ƙasa
duk sukai mata. Sai a lokacin su Aunty Hannah suka sami damar shiga suka dubata da ƙyau suma. Dan
ɗazun Alhaji Hameed ne kawai ya shiga da Pa.
Sun tausaya mata ƙwarai da gaske, dan ƙafar tata ta matuƙar kumbura sai ma ratayeta akai jikin wani
ƙarfe. Barci takeyi ga jinin data zubar ana ƙara mata. Kusan mintuna sha biyar akace su fito dan ba'a
buƙatar kowa ya zauna da ita saboda gudun abinda zaije ya dawo. Hakan yasa dole Aunty Hannah ta
kwashi su Fatima suka koma gida suma. Dan tun ɗazun dama Asabe ke kira da wayar hajiyar birni tana
kuka akan su sanar mata idan Raudha ta rasu ta haƙura kawai. Dan duk wanda yaga Raudha a hoton
dake yawo babu tantama zai ce ta mutu ne, musamman yanda jini yay faca-faca a jikinta cikin ƙanƙanin
lokaci. Danma baƙar rigace a jikin, sai dai adon farin zare da akai mata yasaka jinin bayyana ga idanun
mutane..........✍
*_Tofa wannan fa shine ake kira ƙaddara ta riga fata. Su aunty Hannah na neman ƙulla hanyar dalili, ga
dalilin wanda ya fisu sanin gaibu shi ya ƙulla ta hanyar da basuyi zato ko tsammani ba. Masu karatu yaya
za'a kwashe kenan to?🤔_*
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_Episode 12_*
..........Duk yanda ƴan jarida suka so ɗaukar wani rahoto bayan wanda aka gani a filin idi hakan ya gagara.
Dan an toshe ko'ina da zai basu damar ma sake ganin Raudha ɗin. Koda Alhaji Hameed da shugaban ƙasa
kuma suka fito anso jin ta bakinsa akan wannan al'amari amma ya nuna bazaice komaiba a halin yanzu.
Dole suka barsa ya shige dan kowa yasan shiɗin kaifi ɗaya ne. Idan yace e to lallai e ɗin ce. Idan kuma ya
ce a'a baya canja ra'ayi daga a'a ɗin tasa..
Na farko gidan Taura. Dan duk yanda suke baje kolin farin ciki da gagarumin biki a shagalin kowace
bikin salla wannan karon sai armashin nata yay ƙaranci saboda jimami na abinda ya kusa faruwa.
Ɓangare na biyu gidan su Raudha musamman Asabe da ƴan uwanta su Fatisa. Duk da suma dai su
Hajiyar birni hankulansu ya tashi, sai dai wani sashe na zuciyarsu abin ya musu daɗin. Dan koba komai
suna kallon abinda Raudha ɗin ta aikata tamkar wani silar samun arziƙinsu ne a wannan gaɓar. Daga
hajiya mama har Hajiyar birni sai wani nannan suke da Asabe da ƴaƴanta a wannan yini. Ana kuma
lallashinta akan ta kwantar da hankalinta ta cire damuwa Raudha na samun dukan kulawa.
Ɓangare na uku shine su Mr. JK da rashin nasara ya jefa rayuwukansu cikin ɓacin rai da taraddadi na
ƙaulani. Sai faman tsugunne-tsugunne sukeyi na sabon shiri duk da kuwa bayan azhar suna cikin tawaga
ta farko data isa gidan Taura domin kai jaje kamar yanda manyan ƙasar da ƴan siyasa keta faman yi.
Wasu kuma ta waya suke kira suna jajantawa sakamakon ba cikin Bingo suke ba.
Na ƙarshe shine gidan gwamnati da al'amarin nasu ya rabu biyu. Kason farko shugaban ƙasa da
abokansa su Alhaji Yaro glass. Kaso na biyu first lady da aunty Hannah da komai ya basu mamaki. Sun
riga sun gama tsara yanda haɗuwar Raudha da Alhaji Hameed Taura zata kasance sai gashi ALLAH ya
sauƙaƙa musu ta inda basuyi zato ko tsammani ba. Duk da abun ya ɗan ruɗasu sun shiga matsanancin
farin ciki dan gani suke komai zaizo da sauƙi. First lady zata ƙarasa sauran aikin na ɗora shugaban ƙasa
akan hanyar da zai fargar da Alhaji Hameed haɗa alaƙar auren Raudha da Ramadhan....
(Tofa masu karatu. Yaya kuke ganin hakan zata farune bayan shi uban gayyar da aketa wannan
tsugunne-tsugunne dominsa ma yana can wata ƙasa hankalinsa kwance batare da ya sani ba? Kumuje
zuwa dai muga yanda zata kasance🏃.)
Duk wani cikakken musulmi wannan ranace da bata ɓoyuwa a garesa a duk inda yake a faɗin
duniya. Sai dai ƙarancin yawan mabiya addinin musulinci a wajen ya rage masa armashi da jin daɗin
wannan ranar. Amma dolene zuciyarsa ta kasance cikin shauƙi da godiya ga UBANGIJI daya sake zagayo
masa da ranar.
*Broadway street* anguwace dake a cikin birinin new york dake ƙasar amuruka. Layine mai tarin
abubuwan birgewa da ƙayatarwa kamar yanda mai karatu yasan turawa da gyara muhalli. A katafaren
block dake ɗaya daga cikin gine-gine na musamman a broadway street gida mai lamba goma sha tara
Ƙyaƙyƙyawan farin mutum amma baƙar fata mai tarin kwarjini da cikar kamala ne zaune bisa sofa a falo.
Falo ne haɗaɗɗe da bai cika yawan tarkace ba ko hargitsi.
A kallo ɗaya zaka iya kiransa da tuzurun saurayi dan shekarunsa a ƙala zasu iya tasarma 35. Sanye
yake cikin farar ɗanyar shadda data samu aiki na musamman da bazaka iya mata kallo ɗaya ita da
mamallakinta ka ɗauke kai ba. Sai dai duk da tsadarta da ɗaukar idon da takeyi bai hanata yamutsewa ba
saboda a yanyin dayay zaman bisa sofa. Gaba ɗaya hankalinsa kacokan ya tattara ne ga television ɗin
dake a falon, inda yake kallon tashar dake da alaƙa da ƙasarsa ta NAYA. Bakomai ya sakashi nutsuwa ga
tvn ba sai bikin salla da na idi da aketa nunawa na ƙasar tasa dama sauran ƙasashen duniya.
Duk da fuskarsa bata nuna shauƙin kallon ko zumuɗi ba kwayoyin idanunsa sun gama fallasa asirin
zuciyarsa baki ɗaya. Dan yanda ya tattara dukan hankalin nasa ya isa shaidar komai na ƙayatar da shi.
Basai ance maka ƙyaƙyƙyawa bane, fatarsa kawai ka kalla kasan shiɗin mai ƙyaune. Dan mutane da yawa
kan kira mai irin yanayinsa da suna black american duk da kuwa a ƙasarsa fari yake kai tsaye. Yana da
yanayi mai sanyi a fuska tare da duk wani ado dake ƙawata fuskar gayun wannan ƙarnin. Abu mafi
ɗaukar hankali dake tattare dashi gyararriyar sumar kansa da tasha wani salon aski na musamman duk
da kai tsaye bazamu kirata mai taushi da laushi irin ta larabawa ko turawa ba. Dan kuwa a tsaitsaye take
cunkus kamar yanda akasan sumar baƙin mutum, sai dai ɗunbin gyara da kuɗaɗen da take lashewa yasa
tazam mai ɗaukar hankali da birgewa ga mai kallo. Sai girarsa ta haggu da akai mata wani salon tsagu da
kan iya saka mara fahimta ɗaukar gayune yasa shi tsagawa, sai dai sam ba haka bane tabon raunine a
wajen da ya samesa tun yana primary. Sai ga tabon har girmansa bai dishe ba. Batun yanzu ba mutane
da yawa sunsha ɗauka an kwashe gashin wajen ne tamkar tsagar kitso kawai dan gayu. Kowa yasan
abune mai sauƙi yanzun kaga lips ɗin gayu pink kodan abubuwan da ake tu'ammali dasu domin yin
hakan.
Baza'a kirashi siriri ba, ba kuma za'a ce dashi mai ƙiba ba. Kawai dai mutum ne tsaka tsaki
musamman daya kasance yana tu'ammali da inginan motsa jiki.
Karon farko ya sake waro manyan idanunsa da ada suke a ɗan lumshe bisa television ɗin sakamakon
abinda ya gani. Cikin sassanyar muryarsa mai ɗan kauri da buɗewa ya furta “What?!!” yana zabura gaba
ɗayansa tsaye bisa ƙafafunsa. Dan ba ƙaramin harbawa ƙirjinsa da ƙwaƙwalwar kansa sukaiba a lokaci
guda saboda tozali da abinda ya faru ga kakansa a filin idi.
*_Ramadhan B. Hameed Taura_*. Ya matsa gaban television ɗin da sassarfa dan ji yake tamkar
idanunsa basa gane masa komai daƙyau. Tabbas babu tantama hakanne, dan kuwa ganin mahaifinsa da
ya iso wajen a kiɗime da sauran ƴan uwansa mata ya sake tabbatar masa da komai gaskiyane. Da sauri
ya koma gaban sofa ɗin da yake zaune a da ya sungumi ɗaya daga cikin wayoyinsa uku dake a saman
table. Cikin ƙwarewa ya far sarrafata tare da kutsawa cikin shafukansa na sada zumunta.
Duk da ya daka barkono daga ƙasar haihuwar tasa duk da begen da ahalinsa ke masa yaƙi saurarensu
hakan bai hanashi dinga bibiyar al'amuransu ba batare da sun sani ba. Dan kuwa ya ɓoye kansa daga
yanda zasu iya ganosa kai tsaye, ainahin shafukansa da suka sani kuma duk yayi blocking nasu babu mai
ganin abinda yakeyi sai dai da salon sabon suna da bazai gane ba.
A babban shafin sada zumunta na watsa labaran ƙasar ya fara cin karo da ainahin bayanin abinda ya
farun, harda gajeren video a shafinsu na istagram. Wani irin tsuma jikinsa da zuciyarsa keyi dan kuwa
tamkar an tuna masa da wata rana data kasa shuɗewa a tarihinsa. Ranar da tsayawar numfashinsa ce
kawai shima zata iya ɓaddata a cikin jerin abubuwan da suka zauna masa raɗam a cikin ƙwaƙwalwa.
Kakarsa (Anne), kakansa (Bappi), Mamansa (Gimbiya Su'adah), Babansa (Alhaji Basheer Hameed Taura)
duk suna raye a duniya. Bai taɓa ɗanɗana ɗacin mutuwar wani makusanciba a duniya sai akan matarsa
masoyiyarsa da ƴarsa gudan jininsa. Shiyyasa yake matuƙar jin ɗunbin raɗaɗi da zafin gusawarsu a
duniyarsa ta hanyar da bazai taɓa yafema wanda ya ƙirƙiretaba duk da yasan tana cikin ƙaddararsu.
“Bappi!!”.
Ya faɗa cikin yanayi najin ƙaimi da tasowar mazantaka. Haka kawai zuciyarsa ke raya masa wanda ya
halaka masa Amnah da Haseenah ne suke farautar Bappin sa. Sai ma ƙasan ransa ke tunzurasa da koma
dai an samu galabar cutar da bappin ne aka ɓoye. Karon farko da tun bayan barowarsa ƙasar NAYA
shekaru biyar kenan yakejin tamkar ya rintse ido ya gansa a ciki. Duk da halittarsa ta nutsuwa da cikar
kamala hakan bai hana idanunsa nuna birkicewar da ƙwaƙwalwarsa ke neman yi ba. Da sassarfa yay jifa
da phone ɗin tasa bisa sofa ya nufi dogon glass ɗin da aka raba tsakanin falon da bedroom ɗin barcinsa.
Kasancewar yaja labulen gefe da gefe yasa ake iya hango gadon ɗakin da ya gama haɗuwa shima.
Da wani irin gudu ƙofar glass ɗin ta zuge kanta gida biyu saboda yanda ya danna maɓallin makunnar
da ƙarfin tuwo tamkar itace tai laifin....
Wani irin ruri ɗaya daga cikin wayoyinsa keyi na neman agaji alamar kira, sai dai duk da jinta da
yakeyi baiko nuna alamar zai fito daga bedroom ɗin ba dan yasan wanene ke kiran nashi.
Still kira ya sake shigowa a karo na kusan biyar. Ɓaro-ɓaro sunan A.J ya bayyana a kan screen ɗin. A.J
abokine ga Ramadhan wanda shima mazaunine aƙasar ta amuruka. Kamar yanda suka saba haɗa liyafar
cin abinci a kowanne ranakun bikin salla babba da ƙarama wannan karon ma hakane. Maƙudan kuɗaɗe
suke haɗawa su ƙayata zaman nasu da shi batare da jin hakan a jikinsu ba dan kowa ya tara.
Mafi yawansu sunada mata da ƴaƴa. Harma da masu manyan ƴan mata da samari. Dan kuwa akwai
sa'oin Alhaji Basheer a ciki harma da tsoffi da ƙaddarar zama ta zaunar a ƙasar tsahon shekaru. A irin
wannan zaman ƴammata da yawa sunsha yima Ramadhan tallar kansu amma baya kulawa. Dan ko
fuskar a tunkareshima baya basu balle suyi tunanin dacewa. Manyan ciki kuma kan dunga kwaɗaita
masa maganar sake aure amma baya kulawa nan ma.
Tunda ya fara riskar bikin salla a ƙasar bai taɓa missing wannan zaman ba, dan yana matuƙar ɗebe
masa kewa sosai akan ahalinsa. Hakan yasa rashin isowar tasa ta dami kowa har A.J ya fara danna masa
kira a jajjere. Sai dai kuma ana tsaka da haka dattijo alhaji sufyan harɗo yaci karo da labarin abinda ya
faru ga Alhaji Hameed Harith Taura a filin idi yau. Dan haka yay azamar fargar da sauran ƴan uwansa
maybe labarin ya riski Ramadhan ɗinne shima.
Dukansu sun nuna jimami, yayinda A.J da Mufeed yanke shawarar zuwa gidan na Ramadhan da suke
kira da suna Top gee dansu gani. Fitowa Sakai a cikin garden ɗin Sultana biye dasu, basu hanata ba dan
kowa yasan irin ɗunbin so da ƙaunar da Sultana kema Ramadhan ɗin duk da baya kulata. Cab suka tara
tare da sanar masa inda zai kaisu....
Fara danna ƙararrawar gidan yayi dai-dai ne da fitowar Ramadhan daga bedroom ɗauke da
madaidaiciyar bag daya haɗa abubuwansa masu muhimmanci da zai iya buƙatar amfani dasu. Ya canja
kayansa zuwa ƙananun kaya daya ɗora jibgegiyar rigar sanyi daketa maiƙo da santsi tamkar leda kalar
light blue. Sai hularta mai gashi a cin bakin baƙi tamkar kayan ciki t-shirt mai gajeren hannu da black
jeans wando. Ƙafarsa sanye cikin baƙaƙen takalma boot.
Duk da ba kwalliya yay ba hakan bai hanashi yin ƙyau ba. Baibi takan doorbell ɗin da aketa bugawaba
ya cigaba da karkashe komai na na'urar lantarki dake a cikin falon kamar yanda ya kaso na bedroom.
Da ga A.J har su Sultana binsa suke da kallon mamaki dai-dai sanda ya buɗe ƙofar. Bakinsa da
gashin gemunsa kawai suke iya gani zuwa rabin kumatunsa, dan yaja hular rigar ne ya rufe masa rabin
fuska tare da toshe idanunsa da glass mai nuna blue a jiki.
Mufeed ya faɗa yana ɗan kai hannu ya dafa kafaɗar Ramadhan ɗin dake ƙoƙarin fitowa batare da ya
damu da hanin nasu ba.
Ƙarasa fitowa yay yana zuge zip ɗin bag ɗin hannunsa mai kama da school bag da faɗin “Zan wuce
NAYA? Akwai matsala”.
Atare suka haɗa baki wajen ambaton “Matsala kuma? Miya faru?”. Dan sunfi son suji idan da gaske
ne kar suyi katoɓara. Hannunsa na haggu ya ɗora saman kansa ya zame hular tai baya ya saketa bisa
dokin wuyansa yana ƙoƙarin saka lock jikin ƙofar duk da baya tunanin zai jima acan inhar ya iske komai
lafiya.
Ƙoƙarin sake maimaita tambayar tasa A.J yayi, bai tankashiba yanzu ma sai da ya kammala rufe
ƙofar ya rataya hannun bag ɗinsa ɗaya a hannun haggunsa, hularsa yaja saman kansa tare da ɗan
bubbuga kafaɗar A.J ɗin. “Na riga nayi Booking flight, kuma gab yake da tashi zamuyi waya”. Daga haka
yay gaba a binsa.
Hankali tashe ganin yanda yake komai cikin zafin nama yasa Sultana ƙoƙirin binsa zata kira sunansa
Mufeed ya riƙo hanunta. Kansa yake girgiza mata alamar karda ta tsaidashi ta barsa. A take hawaye suka
ciko mata idanunta da take bin Ramadhan dake ƙoƙarin shiga cab daya tsayar da kallo. Kamar walƙiya
cikin ƙanƙanin lokaci cab ɗin ta ɓacema ganinsu abinka da lafiyayyen titi duk da dokar ƙasar akwai
ƙa'idar da driver kanbi yayin tuƙi...
Anne dake zaune gefen Alhaji Hameed ta faɗa cikin tausasa harshe da nuna kulawa. Ganin baida
alamar tankawa ta cigaba da faɗin, “Mu godema ALLAH da ƙudirin koma wanene bai cikaba duk da wani
ya cutu a dalilinmu. Haka rayuwa take cike da jarabawa. Talaka mai nema cin yanzu da anjima yana cikin
jarabawa babba dake taka rawar gani wajen iya wargaza komansa. Sannan ni'imar arziƙi ga masu arziƙi a
lokuta da dama ɗaukakar a garesu itace gagarumar jarabawarsu. A koda yaushe cikin ɓoye kansu suke,
badan komaiba sai don gudun a cutar dasu ko makamtan hakan, dai-dai da masoyansu na gaskiya taka
tsantsan suke wajen kokwanton neman tabbaci koda kuwa sunada yaƙini masoya da maƙiya zasu iya
shiga a jarabawarsu. Dattijo bamu isa canja ƙaddara ba, dan haka kalmar da tafi cancanta a bakunanmu
a yanzu itace *_Alhamdulillahi_*. Sai fatan ALLAH ya bama yarinyar lafiya itama”.
Sosai kalamanta suka sanyaya masa ransa. Yaja numfashi mai nauyi da sakin guntun murmushi.
Baki ya buɗe da niyar cewa wani abu maganar tasa ta maƙale a maƙoshi saboda abinda idanunsa suka
hango masa a bakin ƙofar katafaren falon nasu. Saurin maida idanun nasa yay akan agogo tamkar wanda
akaima shune da mummunan abu. Ƙarfe goma na dare da wasu mintuna. Tunda suka samu gidan nasu
ya lafa da ƴan jaje da masu zuwa yawon salla sai kowa ya nutsu a sashensa saboda hadari da garin ya
haɗa na alamun saukar ruwan farko na damuna da kowa ke fata.
Sake maida idanun nasa yay ga ƙofar ransa fal tunanin gizon da idanun suka saba masa ne na tsananin
bege da kewar jikan nasu duk da fuskarsa a rufe take da hular rigar sanyin jikinsa hakan bai hanashi
ganesa ba. Hakan yasa itama Anne duban inda ya ƙurama idanun baki wagame tayi........✍
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan🔥😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_Episode 13_*
...........A hankali Ramadhan dake a bakin ƙofar ya cigaba da tako tsaftataccen marble's ɗin falon, dan ya
cire takalmansa tun a corridor ɗin daya raba falon farko da wannan falon, sai safa baka kawai. idanunsa
akan kakannin nasa. Tafiya yake dai-dai da hurowar iskar hadarin dake kaɗa labulolin falon tare da
walƙiya tamkar yana taku a saman kaɗawar tata ne. Harya ƙaraso gaban Baffi basu iya sun motsa ba, ya
durƙushe gaban bisa gwuyawunsa tare da sauke jikkar kafaɗarsa. Hannu ya kai bisa kansa a hankali yay
baya da hular nutsatstsiyar fuskarsa mai cike da kwarjini da cikar haiba ta bayyana.
A hakan ma bai iya dubansu ba, dan har yanzu idanunsa sakaye suke da gilashinsa mai nuna blue.
Maimakon ya zaresa sai matsawa yay ya ɗora kansa bisa cinyar Bappin yana sakin wasu tagwayen ajiyar
zuciya da lumshe idanunsa masu nauyi da fargaba.
A ɓangaren Pa ma yau tare yake da gimbiya Su'adah dan girkintane. Tsananin gajiyar dake tare da shi
ta kaiwa da komowar da yayi yau kashi-kashi ya saka shi yin wanka da ruwa mai ɗumi da taimakon
gimbiya Su'adah. Fitowarsu kenan a toilet ɗin tana tsane masa jiki da towel ƙarami. Ya kai dubansa ga
labulen windows da aka ƙawata adon bedroom ɗin nasa da su. Yanda iska ke kaɗasu abin sha'awa ga
mai kallo. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke batare daya ɗauke kansa a jikin labulen ba ya fara magana a
hankali.
“Da ace Bappi zai yadda da ya bar maganar nan ta takara. Saboda na tabbatar abinda yaso faruwa a
yau yanada alaƙa da wannan siyasar da bana hango wani amfaninta a garemu ko kaɗan....”
Wani irin bugawa ƙirjin gimbiya Su'adah yayi. Domin ba ƙaramin ƙwallafa rai da ƙara jin alfahari
takeba akan batun fitowa takarar tilon ɗanta namiji da Bappi ya kwaɗaita musu tun daren jiya. Zata iya
cewa dukkan farin cikinta na yau da murmushinta yana da alaƙa ne da hakan kai tsaye. Idan ko mijin
nata ya cigaba da nuna adawarsa akan hakan ko kokwanto lallai tana cikin ɗunbin rashin nasara kenan.
Dan kuwa Bappi zai iya saurarensa akan hujjojinsa inhar ya samesa da batun........
Pa ya faɗa cikin katse mata dogon tunanin data faɗa. Numfashi taja mai ƙarfi a ɓoye da ƙaƙaro
murmushi tana kaiwa zaune a gefensa. Maɓallan rigar barcinsa dake ajiye gefe take ɓallewa bayan ta
ɗakkota a hannunta.
“Ba shiru naiba Daddyn Ramadhan, nima wani tunani nakeyi game da maganarka. Tabbas zancenka
nakan gaskiya, dan ni kaina harna fara jin tsoro. Idan har za'a iya harar mana Bappi irin haka akan
wannan batun shi kuma Ramadhan dazai tsaya takarar yaya zata kasance kenan?”.
“Abinda nake hangowa kenan Su'adah. An illata mana yaro a baya batare da mulki ba, har takai ga
ya nisancemu a yanzu saboda tabon da aka bar mana a zukata ya kasa barin ruhinsa. Inaga yanzun da
ake son ɗora masa nauyin abinda ya girma shekarunsa. Suma da suke manya masu shekaru basu tsira ba
balle shi da dudu shekarunsa talatin da biyar. Ko'a tarihi babu wani shugaban ƙasa a wannan ƙasar ta
NAYA da akayi mai ƙarancin shekarunsa fa....”
“Ƙarancin shekarunsa basu bane damuwar Dadyn Ramadhan. Dan kuwa koba komai anzo da wani
sauyine da al'ummar ƙasar NAYA zasuyi farin ciki da shi. Mun cancanci mu damu da gudun abinda zaije
ya dawo, sannan kuma ta wani ɓangaren yanada ƙyau muyi dubi da talakawa masu buƙatar irin
Ramadhan ɗin a yanzun, domin da gaske ƙasar NAYA irin Ramadhan take buƙata da shekarunsa. Badan
shugabannin baya sun gaza ba, a'a suma sun taka irin rawarsu kuma munji daɗin ƙoƙarinsu da yaba
musu, dan mulki ba abune na wasa ba. Wanda ke gefe bai isa sanin wahalarsa ba sam. Dan shi daɗin
kawai yake hangen maiyinsa na ciki yake, sai dai abunda bamu saniba wahalarsa itace kaso 99. Kaso
ɗaya kacal ɗin nan shine kawai jin daɗin ga ma'abota mulki. ALLAH ya sakama shugabanninmu da alkairi,
ya yafe musu kurakuransu yay riƙo da hannayensu. ALLAH kuma ya basu ikon sauke nauyin al'umma
dake kansu”.
Numfashi ya sake saukewa da faɗin, “To amin ya rabbi. Amma duk da haka ina jin tsoro Su'adah”.
“Karkaji tsoro Dadyn Ramadhan. Addu'a kawai zamu duƙufa yi, tare da tunanin ta hanyar da zamu
maido Ramadhan gida a yanzu batare da mun sake ɗorama Bappi wani nauyin ba”.
“Eh kema kinyi batu na hankali. Inko hakane barama na leƙa bappin dan na manta ma ban sanar
masa batun kammala fidda komai na zakkar ba yau, duk mun wuni cikin rashin kwanciyar hankali ba'a
fitarba kamar yanda aka saba”.
Miƙewa tai tsaye tana taimaka masa ya saka jallabiya fara bayan ta ajiye rigar barcin gefe, dan tasan
bazaije sashen su Anne da kayan barci ba. Hakan al'adarsace da girmamawa ga mahaifan nasa batun
yanzu ba. Turare taɗan fesa masa sannan ya fice.
Gimbiya Su'adah ta sauke nannauyan numfashi a ƙasan ranta tana godema ALLAH daya kasance
yau girkintane har taji batun nan taima tufƙar hanci da wuri. Taya zata amince maganar nan ta koma ciki
bayan ta fito. Da farko bataƙibama ace shi Alhaji Basheer ɗinne zai hau shugaban ƙasar ba. Dan koba
komai darajarta zata ƙaru, ta fito daga gidan mulki mafi daraja da kima, gata tana aure a gidan dukiya
sahun farko a ƙasar NAYA dama yankin Africa baki ɗaya. A ƙarshe a kirata first lady. Lallai data amsa
sunanta *_SARAUNIYA SU'ADAH_* ba gimbiya Su'adah ba. Amma ko'a hakan ma ba komai baneba, dan
samuwar mulkin ga gudan jininta wani abune mai girma da za'ayi ƙarnuka da zamanai da bazai mantu
ba. Sannan dole ne a kirata uwar shugaban ƙasar NAYA. Dan haka itace da kanta zata zaɓa masa matar
aure dai-dai da ra'ayinta. A wannan karon bazata sake sakaci irin na farko ba akan matar da Ramadhan
zai aura.
Turus Pa yay tare da ƙoƙarin haɗiye sauran sallamarsa a maƙoshi duk da ta kusan gama fita a
harshensa. Ba komai ya jawo hakan ba sai tozali da yay da gudan jininsa zaune gaban Bappi da Anne.
Gaba ɗaya fuskar tsoffin nasa babu alamun fara'a, yayinda Ramadhan ɗin yay ƙasa da kansa yana
magana a kausashe mai cike da ɗaukar alwashi.
Kai tsaye ya fahimci kausasa harshen nasa nada alaƙa da abinda yaso samun bappin a yau. Sarai ya
sani basai an faɗaba, ɗansa Ramadhan mutum ne mai zafin zuciya ainun, abu kaɗan ke fusatashi ya
hargitse tamkar baisan wani abuba wai shi sauƙin kai. Amma idan ka kallesa a fuska bazaka taɓa ɗauka
ma yana magana mai alaƙa da masifa ba saboda fuskar mutane masu haƙuri da rashin son hayaniya
garesa. Sometimes idan yay abu mutanen da basu san ainahinsa ba sukance bashi bane ba, dan a
zatonsu ko yatsa ka sakama Ramadhan bazai taunaba saboda haƙurinsa da rashin son magana. Girman
kai ne dai kam kowa na masa kallon mai shi kai tsaye, koda sau ɗaya ka fara ganinsa.
Sai dai su duk sun san ba hakan baneba, Ramadhan bauɗaɗɗen mutum ne mai zafi da tsananin
ɗaukar kai (girman kai inji bahaushe😎). Tabbas baida yawan magana badan yana miskiliba, tsabar jin kai
ne kawai ke hanashi magana a lokuta da dama koda ace ya dace yayi ɗin. Tabbas anan ɓangaren ya biyo
mahaifiyarsa ƙwarai da gaske, dan saima ace ya ɗarata izza dajin mulkin a cikin jininsa fiye da ita da aka
haifa a gidan mulkin. Sai dai kuma ta wani ɓangaren yanada wasu halaye kishiyar waɗan can da zama
dashi ne kawai zai iya fiddoma wanda ya sanshi da waɗan can ɗin su.....
“Ramadhan!”.
Pa ya faɗa cikin wata irin murya mai kaushi-kaushi da ɗaci. Dan haka kawai daya tuna yanda suka dinga
bin Ramadhan akan yay haƙuri ya manta komai ya dawo ƙasar NAYA amma ya nuna musu bazaibi
maganarsuba ya shiga dawo masa a rai.
Da ga Ramadhan har su Anne juyowa sukai suna kallon Pa ɗin, dan sam basuji shigowarsaba balle
sallamarsa saboda tasowar iskar hadari dake ƙaruwa.
“Pa!”.
Pa ya faɗa yana ƙoƙarin dakatar da Ramadhan daya miƙe da alamar ɗokin ganin mahaifin nasa da
zumuɗin isowa garesa, dan jikinsa har tsuma yake.
“Pa!......”
Yanda yay maganar babu wasa ya saka Ramadhan duban su bappi, kafin ya sake kallon Alhaji Basheer
Taura.
“Pa.......!”.
“Ramadhan!! Nace ka fita a gidan nan yanzun nan!. Bana son sake ganin wannan fuskar taka!!”.
Alhaji Basheer Taura ya faɗa a tsawace yana nunama Ramadhan hanyar falon.
Wata irin muguwar hajijiyace ta fara ɗibar Ramadhan. Dan dama can shi bayason ihu, musamman
idan yana akan gaɓar bacin rai tuni ake samun matsala kansa ya nema juyewa saboda tsananin yanda
ƙwalwar kansa ke kasa ɗaukar tashin hankali mai shallake tunani. Lokacin da yana yaro idan hakan ta
faru ansha cemusu yanada aljanu ne masu ƙarfi sosai. Sai dai basu taɓa yarda ba dan su sam basu cika
ɗaukar waɗan nan abubuwan da muhimmanci ba (kamar yanda kowa yasan ɗan boko🙏🏻), sai dai hakan
baya hana duk lokacin da abu ya faru makamancin matsalar ta biyo baya Anne ta zauna tai masa addu'a
a ruwa da saman kansa har sai ya samu nutsuwa sannan. Amma abin mamaki zai iya yini yana ajiyar
zuciyar wannan ɓacin ran, ko kuma ya yini a ɗaki yana barci. Sannan sai ya haɗa kwanaki biyu zuwa uku
baiyi magana da kowa ba. sai dai ya samu wajen ruwa ya zauna, ba kuma zaici abinci ba duk da
kasancewar sa ma'abocin son abinci sai Anne ta takura masa shan abu mara nauyi kamar su fura yogurt,
fresh nonon shanu ko na raƙumi da makamantansu. Dan yana tsananin son madara da dukkan
nau'ikanta a rayuwarsa. Bayan aurensa da Amnah idan ransa yay irin wannan ɓacin yakan hucene a
kanta ta hanyar yin tarayya da ita yanda zata jigata har sai an kwantar da ita a asibiti abinka da sikilla.
Dan likitocin kance ko mai lafiya akaima irin wannan kamun babu shakka zataji a jikinta balle Amnah ɗin.
A duk lokacin da fushin ya sauka yakan shiga damuwa idan ya kalli yanda ya fiddata hayyacinta. kai wani
lokaci ma har saida akai mata ɗinki tsabar lamarin Ramadhan yana bukatar addu'a🤦🏻. Amna kam tana jin
jiki da shigar Ramadhan irin wannan yanayin, sau biyu yana sakata ɓarin ciki. da tana raye na tabbatar
zatace hakan shine mafi girman tashin hankali a rayuwar aurenta da Ramadhan ɗin, shiyyasa duk wani
fushinsa take gujewar wanzuwarsa a karan kanta.
Yanda ya fara juya kai jijiyoyin na tashi sama da maƙogwaronsa dake kai kawo a wuyansa, gashin
kansa na mimmiƙewa yasa Bappi fahimtar mike shirin faruwa. Yasan Ramadhan bazaice komaiba, dan
shi mutum ne mai tsananin tsoron saɓama iyaye, shiyyasa daya dage akan bazai dawo NAYA ba a
shekaru biyar ɗin nan abun ya basu mamaki matuƙa, dan duk rintsi baya ƙetare maganarsu.
Da sauri Bappi ya girgizama Alhaji Basheer kai yana miƙewa ya riƙo hannun Ramadhan daya fara
ƙoƙarin ɗaga ƙafa yana jujjuya kansa cikin tafukan hannunsa daya riƙe kan nasa. Tuni idanunsa sun rufe
ruf saboda wata baƙar hajijiyar da yake gani falon na juya masa da wani irin shegen gudu.
Babu abinda ke maimaita kansa a kwakwalwar Ramadhan da zuciyarsa sai *_“Ramadhan!! Nace ka
fita a gidan nan yanzun nan!. Bana son sake ganin wannan fuskar taka!!”._* da Pa ya faɗa.
“Zan tafi Pa, bazan sake nuna maka fuskar nan ba nayi alƙawar.....”
“Shut up!!”.
Bappi ya faɗa da ƙaraji shima yana katse Ramadhan ɗin bayan ya fisgosa ya zube a saman kujerar kusa
da shi. Juyawa Alhaji Basheer Taura yay a fusace yabar falon, shi kansa wani irin jiri-jiri na neman fara
ɗibarsa. Sai hakan yasa yakejin yana tafiya tamkar akan iskar dake kaɗawa har zuwa sashen nasa. Bai
iske gimbiya Su'adah ba. Da alama taje shirin barci. Dan haka yay kwanciyarsa, koda ta shigo bayan
kusan mintuna talatin da kwanciyarsa bai motsaba. Hakan yasa tai tunanin ko yayi barcine. Sai kawai taja
bargo ta lulluɓa masa bayan ta rufe wasu a murafan windows ɗin dan iskar ta fara yawa.
*_WASHE GARI_*
Da mamaki kowa ya tashi yaga Ramadhan a gidan. Sai dai a yanayin da yake na hawa saman dokin
zuciya yasaka bakin yaran gidan rufewa ruf. Dan ko kallonsa kayi bakaso sake ganiba fuskar tamkar
zatayi aman wuta😜.
Gimbiya Su'adah ce kawai ya iya tankama tambayarta itama a taƙaice, dan ita firgitama tayi da
ganin nasa. Har zuciyarta na raya mata kodai da gaske Ramadhan ɗin nada aljanune wai?.
Ko amsa ɗaya bata samu daga tarin tambayoyin da take jera masa ba, sai ma miƙewa yay yana sanar
mata cewar zai koma America.
“America!”.
Ta maimaita da yanayin ruɗani da tashin hankali. ita dake murna ɗanta ya dawo gareta kuma. Kafin ta
sake cewa wani abu yayo waje. Dan dama a bedroom ɗinta ya sameta kasancewar ta duba an kammala
shirya abincin breakfast na Pa tazo dan ta shirya, sannan taje ta tadashi a barcin daya ɗan koma na safe
bayan dawowarsa masallaci.
Har ya fice a sashen baki ɗaya bata dawo hayyacinta ba. Dan da alama sumar tsaye tayi kawai.
Bappi ya faɗa idonsa akan Ramadhan daya fito daga sashen iyayen nasa a wani irin yanayi. Duk da
alamu sun nuna yayi wanka ya canja kaya hakan bai hana fuskarsa bayyana yanayinsa na jiya ba. Sanye
yake cikin wani tattausan tissue yadi da basai ance komai game kallo ba wajen hasashen irin kuɗin daya
lasa na sayensa dana ɗinkinsa. Duk da simple style ne a jikinsa hakan bai hana bayyanar tsadarsa da fitar
ɗinkin ba a bisa ƙyaƙyƙyawar ƙirarsa ta mazantaka da ƙuruciya ba, ga shi baƙi sai farar fatarsa ta sake
haskawa. Babu alamar sumar kansa ta samu gyara yau tsabar yanda ta hargitse, sai dai hakan bai hana
ƙyawunsa bayyana ba harma ya ɗauka hankalin wasu mutane koda ba kowaba.
A tunaninsa airport ɗin zasuje, kamar yanda ya sanarma Bappin yau zai koma bayan sun fito da ga
sallar asuba. Dan haka babu musu ya shige inda M. Adamu ya buɗe masa kusa da Alhaji Hameed Taura
(Bappi). A wata jiƙaƙƙiyar mota data gama haɗuwa. A tsammaninsa ƴan kayan buƙatarsa dake cikin bag
an riga an fiddo masa tuni.........✍
*_Tofa ina Bappi zai kai mana wannan young tiger ɗin mai kama da barkonon noman ranin😎🏃?._*
*_Typing📲_*
*_Episode 14_*
...........Sai da motar ta tsaya a harabar asibitin sannan Alhaji Hameed Taura ya dubi Ramadhan da ke
kwance jikin sit ido a rufe. Sai faman jan numfashi yake a gwame alamar ransa har yanzu a ɓace yake.
Sumar kansa yayma kallon second goma ya sake ɗauke kansa, batare da yace komai ba ya miƙa hannu a
booth ya ɗakko ledar dake ajiye da huluna a ciki ya duba wadda yake zaton zata dace da shigar
Ramadhan ɗin ya ɗakko. Dama shekaran jiya ya sayesu domin Ramadhan ɗin, sai dai ya mantasu ne a
motar bai kuma sake shigartaba sai yanzun.
Kari yay mata sannan ya ɗaura masa akan hannu, hakanne yasa Ramadhan buɗe idanunsa da suka
ƙanƙance da canja launinsu.
Komai baice ba ya ɗauka hular ya ɗora saman kansa kawai batare da duba tayi ko bataiba. Kai Bappi ya
ɗan girgiza da riƙo hannunsa ganin zai fita. Batare da shima yace masa komai ba ya gyara masa ita ta
zauna ɗas tamkar dan shi akayita. Sosai ya fito asalinsa na bahaushe cikakke. Wanka na ɗaukar jikin
Ramadhan ko wanne irine. Sai dai a duk lokacin da ya saka manyan kaya yakan zama babban mutum da
cikar kamalarsa ke daɗa fitowa a zahiri ga masu kallonsa. Sai kaga yayi maka wani irin kwarjini dake saka
mutane jin shakkarsa da bashi girma koda basuyi niyya ba.
Duk da ya fahimci asibiti sukazo bai tanka ba har suka shigo ɗakin da Raudha ke jinya, police ɗin da
president ya bamma Alhaji Hameed Taura biye dasu tamkar jela. Ko'a dacan da ƙuruciya Alhaji Hameed
baya son bodyguard tare da shi balle yanzu da tsufa yay masa kamun kazar kuku, yake ganin rayuwar
ƙiris ta rage masa ma.
Bappi ne kawai yay sallama a zahiri duk da yasan babu kowa a cikin. Ramadhan kuwa a saman
laɓɓansa yayi yana biye da Bappin tamkar dole. Ɗaki ne babba dake ɗauke da komai na buƙatar mara
lafiya ɗan gata. Sai Nurse ɗaya dake tare da Raudha data farka tun asubahin yau. Tun ɗazun doctor ya
shigo yay mata dukan abunda ya dace tare da dubata. Aka kuma bata abinci taci tare da magunguna.
Yanzu haka idanunta biyu tana kallon television ɗin ɗakin da ake nuna wani wasan salla na yara daya
ɗauke hankalinta, yayinda Nurse ɗin ke zaune tana faman latsa wayarta.
Nurse ɗin ta faɗa cikin ɗan rawar jiki tana miƙewa zaune. Ranta fes kamar an bata ƙyautar kujerar makka
yau gata ga babban ɗan kasuwar nan daya gawurta a ƙasar NAYA da ƙetare a gabanta. Tare da young
millioner grandson ɗin sa a gefensa. Dan fuskar Ramadhan sananniyace ga mutane sakamakon rawar da
yake takawa shima akan dukiyar tasu wajen juyata da kuma nuna bajintar taimakon talaka akan aikinsa
na lauyanci. Babban abinda ya sake bayyanama duniya fuskar tasa lokacin daya rasa matarsa sakamakon
shan guba da sukai, dan labarin babu gidan jarida da redio da yanar gizo da bai zagaya ba. Hatta da
Raudha taga labarin duk da a lokacin tana jss 2 ne a secondary.
Dan in bata manta ba alokacin har gulmar tsarin halitta da iya ɗaukar wankan Ramadhan ɗin tayi a
ranta, duk da kuwa a jikin jarida ta gani ita a wajen wata ƙawarta Rahma Salisu.....
Bappi ya faɗa yana duban Raudha murmushi na sake faɗaɗa akan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa.
Murmushin ƙarfin hali itama tai masa, dan haka kawai ita dai dattijon ya shiga mata rai. “Abba ina
kwana”.
Ta faɗa da dasashshiyar muryarta tana satar kallon Ramadhan da ko kallon ɗaya a cikinsu baiyi ba
balle ɗakin. Tunda suka shigo ya jingina da bangon farkon shigowa ya tura hannunsa a aljihu ya fiddo
wayarsa dake tsuwwa yana dubawa. Hakan yasa Raudha bata ganin fuskar tasa da ƙyau yanda ya
kamata. Sai dai ƙamshin turarensa da yanda kayan suka zauna ɗas a halittarsa yay mugun fisgar idanunta
daga kasa barin kallonsa da son tuno a inda ta taɓa ganinsa......
Bappi ya sake katse mata tunani a karo na biyu yana kallon ƙafarta da akai hanging jikin wani ƙarfe, har
yanzu a kumbure take sosai abin tausayi.
“Zadai kiji soon insha ALLAH. ALLAH yay miki albarka. Ya cigaba da baki kariya a duk inda kika shiga a
faɗin duniya. ALLAH ya share hawayenki ya azurtaki da zuri'a ta gari da zata zama lulluɓin nagartacciyar
inuwa ga ƙaddarorinki”.
Hannu Raudha ta kai ta share hawayen da suka silalo mata tana amsama bappi. Zuciyarta sai sake
faɗaɗa take da ƙaunar tsohon.
Magana da Bappi yayma Ramadhan ne ya sakashi ɗan matsowa gaban gadon, a karon farko yayma
Raudha kallo guda yana tura wayarsa a aljihu, tare da ɗauke idon nasa da ya saka tsigar jikin Raudha
tashi. Ƙafar yaɗan kalla, sai kuma ya watsa mata harara. Tun a jiya daya karanta abinda ya faru kafin ya
iso ƙasar, da kuma bayanin da Bappin yay masa akan yanda abin ya faru sai zuciyarsa ke raya masa akan
wani dalili Raudha ta aikata hakan. Dan in babu dalili babu yanda za'ai ta bada jikinta a raunata saboda
kakansa. Na farko kodai akwai shiri a lamarin, ma'ana tanada alaƙa da makashin. Na biyu ko tayi
hakanne domin kuɗinsu ko wani abu makamancin hakan. Na uku tanada alaƙa da waɗanda suka halaka
masa mata da ƴars......
“Ramadhan!”.
Bappi ya ambaci sunansa a nutse ganin kallon banzar da yake yima Raudha a kaikaice. Fuska ya sake
ɓatawa da jan ƙaramin tsaki a ransa. Harya buɗe baki zaiyi magana ya maida abunsa ya tsuke ganin
Bappi ya ɗan ja baya yana kai wayarsa da aka kira cikin kunne alamar amsawa.
Tuni Raudha ta ɗauke idanunta daga kallonsa. Saboda kallon banzar da taga yana binta da shi ya
saka zuciyarta yin ɗaci. Tanada haƙuri, amma tana da zuciya. Sannan ta tsani wulaƙanci koda ga wanda
ya girmeta ne......
A hankali cike da ƙasaitarsa da jin eh ya isa ya taka gaban gadon sosai fiye da farko, ƙamshin
turarensa ck one ya sake sirɗaɗawa cikin hancin Raudha yana keta cikin jininta zuwa ɓargo, saboda
ƙarfinsa da tasirinsa ga ma'abocin shaƙansa. Ƙarfen gadon ya dafa saitin kanta tare da ranƙwafowa har
tana iya jin fitar sautin numfashinsa. Ya saki wani sihirtaccen murmushi mai ɗauke da ma'anoni da yawa
dai-dai gaɓar da yake cafke ƙwayoyin idanun Raudha da mamakinsa ya sata ɗagowa ta kallesa cikin nasa.
“Ki daina yaudararsu, ki kuma tabbatar musu ke *_BAƘAR INUWA ce_*. Idan kikai wasa da gargaɗina
ni zan zame miki *_BAƘAR INUWAr_* da sai kin gwammaci *_GARA RANA DA NI!_*.
A kausashe furucin ya fita daga harshen Ramadhan, cikin ƙasaitacciyar muryarsa mai faɗi da kauri
ya shiga dodon kunnen Raudha. Da ace ba kusa gab yake da kunnuwanta ba, ita da kantace zata ƙaryata
cewar shine ya faɗa ɗin, dan duk wanda yaga yanayin nasu zai ɗauka wata maganace mai daɗi a sanadin
tausayawa.
Kafin ta iya ce masa wani abu ya fincike idanunsa a cikin nata cike da tabbatar da gargaɗinsa. Ya ɗan
dubi Bappi dai-dai yana ɗagowa ya miƙe akan ƙafafunsa da ƙyau. Ganin Bappin su yake kallo sai ya sakar
masa murmushi yana ɗan kai hannu ya shafo ƙeyarsa...
Tabbas wani abu da Ramadhan bai kawo a ransaba a wannan gaɓar ya shiga ran Bappi a bazata. Tun
a daren jiya yake cuɗawa da kwancewa wajen laluben nemo hanyar da zai kwatantama Raudha da
iyayenta alkairinta, amma sai ya gagara samowa. Dan gani yake kuɗi, gida, ko makamantansu dan ya
bama Raudha bai biyata ba. Saboda ita ransa ta fansa. Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci ALLAH ya haska
masa wata hanya da yake ganin ko bai saka mata ba, zai kwatanta kusantata gareshi harya samu alkairi
daga alkairinta a cikin zuri'arsa..... Ya saki wani ƙasaitaccen murmushi yana kai hannu bisa kafaɗar
Ramadhan ya ɗan bubbuga cike da salon manya idan abu yay musu daɗi.
(Lallai sun dace) ya ayyana a ransa yana duban Raudha data kauda kanta gefe zuciyarta na luguden
daka daga kausasan kalaman Ramadhan da zuciyarta ta kasama fashin baƙi. Sai kawai nan ma Bappi ya
fassara kauda kan nata da tunanin jin kunya duk da baisan wane furuci jikan nasa ya furta a gareta ba.
Ramadhan da shi sam baima kawo abinda Bappin ke ayyanawa ba a tunaninsa sai kawai ya nufi
hanyar fita dan gaba ɗaya ya gundura da zaman asibitin. So yake yabar ƙasar nan a daren yau dan tuni ya
kammala booking flight. Sai dai zai tashi ne ta jihar Loss shiyyasa yake son barin Bingo da wuri yaje can
ya ɗan huta kafin daren.
Nanma da kallo Bappi ya bisa yana murmushi, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Raudha da har
zuwa yanzu ruɗani bai bar tunaninta ba...
*_TAURA HOUSE_*
Tun fitarsa take ƙame a tsaye, sai da ta fahimci jinin jikinta sulalewa yake zuwa ƙasa sannan tai
jarumtar jawo numfashin dake neman barin ƙirjinta yana bin jininta dake sauka a ƙafafunta. A ƙa'idar
kowanne ranakun bikin salla na babba da ƙarama washe gari a masarautarsu take yinta ita da dukan
iyalanta dama ahalin masarautar garin ta Bina. Shiyyasa a yanzu haka jirgin da zasu bi a shirye yake tsaf
zuwa jihar BINA fitarsu kawai ake saurare.
Waya ta jawo da sauri dan bazata iya jira har sai ta isa garin Bina ba zuciyarta zata iya fashewa. A
yanda take ƙoƙarin dialing numbern na ƴar uwarta Asma zai baka tabbacin a ruɗe take. Ta saka wayar a
hansfree dai-dai shigarta. Bugun shigar kiran na bugawane dai-dai da bugun zuciyarta. Sai dai abin
takaici harta tsinke ba ɗagaba. Sake kira tai nan ma babu amsa. Sai da ta jera kusan kira biyar amma ba'a
ɗaga ba. Lallai babu lafiya, dan a ƙa'idar gimbiya Su'adah daga kira ɗaya bata sake yima mutum ko yaya
suke, mai-martaba ne kawai keda wannan alfarmar da arziƙin a gareta. Amma a yau sai gata da jera har
biyar batare da taji ta gundira ba.
Da sauri ta maida akalar kiran nata ga mai-martaba saboda zuciyarta ta ayyana mata shine kawai
maganin kukanta a yanzu bama Asma ba. Cikin sa'a kuwa tana gab da tsinkewa a ka ɗaga, domin kuwa
abune a bayyane kowa yasan gimbiya Su'adah ƴar gaban goshin mai-martaba ce saboda sunan wadda ta
riƙesa da yakema kallon uwa aka saka mata.
Cikin girmamawa tamkar tana a gabansa ta rissina tana gaishesa. Daga can ya amsa da sakewa cike
kuma da ƙasaita irin ta masu mulki.
Cikin girgiza kai da sake raunan murya ta ce, “A'a Abi bama mu taho ba. Dama Ramadhan ne yazo NAYA
jiya, bamma san da zuwan nasa ba sai a safiyar yau. Koda ya shigo gaisheni yayiminne tamkar maƙiyarsa
ba mahaifiyarsa ba. Daga ƙarshe yake sanarmin a yau zai koma America. Nama tabbatar yanzu yana gab
da barin ƙasar..” ta ƙarasa faɗa tana sakin wani kuka mai ban tausayi gamai saurarenta.
Mai-martaba ya saki ƙasaitaccen murmushi yana gyara kishingiɗarsa. “Ni ban san randa Mamana zata
girmaba har yanzu. Yanzu dai akan Ramadhan kike ɓatamin hawayenki? To sharesu ki kwantarmin da
ranki. Yanzu babu jimawa mukai waya da Alhaji Hameed akan zasu ƙaraso nan tare da shi, suna airport
ma a yanzu haka”.
Wani irin wawuyar ajiyar zuciya ta saki da murmushi lokaci guda. Sai hawayenta data kai hannu ta
share da faɗin, “Nagode Abbi”.
“Godema ALLAH”.
Tuni ta manta da hawayen fuskarta ta hau sakin murmushi. Koda Addah Asma ta kirata batabi takan
kiran ba dan tasan yanzu zasuje su haɗu ai....
Ita ɗin yarinyace mai kaifin basira da hangen nesa. Hakan yasa tun bayan barin su Ramadhan ɗakin
ta shiga cikin zurfin tunani da fassarar kalamansa. Sai dai kafin ta samu damar samo amsar sallamar ƴan
uwanta da su Asabe harma da kakarsu Hajiyar birni ya katseta. Taji daɗin ganinsu dan dama tunda ta
farka take tambayar likita ina suke. Dan da farko ta tsorata da tsadajjen asibitin da taga kanta a ciki.
Rungumeta Asabe tai tana kuka, dama shi ta kwanayi a daren jiya. Dan gani take Raudha ta rasu ne
su aunty Hannah na ɓoye mata. Hakama Yasmin tana kallon ƙafar Raudha ɗin ta fashe da kuka, kukanta
kuma yaja hankalin su Samha suma dake ƙananan yara suka fara.
Sai da hajiya mama ta ɗan musu tsawa ne ganin aunty Hannah na lallashinsu sunƙi su nutsu. Yanzu
kam tsit sukayi sai Asabe ce ke nata tana jerama Raudha addu'oin samun lafiya....
Kasancewar Alhaji Hameed Taura ba ƙaramin mutum bane cikin ƙanƙanin lokaci zancen sake ziyararsa
asibiti tare da jikansa ta baje kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo. Harma abin ya bama Bappin mamakin
tunda yasan baici karo da ɗan jarida ko gudaba. Sai dai tunawa da cewar yanzu waya ta maida kowa ɗan
jaridar kansa ya sashi watsar da kokwanton.
Yabo dai kam yana samu akan ƙoƙarin tsayawa tsayin daka ga Raudha. Dan yanda kowa yasan
wanene shi ba'ai tunanin zai bada lokacinsa gareta ba.
Duk da Ramadhan nata ɓata fuska a cikin jirgi hakan bai hanashi jin daɗiba a ransa sanda suka iso
cikin masarauta. Dan suna sauka a airport ƙayatattun motoci na alfarma guda huɗu wanda uku ke tare
da hadimai, ɗaya ta ɗaukarsu suka iso filin jirgin.
Alhaji Hameed Harith Taura kowa yasan abokine ga Sarki Abdul-wahab tun da ƙananun shekaru.
Dan kuwa tarihi ya tabbatar da sunyi karatun degree na farko tare a jami'ar Bino. Sannan harkokin
kasuwanci sun sake haɗasu a wasu fannoni kafin mai-martaba ya haye karagar milkin jihar ta Bino. Sai
kuma gashi sun zama surukai a dalilin auren ƴaƴansu.
Yau ranace da masarauta ke cike da baƙi tako ina. Amma hakan bai hana a samarma da su
Ramadhan tarba ta musamman ba. Ramadhan na gama gaisawa da mai-martaba daketa tsokanarsa akan
ya'akai kuma ya baro masu jajayen kunuwan?. Ko sun gaji sun koroshine da kansu. Shi dai murmushi
kawai ya dingayi dan ba kasafai irin wannan wasar ke shiga tsakaninsa da kakannin nasa ba. Daga su
Bappi har su mai-martaban sunyi trianing nashi ne like iyayensa ba kakanni ba. Garama Fulani takan ɗan
tsokanesa. Sai dai kuma shi ɗin bawai ya iya wasan baneba iyakarsa murmushi ko ada can ma balle
yanzun.
Fahimtar magana su mai-martaba kesonyi ya sashi zame jikinsa zuwa cikin gida domin ya gaisa da
kakar tasa da iyaye da ƴan uwa. Yako karancesu da ƙyau, dan yana fitar suka hau tattauna dalilin zuwan
Alhaji Hameed ɗin dan awa ɗaya kacal suke da ita saboda mai-martaba na amsar baƙuncin manyan
mutane masu barka da shan ruwa da barka da salla.
Abubuwa masu muhimmanci guda biyu suka tattauna. Wanda ya shafi auren Ramadhan da Bappi
atake ya sanar ma mai-martaba har yayi masa mata. Da kuma batun fitowa takara da zata bayyana nan
da ƙanƙanin lokaci.
Duk gaba ɗaya mai-martaba yayi farin ciki ya kuma sanya albarka da fatan alkairi a cikin lamarin, tare
da bada goyon baya dan a ganinsa ai babban cigabane jikan nasu ya samu. Daga haka ya ƙara da nasa
shawarwarin shima...........✍
*_Barkanmu da dawowa._*😘😘👌🏼
________________________
*mg's skincare*
Shin Ina matan sukemaza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir
dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane
wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar
gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne
bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌
hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda
sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty
kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan
fata?
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin
Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali
jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal
set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Pamper ur skin🦵
Glow
💯 tested nd trusted🤝
Guarantee
Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
_____________________
https://arewabooks.com/chapter?id=629a77b967809ad6daab2109
*_Chapter 13_*
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_Episode 15_*
..........Su Bappi basufi mintuna talatin da isowaba Gimbiya Su'adah da tawagar ƴaƴanta mata suka iso
suma. Anan ne ta samu damar haɗa hannu da fulani (mahaifiyarsu Uwargidan sarki) da Adda Asmah
suka rufe Ramadhan da faɗa sosai akan abubuwa da dama, ciki harda batun zamansa babu aure, duk da
dai basu fiddo maganar zaɓa masa mata ba.
Shiko dai ya cinkushe fuska yana saurarensu kawai. Sai da sukayi mai isarsu ya basu haƙuri kawai yay
fitowarsa. Dan Bappi ya kirasa akan ya fito su wuce. Idan kuma ya barsa anan to?. Da sauri yacema Bappi
a'a zai bisa, dan so yake yaje ya wuce loss, sai dai bai faɗama bappi ƙudirin nashiba kai tsaye.
Yanzu kam ya iske mai-martaba tare da Bappi da Pa da suka iso da Gimbiya Su'adah. baiyi mamakin
ganin Pa ɗin ba, tunda tun yana ƙarami yasan a irin wannan ranar ta washe garin salla suke zuwa gaishe
da mai-martaba ɗin daman. Zama yay gefen mai-martaba daya nuna masa yana satar kallon Pa da
fuskarsa ke a haɗe alamar har yanzu yana kan fushinsa na jiya. Koda yake har suka baro Bingo dama
baiko kallesa ba duk da har falonsa yaje ya gaishesa.
Sai da suka tabbatar da nutsuwarsa sannan Bappi ya fara magana cikin nuna alamar babu wasa
tattare da shi.
Ramadhan ya ɗago a firgice yana duban mai-martaba. Kafin ya maida dubansa ga Pa da baice uffan
ba.
“Bappi!”.
Bappi dake kallonsa cike da tausayawa a can ƙasan ransa. A fili kam ya dake ya jinjina masa kai.
“Umarnine wannan ba shawara ba Ramadhan. Domin nasan zaka iya insha ALLAH. Zaka kuma kawo
cigaban da muke fata wa ƙasar nan ta hanyar basira da ƙuruciyar da ALLAH yabaka. Domin NAYA irinka
take buƙata, tabbas irinka take buƙata.”
Miƙewa Ramadhan yayi yana girgizama su Bappi kansa. Ya kai hannu ya tura hular kansa baya
saboda zufa dake ɓillowa a kowacce ƙofa ta gashinsa. Babu abinda zuciyarsa ke ambata sai sunayen
ALLAH. Ya sake buɗe baki zaiyi magana Pa ya dakatar da shi....
“Biyayya ga iyayena dole ne a gareka, domin bazasu taɓa jefaka a hanyar halaka ba. Tunda har su
Bappi suka amshi tayinsu, dolene kaima ka amsa da ga garesu kayi biyayya. Idan ba hakaba babu ni babu
kai da ga yau da ga wannan likaci....”
“Baiyi ba Ramadhan. Domin kaima kayi abinda kakeso a shekaru biyar muka kuma ƙyaleka, duk badan
kafi ƙarfinmu ba. Dolene yanzu kaima kabi abinda mukeso dan lokacinmu ne.”
“Ya ALLAH”.
Ya faɗa cikin sake shiga tashin hankali yana komawa baya ya sake zubewa a cikin kujerar da ya tashi.
Gaba ɗaya ƙwayoyin idanunsa sun sake canja kala a lokaci ƙanƙanin. Ɗan sassaucin daya samu na
damuwar jiya wadda ta fita ta sake maye gurbinta. Gaba ɗaya gashin jikinsa ya mimmiƙe sai faman tura
yatsun hannunsa yake cikin sumarsa dan son control ɗin abinda ke taso masa...
Duk da Bappi ya san Ramadhan ɗin yakai maƙura gab yake da birkice musu bai sassauta masa ba.
Dan a ganinsa gara ayita baki ɗaya ta ƙare kawai. Hakan yasa kai tsaye ya ɗora da faɗin, “Sai kuma batun
aure, shima mun riga mun maka mata dan ko munce ka nemo ba kawowa zakai ba. Bakuma zai yuwu ka
hau mulki babu mace ba, idan har ALLAH ya ƙaddara zaka hau ɗin. Dan haka mun gama yanke hukunci
mu zamu nema maka aur.....”
Kafin ma Bappi ya ƙarasa numfashin Ramadhan ya fara fisga. Ya shiga laluben hanun bappin dake
kusa da shi, da ƙyar ya samu ya riƙosa ya damke. Cikin sauri Bappi ya miƙe ya ya rungumesa a jikinsa da
kiran sunansa yana girgizashi.
Su dukansu ɗunbin tausayinsa ne a cikin ransu. Wannan yanayi da yake shiga idan ransa ya ɓaci yana
tada musu hankali, babu irin likitan da basu gani ba, amma iya bincike akan sanar musu lafiyar
ƙwaƙwalwarsa kalau. Sai dai maimakon su maida hankali gana musulinci sai suke sakaci, dan tabbas
al'amarin nasa yana kamanceceniya da nai mai iska ko sihiri, ga diabetis kuma da shima ya zame musu
na gado. Dan shi kuma Bappin ne ke dashi, shima Alhaji Basheer ɗin nada, hakama Ramadhan ɗin da
wasu a cikin yaran gidan ƴammata.
Bappi ya faɗa yana shafa kafaɗarsa da ɗora masa kofin ruwa a baki. Babu musu ya sha kusan rabi, sai
kuma ya miƙe ya sake rungume Bappin. Murmushi Bappi yayi da sake rungumesa da ƙyau shima yana
shafa bayansa.
“Please Bappi a sassauta mini koda maganar auren a janye”. Ya faɗa lokacin da Bappi ke ɗagosa da
ga jikin nashi.
Murmushi Bappi yayi mai ƙayatarwa da shafa sumar Ramadhan ɗin yana girgiza masa kansa. “Babban
sassauci kawai bin umarninmu Ramadhan. Idan kayi hakan sai ALLAH ya albarkaceka da nasarori a
rayuwarka ok?”.
Maimakon amsa sai ya sake faɗawa jikin Bappin ya ƙanƙamesa har takai mai-martaba da baice
komaiba har yanzu sakin murmushi. Shi kansa Pa gefe ya maida kansa yana nasa murmushin dan yasan
mai shiga tsakanin Bappi da Ramadhan sai ALLAH. Shi kansa ya buɗe masa wutane dan yasan sa sarai
akan kafiya da dagiya kan abinda bayaso. Shiko bazai taɓa yarda mahaifinsa yaji kunya ba tunda har ya
riga ya amshi tayin su president ɗin....
*_GOVERNMENT HOUSE_*
Tarba ta musamman Alhaji Hameed Harith Taura ya samu shi da Ramadhan a fadar ta shugaban
ƙasa, kasancewar tun a daren jiya Bappi ya sanarma mai-girma shugaban ƙasa zuwan Ramadhan ɗin
NAYA ta hanyar text Message.
Duk da tarin liyafar da aka shirya domin Ramadhan hakan bai wani birgesaba, dan tunda suka baro
masarautar Bina zuciyarsa bata tare da gangar jikinsa duk da nasiha mai ratsa jiki da mai-martaba da Pa
da Bappi sukai masa.
Sai kuma Raudha dakan faɗo masa a rai. Sai yanzu yake ƙara yarda da hasashensa kan dalilin Raudha
na bama Bappi kariya. Dan haka kawai bazata bada ranta akan wanda bata saniba ko rashin dalilin,
zuciyarsa na sake tabbatar masa a yanzu abinda tayi nada alaƙa da wannan batun na fitowarsa takara,
lallai akwai wani shiri a ƙasa da su Bappi basu fahimtaba. Sai dai wanene ke shiryawa? Akan mi? Akan
wane dalili? Duk bai saniba shima.
A zuciyarsa yake ayyana. (Inko hakane dolene nabi dukkan hanyar daya dace dan na sani koda kuwa
hakan na nufin zai iya rasa raina).
Taro ne daya tara manyan jiga-jigan jam'iyyar tasu, sai dai gaba ɗayansu sunada masaniya akan son
tsayar da Ramadhan takarar. Amma kowa yanada manufarsata ta amincewar kuma. Wani yanki a cikinsu
kamar su Alhaji Yaro glass sune suka san ainahin manufar. Sauran kuma suke kallon hakan bisa
ƙyaƙyƙyawar niyyar manyan jam'iyyar na kawo dai-daito akan rabuwar kawuna dake neman shiga
tsakaninsu a dalilin yawan ƴan takara. Sai dai kuma duk da haka wasun su zukatansu a ƙuntace suke da
rashin son Ramadhan ɗin musamman da suka gansa yaro ƙarami saboda mafi yawansu sun haura sittin
su, kawai dai basu da ƙarfin faɗa ajine sai ya zam dole suka zuba ido wajen bin gangar yarima asha kiɗa.
Bayan anci an sha da ga abinda aka tara wanda Ramadhan ko ruwa bai sha ba a wajen suka fara
gudanar da abinda ya tarasun. Shugaban jam'iyya da sauran jiga-jigai sukayi bayanai da welcoming ɗin
Ramadhan cikin su, tare da fatan zai basu haɗin kai wajen yin aiki tuƙuru da ƙara ɗaga darajar jam'iyya.
Ba wani fahimtarsu yake ba, dan sam hankalinsa baya a tare da su. Amma magana da ido da Bappi
yay masa ta tilasta masa miƙewa yay bayani shima. Bayan godiya da jinjina a garesu ya tabbatar musu
zasu sameshi fiyema da yanda suke buƙata.
Jin kalmar (fiye da yanda suke buƙata) a bakinsa ya sasu ji a ransu zasu iya juya Ramadhan duk yanda
sukeso domin biyan buƙatunsu.....
Tunda Asabe tabar gidan gaba ɗaya sai ya koma tamkar wani zararre. Duk masifarta da gantalin
faɗansu da baya ƙarewa itaɗin ta daban ce a gareshi. Dan a gidan Asaben ce kawai zata samu abunta ta
bashi batare da baƙin ciki ba. Amma ko baba Nafi duk haƙurinta akwaita da halin banza a wani fannin
itama. Sai dai nata da sauƙi akan na Larai.
Da farko Larai tata ƙoƙarin ganin neman auren da Alhaji Maude Dallatu Kema Raudha ya dawo kan
ɗiyarta ne Zabba'u. Dan tata lallaɓa M. Dauda akan hakan tare da banka masa rubutu da magungunan
malam. Ance tsafi gaskiyar mai shi, dan ta ɗan fara samun kansa harma da manta Asabe da ƴaƴanta da
taso yayi, sai dai kuma ba'aje ko inaba aikin ya watse.
Dan a ranar salla tunda labarin abinda ya faru da Raudha yazo kunnensa sai ya rikice harda kukansa.
Ya dinga tsinema Alhaji Hameed Taura akan yaja an kashe masa ɗiyarsa saliha mai addini. Dan kuka
rurus ya zauna yanayi a bakin masallaci. Mutane suka taru a kansa anata bashi haƙuri da lallashi amma
M. Dauda sai sake ɓare baki yake yana fyatar majina.
Daga ƙarshe yace inhar anaso yay shiru sai a haɗa masa kuɗin motar zuwa Bingo inba hakaba yata
kuka kenan har sai Alhaji Hameed Taura yazo Hutawa. Mutane sun san halin M. Dauda ƙwallon ɗan is....
Ne shiyyasa basuyi ƙasa a gwiwa ba wajen fara haɗa masa wasu ƴan kuɗaɗe. Yai kwanaki biyu kenan
kuwa ana haɗa kuɗin a masallaci. Ba wani kuɗin kirki bane suke badawa. Mai hamsin mai ɗari ne kawai,
shiyyasa haɗa kuɗin yaɗan ja lokaci duk da sun san zuwa yanzu ya samu fiyema dana motar.
Ilai kuwa a daren jiya aka tattare kuɗin naira dubu bakwai aka bashi harda canji a sama. Daɗi ya
sakashi fara godiya yana kuka, harda cewa baisan ana ƙaunarsa a anguwar tasu ba har irin haka. Sudai
mutane dariya suka dinga gumtsewa kawai. Shi ko ko'a jikinsa, ana idar da sallar asuba ma ko wanka
baiyiba yaje gida ya canja babbar riga kawai, rigar duk ta fita hayyacinta da tsufa da dauɗa amma bai
damuba. Dan itace kawai rigarsa ta arziƙi ta ganin shugaban ƙasa. Ya dakwarra wata shegiyar hula da ko
wanki babu tare da ita balle sitatin kirki.
Duk jarabar da Larai taita masa da ƙirƙirar suyi rigima ta lalube kuɗin bai kulata ba, sai ma ɗakko
bakko ɗin kayansa data gama shiga uku dan tsufa yay yayi fitowarsa. A ƙofar gida yaci karo da malam
Gambo abokinsa. Yay wani gaba kamar zai kifa sai kuma ya dawo baya ya dafe bango yana hangame baki
da haɗe fuska.
Baki M. Gambo ya washe yana miƙewa tsaye da leda viva ɗinsa a hannu, shi kansa ba ƙaramin a
harmutse yake ba, dan har gwarama m. Dauda ɗin ta wani fannin. “Kai abokina ya kake magana haka
kamar ka manta ni abokinka ne na amana. Ai bai kamata na barka kaje kai kaɗai ba babu kara. Dole ne
na bika muga halin da yarinyarmu ke ciki tare. Mu kuma san matakin da zamu ɗauka akan tsohon nan
Taura”.
Da farko ƙanƙance idanu M. Dauda yayi yana harar M. Gambo Ƙasa-ƙasa. Sai kuma tunawa da yay
M. Gambo ya fisa tujara ƙila idan sun sami ganin Taura zaifi ƙwato musu ƴanci. Dan yayi alƙawarin idan
Taura bai sauraresu ba gidan redio zai dawo ya masa terere duk da a yau yaji a labarai an sake cewa
Taura da jikansa sunje sun sake duba Raudha a asabitin da aka ɓoyeta ana bata tsaro na musamman.
Ciwon Raudha ya damesa, amma a ƙasan ransa gani yake silar arziƙinsa ce a wajen. Dan yasan dai baza'a
nakasta masa ɗiya a dalilin Taura ba Taura yaƙi jiƙashi da kuɗaɗe. Wannan yanada ɗaya daga son zuwan
nasa Bingo...
“A'a ai ba tafiyar bace matsalata M. Gambo, ka sani duk fa abinda muka samo sammaka zanyi ba raba
dai-dai zamuyiba. Dan nasan badan ALLAH kake son mini binbinin nan ba.”
Kamar m. Gambo zaiyi magana sai kuma ya fasa, dan yasan halin buyagin M. Dauda. Lallamashi kawai
ya shigayi harya haƙura suka tafi tasha neman motar Bingo.....
Komai ya ƙwace masa, babbar damuwarsa hanashi komawa da Pa da Anne sukayi America. Dan
Bappi dai yaƙi yace masa komai tunda suka baro gidan gwamnati. Shima ɗin bai yarda ya zauna da kowa
ba ya shige ɗakinsa dake a sashen na su Anne. Koda yake bazamuce ɗaki kawai ba. Dan shima tamkar
wani part ne na musamman a wajen. Falone har guda biyu ƙarami da babba, ƙaramin an shiryasane
kawai dan hutawa, inda glass ne kawai ya rabasa da babban sai labulaye. Sai bedrooms biyu, kitchen,
store, dining, da ƙofar da zata sadaka da backyard inda akai wani haɗaɗɗen ƙaramin garden da yasha
tsirrai masu ni'ima, ga madaidaicin swimming pool a gefe da akai masa wani style da ruwa ke fitowa ta
wani dutsuna tamkar ƙorama. Daga can gefe keɓantaccen wajene da akayi da glass an cikashi da kayan
motsa jiki ().
Duk gidan bamai shigowa wajen sai idan aikosa akai, dan ko baya nan mai kula da shine kawai ke
shigowa saiko Bappi idan yanason kaɗaice kansa. Idan kana hango wajen daga cikin falonsa saboda glass
ne a bangon saika ɗauka bama cikin NAYA kake ba, dan daga falon kana jiyo ƙamshin furanni dana
saukar ruwan dake fita a dutsen nan, ga grass carpet ta ko'ina lamarin ba'a cewa komai.
A yanzu hakan ma dai a cikin garden ɗin yake kwance bisa kujera irin wadda akan ajiye gaban ruwan
nan domin hutawa kawai, ƙafarsa ɗaya a ƙasa ɗaya tana kan kujerar, yayi kwanciyar rigingine ne
fuskarsa na kallon sama, yay filo da hannunsa ɗaya yayinda ɗayan ke riƙe da gorar ruwa, ya ƙurama
sama ido tamkar yana irgen gajimaren dake yawo ne a cikinta.
Abu biyune sukafi komai masa kaikawo a yanzun. Maganar siyasa da su Bappi keson tsundumasa
batare da shi ya taɓa ra'ayin hakan ba. Sai ɗunbin zargin Raudha da yake ganin tayi komai ne da wani
dalilinta kona sakawar waninta. Na ƙarshe ma tana ɗan sukarsa sai dai ba sosai ba, wato maganar aure,
babu zancen ƙara aure a budget ɗinsa, dan haka koma ƴar wacece ake son aura masan shi zai gargaɗeta
ta bijire ma su Bappi. Dan haka baya ɗaukar wannan babbar matsala........✍
To Ramadhan B. Taura bara mugani koba babbar matsala bace kamar yanda ka ɗauka😜🏃🏃.
https://arewabooks.com/chapter?id=629a77b967809ad6daab2109
*_Chapter 13_*
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_Episode 16_*
..........Tunda mai-martaba ya sako zancen Ramadhan a cikin meeting da yakeyi da ƴaƴansa da matansa a
duk irin wannan ranar hankalin Gimbiya Su'adah da Fulani da Adda Asmah yake a tashe. Ba komai ne ya
tada hankalin nasu ba kuwa sai jin mai-martaba yace har Alhaji Hameed Taura yayima Ramadhan ɗin
mata. A cikin satin nan ma zasu tuntuɓi iyayenta dan baya buƙatar abun yay nisa.
Duk yanda gimbiya Su'adah taso daurewa saboda ƴan uba dake a wajen kasawa tai. Ta ɗago a firgice
tana kallon mahaifin nasu. Cike da ƙasaita yace, “Mamana kinada magana ne?”.
Kowa yasan irin son da yake mata saboda sunan wadda taci, dan haka suka shiga ɗan taɓe baki suna
maida kawunansu gefe rayukansu fal hassadar jin Ramadhan zai fito takarar shugabancin ƙasar NAYA a
dalilin kakansa.
“Abi maganar yimasa matar ne sai naga kamar anyi gaggawa, tunda kaga abinda ya faru a baya kamar
ya kamata a bari ya nutsu kafin a sama masa wadda zata dace da shi da matsayin da muke fata zai hau”.
Mai-martaba da ke kallon television kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ɗan murmusa. “Mamana
banda abinki wace nutsuwa Ramadhan ke buƙata bayan wadda ya samu a shekaru biyar da faruwar rasa
iyalinsa. Kece fa kike damuwa da rashin aurensa har kike damuna, yanzu kuma an sama masa kina
jayayya?. Alhaji Hameed bazai taɓama Ramadhan zaɓen matar banza ba, sannan yanada iko akansa irin
wanda ni bani da shi matsayina na kakansa ta ɓangaren mace. Inaga addu'a da fatan alkairi ya kamata
mu masa, dan bazasu taɓa zaɓa masa matar da bazata dace da matsayin da kike kallon ba”.
“Amma Abie....”
Kansa ya girgiza mata. Kafin cikin ƙasaita ya ce, “Na gama magana Mamana”.
Dole tai shiru, sai dai zuciyarta tafasa take tamkar zata kama da wuta. Fulani da bataso Gimbiya
Su'adah yin maganar anan ba ta ɗan harareta ta wutsiyar ido itama. Dole tai shiru har aka tashi taron
kowa ya koma sashensa.
★★
“Ammi wlhy bazan amince ba a wannan gaɓar, wai taya za'ace ni da Basheer dake mahaifin
Ramadhan bamu isa yanke hukunci akan ƴaƴanmu ba musamman ma Ramadhan sai dai tsoffin nan dake
matsayin kakanninsa.”
Gimbiya Su'adah daketa kaikawo a cikin falon hutawa na Fulani ta faɗa cikin tashin hankali. Kafin
Fulani tace wani abu Adda Asmah ta amshe rai ɓace.
“Maganar gaskiya wannan fin ƙargine Ammi. Amma ni ina ganin tun farko harda sakacinmu. Taya zaki
sakar musu ragamar ɗanki bayan shi kaɗai ne tilon ɗa namiji a gidan. Daɗin daɗawa shine kuma
babba.....”
“To Adda ya kike so nayi?, bayan kinsan tun daga yayen Ramadhan suka riƙesa suka hanani, wane
kalar abune banyiba amma sukai kunnen uwar shegu dani tsoffin nan”.
“Amma ai basai ta wannan hanyar ne zaki dawo da Ramadhan jikinki ba. Tun a lokacin ya kamata
kiyita jan ra'ayinsa cikin hikima shi da kansa zai dawo gareki batare da kin nuna musu koda a fuska ba.
Amma ai wannan ƙarfa-ƙarfar tayi yawa. Dan wlhy yanda yakejin maganar waɗan nan tsoffin da mutuwa
ke gab da su bayajin taki ma”.
Tsaki Fulani tayi, hakan ya sasu kallonta su duka. Ta gyara zamanta na ƙasaita tana hararsu.
“Kunfa dameni da surutan banzarku. Ku miyasa a komai baƙwa nutsuwa kuyi abun hankali sai
shirme. K Su'adah yanzu kamata yay ki lallaɓa musan wacece zasu aura masa. Ni yanzun zan tuntuɓi mai-
martaba da batun ƙudirinmu na haɗa auren Aynah da Ramadhan ɗin naji mizaice, duk dai abinsa ai
bazaiƙi jikarsa ba ko?. Indai Ramadhan ne a wannan gaɓar zai dawo garemu, dan bazamu amince ya
samu mulki su Firdausi su cigaba da juya manashi yanda suke so ba. Shine babban jikana na farko, dan
haka nima inason abina”.
Sosai shawarar mahaifiyar tasu ta ɗan basu nutsuwa, dan haka gimbiya Su'adah ta zauna tana sauke
numfashi da ajiyar zuciya....
“Kai wlhy idan sama da ƙar zata haɗe yau sai na shiga naga halin da gudan jinina ke a ciki, kajimin
mara mutunci. Bar ganin kasa waɗan nan kayan kai tunanin zanji tsoronka, kai fa ba komai bane sai mai
gadin gate ɗin asibiti mun sani, ni da kake gani na anan ba ƙaramin tantiri bane, duk wani gidan shege da
shegiya dake ƙasar NAYA da mu akai taron bikin buɗesa saboda gawurtarmu a iya shege. Idan kaji ƙarya
cigaba da nunamin yatsa kaga idan ban karya shege ba naga miza'ayi min”.
M. Dauda ne ke zuba ruwan bala'i a gaban gate ɗin Tk special hospital. Dan security ɗin gate ya
hanasu shiga ciki, shine suka tafi da kokawa akan sai fa sun shiga ɗin. Ganinfa da gaske suke security ɗin
ya ɗaga waya ya kira ogansa. Jin hayaniyarsu ta cikin wayar ne ya tilastama Dr Shamsu fitowa da kansa
dole har wajen gate ɗin.
Dr Shamsu dake ƙarasowa wajen gate ɗin ya faɗa cikin ɗagama security ɗin hannu ganin su M. Dauda na
neman ɓalla masa kunkuru. Dan sun haɗu su biyu sun ƙadandanesa adole sai sun ɗagasa. Ga Daniel ɗin
kuma yayi huɗunsu dan su taba duk ta gama ragaɗe naman jikin nasu.
Cikin bin umarni security ɗin ya janye jikinsa yana ƙwafa da hararsu. Suma harar tasa suke da cigaba
da kumfar baki har sai da Dr Shamsu ya dakatar dasu.
“Ranka ya daɗe dama munzo duba yarinyarmune da aka jima ciwo a dalilin Alhaji Hameed Taura.
Wannan mahaifintane, ni kuma abokinsane kuma ɗan uwansa na ƙut-da-ƙut”.
Dr Shamsu ya ɗan rumtse ido dan shi surutun M. Gambo hawar masa kai yake, a ƙasan ransa yana
auna Raudha da wanda aka kira mahaifin natane. Tabas M. Dauda ƙyaƙyƙyawa ne, sai dai taba duk ta
gama cinyesa ta sake sakashi komawa baƙi. Idan mai nazari ya nutsu tsaf a kallonsa zai ɗanga yanayi na
jini dake tsakaninsa da Raudha, sai kuma kamanin su Fatisa da shi tafi rinjaye duk da suma sun fisa ƙyan
gani da ƙuruciya a yanzun.
“Maganar gaskiya bazai yuwu na yarda daku kai tsaye ba, saboda dalilai masu yawa. Yarinyar nan
kowama zai iya basaja yanzu domin farautar ranta ko nuna dangantaka da ita domin idasa mugun
nufinsa akan Taura. Dan haka kuyi haƙuri idan an sallameta zaku ganta. Dan a yanzu dai babu mai
ganinta saboda tana ƙarƙashin kulawar ƴan sanda”.
“Kutt... Bantan uban can kayyasa. Kai awa da zakace bazanga ɗiyata ba. To wlhy yau an taɓo bala'i, ai
dama nasan za'a rina shiyyasa na shirya tsaf dan yin kayayatu a gidan redion jaharmu. Zan tafi bazanƙi
ba, amma Taura ya saurari saƙona, dama ba'ance mana anji ƙishin-ƙishin ɗin takarar shugaban ƙasa zai
hito ba, to wlhy nine zan fara masa ƙafar angulu ni Dauda uban Raudha mijin Asabe baban Ɗanjuma da
Garbebe.........”
“Ya ALLAH”. Dr Shamsu ya faɗa yana ɗan ja da baya danjin kansa na sara masa bisa surutun M.
Dauda. Su Malam Dauda na ganin haka suka faki idonsa suka kwasa da gudu zuwa cikin asibitin.
Securitys ne suka rufa musu baya. A taƙaice dai cikin ƙanƙanin lokaci suka nema harmutsa asibitin, sai
securitys sukai kama-kamar ɗakkosu zuwa waje. Ganin abun nasu bana masu hankali bane ga marasa
lafiya da basa son hayaniya yasa Dr Shamsu ɗaga waya ya kira Bappi batare da tunanin zai ɗauka ba. Sai
dai Alhmdllhi tana a ringin na uku aka ɗaga. Cikin girmamawa Dr Shamsu ya gaishe da Alhaji Hameed
Taura, tare da jero masa bayanin abinda ke faruwa duk da shima daga can yana iya jiyo hayaniyar.
“Oh ALLAH waɗan nan wane irin mutanene haka? Doctor Please saka wani ya kawomin su gida
yanzun nan”.
Bayan ya yanke wayar ya dakatar da hayaniyar su Malam Dauda da ƙyar yay musu bayani, amma sai
suka ƙi yarda a cewarsu raina musu wayo Dr Shamsu zaiyi dan su bar asibitin. Anyi-anyi amma sunface
basu yardaba, babu inda zasuje. Idan gaskiyane shi Tauran yazo ya samesu a asibitin inyaso sai su bisa.
Sosai zancensu yasa mutane sake musu kallon mahaukata. Yo inba mahautaba taya zasuce Taura da
kansa, mutum lamba na biyu a masu kuɗin africa, na ɗaya a NAYA yazo nan domin su kawai.
Shidai Doctor Shamsu rasama yanda zaiyi yay, sai dai cikin ikon ALLAH yana tunanin miye mafita sai ga
Bappi ya kirashi. Cikin rawar jiki ya ɗauka, ya kora masa bayanin halin da ake ciki. Murmushi kawai yayi
da cewa, “Karka damu ina zuwa”.
Idanu Dr Shamsu ya ɗan kwalalo da hangame baki na mamaki, sai dai kafinma yace wani abu Bappi ya
yanke wayar.
Bappi ya ajiye wayar yana duban Ramadhan dake gefensa yana shan furar da Bappin kesha shima,
tun wayar farko da yayi Anne ta tambayi lafiya ya mata bayani, amma duk da Ramadhan ɗin na'a wajen
ko tari baiyiba, furarsa kawai yake sha yana sarrafa lap-top ɗinsa kamarma baya a wajen.
“Ramadhan!”.
Ɗago nutsatstsiyar fuskarsa yayi mai ƙarancin hayaniya yana kallon Bappin, kafin yace wani abu Bappi
ya taresa da faɗin, “Tashi muje ka kaini TK hospital”.
Tuni ɗan sakewar fuskar tasa ya ɓace, sai dai kuma babu damar yin gardama, dan shima Bappin ya
tsuke tasa fuskar. Cikin marairaicewa ya maida dubansa ga Anne tamkar zai fasa kuka.
Ɓata fuska ya sakeyi da janye idanunsa, batare da yace komaiba ya kashe lap-top ɗin ya miƙe, jacket
ɗinsa baƙa mai ƙyalli dake ajiye saman kujerar gefensa ya ɗauka ya ɗora saman baƙin wandonsa da
baƙar t-shirt, yanda t-shirt ɗin ta kama jikinsane yasa ƙyawunsa da yanayinsa na mutum mai tu'ammali
da motsa jiki ya bayyana. Sosai sumar nan tasha gyara yau sai ƙyalli takeyi. Ɗan corridor ɗin dake hanyar
bedrooms ɗin Anne ya nufa, ya buɗe wani ƙaramar drawer na glass da aka saka domin ado kawai ya ciri
key batare daya duba na wace mota ya ɗauka ba. Dan duk keys ɗin motocin da suke amfani dashi anan
sashen nanne wajen ajiyarsu.
“Furar fa!?”.
Anne ta tambaya lokacin da Ramadhan ɗin ke ɗaukar p-cap ɗinsa zai ɗora saman kai, dan yasan Bappi
sai yayi magana akan gashinsa.
Hular ya gyara ta rufe masa fuska sosai, ciki-ciki yace, “Na ƙoshi”.
A yanda yay maganar Anne tasan a ƙufule yake, dama yaya lafiyar giwa. Tunda akai masa zancen
mulkin nan da aure ƴar sauran fara'ar fuskar tasa ta ɓace ɓat duk da shi ba mutumne miskili ba,
maganarce dai sai ya zaɓa da wanda yay niyyar yi saboda jin kansa da yay gado gurin uwa. Gaba ɗaya a
kwanaki biyun nan daga gaisuwa babu ruwansa da kowa a gidan. Gashi kuma Ramadhan yayi mugun
tsanar driving a rayuwarsa, ita da Bappi ne kawai ke shigar masa hanci akan ya tuƙasu ko yanaso ko
bayaso. Amma daya tuƙa mota ya gwammaci ma ya hau mashin, shiyyasa mashina ɗinsa kusan uku a
gidan.
Duk da yanda yaga bayan motar daya ɗakkoma key tayi ƙura haushi ya hanashi komawa ya canjo key.
Sai Alu ya ƙwalama kira akan yazo ya fidda masa ita daga runfa. Lokacin da Bappi ke fitowa cikin jallabiya
dan bai canja kayaba hula kawai ya sanyo saboda yamma ce garin yayi luf da alamar hadari. Ramadhan
dake amsar motar a hannun Alu ya miƙa hannu ya buɗema Bappin gefensa, dan yasan in har shine zai
tuƙasa a mota baya zama baya.
Koda Bappi ya shigo komai baice masa ba ya ɗaura belt tamkar yanda Ramadhan ɗin ke ƙoƙarin saka
nashi, dan shi ƙa'idarsa indai zaiyi tuƙi baya ƙin saka belt ɗin, dan mutum ne mai tsananin son bin doka
koda ace sauran ƴan ƙasa na mata riƙon sakainar kashi.
Tunda motar ta shigo Doctor Shamsu ya fahimci su bappi ne, sai ya zare jikinsa da ga wajen hayaniyar
ya nufesu. Shine ya buɗema Bappi ƙofa ya fito, zai risina domin gaisheshi Bappi ya hana ta hanyar riƙo
hannunsa. Cikin kunya da girmamawa Dr. Shamsu ya yarda suka gaisa, kafin yace, “Ranka ya daɗe sun
riga sun tara mutane, ina ganin muje daga ciki sai na shigo da su”.
Bappi baiƙi hakan ba, dan daga inda yake yana hango yanda M. Dauda da abokinsa ke zazzaga masifa
ga mutane da securitys ɗin asibitin zagaye da su. Wasu na musu kallon mahaukata wasu na dariya, wasu
najin daɗin abinda sukeyi na yaɓa magana ga Alhaji Hameed Taura.
Ramadhan da baida niyyar fitowaba sai ya kwantar da kujera ma abinsa ya lumshe idanu tare da ƙara
ƙarfin a.c dan garin yay luf-luf dayin dumm alamar hadarine, sai ɗan zafin ya bada yanayin jinsa a cikin
jiki kawai.
Da ƙyar Dr. Shamsu ya lallaɓa su M. Dauda zuwa office ɗinsa. Sai dai duk wani iya shegen da suka
shigo da shi suna cin karo da fuskar kamala ta dattijon arziƙi Alhaji Hameed Harith Taura ya gudu. Cikin
ɗan rawar jiki suka zube a ƙasa tun daga ƙofar office ɗin. Ɗan murmushi yay musu yana girgiza kansa.
“A'a haba kutashi ku ƙaraso Please”.
“Alhmdllhi Doctor ya kirani yaymin bayanin komai game da zuwanku nan, kuyi haƙuri ba'a hanaku
shiga gareta bane dan baku isaba, kawai dai saboda tsaro ake taka tsantsan, gashi kuma bamu da
tabbacin abinda kuka faɗa ɗin...”
“Wlhy ranka ya daɗe ni mahaifinta ne, ama ɗauka hotona a nuna mata”. M. Dauda ya faɗa cikin zillo
yana katse Bappi.
Murmushi Bappi yayi, dan shima dai yaga yanayin jini, sai dai taba data cinye M. Dauda ɗinne ya
ɓadda ainahin kamanin nasa da Raudha.
“Ai bama sai ankai ga nan ba. Yanzu bara muje ɗakin kawai”.
Kafin ma Bappi ya miƙe su har sun fice, ya ɗan girgiza kansa yana murmushi dan dariya suke bashi.
Suna abune tamkar wasu firgitattu...........✍
https://arewabooks.com/chapter?id=629a77b967809ad6daab2109
*_Chapter 13_*
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_Episode 17_*
............★Raudha na zaune yau an cire ƙafar tata a jikin ƙarfen dan kumburin ya sauka sosai, maimakon
tayi ramar ciwo sai ta ƙara haske da ƙyau saboda samun canjin waje, ga abinci mai ƙyau ga a.c.
Idanu taɗan waro saboda mamakin ganin mahaifin nasu, cikin rawan baki tace, “Abbanmu!”.
Wannan kawai ta isa amsa ga bappi, dan cike da zumuɗi shima M. Dauda ya nufa gadon yana ware
hannuwa wai zai ringume Raudha irin na turawa kar Bappi ya rainasu yaga su ƴan ƙauyene basu iya
tattalin ƴaƴa ba. Sai dai kuma tunkan ya ƙaraso Raudha tai saurin ɗaukar filo ta tareshi tana faɗin,
“Abbanmu lafiya?”.
Sosai dariya ta nema kufcema Bappi, yay ƙoƙarin kauda kansa yanayi ƙasa-ƙasa. Dan M. Gambo ya
matsa da sauri ya ɗirkama M. Dauda dundu a baya. “M. Dauda ka nutsu mana miye haka zaka zubar
mana da mutunci”.
Harararsa M. Dauda yayi, cikin yin ƙasa da murya yace, “Kai baka gane ba, idan ba'ayi hakan ba ai sai
attajirin nan ya ɗauka bama kula da ƴaƴanmu, kasan su haka sukema ƴaƴansu kamar larabawa da
turawa. Ko so kake yay tunanin dan munga sun raɓesune muka fara son su”.
“Eh kumafa hakane kayi gaskiya, sai dai kasan Raudhatu ustaziya ce bazata yarda ba fa, karma kaja ta
bamu kunyar datafi wadda muke gudu”.
Duk zancen nasu sarai Bappi najinsu duk da a hankali sukeyi, dan shi ALLAH ya bashi ƙarfin ji, zama a
iya cewa a wajensa Ramadhan ya gado ƙarfin ji, ko yaya kai magana kusa da su sai sunjika da izinin
ALLAH, dan haka yay saurin katsesu dan karsu kasheshi da dariya. Ya gyara tsaiwarsa dayin gyaran murya
yana faɗin, “Ya kamata ku dubata sai muje muyi sallar magrib, na kuma san masaukinku......”
Kafinma ya kai ƙarshe M Gambo ya katsesa da faɗin, “Ai bamu da wani masauki yallaɓai, dan shi M.
Dauda ya rabu da gyatumar tata shiyyasa ta taho nan ita da yaran wajen tata gyatumar. Dama yanzu
haka munzo biko ne da duba jikin Raudhatun”.
Raudha dake jin tamkar ta fasa ihu dan takaicinsu ta kauda kanta gefe idanunta na tara ƙwalla. Tana
son mahaifinta, tana kuma fatan ya nutsu ya bar duk abinda yakeyi na ashsha, sannan sam bata baƙin
cikin nunasa matsayin uba dan bata da kamarsa..
Bappi yay saurin dakatar dasu, “Ok ok babu damuwa muje muyi sallan first dai yanzu, sai musan
abunyi kamar zaifi”.
Badan sun so ba suka bisa. Dan gaba ɗayansu idonsu nakan Haɗaɗɗun kulolin abincin dake gefen
gadon Raudhan. Sai haɗiyar yawu suke tunkan suga abinda ke a ciki.
Suna fita doctor na shigowa. Hakan yasa Raudha roƙonsa aron waya dan gara ta kira Mommy ita kam
bazata iya da halin Abba ba. Shima Dr Shamsu ya gamsu da hakan, dan haka babu musu ya bata ta saka
number Mommyn, cikin sa'a kuwa bugu ɗaya aka ɗaga. Wani daɗi ya kama Asabe saboda jin muryar
Raudhan Alhmdllhi, duk da dai da safe sunzo asibitin dubata ita da Aunty Hannah ma.
“Mommy dan ALLAH kizo asibiti wlhy Abba ne yazo shida baba Gambo”
Zumbur Asabe ta miƙe har tana neman yadda zani. Shi dauda ɗinne yazo Bingo harma asibitin da
kike?”.
“Wlhy kuwa mommy gasu ma tare da baba alhaji (Bappi take kira haka). Yanzu ya jasu suka tafi
massallaci”.
“Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Ashe kuwa zanci kaza kazan ubansu a garin nan. Ni yanzu babbar
matsalata baza'a barni shiga asibitin ba....”
“Mommy dan ALLAH ki kwantar da hankalinki banga abin faɗa anan ba. Kizo asibitin Doctor zai shigo
dake yace. Amma mommy dan ALLAH karki tayasa kuyi rikici Please”.
Tai maganar tamkar zatai kuka. “To” kawai asaben tace mata ta yanke wayar, badan tasan zata iya bin
maganar Raudha ɗin ba.
Fulani ta faɗa a hankali cike da ƙasaita tana duban mai-martaba dake kishingiɗe a tsakkiyar falon
hutawarsa da ko iyalan nasa ba kowacce keda ikon shigarsaba sai Fulani kawai.
Bai motsa ba, sai dai ya saki wani murmushin ƙasaita irin na manya, masu kuma ji da girman mulki.
Kafin ya ɗago idanunsa ya ɗan dubeta ya ɗauke kansa.
“Wai miyasa ku mata a koda yaushe baku da hangen nesa ne? Yanzu banda dai son neman magana
miya kawo zancen haɗa Aina'u da Ramadhan aure? bayan kunji Alhaji Hameed ya zaɓa masa mata...”
“Humm mai-martaba kenan, ni a ganina ai hakan ba wani abu bane, ƙara danƙon zumincine, ka tuna
fa Ramadhan shine jikanka na farko namiji a gidan nan, da ace shi ɗin ɗane da namiji ya haifa ba mace ba
shine kamarfa magajinka a yanzun, amma sam yaron nan baya son zama cikinmu, akoda yaushe sai
dangin ubansa saboda Firdausi ta gama shanyesa su kaɗai yake gani ita da mijinta, amma idan muka
haɗashi aure da Aina'u ta tayamu yaƙin jawosa jikinmu ai muma ka.......”
“Ya isa dan ALLAH. Yanzu nan Wasila bana hanaki irin wannan zancen ba? Yanzu miye abin asiri dan
Ramadhan yafi buƙatar ya rayu a gidan su?. Karfa ki manta can ɗin shine adonsa, kuma shine
tunƙahonsa, to bana son ƙara ji, hakama maganar haɗasa da Aina'u inhar ba sune suka sasanta junansu
ba bana buƙatar sake jinta. Dan har abada Alhaji Hameed bazai saka doka na karya masaba koda akan
ƴaƴana ne balle jikansa da yake da iko da shi tamkar yanda yake da iko akan mahaifinsa. Kuyi masa fatan
alkairi kawai ku tsaya matsayinku”.
Fulani ta taune lip ɗinta da ƙarfi da haƙora kamar zata hudashi, sai dai sanin halin mijin nata yasata
sakin ɗan murmushin yaƙe da cewa, “To shikenan ranka ya daɗe, yanda kace ai haka za'ayi insha ALLAH
anbar zancen. Dama can rashin zama nayi nazarine akan batun shiyyasa ban fahintaba.”
(Hummm Fulani kina kaka inaga gimbiya Su'adah uwar miji. To maji yaya za'a kwashe to😜🏃).
___★____★___
*_BINGO CITY_*
Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Asabe da M. Dauda lokacin da akai kici-ɓus. Dan kuwa dai doctor
Shamsu da kansa ya shigo da Aunty Hannah da Asabe, shigowarsu babu jimawa kuma Bappi da su M.
Dauda suka dawo ɗakin domin yin sallama da Raudha.
Asabe ce ta fara janye idanunta tana jan tsaki, hakan yasa M. Dauda da jikinsa ke tsuma da sabuwar
ƙaunarta matsowa kusa da ita cikin ɗan rawar jiki. “Haba Asabe nine fa Dauda ɗinki, dan ALLAH karkiyi
fushi dani wlhy sharrin shaiɗanne”.
Hannunsa dake neman taɓata ta buge tana faɗin “Kaine sheɗan ɗin kanka ai macuci kaw......”
“Mommy Please!!.....”
Raudha ta faɗa tana fashewa da kuka dan tasan komai zai iya faruwa akan iyayenta na raba hali. Asabe
zata sake magana Bappi daya fahimci su ɗinne iyayen Raudha ɗin yay saurin dakatar da ita.
“Inaga nan ba wajen magana bane, kamar zaifi muyi haƙuri muje daga waje ko masaukinku ko? Ko
kuma mu bari zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.....”
“A'a dan ALLAH ranka ya daɗe gara ayita yau ta ƙare, idan ta bar nan bazata sake yarda na gantaba,
zama ta iya sace Aminar daga nan ɗin itama”.
Harara Asabe ta balla masa, sai dai riƙe hannunta da aunty Hannah tayi ya sata yin shiru ta haɗiye
abinda taso faɗa.
★
A tare suk rankaya gidansu Asabe, sai dai Bappi motar Dr Shamsu yabi yace Ramadhan ya koma gida,
dan sanda suka fito barci ya samesa yanayi a cikin mota, ya sanshi da barcin wuri, dan shi ƙa'idarsa da
tara na dare tayi to ya kwanta kuma. Sai dai kwana biyun nan daya tsinta kansa a NAYA hakan bai
kasanceba, shiyyasa daya ɗan kaɗaice sai ya kama barci saboda tsabar buƙatarsa da yake yi.
Rikicewa sosai Hajiyar Birni tayi da ganin Alhaji Hameed Harith Taura har cikin gidanta. Mutumin da
bata taɓa tunanin koda ganin motar hawansa ba a hanya balle shi kansa. Babban abinda zai birgeka da
shi babu wani damuwa ko tsantsamin gidan tare da shi, hasalima da aka kawo ruwa shine ya fara sha
tare da godiya.
Su M. Dauda dai an nutsu saboda hararar da Hajiyar Birni ke antaya musu tamkar ƙwayar idonta zai
fito.
“Kuyi haƙuri da lattin zuwan gareku matsayin wanda ƴarku tai kasadar bama kariya. Da farko dai
naso ace sai ta samu lafiya zanzo da kaina na kawota gareku nai muku godiya na kuma baku haƙuri. Sai
dai an samu akasin hakan a dalilin zuwan waɗan nan bayin ALLAH da ayanzu na fahimci shine mhaifin
*Raudhat*. Duk da dai na haɗu da ita mahaifiyarta a aaibiti tun randa abun ya faru, hakama ku da
bansan matsayinku garetaba har yanzun. Zanyi amfani da wannan damar domin neman afuwarku, ku
gafarceni, da nasan Raudhat zatayi wannan kasadar domin ni tabbas zan dakatar da ita, sai dai masu iya
mafana kance ƙaddara ta riga fata, sai muce ALLAH ya bata lafiya ya albarkaci rayuwarta. Ku kuma kuyi
haƙuri ku koma tare dan na fahimci baƙwa tare da juna, kuma Raudhat batajin daɗin hakan”.
Kafin kowa yace wani abu hajiyar birni ta amshe zancen cikin washe baki. “Ai muke da godiya ranka
ya daɗe, ALLAH ya saka da alkairi bisa kulawar daka nuna akan Raudha, dan bamu taɓa zaton hakan ba.
ALLAH ya kara lafiya da nisan kwana. Suko babu sauran aure a tsakaninsu dan saki uku ne yallaɓai......”
M. Dauda yay wata zabura tare da fashewa da kuka. “Ni wlhy ina son matata kuma a bincika ba'a
cikin hayyacina na saketaba ranka ya daɗe...”
“Eh wlhy wani malami yace asiri Larai ta maka ai”. M. Gambo ya amshe zancen yana matsar kwalar
ƙarya shima. Dan dukansu kowa da abinda ke ransa tsakanin shi da M. Dauda ɗin.
Hajiyar birni ta amshe zancen da faɗin, “ALLAH yayama wannan malami albarka tare da Larai, dan
sun taimakeni da suka aikata wannan asiri matsiyaci”.
Kuka M. Dauda ya sake fashewa da shi yana fyatar majina da tsohuwar babbar rigarsa tare da
matsawa zai duƙa gaban hajiyar birni ta daka masa tsawa. Itama Asabe miƙewa tai cikin masifa sai dai
duk Bappi yay azamar dakatar dasu dan shikam baisan hayaniya a rayuwarsa.
“Inaga dan ALLAH ayi haƙuri tunda dukanmu nan ba yara baneba. Kamar wannan magana tana
buƙatar nutsuwa kuma tsakaninku ne. Dama nima akwai abinda ke tafe dani game da Raudhat. Dan
tayimin abinda wani mahaluki bai taɓa minba a rayuwa, bani da abinda zan sakanka mata da shi amma
ina buƙatar irinta a kusa dani. Ma'ana inason ku bani aurenta dan ALLAH ko ta hanyar hakan zan samu
damar kwatanta mata kwatankwacin alkairin data min nima...”
Gaba ɗayansu suka waro idanu a kansa, tare da auna shekarunsa dana Raudha. Cikin rawar baki
Asabe tace, “Alhaji kai da kanka?”.
Karon farko ya saki ɗan murmushi domin ganin yanda duk sukai diri-diri, gasu dai a mu'amulat
tamkar mutanen banza, ƴarsu kuma nutsatstsiya kamila, amma ashe sun san abinda ya cancanta, amma
bara ya sake gwadasu. Numfashi yaja ya fesar da gyara zamansa.
“Eh ni da kaina”.
M. Dauda ya faɗa cikin zallo da rawar jiki yana sake gurfana gaban Bappi tamkar mai neman gafara.
Da sauri Asabe ta amshe da, “Nidai dan ALLAH ka gafarceni Alhaji ban amince ba, Raudha bazata
auri tsoho sa'an kakanta ba. Son zuciyar da naso tafkawa a baya na biye maka Dauda kan alhaji Maude
Dallatu ya kaimu ga zuwa wannan matsayin, yanzu ko na gane gsky mutuncin ƴaƴana da ƙyautata
rayuwarsu yafiyemin komai a duniya dan sune gatan wata rana. K....”
Hajiyar birni ta faɗa cikin daka tsawar data saka Bappi toshe kunne tilas. Aunty Hannah ma da illahirin
jikinta ke rawa tun fara mganar Asabe saurin fincikon Asaben tai baya da faɗin, “Asabe kina da hankali
kuwa? Kinsan wanene shi a ƙasar nan?”.
Kuka Asabe ta fashe musu da shi. Cikin matsar kwalla tace, “Adda ni babu ruwan da koshi ɗin
wanene. Ina duba rayuwar ƴaƴana ce, bana fatan su tashi a irin tamu rayuwar, fatana suyi ƙyaƙyƙyawar
rayuwa bawai ta kuɗi ko son duniya ba. Dan haka ku gafarceni, ko ni akace na auresa yamin tsufa balle
Raudha”.
A tare suka hayayyaƙo mata har M. Dauda dake jin a yanzu baya buƙatar lallaɓa Asabe, dan zata
masa ƙafar angulu ta kaisa ta barosa. Ganin suna neman harmutsa falon Bappi ya dakatar dasu cikin
roƙo. Sai da suka nutsu ya fara magana cike da dattakonsa da kamun kai.
“Lallai wannan baiwar ALLAH ta fiku gaskiya, dan kuwa tayi ƙyaƙyƙyawan hange da iyaye da yawa
kan kasayi harma da ƴammatan wannan zamani akan auren wanda yake da manyan shekaru. Lallai ke
ɗin uwace ta gari, kuma na gode da yanda kika nuna mutuncin ƴarki da farin cikinta shine gaba a ranki
fiye da kuɗi ko wani matsayin da rayuwa ke bama bawa mai ƙarewa. Banzo nan dan na koma da
buƙatata ba. Dan haka zan sake roƙonki a karo na biyu. Ina son ki yarje mijinki mahaifin ƴarki ya bama
jikana auren ƴarku dan ALLAH badan wani matsayi namu ba ko abinda muke da shi. Domin Raudhat a
yanzu tana buƙatar ta samu tsaro kodan rayuwarta dake a cikin haɗari, to zamanta anan tare daku kuma
komai zai iya faruwa harya shafeku. Badan mu zamu iya kareta ko hana wani ƙaddara sauka gareta ba,
domin muma bayin ALLAH ne kamar ita, kamar kuma ku. Alkairin da taiminne yasa nakejin kwaɗayin
ɗaukarta ta zama ɗaya daga cikin family ɗina. Ta kuma haifamin jikoki daga tsatsonta da nake fatan suyi
koyi da ƙyawawan halayenta wanda tarihi bazai taɓa gogewaba daga abinda ta aikata na alkairi a
gareni”.
A kusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya, tare da zubama Asabe ido. Zukatansu har zallo suke nason
jin amsar da zata bama Bappin.
Taja kimanin wasu dogayen mintuna tamkar mai nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.
“Amma dan ALLAH Baba miyasa bazaka duba akwai tazarar rata tsakanin jikanka da ɗiyata ba.....”
“Babu wani banbanci ɗiyata, domin kuwa dukanmu ALLAH ne ya haliccemu, ya kumace mu bauta
masa shi mai rahamane ga duk wanda yayi biyayya ga hakan, sannan mai azaba ne ga duk wanda ya
bijire masa. Dan haka ki sani babu wanda yafi wani a gun ALLAH sai wanda yafi jin tsoronsa. Ni da ku da
Raudhat duk abu gudane. Mutanene masu barci, masu kashi, masu mantuwa, masu shagala, masu...
Masu.... Masu..... Da yawa.”
“Hakane ranka ya daɗe. Na gamsu da bayaninka, zan kuma iya amincewa da buƙatarkane idan har
Raudha ta amince da auren jikan naka”.
Babu wanda baija ajiyar zuciya ba a falon, kafin suɗan ƙara tattaunawa da Bappi, daga ƙarshe yay
musu sallama suka rakasa har wajen Dr Shamsu dake jiransa a mota dan shi bai shigo ba. Tare da su M.
Dauda suka tafi, dan yace zai kama musu masauki tunda nan babu wajen kwana.
https://arewabooks.com/chapter?id=6299deaa67809ad6daaa6509
*_Chapter 11_*
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
*_Typing📲_*
*_Episode 18_*
............Tun bayan wucewar su Alhaji Hameed Taura Aunty Hannah keta faman kai kawo a ɗakinta da
kiran number First lady. Sai dai kuma tayi kira yakai biyar amma ba'a ɗagaba. Ta sake duban agogo ƙarfe
goma da mintuna ashirin da huɗu. Tasan yanzu first lady batai barci ba, da wahala kuma ace tana tare da
president, sai dai idan wayar ta bari a wani waje. Wannan tunanin ya sata canza akalar kiran ta tura
mata guntun saƙo, da ga haka ta ajiye wayar ta faɗa wanka zuciyarta fal wasiwasin ta yanda zata
ɓulloma Raudha da Asabe su amince da auren nan cikin sauƙi.
*_WASHE GARI_* first lady ce ta tada Aunty Hannah a barci, dan ko sallar asuba bata tashi tayi ba har
kusan 7am. Da ƙyar ta lalubo wayar takai kunnenta tana faɗin, “Hello waye?”.
Amsar da first lady ta bata ya sata wartsakewa babu shiri ta tashi zaune. “Ranki ya daɗe sorry barka
da safiya! Wlhy barcine a idona”.
Kanta ta jinjina saboda amsar da first ladyn ta bata tana faɗin, “Okay to babu damuwa gani nan
zuwa yanzun nan insha ALLAH”.
Su Asabe na a falo suna karyawa aunty Hannah ta fito cikin gayu na ɗaukar hankali. Fatisa da Fatima
dake sanye da Uniform ɗin wajen abincin Hajiyar Birni suka fara gaisheta da yaba ƙyan nata. Tai
murmushi tare da musu alamar love da yatsunta. Kafin ta ɗauka doya guda a cikin plate ɗin Asabe. “Ƴar
uwa barka da safiya”.
Duk da Asabe tayi mamakin gaisuwar saita share ta amsa mata. “Barka dai Adda fita zakiyi ne?”.
“Aiko da zakibi ta wajen asibiti ne dana biki sai na sauka dan inason yin magana da Raudha game da
zancen nan na jiya karma suje su yaudareta abun yay nisa gara na sani”.
Hajiya mama dake fitowa daga kicin a masife tace, “O ke Asabe wai mike damun kanki ne dan
ALLAH? Ƙiri-ƙiri kina neman mana baƙin ciki da arziƙin dake tinkaromu!. Alhaji Hameed Harith Taura fa
akace. kinsan wanene Taura kuwa a ƙasar nan dama Africa gaba ɗaya?”.
Kafin Asabe tace wani abu aunty Hannah tai murmushi da amshe zancen tana ƙyaftama Hajiya
mama babbar yayar tasu ido. “A'a Hajiya Mama karkiga laifin Asabe. Tana da gaskiya wlhy, ya kamata
muji ta bakin Raudha mu kuma binciki halin yaron, dan aure ba abin wasa bane. Tunda ba kuɗin zata
aura ba mai kuɗin zata aura”.
“Yauwa Adda dan ALLAH ki fahimtar dasu. Dan naga su dukiyar waɗan nan mutanen kawai suke
kallo har shi uban nata da dama kwaɗayayye ne. Yanzu idan ta auresa bata son sa, ko taje tana shan
wahala fa? Ai kunga mun tauye mata rayuwa”.
Hajiya Mama ta danne ɓacin ran maganar Asabe da ƙyar tana ƙaƙaro murmushi. “Hakane kuma
Asabe yanzu na fahimceku. Ki bar Hannah kawai ta wuce maje wajen Raudha ɗin tare tunda dama jiya
banje ba”.
Badan Asabe taso hakan ba ta amince. Aunty Hannah tai musu sallama ta fice kusan tare da su Fatisa
da zasu hau keke napep dan hajiyar Birni tuni ta jima da wucewa ita.
*_GOVERNMENT HOUSE_*
Tun tattaunawar da sukai da aunty Hannah ɗazun da safe ta kasa zaune ta kasa tsaye, dakon
shigowar shugaban ƙasa kawai take gidan, amma har zuwa yanzu ƙarfe goma sha biyu na dare babu shi
babu labarinsa. Duk da dai tun kusan tara na daren ya shigo gida, sai dai sun shiga meeting ne shi da su
Alhaji Yaro glass, kuma har yanzu basu fitoba. Tai ɗan gajeren tsaki tana tura hular kanta baya ta faɗa
saman kujerar, duk da sanyin ac dake gauraye da falon wata irin zufa takeji mai mannewa iya fata da jini.
Ta zame rigar sama ta kayan barcinta dan itama nauyi take mata saboda tsabar ƙaguwa. Rashin mafita
ya sata zamewa ta kwanta a kujerar, dan ta ɗau alwashin ko zai kai asuba tana nan tana jiransa.
Shugaban ƙasa da ya shigo a matuƙar gajiye ya faɗa lokacin da yake zubewa saman kujerar gefenta.
Zumbur ta miƙe zane tana ware idanunta a kansa, sam bataji motsinsaba, duk da dama tasan shi bai
damu da sallama ba dan zai shiga waje.
“Lafiyar nan da sauƙi wlhy tun ɗazun zaman jiranka nakeyi anan excellency ”.
Fuska ya sake ƙwaɓewa yana ture hularsa. Cikin tabbatar da matuƙar gajiyar dake tare da shi da barci
yace, “Bushira kiyi haƙuri babu abinda nake buƙata a yanzu irin barci da wanka”.
“Shiruna bazai yuwu ba, inko nayi to zai iya cutar damu baki ɗaya. Dan maganar ta shafi shugaban
ƙasar da kuke son ɗorawa na wucin gadi” Bata bashi damar yin magana ba ta cigaba da tata maganar
saboda ganin ya bada hankalinsa gareta. “Tunda ka sanarmin ƙudirinku akan Alhaji Hameed da jikansa
daya kawo a maimakonsa naketa nawa ƙoƙarin nima. Dukanmu munsan Ramadhan a yanzu baida mata,
tunda kune kukai sanadin rasa matar tasa, shiyyasa nake ganin a yanzu ma inhar kuna buƙatar
mutuwarsa kamar yanda kuka tsara (wa'iyazubillah 🤦🏻) to dolene sai mun haɗa da matarsa, dan itace
mafi kusanci da shi da zatai mana aiki batare da wani zargi ya shiga ba. Kaga kenan mune ya dace mu
bashi mata a karo na biyu”.
“To amma.....”
“Nasan tambayarka itace bai wuce ina zamu samu ba? To na gama da wannan matsalar, yarinyar
data bama Alhaji Hameed kariya a filin idi ɗiya ce ga ƙanwar Hannah tsohuwar matar Alhaji Yaro, kuma a
yanzu haka Alhaji Hameed ya buƙaci su bama Ramadhan auren yarinyar, sai dai mahaifiyarta na neman
bijirewa dan tace sai idan yarinyar naso. Amma babanta ya yarda saboda shegen ƙwaɗayi, hakama
hajiyar birni da su su Hannah ɗin, duk da dai ita Hannah muna tare, dan itace ma ta tabbatar min inhar
Asabe ta nunama yarinyar bataso itama bazata amince ba saboda tanada kafiya da son uwar sosai......”
“Bushira sorry na katseki, ni abinda ban fahimtaba anan, ribarmi zamuci na shiga maganar tunda sun
gama ƙulla zancen auren? Inhar kuma yarinyar zata iya bijirema auren muma zata iya ƙin amsar
buƙatarmu ai. Sannan karki manta Hannah zata iya yin komai danta rama korar kare da Alhaji Yaro yay
mata. Imagine ma ace kina tare da Hannah har yanzu batare dana sani ba”.
“Duk yanda kuke tunanin Hannah ba haka take ba, tana son Alhaji yaro har yanzu, kuma ta san ba
laifinsa bane laifin Fanta ne. Amfanin auren yarinyar nan a garemu Hannah zata iya sakata tai mana
aikinmu cikin siyasa batare da ita kanta tasan ita ta kashesa ba, kai koda ta sani ko muna tunanin zata
sani itama zamu iya kashetan dan mulkin dai ya koma hannun Alhaji Yaro. Kasan kuma inhar zaka
taimaka Hannah ta koma gidan Alhaji yaro zata aikata komai har mutuwar yarinyar, dan da arziƙi a garin
wasu gara a naku, a garin wasunma gara a gidanku, a gidankun ma gara a ɗakinku, a ɗakinkun ma gara a
kanka. So zataima kanta yaƙine itama”.
Karon farko ya kwashe da dariya yana kamo hannunta. “Oh woow gimbiyata! yanzu dai na fahimci
komai wlhy. Gaskiya kinada kai tawan. To amma mu yanzu wace rawa zamu taka?”.
“Yauwa yanzu kai magana shugaban ƙasar NAYA. Abinda zakuyi shine ku samu mahaifin yarinyar ku
jikesa da mahaukatan kuɗaɗe. A bashi gidan zama, itama uwar a jiƙeta tare da mahaifiyar su Hannah ɗin,
dama duk wanda keda faɗa aji akan auren. Sannan ku samu Alhaji Hameed ku nuna masa goyon
bayanku akan auren da nuna cewar yayi hallaci ya cancanci yabo, kar kuma ya yarda yarinyar ta suɓuce
ga Ramadhan dan irinsu akeso ga mulki zasu taimaki talaka. So ko yarinyar ta bijire bataso bazata taɓa
samun haɗin kan kowaba ita da uwar dole su amince”.
Tashi yay kawai ya rungumeta, ji yake tamkar ya haɗiyeta dan daɗin wannan shawara tata. Tun a
daren ya turama su Alhaji Yaro glass saƙo da ɓoyayyar number ɗinsa da su kaɗai keda a laƙa da ita akan
gobe akwai mitin ƙarfe 6 na safe kafin ya fita office.
Dukan shawarar da First lady ta bada su Alhaji yaro glass sun aiwatar da ita ta hanyar nuna cewa
sunyine dan Alhaji Hameed Taura da kuma Ramadhan dake matsayin surukinsu a da, dama zamansa
haka babu aure na damunsu. Hundred percent Alhaji Hameed Taura ya yarda.
M. Dauda kam da su Hajiyar birni haukacewa sukai dan farin ciki, dan manyan kuɗaɗe da aka mallaka
musu. M. Dauda, hajiyar birni. Asabe, Hajiya mama. M. Gambo. Kuɗaɗene da zasuja jari. Koda Asabe ta
nuna hakan bai mataba hajiyar birni masifa ta dinga mata, harda rantsuwar inhar bata yarda Raudha ta
auri Ramadhan ba wlhy sai ta tsine mata, kuma sai dai ta ɗau Raudha subar garin dan bazata zauna
inuwa guda da mai mata baƙin ciki ba.
Kalaman hajiyar birni yay matuƙar tada hankalin Raudha da aka sallamo daga asibiti yau, dan
Alhmdllhi ƙafarta tayi sauƙi sosai saboda kula da take samu da ingantattun magunguna gashi bata da ƙan
jiki. Bazataso a sanadinta a tsinema mahaifiyartaba. Sannan idan sun bar nan ina zasuje, tunda babu
wanda ke garesu sama da su a yanzun. Dan haka tace ita ta amince zata auresa duk da batajin son
Ramadhan a ranta ko kaɗan, sai dai a gani guda datai masa har zuwa yanzu tanajin kwarjininsa cike da
idanunta, yayinda kalamansa ke zaune daram cikin ranta shiyyasa takejin matuƙar tsoro. Amincewa
aurensa na nufin tabbatuwar kalamansa gareta, sai dai kuɗi ya rufe idanun iyayenta sun kasa fahimtar
ni'imar da suke ganin suna ciki *_BAƘAR INUWA..._* ce, gara ranar da suke ciki da ita. Zata amince
domin gujema hawan tsinuwa akan mahaifiyarta, zata kuma amince dansu samu farin ciki koda ita zata
rasa nata farin cikin. Dan duk wanda ya dubeta ya dubi Ramadhan ya tabbatar shi ba tsaran aurenta
bane ba, kawai dai kakansa ya kalli abinda tai masane da tunanin zai mata tukuyci da auren alhalin bazai
zame mata irin inuwar da shi yake hango mata ta jin daɗi ba.
A lokacin da waccan cakwakiya ke gudana a gidan su Raudha anan fadar shugaban ƙasa shugaban
jam'iyya ne ya fitar da sunan ɗan takara a yau a zaman taron da akayi yau ɗin na manyan jam'iyyar. Inda
kamar dai yanda aka saba wasu suka nuna jayayya akan Ramadhan ɗin kodan ƙarancin shekarunsa, tare
da kawo hujjar bai san siyasa ba, bakuma zai iya ba tunda bama zaman ƙasar yake ba, bai san komai na
wahalar talaka ba.
Idanu Ramadhan ya rumtse da ƙarfi saboda wani irin sarawa da kansa yake masa a dalilin hayaniyar
da ɗakin taron ya kaure da shi. Dama da ƙyar Bappi ya sakashi zuwa wajen taron har sai da ya nuna ɓacin
ransa shi da Anne da Pa. Koda ya shigo yaga mutanen dake wajen daga sa'an Pa sai sa'annin Bappi baiji
ko ɗar ba, a lokacinne ma yaji kibiyar son yin mulkin ta soki ƙirjinsa. Dan yana ganin yakamata sumafa
matasa ace anayi dasu a ƙasar NAYA dan sune ƙasar.
A yanzu kuma boren nasu ya sake harzuƙa zuciyarsa dajin eh lallai zai amince ya amshi mulkin ƙasar
NAYA inhar ALLAH ya saka hakan a cikin ƙaddarar rayuwarsa. Da ƙyar shugaban jam'iyya ya tsawatar akai
shiru, kafin ya yanke hukunci akan gobe za'ai primary election duk da a ransa yasan dolene candidate
nasu ya tsallake. Duk sun amince da hakan, daga haka kuma taron ya watse wasu ransu ɓace wasu ransu
fal murna, sai dai masu murnar zukatansu sun rabu gida biyu akan dalilin murnar.
Wani meeting ɗin su Alhaji yaro glass suka sake shiga iyakarsu kaɗai akan batun, kafin kuma da
yamma shugaban ƙasa da shugaban jam'iyya su sakeyin wani zaman da wasu jiga-jigan jam'iyyar.
*_JIHAR DILLO. HUTAWA L.G.A_*
Koya ya shiga matuƙar mamakin yanda M. Dauda ya dawo garin hutawa a jiƙe da kuɗaɗe shi da
abokinsa, dan maimakon su rufe sirrinsu sai sukazo sunama jama'a fankama da kuɗi da nuna sumafa sun
kai yanzun. bama shi ba abokinsa M. Gambo ma dai ajiƙen ya dawo. Nan take aka fara ƙananun magana
da dangantasu da ɓarayi saboda hankalin jama'a ya tashi musamman da suka san dai ba ko sisi su M.
Dauda ke magani ba, dan inhar ba sata ba ko wannan kidnapping da akeyi ba babu ta yanda za'ai daga
barinsu gari na kwana uku su dawo haka. Aiko nan take manyan anguwa suka haɗa kai suka kai ƙararsu
gidan hakimi, hakimi baiyi ƙasa a gwiwa ba ya aika a ka kira masa su M. Dauda daya saka innarsa da
iyalansa haɗa ƴan kayansu dan so yake a gobe ya fara gyaran gidansa. A gefe kuma yana tunanin sake
sabon aure da lallaso Asabe ta dawo (bayan saki uku ne tsakaninsu🙄).
Hakimi da ƴan fadarsa babu kalar binciken su M. Dauda da basuyiba amma sun dage akan sufa
basu kuɗin nan akayi. Ganin kamar suna son rainama fada hankaline saboda ambatar sunan manyan
mutane da sukayi yasa hakimi saka ƴan sanda suje da su. Haka kuwa akayi, a ranar a police station suka
kwana, washe gari hakimi kuma ya kai magana fadar mai-martaba sarkin Dillo. Bako a ɓata lokaciba
wajen yayubar su M. Dauda sai cikin birnin Dillo fadar sarki.
Nan ɗin ma dai amsar da suka bama hakimi ita suka bama sarki akan inda suka samo kuɗi, sai dai
shima bai gamsu ba saboda sunayen da su M. Dauda ɗin suka ambata na manyan mutane. Sai ma
hankalinsane daya sake tashi dan gani yake kamar su M. Dauda nason yin amfani da sunan manyan ne
dan ɓata musu suna. Baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen fara neman waɗanda yakeda kusanci da su ciki harda
Alhaji Hameed Taura da tarihi ya nuna karatu ya taɓa haɗasu a jami'a.
Da ƙyar ya samu damar magana da shi a ranar ta hanyar P.A ɗinsa, bayan sun gaisa cikin mutunta
juna matsayinsu na manya da ƴar tsokana ta tsoffin abokai mai-martaba yayma Bappi bayani game da su
M. Dauda. Da farko sam Alhaji Hameed Taura bai gane ba saboda baiyi tunanin su M. Dauda sun koma
ba, kuma shi har yanzu ma bai basu ko sisi ba su shugaban ƙasa ne sukai musu ƙyauta. Sai da aka haɗashi
da M. Dauda, yana ko jin muryarsa ya gane, amma duk da haka sai yasa aka tura masa hotunansu ta
email.
Yana gani kuwa ya gane, dan haka yayma mai-martaba bayanin da zai iya fahimta. Jin alaƙar dake
shirin faruwa tsakanin su dan babu wanda baisan abinda yaso faruwa da Alhaji Hameed ɗin ba ran salla
sai shima mai-martaba ya shiga mamaki, harma yake cema Alhaji Hameed anya kuwa baya ganin tun
farko dama akwai dalilin daya saka yarinyar masa garkuwa.
Alhaji Hameed Harith Taura mutum ne mai sauƙin kai da tsarkake abu koda ace yazo a yanayin daya
kamata a zargesa, hakan yasa shekaru aru-aru su Alhaji Yaro glass keta cutarsa yana ƙyautata musu zato
dan bai taɓa damuwar zama ya zargesu ba. Cikin nutsuwa ya fahimtar da mai-martaba shi dai zaiyi ne
bisa ƙyaƙyƙyawar niyya, kuma baijin yarinyar zata aikata haka dan yarinyace ƙarama kuma nutsatstsiya.
Cikin ƙanƙanin lokaci mai-martaba ya yarda dan shima mutum ne mai fahimta, harko yay alƙawarin
za'a dama dashi a harkar bikin shine ma uba ga Raudha tunda dai a ƙarƙashin mulkin jiharsa take. Alhaji
Hameed yayi matuƙar farin ciki yayi kuma godiya.
Wannan shine ya wanke su M. Dauda wajen hakimi da sarki, sai dai ga jama'ar gari sun ƙara gaba
wajen ƙananun magana musamman da akaita dawo da zancen abinda Raudha tayi da kuma dalilin
rabuwar Asabe da M. Dauda ɗin da ba'a wani jima ba. Kafin kace kwabo zance yaje bakin ƴan jarida da
yanar gizo harya fara yawo...........✍
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
19
*_Typing📲_*
*_Episode 20_*
Ƙananun magana da surutan dake faruwa a gari dama wasu manyan kafafen yaɗa labarai dana yanar
gizo baisa Alhaji Hameed Taura ya damu ba ko janye maganar auren Raudha da Ramadhan. Dan
cecekucen jama'a yayi dai-dai ne da cin primary election da Ramadhan yayi zancen tsayawarsa takara ta
fito fili. Aifa jama'a da ƴan siyasa ƴan bani na'iya suka samu nayi, yayinda magoya baya keta faman
murna. Ƴan jam'iyyun hammaya kuwa tuni suka fara cece kuce akan sam Ramadhan bai cancanci fitowa
takarar shugabancin ƙasar NAYA ba. Saboda dalilai masu yawa.
Ɗan jarida dake hira da wani riƙaƙƙen ɗan siyasa a jam'iyyar hamayya ya gyara zama da faɗin, “Ranka
ya daɗe miyasa kuke ganin bai cancanta ba bayan shiɗin matashine mai jini a jika da ba'a taɓa ko
kwatanta shugaban ƙasa mai ƙarancin shekarunsaba a ƙasar NAYA? Sai nakega kamar wannan wani
al'amarine daya kamata kowa yay murna da shi tare da yabama jam'iyya mai mulki data kawosa dan
sunyi abinda ba'a taɓa yiba suma. Sannan Ramadhan B. Taura kowa yasan gidansu akwai kuɗi, a cikinsu
ya tashi babu yanda za'ai ya handame kuɗin Al'umma tunda ba baƙonsa bane kuɗin”.
Wata ƙasaitacciyar dariya Alhaji Andi ƙaura ya sake. Kafin ya haɗe fuska da faɗin, “To ai kuɗin daya
tashi a ciki suna ɗaya daga cikin abinda yasa bazai iya ba. Banda matsala da ƙarancin shekarunsa dan
koba komai muma muna buƙatar matasan ayi dasu. Sai dai kuma Ramadhan B. Taura bai cancantaba
saboda baisan komai ga wahalar talaka ba. Idan baka saniba bara na faɗa maka. Shekaru biyar da suka
wuce an kashe matar Ramadhan B. Taura da ƴarsa ta hanyar kai musu guba har gida cikin fridge sukasha
suka mutu. Idan har wanda bazai iya bama iyalansa tsato da za'a halakasu har gidaba, tayaya zai bama
ƴan ƙasa? Maimakon fa a tsaurara binciken gano wanda ya aikata sai ma yabar ƙasar gaba ɗaya ya koma
America da zama. shine bai tashi dawowa ba sai yanzu wai shi yazo yay mulkin ƙasa. Inama laifin ya fito
kansila ɗin anguwarsu ko ƙauyen Taura, amma ba NAYA ba dan babu abinda zai iya. Kai kana gani ko
primary election ɗin nan ba kuɗi daliget sukaci ba da sauran ƴan takarar da suka janye masa tunkan fara
jefa kuri'a?. Hutu da jin daɗi ya iya, yaje yayi kayarsa yabar wanda suka san wahalar talaka suyi mulkin
ƙasar NAYA”.
“To amma ranka ya daɗe sai nake ganin kamar jama'a zasuce kana faɗar duk wannan ne saboda
kaima ana zargin takarar zaka fito a jam'iyyar hamayya?”.
(Dariya).
“Dan kawai zan fito takara sai a danganta zancena da ita. To nabama duk mai saurarenmu damar zuwa
ya binciki, shin a zancena akwai ƙarya kuwa?”.
“To amma ranka ya daɗe idan za'a duba a yanzu haka Ramadhan B. Taura yana shirin angwancewa
ne da ɗiyar talakawa, wadda kowa ke ganin halaccine garesa bisa itama nata hallaccin data nuna akan
kakansa wanda taima garkuwa aranar salla a filin idi. Shin wannan bai kai a yaba masa ba kuma a ƙara
tabbatar da yasan kishin talaka da darajarsa ba?”.
“To ai wannan maganar auren nasa ga kowa ma abayyane take. Dama sunyine domin duniya tai irin
tunaninka, inba hakaba taya kake tunanin yaro kamar Ramadhan B. Taura young millioner da tun yana
ciki ake tara masa kuɗi a accaunt zai auri ɗiyar talaka mai wahalar neman na masara a kullum. Kai ita
kanta yarinyar ma a majiya mai ƙarfi tayi abinda tayine dama saboda an biyata. Sune suka sakata tayi
hakan domin ayi irin tunanin da kayi. ka auna mana, dayin abun da fitar sunansa matsayin ɗan takara
gaba ɗaya sati biyu kenan”.
Ɗan jarida ya jinjina kansa yana kallon fuskar camara man. “To jama'a kuna dai jin tattaunawarmu
da Alhaji Andi ƙaura acikin shirin SIYASA RIGAR ƳANCI dake zuwa muku anan gidan tv na G tv. Gashi mun
kwararo bayani kuma lokaci ya ɗaga mana hannu, amma ku mana afuwa sati mai zuwa zakuji ƙarashen
wannan fira insha ALLAH, zakuma kuji amsoshin zantukan Alhaji Andi ƙaura daga bakin makusancin ko
nace jam'iyya mai mulki shima insha ALLAH”.
Ɗauke hotunansu ya saka Raudha cusa kanta cikin ƙafafu ta fashe da kuka. Tun farkon fara hirar ta
zauna kallo sakamakon cin karo da hotonta da tayi tare da na Ramadhan. Da farko rikicewama tayi dan
bata gane shi bane, sai da hajiya mama dake zaune a falon tana kallo ke faɗin, “ALLAH dai ya kaimu
randa zanga wannan zuƙeƙen surikin namu ya zama shugaban ƙasar NAYA ɗiyata first lady, ɗiyata da
zakimin baƙin cikin zama uwar first lady”.
Cikin rashin fahimta Raudha ke duban hajiya maman, sai kuma ta maida hankalinta ga tvn dan itako
batama san wanda ake kira da mijin nata ba ya fito takarar shugaban ƙasa. Sosai hankalinta ya sake tashi
dajin wannan hira musamman abinda Alhaji Andi ƙaura ya faɗa akanta. ALLAH shine shaidarta batayi dan
a yaba mataba. Hasalima batasan wanene Alhaji baba ba alokacin. Amma gashi nan ta shiga bakin
duniya yau harda masu fassara al'amarin da cewar an biyatane dan tayi, wasu na faɗin neman suna da
neman gindin zama ne dama. Wasu na faɗin dan kuɗi tayi.
Surutu dai iri-iri gasu nan marasa daɗin ji, ita kanta zuwa yanzu harta fara ganin gaskiyar zantukan
mutanen, dan tana da tabbacin Ramadhan yafi ƙarfinta. Musamman da zancen fitowarsa takarar
shugabancin ƙasar NAYA ya bayyana. Sannan ita tun da ake maganar auran nan batajin ma shi ya sani,
tunda tun randa yaje asibitin nan bata ƙara ganinsa ba. Sai ma hannunka mai sanda dayay mata akan
zame mata *_BAƘAR INUWA_* inhar bata faɗi dalilinta na bama kakansa kariya ba. Idan har shi zaiyi irin
wannan tunanin dan jama'ar gari sunyi mizaisa ta zargesu.......
“Raudha!”.
Asabe ta sake kiran sunanta a karo na biyu. Ɗagowa tayi tana dubanta dan bataji na farkon ba. Cikin
tausayin ƴar tata tasa hannu ta ɗagota ta rungume. “Haba Raudha kukan nan ya isa mana. Kina sake
tayarmin da hankali wlhy. Ni nasan bakison auren nan, bansan miyasa kika amsa musu ba.....”
Cewar Hajiyar birni dake fitowa daga ɗaki a fusace. Dan yau da wuri ta baro shago saboda tana shirye-
shiryen daina zuwa wai dan zata zama kakar matar shugaban ƙasa (🤔😝😂lol).
Raudah ta saki Mommynta da sauri saboda gigitacciyar tsawar da Hajiyar birni tai mata. A take hajiyar
birni ta haɗasu su duka ita da Asaben ta zage tas Hajiya mama na tayata. Sai da Aunty Hannah ta shigo
gidan kusan goma na dare sannan tasa baki dan har lokacin sunata mita.
*_TAURA HOUSE_*
A ɓangaren Ramadhan ma da duk ƴan gidansu sunga hirar da akai da Alhaji Andi ƙaura, hakan kuma
yasa Gimbiya Su'adah jin wa ɗanta zai aura. Dan tayi-tayi Pa ya sanar mata dama yaƙi. Sai gashi yau taji a
shanun ƴan talla.
Cikin lokaci ƙanƙani ta birkice, su Lubnah na tambayarta amma bata sauraresu ba. Da suka cigaba
da damunta ma tsawa ta daka musu tai wurgi da wayar da take neman Fulani taƙi shiga ta fice zuwa
sashen Pa duk da yau ba itace da girki ba. Zaune ta iskesa shi da Hajiya Mufida sunata hirarsu. A kallo
ɗaya da sukai mata suka fahimci babu lafiya. Dan kowa a gidan yasan shegen girman kai da isar Gimbiya
Su'adah. Duk da tanada tsananin kishi kishiya bata isa fahimtar komai daga garetaba. Dan batayin wani
abu da za'a samu kafar rainata, ko kallon banza bata amince zamanyi da kishiyaba dan tace zubar da
mutunci ne. Hakan kuwa da takeyi yayi tasiri, dan kame kan nata yasa ko shirmensu suke yakan tsayane
iya su biyu, ballema suma ɗin kowa ji take da kanta abunka da kowa ubanta ya tara kuma akwai ilimi,
dama hayaniyar tasu bata wuce ta harara ko rainin wayo anama juna yatsine-yatsine ko ɗaukar kai.
Tsam hajiya Mufida ta miƙe tana tattare wayoyinta, cike da kulawa ta dubi Pa. “Bara nayo shirin barci
kafin ku kammala”.
Kansa kawai ya ɗaga mata idonsa akan Gimbiya Su'adah datai zaman ƙasaita a gefensa fuskarta
tamkar zatayo aman wuta. Sai da ta tabbatar Hajiya Mufida ta bar sashen saboda akwai cctv da ake
ganin shiga da fitar kowa daga nan falon sannan ta dubi Pa.
Kansa ya ɗan girgiza ya ɗauke ya maida ga tv. sai da yaja numfashi ya fesar kafin yace, “Komi yasa?”
batare da ya sake kallonta ba.
Bata damu da yanda yay ɗin ba, cikin kaushi da nuna a wuya take tace, “Saboda bata dace da shi
ba. Taya za'ace duk ƴaƴan sarakunan ƙasar nan dana attajirai da masu mulki arasa matar da za'a bashi ya
aura sai wannan?! Wad......”
Cikin sauri ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Su'adah bana son hayaniyar banza. Shin
ɗanki aure bautar ALLAH zaiyi? Ko auren kuɗi ko mulki?. Sannan ma ina zuwa, kina nufin Bappi bai isa
zartar da hukunci bane a kan ɗayanmu? Ita yarinyar kuma kinsan ƴar waye da kike wannan hanƙoron.”
Zatai magana ya sake dakatar da ita. “Karma ki ɓata lokacinki a banza. babu abinda zai hana wannan
auren sai idan Ramadhan ne ya mutu, ko ita yarinyar insha ALLAH”.
Ta faɗa a harzuƙe tana miƙewa zata fice batare data san katoɓara da suɓutar bakin da tayiba. Wadda ta
saka Pa binta da kallo ƙirjinsa na bugawa. (Gimbiya Su'adah ta manta har yanzu akan binciken wanda ya
kashe matar Ramadhan da ƴarsa akeyi, tun kuma a wancan lokacin an tabbatar musu wanda ya ajiye
gubar suka sha sai dai idan yanada alaƙa dasu ne tunda duk wanda yazo birthday ɗin Haseenah
makusancinsu ne. Sannan kafin wancan auren ma ta nuna borenta na ƙin Amnah saboda tanada sikila).
Pa ya faɗa a razane yana miƙewa zaune sosai. Zuciyarsa fal fargaban kar dai Su'adah nada alaƙa da
kisan Amnah. Da sauri ya girgiza kansa. Dan a halayenta babu mai kamanceceniya da iya kisan rai. Barta
dai da gadara da girman kai wannan kuma ya tabbatar jinin mulki ne ke yawo a jikinta. To amma miye
ma'anar furucinta na yanzu? Anya kuwa babu lauje cikin naɗi.
Hankalinsa ya tashi matuƙa da wannan tunane-tunanen, harta kaisa ga fitowa daga sashen zuwa
sashen iyayensa. A falo ya iske su harda ƙannen kakannin nasa su Inna sunata hira hankalinau kwance.
Yanayinsa ne ya saka Yafendo tambayarsa ko lafiya?.
Da ƙyar ya iya haɗiye kaso sittin cikin ɗari na tashin hankalin daya shigo da shi, ya ƙirƙiri murmushin
dole ya aza a fuska yana girgiza kansa. “Ba komai Yafendo, dama nazone akan batun Ramadhan”.
Bappi ya sauke ajiyar zuciya a hankali, “Dama muma shi muke tattaunawa anan, dan munga dukan
hirar da akai da Alhaji Andi ƙaura, nasan kuma itace kaima ta hargitsoka. Karka wani damu, dama
wannan itace siyasar, duk wani abu da zasu masa yarfe damu kanmu yanzu bazasu gajiya wajen
bincikosa ba. Sai dai mu mun riga munsan kanmu, addu'a kawai za'a dage da ita. Insha ALLAH a cikin
satin nan za'a kai kuɗi a tsaida magana, sai a ɗaura auran bayan an gama zaɓe hankalinmu ya kwanta.”
“Bappi haka shine dai-dai amma idan son samune dama a ɗaura auren kawai yanzu, sai ta cigaba da
zama a gidan nasu bayan zaɓen sai ta tare ɗin”.
Ɗan jimm Bappi yay yana tunani, kafin yay magana Anne tace, “Ya kamata ku fara jin ta bakin
iyayenta dai, ku basu haƙƙinsu har sai sun yanke muku lokacin da sukaga ya dace da su. Da campaign da
zaɓe har zuwa rantsarwa inaga watanni uku ne zuwa huɗu ai. To idan kunji ta bakinsu kunga yayi nisa sai
ku roƙi alfarma. Kokuma shi uban gayyar ku tuntuɓesa ko yanada wani lokaci daya tsara”.
Bappi yace, “Masha ALLAH hakan yayi kuwa. insha ALLAH zanyi magana da Ramadhan ɗin da safe
idan ALLAH ya kaimu, na tabbatar yanzu yay barci. Ni bammasan yanda za'a kwashe da shi akan wannan
barcin wurin ba yanzun. Dan kuwa ba nasa bane ba barci inhar da gaske ƙasar NAYA zai riƙe da ƙyau”.
__________________________________
Alhmdllhi kamar yanda su Bappi suka yanke shawara an kai kuɗin auren Raudha Hutawa, dan Bappi
ya dakatar da M. Dauda sake zuwa Bingo da yay niyyaryi akan son lallaɓa Asabe ta koma aurensa, yace
yay haƙuri suɗan kammala wasu abubuwan. Shima M. Gambo ya bashi shawarar ya zauna su taya
Ramadhan campaign anan daga baya sa san dabarar lallaɓa Asaben, sai shima ya gamsu.
An amshi kuɗin auren Raudha harda hakimi, hakama dangin M. Dauda kowa so yake ace da shi akayi.
Anba M. Dauda zaɓin tsaida lokaci, babu wani tunani ya yanke watanni huɗu. Duk da ba haka Bappi yaso
ba sai baice komaiba sukai fatan ALLAH yasa haka shi yafi alkairi. Dan shima Ramadhan ɗin koda ya
tuntuɓesa cayay wata huɗun, dan yafi son maida hankali akan wannan maganar campaign ɗin, ya kuma
kawo hujjar idan akai auren yanzu za'aga kamar yayine dan amfani da Raudha wajen campaign. Sai dai
abinda Bappi bai sani ba Ramadhan so yake ya zamewa auren, so yake kafin wata huɗun ya samu wani
ya aurama Raudha ɗin batare da sanin su Bappi ba.
★★★
A ɓangaren ƴan jam'iyya babu ɓata lokaci aka hau campaign ta kowanne ɓangare bayan an bada
damar hakan ga ƴan takara ta kowanne fanni. Duk wani ɗan uwa da abokin arziƙi ya fito domin tallata *_
Brr Ramadhan B. Hameed Taura (Young millioner)_* kamar yanda matasa ke kiransa. Ta ko ina posters
nashine ke yawo. Matashi na matasa kenan.
Duk wani ƙarfin halin Ramadhan da tunanin zai iya sai abin ya koma bashi tsoro, lallai siyasa ba wasa
bace ba. Ƙoƙari yake yaga ya hana duk wani ɗora matasa akan ta'addaci na basu ƙwaya da makamai da
wasu manya keyi amma hakan ya gagara. Dan su Alhaji Yaro glass sun rigada sun kammala shirinsu tsaf a
bayan fage. Hasalima Ramadhan baida maraba da hoto game da kowanne irin tsari nasu. Sai dai duk
wani tsari nasu mara kyau sun binne iya su. Mai ƙyawunne kawai suka fiddo garesa. Hakan yasa yake
cigaba da musu kallon mutanen kirki.
Tabbas an kaɗa gangar siyasa. Mutanen ƙasa kuma sun amsa. sannan Alhmdllhi ta ko ina Ramadhan
ya samu karɓuwa musamman a wajen matasa ƴan uwansa. Dan suna ganin wannan karonfa yaƙin
nasune bana kowaba. A gefe kuma ƴan siyasa nata yarfe ga abokan hamayya. Musamman Ramadhan da
tako'ina aka sakashi tsakkiya akan bai cancantaba. Ta yaya wanda ko aure baida shi zai iya riƙa ƙasar
NAYA. Taya mai ƙarancin shekaru irinsa zai iya riƙa ƙasar NAYA? Taya ɗan gata irinsa zai iya riƙa ƙasar
NAYA? Taya... Taya... Tay.... Dayawa suketa faman lissafi.
Sai dai kuma masu iya magana kance _zakaran da ALLAH ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho
sai yayi_. To hakanne kam ga Ramadhan, dan tako ina bakajin sunan kowa sai na _Young millioner_ ga
ƙuruciya ga kuɗi ga gayu ga ƙyawu.
A ɓangaren ƴammata suma ba'a barsu abaya ba wajen yaƙin ganin sun ture gwamnatin Raudha sun
maye gurbinta. Wasuko gani suke koda ita babu abinda za'a fasa fatansu dai Ramadhan ya amshi tayi
kawai. Dukan saƙonsu da shishshiginsu yana hankalce da shi. Sai dai kuma basune agabansaba yanzun.
Ita kanta da aka saka masa ranar auren da ita bata gabansa. Dan yakanma manta da wata saranar aure
dake a kansa gaba daya. Shi hatta sunan Raudha sai abakin ƴan siyasa ma ya fara jinsa. Kuma bazaice ya
riƙeba duk da ana yawan ambata saboda yarfe da ake masa akan batun aure dama auren nata da
mutane kan fassarasa a siga kala-kala.
Kallo ɗaya zakai masa ya baka tausai, duk ya rame yayi duhu saboda wahalar campaign da rashin
barci. Duk ƙoƙarinsa nason ganin kowa ya fahimcesa hakan bai hana wasu jifansa da kalmar *Mai girman
kai ba* susukance ya cika girman kan tsiya da izza. Duk lokacin da kalmar nan ta fito a bakin wani ɗan
siyasa yakanyi murmushi, dan shi dai wannan girman kai nasa da aketa faɗa har yanzu bai ganinsa..........
✍
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan💋💋💋_.
*_Typing📲_*
*_Episode 21_*
.............★A ɓangaren gimbiya su'adah da fulani da Asmah suna akan bakansu na ganin sun hana auren
Ramadhan da Raudha suma. Sai dai kuma hayaniyar campaign ta sakasu ajiye wannan batun gefe. Kowa
fatansa a yanzu Ramadhan ya haye mulki kawai, daga nan koma miye zai biyo baya sai ayi. Dan sun ɗau
alwashin yaronsu bazai auri ɗiyar talakawa ba. Zuwa yanzu sunyi bincike mai tsanani akan Raudha har
Hutawa, shiyyasa suke tunanin karya lagon su Bappi da wannan sirrin a haukarsu.
★★★
Raudha kam tun kwanaki biyu da kai kuɗin aurenta aunty Hannah da First lady suka yanke shawarar
ɗauketa anan gidan, tare da kafama hajiyar birni hujja da kar Asabe ta zugeta, aiko tai azamar amincewa
dan ita kanta lamarin Asaben tsoro yake bata duk da tasanta da kafiyar tsiya tunba yanzu ba. Tunda
itama haka tayi ga masu kuɗi na sonta a wancan lokacin amma ta dage sai M. Dauda, itako a yanzu
bazata yarda Asaben tai mata baƙin cikin samun abubuwa da damaba a dalilin auren Raudhan. Sun
maidata wani gida keɓantacce wai ana koya mata dabarun mulki irin na first lady. Bawai suna mata
hakan danta ƙaru ba, sunayine kawai danta saki jiki dasu har idan buƙatar sakata musu aiki ya taso anan
gaba tayi babu musu.
Kasancewar an haɗota dasu Yasmin kuma harda aunty Hannah duk da bata cika zama ba saboda
yawon campaign sai hankalinta bai tashiba sosai, ga wata dattijuwa da sukace tana aikine a fadar
shugaban ƙasar shekaru goma kenan cir na mulkinsa mama tambaya, sai ƙarin mutane biyu ƴan gayu
sukuma masu koya mata abubun daya shafi gyaran jiki da dai sauransu. Sai shahararriyar mai kayan
gyaran jikin nan dake gyare Raudha ɗin lungu da saƙo da ingatattun kayanta kayan ƙamshi dana sanyi
*AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* _(guys ku garzaya dan zaku samu duk abinda kuke
buƙata ga amaryar kb, daga kayan ƙamshin jiki, gida, kayan mata, maganin sanyi ingantacce😋😘😍🤗)_
Kuma akwai wata islamiyya dake anan kusa da gidan saboda matsawarta yasa suka sakata ita dasu
Yasmin. Sai dai bata fita sai da dogon hijjabin Uniform ɗin makarantar harda niƙaf. Ba'a dabarun mulki
kawai aka tsayaba har gyaran jiki dasu saka kaya, girki duk koya mata akeyi, dan ma Alhmdllhi dama ta
iya abubuwa da yawa na aikin cikin gida sai dai bana ƴan gayu irin haka ba, ba kuma sosai take girki ba a
gida saboda icce suke amfani da shi ita kuma Asthma.
A gefe kuma damuwar auren nata na nan daram a ranta. Musamman yawan ganin Ramadhan da
takeyi a tv saboda campaign yanzun. Hakama idan ta fita islamiyya duk da anguwace ta manya tana
ganin posters nashi. Ita kanta tasan ƙyaƙyƙyawane, yanayinsa da kwarjininsa dole ya shiga ran mai
kallonsa da hanzari, sai dai ko kaɗan batajin sonsa a ranta, kamar yanda tasan itama bazai taɓa ya sota
ba. ita da kanta kuma tana tilastama kanta saka ƙinsa a ranta saboda wasu dalilai
★Al'amarin campaign ya miƙa, kowa yana hangen nasara tattare da Ramadhan duk da masu iya
magana kance siyasa kamar mace mai ciki ce, ba'a san mi zata haifa ba. Abubuwa da yawa masu daɗi da
marasa daɗi sun faru a wajen campaign ɗin nan, wasu sun wuce an manta, wasu ko bazasu gogu a
zuciyaba sai bayan mutuwa.
Da gaske Ramadhan ya manta da batun wata Raudha saboda hargitsin campaign, sai idan wani ya
ambaci sunanta ko zancen auren nasa ya fita a bakin wani yake tuna wata sa rana dake kansa ta aure. Sai
dai ga Bappi da Pa da Anne ba haka bane, dan sunata shirye-shiryensu na biki duk da hatsaniyar
campaign ɗin da kowa ke a ciki. Ga gimbiya Su'adah kuwa tunda ta gama binciki tushen Raudha
hankalinta ya sake tashi ta birkicema Pa. Ko kulata baiyiba balle ta samu amsa. Hakan ya kuma ɓata
ranta ita da su Fulani, batare da sanin kowaba suka shiga ƙulle-ƙullen yanda zasu ɓadda Raudha, sai dai
sunbi duk wata hanya data dace amma basu sameta ba saboda ɓoyeta da akayi. Wannan dalilinne yasa
gimbiya Su'adah tun karar Pa ana gab da rufe campaign.
“Wai nikan nakega ya kamata ko sau ɗayane ai matar da Ramadhan zai aura a ganta wajen
campaign, kar mutane su fassara rashin ganin nata da wani abu kuma ai”.
Shiru kamar Pa bazai amsaba duk da tasan ya jita sarai, sai da ya gama kallon rahoton da akeyi a tv
game da taron campaign daya faru na Alhaji Andi ƙaura a jihar Sato sannan, cikin fushi dajin ɗacin
kalaman da Alhaji Andi ƙaura yay amfani dasu a wajen da yarfen da yayma Ramadhan yasa muryarsa
kausasa.
“K dake matsayin uwarsa tunda aka fara campaign ɗin kinje ne?”.
Fuska ta kumbura, cikin zafinta tace, “Miye alaƙar ganina da ganinta a wajen? Kuma ni ai inada masu
zuwamin”.
“To itama ai danginta sunje sun wakilceta, dan mahaifinta campaign ɗin da yayi a yankinsu bana
tunanin wani a gidan nan yayi kwatankwacinsa ma.”
“Tunda ko yana neman gindin zama da shegen kwaɗayi ai dole yayi. Imagine yarona kamar
Ramadhan dake da kowane irin gata na duniya ya ƙare da auren ƴar karuwa da ɗan duniya. Jikar mai
tuwo-tuwo tikari a saudia. Miyasa idan dan alkairin da tayinne baza'a bata kuɗi itada iyayen nata ba
tunda su sukafi buƙata. Sai an wani ƙaƙabama yarona? Idan kuma auren nata dole ne basai a samu wani
a bashiba a ma'aikatan gidan nan”.
Pa yasan ya cigaba da saurarenta zai iya mata abinda duk yazo masa a rai, dan haka ya miƙe tsam ya
bar mata falon. Hakan ba ƙaramin sake ƙona mata rai yayiba, dan harda ƙwalla suka taru mata a ido,
zuciyarta na ƙarajin tsanar Raudha da duk wanda ya shafeta. Tayi alƙawarin koda sunfi ƙarfinta anyi
auren nan wlhy sai Raudha ta gwammace mutuwa da rayuwa.
Da wannan ɓacin ran ta yini ranar, da daddare ta buƙaci ganin Ramadhan, duk da yanda yake a
matuƙar gajiye dan yau jihar Nobama sukaje campaign haka ya daure ya amsa kiran nata. Tunda ya shigo
take kallonsa, duk ya rame yayi duhu saboda wahalar kai kawo, sai dai hakan bai dametaba, dan tasan
yana samun mulki zai koma normal harma yafi da.
Ya faɗa cike da girmamawa yana kaiwa zaune kujerar dake gefenta. Tab.. ɗin hannunta ta ajiye cike da
ƙasaitarta tana dubansa. “Baka dai, lafiya ne na ganka sukuku?”.
Numfashi yaɗan furzar, cikin muryarsa mai ɗan faɗi yace, “Kaina ke ciwo, nasan hayaniyarnan ce
kawai”.
“Bana son na cika yawan shan maganinne, nasan da nayi barci zan ware”.
Baki kawai ta ɗan taɓe, ta sake harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya da tsuke fuska. Dan tana so ya fahimci ba
zancen wasa bane. “Ina muka tsaye game da auren wannan yarinyar da aka ƙaƙaba maka?”.
Baya ya ɗanyi da jikinsa ya kwantar a kujerar, ya lumshe idanunsa tamkar baiji mitace ba. Kusan
sakan biyar sannan ya furzar da iska batare daya buɗe idanun ba. “Babu wani abu da zan iya yi akan
auren nan tunda Pa da Bappi da Anne sun dage, kawai na yanke zan auretan daga baya zan san abunyi”.
“Jikar tikari mai tuwo-tuwon zaka yarda ka aura? To bara na faɗa maka idan ma baka saniba.
Uwarta kanta sai da tai karuwanci, a barikinne ma ta haɗu da uban yarinyar dan shima ɗan duniyarne na
bugawa a magazine, daga kakarta har ƴan uwan uwarta duk karuwai ne har yanzun. Idan ma barci kake
ka farka, duk yanda zaka zame ka zame kafin cikar waɗan nan kwanakin da suka tsaida”.
Harga ALLAH maganganunta sun sokesa. Kuma dama tayi amfani dasu ne dansu soke-san tunda
tasan yanda ya tsani karuwai tun yanada ƙarancin shekarunsa balle yanzun. Idanunsa dake kumbure da
ɗan ja a cikinsu saboda rashin samun isashen barci ya zuba mata. Sai kuma yaɗan janye cikin taune lips.
“Maa waya faɗa miki?”.
Harara ta danƙara masa tana miƙewa, “Kaje ka bincika tunda na saba maka ƙarya...” Tana faɗa tabar
wajen.
“Maa Please.....”
Ya faɗa da sauri yana ƙoƙarin ganin ta tsaya amma tai masa banza ta shige. Jagwab ya koma ya zauna a
kujerar yana dafe kansa daya ƙara ƙarfin gudun ciwo. _(Ƴar karuwa, jikar tikari mai tuwo-tuwo. Ubanta
ma a yawon duniya suka haɗu da mamarta sukai aure, sannan duk ƴan uwan uwarta karuwaine har
yanzun)._ “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un”. Ya faɗa a fili yana dafe kansa da ya sake wata irin sarawa
kamar zai faɗo ƙasa. Duk yanda yaso miƙewa a wajen kasawa yay. ALLAH ya taimakesa sai ga Rafi'a
ƙanwarsa ta uku ta shigo falon da shayi a hannu da waya a kunne alamar magana takeyi.
Cikin sauri tace, “Subahanallahi Yaya!”. Wayar da kofin shayin ta dire bisa centre table tayo kansa,
duk yanda taso taimaka masa ya tashi ta kasa, dole ta fita ta kira Pa da sauran ƴan uwanta dake can
babban falo kowa na harkar gabansa. Waɗanda ke a cikin ɗakunan barcinsu kuma suka firfito suma
saboda yanda take kwakwazon kiran Pa.
Komai Pa baice masaba, sai taimaka masa da yayi ya miƙe, da kansa ya kaisa har sashen su Anne su
Rafi'a biye da shi hankali tashe, wasunsu ma hawaye sukeyi duk da bawai ya suma bane ko yanayi yayi
tsamari. Kawai dai idan ka kallesa kasan babu lafiya tare da shi.
Suma su Anne hankalinsu ya tashi, a take aka nemo doctor duk da yace su barshi shi lafiyarsa ƙalau,
amma basu sauraresa ba. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga doctor Shamsu. Koda ya dubasa sai yace musu
gajiyace da ƴar damuwar data saka jininsa ɗan haurawa. Sai kuma sugar ɗinsa yayi low sosai da alama
kwana biyu baya kula da shan maganinsa.
Da ƙyar Ramadhan ya yarda aka saka masa drip, sai da Bappi yay masa jan ido ma, ALLAH ya taimaka
bai jima da fara shiga jikinsaba barci mai nauyi yay awon gaba da shi. Su duka tausayinsane ya kamasu.
Dan sun san yana matuƙar ƙoƙari akan abinda bai saba ba. Duk da yana zirga-zirgar kasuwanci ba irin
wannan bace. Dan ko hayaniyar campaign ɗin nan tashin hankaline. Balle kuma akwai ƴan kunji-kunji
kala-kala a gefe ga abokan hamayya dama abokan tafiyar.
Duk fita sukai suna masa fatan samun lafiya ganin yayi barci. Sai dai ran Pa a ɓace yake sanin
Gimbiya Su'adah ce ta sake saka Ramadhan ɗin cikin wannan yanayin, kuma duk abin nan da akeyi babu
idonta a wajen.
A ɓangaren gimbiya Su'adah kam duk taji komai, taƙi fitowane danta sake jaddadama Ramadhan
fushinta ya tabbatar da zancen bana wasa bane. Dan taji daɗin yanda taga zancen yayi tasiri a ransa.
Hakan yasa babu ɓata lokaci ta kira Asma data bata shawarar ta sanar mata. Cikin jin daɗi adda Asmah
tace, “Su'adah ai dama na faɗa miki hakanne kawai zaisa Ramadhan yay mana biyayya. Ni yanzu ina
ganin mu haɗa wani shiri da zai sake sakashi tsanarta. Suma kakannin nasa susan mike faruwa idan ma
basu sani ba”.
“Su'adah ki kwantar da hankalinki, babu ta inda wannan zai shafi Ramadhan. Sai ma ɗaga darajarsa
da zai ƙara”.
Wani irin takaici ya baibaye Adda Asmah daga can, ji take kamar ta jawo ƙanwar tata ta hau duka.
Amma a fili sai tace “To hakan yayi”.
Koda Gimbiya Su'adah ta kira Fulani ta sanar mata zaginta ta hau yi. Duk da ta yabama ƙoƙarin ta na
farko akan sanarma Ramadhan su waye dangin Raudha ɗin. Amma maganar fita da tsiraicin suce Raudha
ce da wani wannan gangancine. “Ku miyasa baku da hankali. a tunaninku dan kunyi video na bogi kunce
itama yarinyar karuwace zai hana mutuncin Ramadhan taɓuwa ne. To idan baku san siyasa ba ko mulki
ku farka. Wannan abun zai iya ruguza duk wata nasarar da muka samu a campaign duk da kuwa bai
aureta ba, idan ma baku sani ba zancen auren nan nata shi kansa wani mutunci ya ƙara masa ga al'umma
har a wajen campaign. Idan zamu kaudashi kuwa zamuyine a sirrance bawai mu nuna wa duniya ba
marasa tunani kawai. Ku fitar da video ɗin abokan adawa sujuyar da shi akan tare take da Ramadhan ɗin
a ciki shashashu kawai”.
Shiru gimbiya Su'adah tai da waya a hannu dan Fulani na gama faɗa ta yanke wayarta. Itama irin
wannan tunanin tayi tun farko shiyyasa ta bijirema Addar tata. Inko hakane gara ta tattara zancen
Raudha gefe tukunna, dan duk abinda zai hana ɗanta hawa mulkin nan zata kwana ta yini yaƙi da shi ne.
______________________________
Badan Ramadhan ya warke ba ya miƙe ya koma filin daga, amma Alhmdllh ɗan ƙarin ruwan da akai
masa yasa jikinsa yin daɗi. Ranar wata juma'a bayan sakkowa massallaci yay campaign nasa na ƙarshe a
ƙauyensu Taura. Inda ɗunbin jama'a suka taru har abin ya bama mutane tsoro musamman abokan
hamayya irinsu Alhaji Andi ƙaura. Su president kam ji suke kamar su goya Ramadhan a baya dan daɗi.
Dan kuwa sun san burinsu na dawowar mulki garesu ya gama cika. Sai kuma fatan kauda Ramadhan a
shekaru biyun da suka ɗiba masa (wa'iyazubillah. Sun manta ran kowa a hannun ALLAH yake. Sannan
shike bada mulki ga wanda yaso a kuma lokacin da yaso).
Muslata irin farin cikin da Ramadhan ya shiga a yau ɓata lokaci ne. Dan kuwa ya tsorata da yawan
mutanen da suka taru dominsa. Har yanaji a ransa kodai akwai aljanu kamar yanda wasu ke faɗa ne. Sai
dai farin cikin nasa bai hana jin ɗacin da tsanar Raudha da ahalinta ba. Duk yanda yake turesu a ransa
sun kasa gushewa.
______________________________
A faɗin ƙasar NAYA da kewaye yau itace daren zaɓen shugaban ƙasa. Dan haka ta kowanne sashe
akwai abinda ke gudana ga kowa. Wasu fatan nasara, wasu shirye-shiryen kota kwana, wasu addu'oi. A
cikin masu salla da addu'a a wannan dare harda Ramadhan, Anne, Bappi, Pa, Yafendo, Inna da wasu a
cikin ƴan uwan ahalin Taura. A masarautar Bino ma dai Mai-martaba ya kwana raya wannan dare.
Yayinda irinsu Gimbiya Su'adah sukejin mulki kamar sun samesa ne.
Duk da Raudha bata jin son Ramadhan ta masa fatan alkairi, harta kwanta kuma zuciyarta taita
zingurinta akan ta tashi tayi salla ko raka'a biyu ne. Tabi shawarar zuciyarta tayi kuma ta roƙi ALLAH
samun shugaba na gari bawai Ramadhan ba.
*_WASHE GARI:_* kusan tara na safe Feena ta shigo ta sakata shiga wanka. Batare da tasan dalili cewa
tai wankan ba tace ai yanzu tai wanka ita. Fita Feena tayi, babu jimawa ta dawo da kaya a hannu da
makeup kit. Sam Raudha batason wannan ƙaƙale-ƙaƙalen, amma saboda Aunty Hannah ta shigo ta mata
magana dole ta amine akai mata light make-up ɗin. Sannan ta saka kayan da aka kawo matan. Tabbas
tayi ƙyau, sai dai bazata iya fita da gyalen da aka haɗo kayan da shi ba. Dan haka ta ɗakko gogaggen
hijjab ɗinta daya shiga da kayan ta saka. Duk jarabar aunty Hannah dole ta barta dan kuka ta sanya
musu.
Tana zaune fuska a kumbure tana shan tea ɗin da aunty Hannah ta tilasta mata sha Yasmin ta iso
da saƙon “Mom wai ga baƙon yazo inji mama tambaya”...,
Cikin sauri aunty Hannah ta amshe kofin shayin hannun Raudha ɗin. “Sai ki tashi tunda dama haka
kike so ki fita bakici komai ba. Sai ki tashi ya iso kuje ku jefa ƙuri'a muma zamuje tare da tawagar
shugaban ƙasa”
Sosai gaban Raudha ya faɗi, ta ɗago da sauri ta dubi Aunty Hannah. Sai dai kafin tai magana Feena
ma ta shigo.
Da sauri Aunty Hannah ta miƙar da Raudha, bag ɗin da zata riƙe mai ƙyau ta saƙala mata a hannu, hakan
sai yay matuƙar sake fito da tsarin kwalliyar tata musamman da hijjab ɗin ke iya cinyarta kawai, gashi
mai hannu, ya kuma ɗau guga ya kwanta luf da haska ƙyaƙyƙyawar farar fuskarta kasancewar blue color
ne, sai hakan ya ƙara bama skirt ɗin nata fitowa sosai ya buɗe. Kamar zata fasa kuka ta zura takalman da
aka ajiye mata masu ɗan tudu da suka sake fidda ƙyawun ƙafarta.........✍
*_Typing📲_*
*_Episode 23_*
............A ɓangaren Ramadhan kam yama manta da wani batun aurensa balle Raudha. Harkokin gabansa
kawai yakeyi na shirye-shiryen rantsarwa da zaman meeting-meeting da suke yawanyi da ƴan jam'iyya a
gidan gwamnati. Shi kansa ma haushi meeting ɗin ke basa a mafi yawan lokaci, dan wasu yakan rasa
gane kansu balle inda suka dosa. Sai dai yana nutsuwa dai wajen maida kansa yaron da suke kallonsa
yana karantar komai da nanufofinsu.
Sai dai abinda Ramadhan bai sani ba a garesa ne kawai ya manta da abatun aure, ga jama'ar gidansu
da masu so da masu ƙi duk abin na ransu. Domin shiri su Anne keyi na musamman akan auren, lefe ya
kammala haɗuwa tsaf, hakama abubuwan da duk za'a buƙata ga taron biki.
A ɓangaren su gimbiya Su'adah ma dai suna nan akan bakansu na hana tabbatar wannan aure, sai
dai kuma tun randa Pa ya ritsata tana waya da Asma yaji kuma mi suke faɗa yaja mata dogon gargaɗi,
tare da alwashin inhar wata matsala ta shigo a auren nan ta shirya amsar matsala a nata auren itama.
Wannan ne ya tada mata hankali ya kuma ja mata birki, sai ta koma zungurin Ramadhan akan auren. Sai
dai kuma rashin zamansa a gidan ya taimakesa da masifarta.
A yanzun kullum cikin ƙulla yanda zasuci uban Raudha suke inhar ya tabbata sai anyi auren. Tare da
ɗaukar alwashin aurama Ramadhan Aina'u koda daga baya ne.
A hutawa ma dai Mal. Dauda ya shirya tsaf, dan gyara na haƙiƙa yayma gidansa tamkar bashi ba. Ya
baza ɗinkuna yayma kuma kowa na gidan. A yanzu haka Innarsa da ƙaninsa da iyalinsa suma sun dawo
nan gidan da zama. Hakan yasa Larai ta rasa kataɓus dan Inna cin uban surukai take babu ɗaga ƙafa.
Balle ma yanzun da take ganin ɗanta yay arziƙi, ai koda wasa babu wanda ya isa zagin Asabe a gabanta
duk da bata nan. Takance Asabe ai farar uwa ce tunda gashi sanadin ta haifi Raudha suna hutawa.
Takanji takaicin saki ukun da ta saka Mal. Dauda yay ma Asabe a yanzun. Inama ɗaya ne ko biyu da
yanzu sai ta dawo abinta.
To anan ma dai shirinsu suke tsaf duk da babu amarya har anko an fitar ma.
*_SATIN BIKI_*
Shiga satin biki ya saka ango da amarya dawowa cikin hankalinsu. Dan kuwa sun tabbatar yanzu kam da
gaske ake ƙwarai. Ta ko ina sanar da wannan ɗaurin aure ake a kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo,
yayinda wasu baƙi dake ƙasashen ƙetare suka fara sauka ciki harda su Sultana daba taron bikinne ya
kawotaba kai tsaye. Dan tunda akace Ramadhan ya fito takarar shugabancin ƙasar NAYA take son zuwa,
sai kuma ga batun aurensa da yay matuƙar tada hankalinta har takaita da kwanciya asibiti. Halin data
shiga yasa Babanta yarda su Mufeed suzo da ita taga Ramadhan ɗin.
Sai dai kuma tun jiya suka iso amma ganin Ramadhan yay musu wahala saboda yana can suna shirye-
shiryen zancen rantsarwa. Za'a ɗaura auren ne juma'a, asabar ayi rantsuwa, lahadi su tare gidan
gwamnati tilitin shugaban ƙasa ya fara shiga office.
______
Ga amarya kam itama ta yarda dai auren nan babu fashi, tunda aka shiga satin bikin aka sake ninka
yanayin gyaran jikinta da akeyi, tayi ƙoƙarin toshe duk wata hanya bata sake haɗuwa da Alhaji yaro glass
ba duk da yana yawan zuwa gidan yanzun. Ana saura kwanaki biyu ɗaurin aure daren da washe gari za'a
maidata Hutawa kusan sha biyu yunwa ta addabeta, dan duk yinin yau bataci wani abincin kirki ba
saboda damuwa. Bata son auren nan ko ɗigo a ranta, gefe ga tsoro da fargabar tsantsar ƙiyayyarta data
hanga a cikin idon Gimbiya Su'adah da wasu a ƙannen mijin nata. Jin har kamar zuciyarta na tashi dan
yunwa ya sata fito da nufin zuwa kitchen ko tea ta haɗa.
Da sauri taja birki jin kamar ana magana ƙasa-ƙasa dai-dai tana ƙoƙarin sanyo ƙafarta a falon, ta ɗan
laɓe tana leƙe daga corridor ɗin ɗakunan barcinsu ita da su Yasmin. Aunty Hannah ta hango da wasu
mutane uku, babu wanda ta gane a cikinau sai Alhaji Yaro glass kawai. shima dan rabin jikin aunty
Hannah nakan nasane. Dan tana zaune kusan a jikinsa ne ko kunyar sauran mutanen bataji. amma
sauran ukun babu wanda ta sani.
Jin an ambaci sunanta yasa gabanta faɗuwa. taɗan sake matsowa daf da hanyar fita corridor ɗin ta
kasa kunne taji da ƙyau.
Wanda yake a kujerar ƙarshe mai sanye da jallabiya baƙa ya ƙara fuskantar aunty Hannah yana faɗin,
“Hannah kinga dai mun matuƙar yarda da ke, dukkan wani shirinmu a yanzu tamkar ya rataya a wuyanki
ne. Bama son kuskure ga yarinyar nan, dan idan aka samu kai tsaye ke zamu ɗaurama alhakin hakan”.
Kanta ta jinjina masa tana tashi zaune sosai. “Alhaji Wada karkaji komai, na riga na ɗaura Raudha
bisa kowacce irin hanya da bazata iya bijire mana ba. Ku ɗauka tamkar yaron nan ya mutu ya gama a
shekara biyun da kuka ɗeba masa. Adai ɗaura auren jibi, da zarar sun tare za'a fara bata maganin tana
saka masa a abinci, ko abin sha kamar yanda first lady ta sanar min..”
“Hakan shine dai-dai, dan munaso ya fara masa aiki a hankali yanda ko bayan mutuwarsa za'a ɗauka
diabetis ɗinsa ce ba wani ba, tunda dama maganin zai ƙara ƙarfin diabetis ɗinne ya kuma haifar da
hawan jini mai ƙarfi. Sannan a yau da safe duk wani poison an sakashi a cikin ac ɗin falonsa da bedroom
dan a hankali mukeso ya fara ratsa jininsa shima ta yanda zai zama bashi da wani kuzarin nutsuwa yay
aikin ma, dan cikin idon yaron nan ka kalla kasan bazaiyi mutunci ba. Yana gama gane kan mulkin nan
mukanmu ba ɗaga mana ƙafa zaiyiba wlhy.”
Alhaji Yaro glass ya karɓe da faɗin, “Ai dama shegene yaron nan, yanda kaga kakansa da taurin kai
haka shima yake. Ni gani nakema mizai hana ita Raudha mu fito mata ƙuru-ƙuru akan aikin da muke son
tai mana kawai dan yarinyace sai yanda mukai da ita.”
“A'a wannan ganganci ne, idan kuma aka samu akasi ya faɗa sonta fa? Ko kuma itama tana sonsa
yanzu haka? Dan yaron nada qualitys ɗin da mata zasu so sa a ƙanƙanin lokaci. Giyar soyayya kuwa zata
iya janta ta sanar masa. Kawai muyi yanda muka tsara ayi amfani da ita”.
Cikin zafin rai Mr MM yace, “Idan ma mun sanar matan tace zata tona mana asiri halakata zamuyi
itama a banza....”
“Ai ko yanzu ɗin ba tsira zatai ba. Kana tunanin zata dinga shaƙar gubar nan ta cikin ac ta tsallake
itama. Yanda zata dinga masa illa a hankali itama hakanne zata kasance. Sai dai akwai wata allura da
za'ai mata wadda gubar bazata yi tasiri a jikinta da wuri ba kamar shi”.
A tare duk suka kalli Aunty Hannah bayan sun ɗauke idonsu ga Dr Bonba daya gama bayanin.
Kanta ta kaɗa musu tana watsa hannaye baya. “Miye na kallon nawa?, kun san dai Raudha ɗiyar
ƙanwata ce. Duk da kuwa ina son zama first lady bashike nuna bana son abata ba. Nasan bai wuce kuce
ya shawarar ta canja ba game da allurar riga kafin guba. Ku zauna kuyi tunani da hankalinku, babu ta
yadda za'ai mu bari gubar tai tasiri a jikinsu lokaci guda, dan komai zai fito ne. Amma idan bayan ya shi
ya mutu ne itama ta mutu za'a iya cewa zuciyartace ta buga saboda rashinsa itama tabisa”.
“Woow!”.
Suka faɗa a tare suna tafawa. Shugaban ƙasa mai sauka yace, “Hannah kinada basira, anya kuwa idan
mutumina ya zama shugaban ƙasa bake bazaki koma juya ƙasar ba kuwa?”.
Wata shegiyar dariya tayi tana juya idanu, Alhaji Yaro glass ya sake rungumota jikinsa da manna
mata kiss a kumatu. “Inaga shugaban ƙasa biyu kam zakuyi”. Ya faɗa cikin raha. A can ƙasan ransa kuwa
yana ayyana ashe kuwa itama zata mutu nan kusa, dan Hannah bata isa shiga masa hanci bai fyatota ba
duk da take matarsa.........
Zuwa yanzu sosai hajijiya ke neman yadda Raudha a ƙasa. Tai azamar dafe bango jin zata zube a ƙasa.
Laɓɓanta sai faman rawa sukeyi amma sun gagara furta komai, dan ko tace zata furta ɗin batasan mi
zata furta ba. Da ƙyar ta cigaba da laluben bango ta koma ɗakinta, batasan a yaya ta zube saman gadon
ba harda jan bargo ta lulluɓe, jikinta ya shiga wani irin karkarwa na rawar sanyi
Yanzu ta fahimci ba ahalin Ramadhan bane zasu zama BAƘAR INUWAR ta ba, ba Ramadhan bane
BAƘAR INUWAR ta ba, aunty Hannah itace BAƘAR INUWAR ta. Shi kansa Ramadhan sun tittiɗashi ya hau
kujerar mulki ne badan ya ni'imtu ba, badan ta zame masa INUWA da irinsu talakawa suke hangen masu
mulki na ciki ba. bai san sun kaisa BAƘAR INUWA bane, gara ace a rana yake da shiga cikinta. ta sake
fashewa da kuka.
ALLAH sarki talaka. A kullum gani yakeyi shi a RANA YAKE, mai mulki shike cikin Ni'imtacciyar inuwa,
ashe baisan da wata BAƘAR INUWAR MUKIN gara ranar da shi yake a ciki ba. Yau gashi saboda mulki
yayar mahaifiyarta ta ɗauketa da hannunta ta kaita BAƘAR INUWA. Shiyyasa suka dage ashe, shiyyasa
suka hana mahaifiyarta nuna ƙin auren, shiyyasa suka babbake ko ina da ina. Miye mafita? Zata bijirema
auren ne ta hanyar guduwa ko zata haƙura ta zauna ta ceci rayuwar wanda a yanzu take kallo da fatan ya
zama adalin shugaba madubin al'umma kamar yanda talakawa suka ɗora yaƙininsu a kansa da ƙwarin
gwiwarsu?.
A take kanta ya fara sarawa, dan tama rasa kalar tunanin da zatayi saboda ƙarancin shekarunta. Ga
wani irin tausayin Ramadhan ɗin da ahalinsa na dirar mata a zuciyarta, dan ta taɓajin cewar kakansa
Baba alhaji aka bama takarar shi kuma ya bashi saboda yace bai ra'ayin mulki a shekarunsa. Ashe baisan
ya kai jikansa BAƘAR INUWA bane. Tabbas bazata iya fahimtar komaiba a yanzu dole saita san komai,
sanin komai kuma bazai yuwu a gareta ba sai ta yarda da auren Ramadhan. Sai dai kuma tana buƙatar
shawara wajen na sama da ita, wazata tunkara? Hajiyar birini! (Kai a'a gwaggo sai a hankali ce) Hajiya
mama (kai itama a'a duk tafiyar ɗaya ce) Mommynsu! (Ina bazai yuwu ba zata sake tada mata hankali)
Su Fatisa! (Ina basu da hankalin da zasu iya fahimtarta ta wani fanin ma gara ita). Take wani irin zazzaɓi
mai zafi ya rufeta, sarawar da kanta keyi ya ƙara ƙarfi..
Koda suka wayi gari da safe Raudha babu lafiya aunty Hannah bata kawo komai a ranta ba sai
tunanin fargabar aure da akasan kowacce amarya da shi. Tunda sassafe suka nufi can gidan dan yau zasu
wuce Hutawa su duka har Hajiyar birni. Su Fatisa kam tun jiya suka wuce harda su Yasmin.
Asabe ce kawai ta damu da ganin halin da ɗiyar tata take ciki. Suko hankalinau nakan kuɗaɗen da
aka aiko daga gidan su Ramadhan injisa aba amarya na hidimar biki, sai tarin kayan rabo. Ko irin ɗan faɗa
da nasihar da akema amarya babu wanda yay mata a dangin mahaifiyar tata. Sai ita Asaben ce ta jata
gefe taita lallashinta da mata nasiha. Tare da ƙarfafa mata gwiwar ta ɗauka Ramadhan shine zaɓin
ALLAH a gareta. Maybe shine kuma mafi alkairi. Dan ita kanta tayi addu'a tayi sadaka akan rushewar
wannan aure amma babu alamar zai rushe ɗin.
Raudha ta yarda da maganar Mommy takuma ɗauki aniyar haƙuri, dan ita kanta tayi addu'ar sosai
akan zaɓin ALLAH game da auren komai kuma bai canja ba, tunda gashi har gobe idan ALLAH ya kaimu
ɗaurin aure.
Ƙarfe kusan sha biyu suka bar Bingo zuwa jihar Dillo a ƙaramar jukumar hutawa. Kasancewar
lafiyayyar motace kuma drivern yasan aikinsa zuwa huɗu na yamma sun iso. Asabe tayi mamakin yanda
aka tarbesu, ga gidan nasu data sani duk ya cinye a baya ya zama wani haɗaɗɗe yanzun. Dan harda su
gate aka saka.
Kowa burinsa yaga Raudha matar shugaban ƙasa. Dan haka maƙwafta da ƴan anguwa sukaita
tururuwar shigowa ganin amarya. Sai dai kuma ita amarya Raudha ta ɓoyewa ganinsu saboda zazzaɓi
dake damunta har yanzu. Abu biyu ke tayar mata hankali. Zancen su Aunty Hannah da tsarin auren nasu
daya sha banban dana saura. Babu wani jituwa tsakaninka da ango balle wani maganar biki ma ya shiga.
To gaba daya ma sau biyu ta taɓa ganinsa a zahiri, babu kuma wanda wata maganar kirki ta shiga
tsakaninsu a ciki.
Duk yanda taso cigaba da zurfafa tunanin nata dole ta haƙura saboda hayaniya da gidan ya ɗauka.
Kai kace yau ne ɗaurin aure. Ga dj ya warware kiɗa tun da safe dan su Fatisa suka ɗakkosa tun daga
Bingo. Tun kuma a daren jiya aka fara raƙwashewa duk da amarya bata iso ba. Shiko Mal. Dauda dama
babu ruwansa, dan shi kansa yana gefe da abokansa yana ɗan rausaya ƙafa saboda yanda kiɗan ke
shigarsa tsumin baya na neman motsawa.
Kowa ka gani a cikin farin ciki yake a gidan, ƴan uwa da wandama kalan dangine duk bakuna a
washe. Musamman Inna dake nuna cewar yanzu tafi son su Raudha fiye da kowa a duniya. Larai ce
kawai take cikin tashin hankali, dan ta koma gidan malaminta yafi sau shurun masaƙi yana cemata ta dai
jira ai ba'a ɗaura auren ba ko. Kowace daƙiƙa ta agogo dake matso da lokcin ɗaurin auren na bugawane
da bugun zuciyar larai. Duk ta fita hayyacinta tsabar rashin nutsuwar zuciya. A daren jiya har faɗa sukai
da Mal. Dauda ya shashaheƙa mata mari da tabbatar mata idan ta ɓata masa farin ciki a taron bikin nan
zai yanka mata jan ticket ɗin komawa gidansu dan bazai zauna da mai masa baƙin ciki ba.
Wannan shine dalilin daya sakata kama kanta sai idan ta shiga ɗaki taita haɗiyar zuciya. Baba nafi kam
babu ruwanta. ta shige cikin dangin Asabe dana mijinta anata harkokin arziƙi da ita. Hakama ƴaƴanta na
ma'auri da wanda basuyi auren ba. Yanda take ɗin yasa Mal. Dauda mata ƙyautar kuɗi masu tsoka wai
itama ta tarbi baƙinta.
A daren ranar duk yanda Raudha taso maƙalewa taƙi fita ƙofar gidan inda su Fatisa suka tara
ƙawayensu dama wanda ba'a gayyataba hakan bai yuwu ba. Acewarsu yaune sukai taronsu na ƙawaye.
Dole aunty Hannah ta matsa mata shiryawa cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar Material a cikin akwati
guda da aka kawo mata na kayan fitar biki. dan ba'a kawo lefe ba Ramadhan ya hana. Yace idan an ɗaura
zai bata da hanunsa. Su Bappi sun goya masa baya dan auren Amnah ma haka yayi. Shiyyasa aka kawo
mata kayan fitar biki kawai da aka ɗinka akwati guda da duk abinda zata buƙata na ado.
Light makeup Feena da suka taho tare saboda kwalliyar amarya tai mata, aka gyara mata dogon
gashinta data gada wajen Asabe tare da naɗa mata ɗauri mai ƙyau. Kanta ke matuƙar ciwo ga zafin
zazzaɓi amma haka ta daure ta fitan. Nanfa ƙawaye suka shiga mata hotuna duk da dare ne harma da
jama'ar gari. Burin kowa ace ga hoton matar shugaban ƙasa a wayarsa ya samu na fafar faɗama wasu
yanada alaƙa da ita koda anan gaba idan ganinta ya musu wahala. Wasu ko a take suka shiga watsashi a
media dan hannayensu na ƙaiƙayi.
Wajen ya sake ƙawatuwane lokacin da Hajiyar birni tazo ta farke ƴan ɗari biyar-biyar ta hau yima
Raudha liƙi. Sai itama aunty Hannah ta farke ƴan dubu-dubu. Sai ga Mal. Dauda ma da kansa ya farke
nasa dubu-dubun. Nanfa yaran dj da mutane suka shiga wawaso. Abu kamar wasa sai ya zama gasa
akaita shigowa anama Raudha liƙi. Wasu ma ƴar dubu ɗaya ce suke canzowa goma-goma ko biyar-biyar
suyi dan dai ace suma sunyi.
Alhmdllhi dai sai ga taron ya zama wani ƴar ƙwarya-ƙwaryar wasa. Amarya ce kawai zuciyarta ke a
ƙuntace da damuwar data dameta. Suna mata kallon wadda zata shiga Ni'imtacciyar INUWA basu san
BAƘAR INUWA bace, gara ranar da suke ciki ta fita kwanciyar hankali.
Jirin da tace tanaji yasa Hajiya mama maidata cikin gida, aka bata tea da magani tasha ta kwanta.
Kasancewar maganin naɗan saka barci aka dace barcin yay awon gaba da ita dan dama akwai bashinsa a
kanta.
*_WASHE GARI_*
Tunda farar safiya motocin jami'an tsaro kala-kala suka fara shigowa garin Hutawa suna masa zobe.
Al'amarin tuni ya fara tsorata masu tsoro suka nutsu a gidajensu. Zuwa ƙarfe sha biyu garin ya fara
ɗaukar haramar baƙi. Babu abinda ke danno kai cikin garin sai jibga-jibgan motoci da suka ƙoshi. Kai
harda su helicopters. Tuni gidan hakimi daya amshi ɗaurin auren ya cika ya tun batsa da manyan ƙasa
dana baƙin ƙetare. Dan babu kalar fatar da bazaka samu ba. Tunkan shugabanci gidansu Ramadhan
babban gidane sannne, sai ya zam samun mulkin ya sake haskesu.
Ƙarfe sha biyu da rabi dai-dai tawagar shugabn ƙasa kuma ango *_Ramadhan B. Hameed Taura_* ta
dira cikin garin hutawa. Dan tun a daren jiya nasa baƙin ta kowanne ɓangare ke danna kai birnin Bingo,
yau kuma suka ɗungumo a motoci zuwa Hutawa, duk da kuwa su Alhaji yaro glass sun so hanashi ya
tabbatar musu bazaibi jirgi ba zaizo a mota saboda wani dalilinsa.
Ta ko'ina garin ya sake harmutsewa. yayinda wasu a abokan nasa ke matuƙar mamakin inda
Ramadhan ɗin ya ƙwaƙulo matar aure a wannan garin da idan ka ɗauke ɗai-ɗaikun manyan gidaje da
lafiyayyen titi babu komai a cikinsa sai hayaniya da tarkacen talakawa (🙄🤗ALLAH mun gode maka daka yimu
a talakawa).........✍
*_Sai ku shirya. Dan bai kamata ayi bikin nan babu mu a wajen ba gskiya. Zafafa biyarma duk zasuje. Dan
suna nan suna sallar dare shugaban ƙasa Ramadhan ya haɗasu da muƙaman ministoci_*
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku
inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour
za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan
*Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent
da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_Episode 24_*
............Kusan tare tawagar ango da tasu Bappi ta iso tare da forma president. Sai wasu gwamnoni masu
sauka dama wanda sukaci zaɓe. Dama wasu tuni sun iso, dan a kaf jihohin ƙasar NAYA arba'in da ɗaya
babu gwamnan da baizo ɗaurin auren nan ba da sarakunan gargajiya. Sai waɗanda lalura ta hana kuwa,
suma sun bada wakilai. Hakama masu ƙananun muƙamai irin members na majalisa dama na jihohi da
cabinets na tsohon shugaban ƙasa dana gwamnoni, attajirai da manyan malamai, kai harma da jama'ar
gari da aba'a gayyata ba. Dan a cewarsu dole suzo su kashe kwarkwatar ido, ɗurin auren shugaban ƙasa
guda ba wasa ba.
Tsabar cikar da garin yayi sallar juma'a wasu har akan tituna, motoci kam har an rasa wajen fakin.
Badan jami'an tsaro dake zagaye da garin ba ma da ba'asan yaya zata kaya ba.
Ango yayi shar cikin wata muguwar ɗanyar shadda da zaman neman addin kuɗin da aka sayeta ma
ɓata lokacine. Takalma da agogon hanunsa zuwa hula kuwa dole a kirasu na musamman. Yayi fayau
dashi saboda ƴar ramar campaign da har yanzu bai gama cikowa ba.. Ga gyaran fuskar da ya sha da
tsagar kan gashin girarsa na tabon ciwo sun sake ƙawata fuskar tashi. Ƙamshi yake na musamman, ga
securitys zagaye da shi, kai kace zasu iya karesa daga cika aiken mala'ikan mutuwa ne (😕🤕).
A kusa da kakansa Bappi yay salla a sahun farko, ɗayan gefen haggunsa Mal. Dauda ne hakimi a
gefensa. Sai can ɓangaren shugaban ƙasa mai sauka tare da mai-martaba da sarkin Dillo. A yau sarkin
musulmi ne ya jagoranci sallar juma'a. Bayan idar da salla aka gudanar da ɗaurin aure kamar yanda
shari'a ta yarda. Jikin Mal. Dauda sai rawa yake, dan harga ALLAH a firgice yake ganinsa tsakkiyar
manyan mutane da bai taɓa tunani gani ba koda a mafarki. Daya sani ya bari ƙanin nasa ya karɓi auren
kamar yanda Inna tace. Amma sai ya bijire dan kar wasu su zata ba shine mahifin Raudha ba. Ko wani
yayima Sabilun alkairi saɓanin shi daya cancanta.
A hankali shugaban ƙasa Ramadhan ya lumshe idanunsa lokacin da ake sanar da ƙulluwar auren nasa
kamar haka. *_(Alƙawarin ALLAH ya cika. Domin kuwa Aminatu Dauda Haladu ta zama mata ga
Ramadhan B. Hameed Taura. akan sadaki mai daraja. ALLAH ya bada zaman lafiya da zuri'a mai
albarka)_*.
Annan take waje ya ɗauki gungunin faɗin amin, yayinda irin su Alhaji Yaro glass ke faɗin (Ba amin ba)
a zukatansu. Gefe kuma daga can wajen masallaci aka shiga busa algaitu daga sarakuna domin
girmamawa ga shugaban ƙasa. Yayinda maroƙa suka shiga kirari da yabo ga ango kuma shugaban ƙasar
NAYA.
Wani irin iska ce mai shiga jiki da sanyi tamkar na tsakkiyar hunturu suka shiga ratsa Ramadhan
batare da yasan dalili ba. Tabbas bayajin sonta, yayi biyayya ne kawai ga iyayensa. Shiyyasa ya rasa
dalilin yanayin daya shiga a yanzun. Dan lokacin aurensa da Amnah tsintar kansa yay kawai da zumuɗin
ganinta a lokacin da aka shafa fatihan aurensu. Saɓanin yanzu da yake jin tamkar an sake aza masa wani
nauyine bisa kansa bayan wanda yake ɗauke da shi. Ya shiga sauke ajiyar zuciya a hankali lokacin da
Bappi ya rungumesa yana musu addu'ar zaman lafiya da fatan alkairi.
★★★
A can gidan su Raudha ma taƙe yake da mutane har wani baya iya jin zancen wani. Amarya na maƙure
jikin Asabe dan zazzaɓi ne mai zafi a jikinta har amai tayi ɗazun saboda takura mata taci abinci da Hajiyar
birni tayi. Kwalliya kam sai da hajiyar birnin da Aunty Hannun sukai tamkar zasu halakata dan bala'i
sannan ta amince akai mata.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta fito tamkar tauraruwa cikin taurari. Tayi ƙyau harta gaji, musamman da
sarƙan gold ɗin wuyanta tai mata wani irin masifar ƙyau da haska fatarta. Duk yanda akaso ta fita tsakar
gida ƙi tayi, dan har aka fara guɗe-guɗe a cikin gidan na jin an ɗaura auren bata leƙo ba, sai ma fashewa
da tai da kuka mai ban tausayi, dan tasan tata ta kare. Wannan auren tamkar mabuɗin buɗe hanyartane
na zuwa lahira ita da wanda ta aura ɗin.
Tana daga kwance tanajin labarin taron mutanen da aka tara wajen ɗaurin auren nata. Sai taji komai
ya kuma kwance mata a ƙwaƙwalwa.
★★★
An kammala ɗaura aure mutane suka fara kama gabansu. Wasu garuruwansu suke komawa, wasu
Bingo. Kafin la'asar sai yazam tsirarun mutane suka rage sai tulin jami'an tsaro. Shi kansa angon ana idar
da sallar la'asar jirgin helicopter yazo ya ɗaukesa. dan tawagar da yazo da ita ta abokansa da abokan
kasuwanci tuni sun kama hanyar Bingo. Ibrahim babban abokinsa tun na ƙuruciya ne kaɗai anan tare da
shi. Duk yanda Ibrahim ɗin yaso yaje yaga amarya tare da sauran abokai ayi hotuna Ramadhan bai bada
fuska ba. Dole suka haƙura tunda sun san gobe idan ALLAH ya kaimu dole ne su ganta a wajen dinner da
kuma rantsarwa ranar lahadi.
Ɗagawar jirgin ango babu jimawa jerrrun motoci talatin cif suka sake shigowa garin Hutawa. Sai na
jami'an tsaro dake biye da su kai kace shugaba ƙasar akazo ɗauka, sai dai kuma ko basuzo ɗaukar
shugaban ƙasa ba sunzo ɗaukar mata kuma amaryar shugaban ƙasa. (😜😜 wayaga Mino first lady. Lol)
A yanzun kam ma kukan Raudha ta kasa, dan anan ɗin ma babu wanda ya zaunar da ita yay mata
faɗa balle nasihar aure ko lallashinta. Damuwarsu kawai karsu rasa motar zuwa kai amarya. Andai kira
Mal. Dauda sunyi sallama. koda yazo shima ɗin sai ya ɓige da matsar ƙwalla yana jaddada mata inhar
bata zauna lafiya gidan mijinta ba harya sakota tai masa baƙin cikin wannan NI'IMTACCIYAR INUWAR da
ALLAH ya tsundumasa sai ya taine mata. Kuma babu shi babu ita. Ko kasheta kullum Ramadhan zai
dingayi ana sake busa mata sabon numfashi baice ta nuna masa damuwarta koda a fuska ba.
Jikin Asabe ya ƙara sanyi da kalaman tsohon mijin nata da ayanzu takema kallon wanda baisan ciwon
kansa ba. Yayinda tausayin ɗiyarta ya ƙara mamayeta. Sai dai babu yanda zatayi dan su Hajiyar birni sun
hanata kowane irin ƙarfin iko na uwa, komai sun mamaye.
Zuwa ƙarfe biyar da wasu mintuna kowacce mota ta ɗauki iya adadin mutanen da zata iya. Yayinda
suka fita cikin garin Hutawa a jere motar amarya a tsakkiya. Gaba da baya jami'an tsaro ne.
Wani irin sarƙewa numfashin Raudha ya shigayi alamar Asthma ɗinta zai tashi, dan kuka. ALLAH yasa
Hajiya mama dake a motar tai saurin fahimta taja hand bag ɗin Raudha da sauri tana laluben inhaler ta.
Da ƙyar ta samota aka shaƙama Raudhan. Sai da numfashinta ya dai-daita suka shiga sauke ajiyar zuciya
ita da Hajiya Zuhrah dake tamkar ƙanwa ga Pa. uwa ga su Ramadhan. Dan kuwa Yafendo ce ta haifeta.
Itace babbar ɗiyarta, sai dai tana Australia tare da mijinta dake matsayin ambasada a can. A yanzu ma
biki ne da bikin rantsar da Ramadhan ya kawosu ƙasar. Komi na kammala kuma zasu juya.
Tuni tausayin Raudha ya sake mamayeta, dan tunda ta ganta ƴar ƙarama take mamakin yanda
iyayenta suka amince suka mata aure (kusan su irin manyan nan wayayyu ƴaƴan sai sunci boko sun
ƙoshi, wani lokacin ma ba bokon ke hanasu yin auren ba, ra'ayine kawai da tunanin za'a yanke musu jin
daɗin rayuwar ƴammatanci ko samartaka. Shiyyasa suke ganin masu aurar da yara 17years zuwa 20
tamkar ganganci sukai🤧).
*_______________________*
*_BINGO CITY_*
Kamar yanda aka nuna ɗaurin auren shugaban ƙasa Ramadhan live a gidajen tv haka aka nuna tahowar
amarya da isowarta bingo ma. Inda duk da ɗunbin mutanen nan dake cike da Taura house da wanda
sukayo ma amarya rakiya hakan bai hana Anne da ke fama da tsufanta ba fitowa tarbar amarya ita da su
yafendo. Fulani na zaune tare da su suka fito amma batako motsa ba. Dan tona irin baƙin cikin da suke
ciki game da auren nan ita da Asmah da gimbiya Su'adah ɓata lokacine. Abinda kawai suka sani shine sun
tanadama Raudha bama-baman bala'in da sai ta gudu gidansu da ƙafafunta. Dan shi kansa Ramadhan
ɗin jiya ya sha masifarsu saboda yace suyi haƙuri shi bazai iya bijirema Pa da Bappi akan maganar auren
nan ba.
Aiko sukai masa ca gimbiya Su'adah harda kuka wai Anne ta asirce mata shi bayajin maganarta baijin
ta mahaifiyarta da ƴan uwanta. Shi dai bai sake ce musu komai ba, da ga ƙarshe ma kiran wayarsa da
akaine tai bailing sa ya samu ya gudu musu. Har zuwa yanzu kuma basu sake ganinsa ba, dan koda ya
baro Hutawa kai tsaye wajen meeting ɗin da zasuyi da shugabannin jam'iyya na jihohi ya wuce.
Sosai ahalin Raudha sunji daɗin tarbar da akai musu. Tun daga kan shimfiɗar fuska har zuwa ta
wajen zama da abinci dana sha koma Alhmdllhi. Mafi yawancinsu kuma ba ƙaramin rikicewa sukai da
ƙaton mansion ɗin na Taura ba. Har takai wasunsu ma sun gagara bakin magana.
Babu wani event a yau, dan Bappi ba mai son yawan bidi'oi bane, shiyyasa da wahala kaga anyi taron
biki a gidan ana wannan events ɗin na almubazaranci da dukiya, komai yana tafiyane gwargwado, sai
abinda ya zama wajibi kamar abinci wannan kam har sai kaci nama ka gaji duk haɗamarka da zura...😜
WASHE GARI ma babu wanda yaga idon ango har kusan azhur, dan jiya bai dawo gidan ba sai kusan 3am.
Hakan ya sakashi maƙalewa a part ɗinsa yaki fitowa. Ko sallar asuba a gida yayi saboda makara da yay.
Masu kiɗan ƙwarya sunyi wasa daga safe zuwa azhar ɗin anan cikin gida. Abin kuma ya ƙayatar da
mutane dan kowa yayi farin ciki. Inda amarya tasha ƙyau harta gaji. Dan nasiha da lallashin da Anne tai
mata a daren jiya yasaka mata nutsuwa ta daure tabar kuka kasancewar a ɗakin Anne ta kwana tare da
ita. Takoji daɗin kasancewa da tsohuwar, tare da ƙarajin ƙaunarta a zuciya da ɓargo.
Ansha ɗinkuna an kuma sha liƙi, abun mamaki harda gimbiya Su'adah da Adda Asmah a masu liƙi, dan
Fulani ce ta basu shawarar suma suje suyi tunda su Hajiya Mufida sunyi. Karta yarda kishiyoyi su fita
nuna iyayi ga auren ɗanta. Irin wannan sakacin tayi tun farko har Anne ta mallake mata shi a matsayinta
na kaka.
Adda Asmah ta rungume Raudha da kanta ke a ƙasa bayan ta gama mata ruwan ƴan dubu-dubu.
“Kinci nasarar shigowa cikin zuri'ar Taura ƴar *_KARUWAI_*”.
A bala'in firgice da rawar jiki Raudha taso janye jikinta. Sai dai Adda Asma ta sake matse a cikin nata
jikin kasancewarta mace mai ƙiba. A kausashe ta cigaba da faɗin, “Sai dai hakan ba shike nuna
Ni'imtacciyar inuwar da kike kwaɗayi keda Karuwan danginki bace kika shigo.....”
Ta saketa tana miƙewa tsaye da ƙyau, ƙasa Raudha tai da kanta jikinta na wani irin rawar tashin
hankali. Adda Asmah ta saka hannunta dake cike da zabban gold da bangles ta ɗago haɓar Raudha.
Idanunta ta tura cikin na Raudha da ƙarfin tsiya tana murmushi, wanda ya gansu daga nesa sai ya ɗauka
wani maganar alkairi da yaba Raudha take. A kausashe da salon murmushin makircin tace, *_“BAƘAR
INUWA_* ce da gwara ranar da kika baro da ita yarinya”.
Ta ƙare maganar da sakin fuskar Raudhan ta sake rungumeta sannan ta saketa. Ko tari gimbiya
Su'adah batai ba. Sai dai fuskarta da ɗan murmushin ƙasaita. Kowa yasan halinta na girman kai shiyyasa
babu wanda ya damu da yanayin nata, dan likin ma data fito taima amarya ya bama wasu mamaki. A
haka dai taron ya tashi ƙwaƙwalwar Raudha a harmutse a kuma cushe. Dan tun kalaman Adda Asmah sai
kawai ta koma ambaton sunayen ALLAH dan shine kawai zai iya zame mata mafita a zuciyarta yanzun.
Tana ɗakin Anne bayan ta idar da salla Fatisa da Fatima zaune kusa da ita suna magana take jiyo ƴar
hayaniya ambaton sunan shugaban ƙasa dake amsa sunan mijinta a yanzun. Idanunta ta ɗan rumtse a
hankali tana jan numfashinta zuwa tsakkiyar ƙirji. Buɗe ƙofar ɗakin na Anne da shigowar mayen ƙamshin
turarensa cikin hancinta ya sata saurin buɗe ido. Ƙirjinta ya ɗan harba saboda haɗa ido da sukai, dan tuni
su Fatisa sun miƙe daga kusa da ita suna gaishe shi. A taƙaice ya amsa musu yana janye idonsa akan
wadda har yanzu bama gama tantance kamanin nata yay ba. Indama ace su Fatima kama suke da ita to
da wahala ya iya ganeta a yanda ya shigo ya samesu.
Tuni Raudha ta janye idanunta tai ƙasa da kai, sai dai jin fitar su Fatisa a ɗakin yasa taji kamar ta
miƙe ta zura da gudu ta bisu su fita tare.
“I..ina y..yini”.
Ta faɗa cikin rawar harshe da in'inar da batasan daga ina ta samota ba lokacin da take jin tamkar
takunsa na kusantota, duk da kuwa akwai lallausan Turkey carpet da ƙamshin daya yake fitarwa ma na
musamman ne tamkar ba ɗakin tsohuwa ba.
“Assalamu alaikum”.
Muryar Anne da buɗe ƙofar suka katse sauraren Raudha da ga jiran amsa gaisuwarta gareshi. A hankali
ta saki numfashin data riƙe a tsakkiyar ƙirjinta tamkar mai jiran ace ar ta haɗiye abinta cikin ciki.
Shugaban ƙasa Ramadhan dake ƙoƙarin ƙarasawa saman ɗaya daga kujera biyun dake a bedroom ɗin
na Anne ya kai zaune yana amsa mata sallamarta. Yayi matuƙar ƙyau cikin shadda ash color data wadatu
da jiƙaƙen ɗinki da ƙyawun surar da ALLAH yay masa. Da gani basai an faɗaba maiƙonta kawai ya isa
amsa ga mai hasashen kuɗinta.
“Wai sai yanzu ake ganinka a gidan nan Ramadhan?”.
Anne ta faɗa tana kaiwa zaune bakin gado gab da Raudha dake a ƙasan carpet. Dan ko Anne tace ta hau
gadon bata iyawa saboda kunya.
Ɗan murmushin daya tsaya masa iya kumatu yayi yana duban tsadadden agogonsa _Breitling_ dake
ɗaure a tsintsiyar hannunsa Silver. “Anne barci ne naji zai halakani shiyyasa na kulle kaina kawai”. Ya
faɗa cikin muryarsa mai faɗi da kauri. Sai dai a hankali yake maganar tamkar baya so.
“To ALLAH dai ya rabamu dayin ragon shugaban ƙasa anan, Aminatu sai kin dage da addu'a kam”.
Yanzun ma gajeren murmushi kawai yayi, sai dai ambaton sunan Raudha da tayi ya sakashi ɗan
dubanta ya ɗauke ido. A ransa ko rayawa yake (a haka dai tamkar mutuniyar kirki, sanin gaskiyar
al'amarinta sai ALLAH). Dan shi tozali kawai da yay da Mal. Dauda jiya ya sake gaskata maganar su Maa.
“Abinci fa?”.
Anne ta katse masa tunani. Agogon nasa ya sake kallo yana ɗan furzar da iska. “Idan da fura kawai a bani
ya isa Anne”.
“Fura kam tayi kaɗan ga wanda baiko karya ba. Banajin ma kaci wani abu daren jiya”.
Ya faɗa a yanayin nuna rauni kamar na shagwaɓa. Kasa daurewa Raudha tayi sai da ta saci kallonsa. A
ranta tana faɗin (humm). Oho baima san tanayi ba. Dan telephone dake kan table Anne tai amfani da ita
wajen sakawa a kawo masa abinci. Babu jimawa kuwa ɗaya daga cikin amintacciyar ma'aikaciyar gidan
ta kawo masu damammiyar fura datasha haɗi da gasashen naman rago mai romo, sai shawarma.
Babu ko jin nauyin Raudha dake zaune ya zare agogo ya gyara zama. Anne ta duba Raudha da keta
wasa da zoben hanunta cikin kulawa. “Aminatu kema ai ba abincin kikaci ba, tashi kije kuci ko ƙyaji
ƙarfi”.
Da sauri Raudha ta girgiza kanta. A ranta tana faɗin (tab ɗi ni zanci abinci da shi?) a fili kam sai tai
saurin faɗin, “Anne na ƙoshi wlhy”.
Lallaɓata da lallashinta Anne ta shigayi amma ta dage ta ƙoshi, harda ƴar ƙwallarta da taso bama
Anne dariya ma.
Duk da a kunnensa suke duk zantukan nasu ko nuna alamar yama san sunayi baiyi ba. Furarsa da
nama yaketa ci a nutse hankali kwance. Hakan yasa Anne taɓe baki tana dubansa, cikin ɗan tsokana
tace, “Da yake mai abincin ma marowacine Aminatu ai kinga yayi shiru dan kar aci”.
Yasan da shi take, dan haka ya ɗago idanu yakalli Annen. Cikin yamutsa fuska yace, “Kai Anne, kunzo
kunce zakuci ne na hana?”.
Addu'ar dawowa lafiya Anne tai masa, hakan yasa itama Raudha a hankali ta furta ALLAH ya tsare
batare da tayi tunanin shi da Annen zasu jita ba. Sai dai kuma amsawar da Anne tai da “Amin ya rabbi
Aminatu” ya sata fahimtar tajita. Shiko bata tunanin ya amsa harya fice abinsa.........✍
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_Typing📲_*
*_Episode 25_*
..........*_8:15pm_*
Gagarumar dinner ɗin da su Alhaji yaro glass da Shugaban ƙasa mai sauka suka shiryama su
Ramadhan ɗin ta fara gudana. Ƴaƴan manya ne da manyan ƙasar kansu kawai kake gani a wajen. Amarya
da ango sunsha ƙyau har sun gaji. Dan zaman bayyana ƙawatuwar shigarsu da docration na wajen ma
ɓata lokacine. Anci ansha daga kayan daɗi kamar babu gobe. Yayinda ango ya hana amarya tashi daga
inda suke zaune ko sau ɗaya. Dan haka wanda sukai musu liƙi ma anan suka iskesu wajen zamansu
sukayi. Cake ma nan aka kawo musu suka yanka a zaunen basu tashi ba. Humm sabon salo kenan wai
rawa agaɓar gacci. Dan kuwa ƴan jarida da masu jiran ayi suce tuni sun sami abin faɗa.
Sai faman cece kuce suke na cewar wai mi Ramadhan ɗin ke ɓoyewane da ya hana a ga matar tasa
yanda ya kamata. Dan kuwa duk da kwalliyar da taci yau fuskarta sanye take da facemask, kuma shine da
kansa ya sanya mata sanda suke tahowa a mota. Ita kanta ta kasa fahimtar minene dalilinsa na son ɓoye
mata fuska a duk sanda suka haɗu? Shin *_BABU SO! MIYA KAWO KISHI?!_* (Wannan littafi na nan tafe
a gareku ba babu so miya kawo kishi? Insha ALLAH😉🤗😄). Bata da mai bata amsa dan haka ta haɗiye a
ranta.
Ƙarfe sha biyu dai-dai aka tashi, bayan mawaƙa kala-kala sun baje basirarsu tunda daga kan na
hausa har zuwa na turanci. Hakama masu wasan barkwanci. Kamar sanda suka taho yanzu ma sun koma
gidane bisa tsaron na musamman daga jami'ai. Kamar kuma ko yaushe har suka iso ɗin ko kallo bai
haɗasu ba ita da shi balle magana. Yay mata rakkiya har ɗakin Anne da basu riga sun iso ba su yay
wucewarsa nasa part ɗin ya barta da sakin numfarfashin data tara a ƙirji. Duk da ko sau ɗaya bai wani
taɓata ba, dan ko hannunta bai riƙeba a wajen dinner ɗin ƙamshin turarensu ya cakuɗe dana juna har
baka iya banbance wanda take yi saboda ƙarfin nasa, ta kwanta lamo a gefen gadon Anne batare data
iya cire ko zobe a yatsanta ba. Batasan mi zatai tunani ba a yanzu, girman mijin nata a mulki, ko auren
nasu da baida alƙibilar kwatantawa?. Rabuwa da iyayenta ko shiga BAƘAR INUWAR da su suke hasashen
Ni'imtacciyar inuwa ce a gareta?. Manufar su aunty Hannah a kan kashe su, ko tsananin ƙiyayya da
ƙyamar da take hange a idon uwar mijinta da sai a yau wajen dinner tasan matsayinta na mahaifiya ga
Ramadhan ɗin?. *_“Ya ALLAH kaji tausayina. Nayi tawassali da sunayenka ƙyawawa masu tsarki. Da kai
na dogara dan bani da kowa sai kai ɗin tun farkon fari. ALLAH ka ƙyautata ni'imarka garemu a ƙarƙashin
wannan BAƘAR INUWA da kowa kema kallon Ni'imtacciyar inuwa a garemu.”_*
Hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunta zuwa kumatunta har saman facemask ɗin fuskarta
da ta gagara cire koda shi ne. A wannan yanayin gidan ya fara ɗaukar hayaniyar mutane alamar an dawo
dasu gida suma. Dole ta miƙe ta fara zare sarƙa da tarkacen jikinta gudun kar Anne ta zargi wani abu.
Duk da kuwa a ranta yanzu hankalinta yafi karkata da kwanciya akan ta tunkari Anne da batun da taji a
bakin su Aunty Hannah. Sai dai kuma bata son tozarta yayar mahaifiyar tata dan koba komai bata da
kamarsu a duniya, tunda gashi har ana aibantata da halayensu da suka aikata tunkan haihuwarta.
★★★
WASHE GARI aka gudanar da rantauwa ga shugaban ƙasa da gwamnoni. Kum harda Raudha shugaban
ƙasa Ramadhan yaje wajen. Sai dai tana cikin dogon farin hijjab da facemask yau ma. Abin ya sake burge
jama'a musamman talakawa. Da kuwa idan akai dubi da yanda mafi yawan matan gwamnonin suka
cakire cikin shiga ta rashin mutunci da kece raini a yau ɗin. Ga gwalagwalai dake ƙyalli da walwali a
jikinsu tako ina. Hatta da Hajiya Fanta da aunty Hannah matan vice president shigar tasu ba'a magana.
Sai dai a kallo guda zaka gane ran Hajiya Fanta a ɓace yake saboda kasancewar aunty Hannah a wajen
bayan mijin nasu yace mata da ita kaɗai zaije banda Hannah. Dan tunda aka maida aurensa da aunty
Hannah suke tafka rigima har yanzu kuma babu daɗi a tsakaninsu, tace sai ya saki aunty Hannah ɗin.
Shiko ya tabbatar mata hakan bamai yuwuwa bane dan Hannah nada muhimmanci a tafiyarsa ta yanzun.
Ga ƴan siyasa kuwa sai suka fara takale-takale da zungure-zunguren batun saka facemask da
amaryar ta shugaban ƙasa ke yawan yi, dan tunda ya far bayyanata wa duniya ranar zaɓe ba'a taɓa ganin
real face nata ba sai da facemask. To yau ma al'amarin yaci uban na da, dan farin siririn gilashi da
Raudha ta saka a idonta saboda kumburin da ya ɗanyi na kuka da rashin isashen barci ya ƙara mata wani
ƙyau da burge mai kallo. Ga facemask da ya saka ba'a ganin ainahin face nata kuma. Sai haka ya zam ba'a
ganin komai nata a waje sai tafukan hanunta kasancewar hijjab ɗin data saka mai hannu ne.
Uban gayyar shima fararen kayane a jikinsa na wani haɗaɗɗen boyal ɗinkin babbar riga. Ya kawo
hularsa tangaran data fita a fice ya murza. Bayan kammala Rantsuwa suka wuce wajen bikin da aka
shirya gudun mawa da ga Mai-martaba. Ƙarfe biyu aka tashi aka dawo da Raudha kawai gida, shugaban
ƙasa Ramadhan kuwa gidan gwamnati aka tafi masa rakkiya. Bayan idar da sallar la'asar aka gabatar da
walima da addu'oi daga manyan malamai har zuwa ƙarfe shida na yamma. Daga haka taro ya tashi lafiya
kuma zuwa anjima za'aima amarya rakkiya gidan gwamnati insha ALLAH tunda angonta ya tsufa acan.
★★★_______★★★
An yima amrya shiri na musamman domin miƙata gidan gwamnati da zasu zauna insha ALLAH. Ba
wasu mutane masu yawa bane zasuyi rakiyar, dan haka da wuri aka kaita ga gimbiya Su'adah da su Adda
Asmah da sauran matan Pa su Hajiya Mufida.
Duk da a lulluɓe fuskar Raudha take da golden color na veil hakan bai hana gimbiya Su'adah jefa
mata kallon tsana ba. Da ƙyar ta iya dauriyar cewar “ALLAH ya bada zaman lafiya”. Daga haka ta tsuke
bakinta. Sai su Addah Asmah ɗinne keta karaɗin kwarara addu'oi ga amaryar da ango. Abinda gimbiya
Su'adah tayi yasa mutane da yawa fara tsarguwa, dan kuwa basuji daɗin yanda ta sallami surukar tata
matar ɗanta na farko ba kuma namiji tallin tal.
Raudha da dai ba sanin mi ake ciki tai ba. Dan kanta a duƙe kuma a lulluɓe. Tunda ba wani farin sani
tai musu ba bata iya tantance muryoyin da sukai magana ba. Daga part ɗin Gimbiya Su'adah part ɗin
Hajiya Shuwa aka nufa da ita. Itako ta mata ƙyaƙyƙyawar addu'a harda ƙyauta da babu wanda yasan
minene a cikin dan an riga anyi packaging nashi da leda mai ƙyalli alamar gift. Hakama Hajiya Mufida
tarba ta mutuntawa taima amaryar da doguwar addu'ar zama lafiya harda fatan nan da baɗi a sake
taron suna. Itama dai tayima amarya ƙyautar cheque na kuɗi da babu wanda yasan adadi tunda a ninke
takardar take. Sai wani ɗan box a cikin ƙaramar bag.
Bisa jagorancin Hajiya Mufida aka kai Raudha ga Pa. Inda shima yay masu doguwar addu'a da nasiha
ga Raudha tare da ƙyautar key na mota galleliya. Sai sashen su Yafendo inda can ɗin ma tasha addu'oi da
kyauta ga dangin su Ramadhan ɗin. Daga haka aka sake maidota wajen Bappi da Anne suka sake musu
addu'oi, Bappi ma yay mata ƙyauta a dunƙule wadda babu wanda yasan minene. Hakama Anne, koda
yake gara na Anne da alama harda kayan turare dan ƙamshinsu tuni ya addabi hancin kowa. _Sisters
turarurrukan *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* daban suke dana saura. Zaka tabbatar
da haka ne kawai yayinda ka mallaki naka. Ba turare kawai take saidawa ba. Harda kayan gyara amarya
galla-galla na musamman da sai an gwada akan san na ƙwarai. Sirrinsu daban ne, idan nace na daban,
ina nufin na daban dana saura😉😘😘🤗_.
Har cikin mota Anne ta kawota, tare da sake musu addu'a domin tuni ango shi ya shiga fadarsa.
Amaryarsa kawai yake jira a kai masa.
Har suka iso a tafiyar da bata gaza mintuna a shirin ba saboda jiniya da aka sakama motocin yasa
akaita basu hanya, wannan yasa suka iso cikin ƙanƙanin lokaci. Amarya dai bata buɗe ido ba yanzu ma.
Sai dai kunnuwanta naji mata yanda ƴan rakiyar tata ke ta yaba wannan katafaren gida first class.
Tsirarun ƴan uwanta kuwa da akazo dasu rikicewa sukai. Bataga laifinsu ba, dan masu shiga ƙasashen
duniyar ma da kuɗin ƙugunsu sun yaba balle su.
Ita dai babu komai a ranta sai addu'oi, dan zuciyarta sai faman tsinkewa takeyi musam da kalaman
su aunty Hannah ke dawowa a cikinta tamkar bitar karatu, sai dai Alhmdllhi mafitar data samu a safiyar
yau da matakin data ɗauka tana fatan zuwa yanzu an kauda matsalar farko da takema fargaba kafin
masu zuwa. Kamar yanda Anne ta gargaɗeta da yin addu'a haka ta dingayi a duk takun da zatayi har suka
iso ainahin cikin babban falon farko na gidan.
Gaban Raudha yay masifar faɗuwa. Tai azamar rumtse idanunta tana ambaton sunayen ALLAH masu
tsarki, daga haka bata sake fahimtar komai ba har suka iso inda aka sanar mata falonta. Kamar yanda
Hajiya Zuhrah da suka iske gidan suna jiransu ta ambata, ita da ƙanen Ramadhan biyu dake aure
Mardiyya da Safina, sai wata cousin ɗin su Pa itama mace mai kirki hajiya Mariya, tun sanda za'ai
rakkiyar shugaban ƙasa suka shigo tawaga akai masa rakkiya tare da su.
“Inaga mu barta iya nan kawai, shi mijin nata idan ya shigo da kansa sai ya kaita ɗakin da yaga ya
dace su zauna ko?”.
Cewar Hajiya Mariya. A tare su hajiya mama suka nuna gamsuwa. Sai dai aunty Hannah ta taɓe baki
dan tasan sun riga da sun zaɓa musu ɗakunan da zasu rayu ta hanyar saka ƙaramin symbol a saman
ƙofar bedrooms ɗin ta ciki bisa shirinsu. Dan haka cikin kwantar da murya tai magana tana duban hajiya
Mariya da murmushi. “Amma auntyna ayi amarya a falo? Kodai muyi haƙuri a kaita nata bedroom ɗin
yazo ya sameta kamar kowacce amarya shima, koba komai zai tabbatar shima a yau ba shugaban ƙasar
NAYA kawai yake ba, ango mai amarya fil a ledarta ne”.
Yanda ta ƙare maganr da ɗan shakiyanci ya sakasu sakin dariyar manya. Hajiya Mariya mace mai
sauƙin kai da fahimta. tace, “Kumafa kin fini gskiya ƴar uwa, dan gara ya tabbatar da gaske muke yau
muke son jika da izinin ALLAH”.
Nan ma dariyar suka sanya, tare da kama Raudha da kanta ke lulluɓe har yanzu, dan sam bama
fahimtar zantukan nasu take ba ita kam. Har bedroom ɗin da suka zaɓa mata aka kaita, sai dai kuma an
samu akasi ba wanda su aunty Hannah suka tanada dominta bane. Amma batace komaiba, ta barwa
ranta zata dawo da kanta tasa Raudha komawa can ɗin cikin sauƙi.
Anan ma dai su Hajiya Mariya Nasiha suka sake mata mai ratsa jiki, kafin su tattara su fito suna mata
sai da safe.
Sai a yanzu Raudha ta samu damar rushewa da kuka. Ta zame ta kwanta kan katafaren gadon da
tasan ko bata kallaba ya haɗu harya gaji. Ji take inama ba'a haifeta tazo duniya ba, inama Abbansu bai
saki momynsu ba har sukazo Bingo. Inama ranar batazo idi ba har ƙaddara ta sakata shiga hurumin Alhaji
Hameed Harith Taura. Inama... Inama.... Inama. Sai dai bakin alkalami ya bushe, bushewa irin wadda
idan akace sai an tausasashi karyewa kawai zaiyi yabar tawada dabin yatsun hannu.
Kuka taci sosai a wajen har kusan rabawar dare, Ba kuma tako ɗaga mayafin nata ba balle ta kalli wani
abu daya shafi ɗakin kamar yanda bata kalli falon da gidan ba sanda zasu shigo, wani wahallen barci da
zazzaɓi suka fara fisgarta, duk da kuwa kafin yau tasan tana da burin ganin fadar shugaban ƙasa tamkar
kowane ɗan ƙasa. Har lokacin babu angon nata babu alamarsa, ta riga da ta fidda rai da shigowarsa, duk
da dama bata sanya ran hakan ba tun farko. Tasan bata kai kodarajar ma'aikatan gidansu ba. Ya amshi
aurentane kawai saboda halacci ga kakansa. Bazai sota ba, kamar yanda itama batajin son sa ko kaɗan a
ranta. Sai dai tana tausayinsa matsayin shugaban ƙasarta dake cikin wani tarko mai wahalar sha'ani da
nazari ga wanda baida yawan maida hankali akan abu. Harga ALLAH tana cikin razanin zantukan su Aunty
Hannah har yanzu. Dan ko maganar aunty Hannah taji a kwanaki ukun nan ji take kamar ta saki gudawa
a wando saboda razana da mamaki. Yanzu miya kamata tayi a wannan ranar da tasan shugaban ƙasa zai
fara kwana a ɗakin da take da tabbacin an haɗa Poison da suka ambata cikin ac ɗin tunda bata da
tabbacin saƙonta ya kai ga Bappi zuwa yanzun? Zata fito ta sanar masa ko zata jira taga idan saƙon nata
yay nasarar kaiwa, ko yaya zatayi?. Wa zata tunkara da sauran batun ya bata shawara ne? Idan ta samu
nasarar daƙile wannan ta poison ɗin ac?. Wane damar yunƙurine da ita a wannan dare na farko a gareta
na shiga BAƘAR INUWA tare da shugaban ƙasarta?, idan tayi yinƙurin faɗa masa ya tuhumeta da a ina ta
sani wace amsa zata bashi?, idan ta iya faɗa masa komai tanada tabbacin zai yarda ba turotan sukai ba
kamar yanda su can yake a garesu zasuyi amfani da ita ne wajen cutar da shi. (“Ki daina yaudararsu, ki
kuma tabbatar musu ke *_BAƘAR INUWA ce_*. Idan kikai wasa da gargaɗina ni zan zame miki *_BAƘAR
INUWAr_* da sai kin gwammaci *_GARA RANA DA NI!_*) furucinsa a randa ta fara ganinsa a TK special
hospital tare da kakansa, cikin halin ciwo take amma ya rumtse ido ya faɗa mata waɗan nan kalaman da
tasan sune gaskiyar abinda ke a ransa. Inaga yanzu kuma da take cikin mugun ƙullin da bashi kaɗai ba,
mutane da yawa ma idan suka ji bazasu fahimceta ba. Dan kuwa ba kowa ya gama yarda domin ALLAH ta
bama dattijo Alhaji Hameed Taura garkuwa ba ranar idi, ciki kuwa harda mijinta, shugaban ƙasarta kuma
a yanzun..
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*N
*_Typing📲_*
*_Episode 26_*
............A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa yana cikin gidan lokacin da aka kawo Raudha, sai dai yana tare
da wasu manyan mutanen ƙasar NAYA da sukazo masa gaisuwar barka da shigowa gidan gwamnati.
Daga haka suka cigaba da tattauna wasu abubuwa da suka shafi ƙasar tare da shi. Zaman saurarensu
kawai yayi da tankaɗa da rai-rayar dukan kalamansu. Alhmdllhi zaman kuwa ya masa daɗi duk da yana
buƙatar son kwanciya ya huta, dan ya fahimci abubuwa da dama wanda ada bai kawosu cikin ransa ba.
Bai samu shigowa ba sai kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare, a galabaice yake da son kwanciya da kuma
jin yunwa, dan haka ido rufe yashigo ciki batare da tunawa da wanzuwar Raudha matsayin mata kuma
amarya a gidan ba.
★★
Hasken ranar daya leƙo ta cikin labulen window ya haske fuskar Raudha ya sata fara motsa idanun
da gyar, dan kanta har yanzu ciwo yake mata har a cikin barci. Idanun ta buɗe da ƙyar kuma a hankali,
sai dai hasken ya sakata sake maidasu ta rufe sannan ta kare fuskar da hanunta. Sake buɗewar tai duk da
nauyin da yay mata. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi, tare da bin jikinta da kalllo zuwa ɗakin, ganin time ya
sata tashi a zabure ta diro ƙafafunta bisa tattausan lafiyayyen carpet dake gaban gadon. Bata da
nutsuwar cigaba da kallo da mamakin ɗakin, ta nufi ƙofar da zuciyarta ke tabbatar mata toilet ne. Ilai
kuwa tayi sa'a dan ta dace da hasashenta. Nan ma bata damu da zaman yima komai kallon ƙurilla ba,
duk da akwai abubuwan kallon kuwa bila adadin, tai alwala ta fito.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin data idar da salla. Tsami da ciwon zazzaɓi dake cin
ƙashinta ya sata yanke shawarar sake komawa cikin toilet ɗin tayo wanka da ruwa mai ɗumi. Sosai taji
daɗin jikinta, sai da ta fito kuma idonta ya raina fata, dan babu kaya ko ɗaya a ɗakin sai na jikinta. Jiri da
takeji da rashin mafitar inda zata nema kayan sakawa ya sata faɗawa gadon ta sake kwanciya tare da jan
bargo ta ƙudundune. Rawar sanyi ta fara a hankali kafin wani zazzafan zazzaɓi da yafi na daren jiya yay
mata rijib.
★★
Tun kammala tsaftar lungu da saƙo na gidan da farar safiya da ma'aikatan gidan sukai shugaban
ma'aikata ya tattaro kowa sukai zaman dakon fitowar first lady dinsu domin gabatar mata da
kawunansu. Sai dai kuma har kusan goma na safe babu ita babu alamarta. Shugaban ƙasa ko tun bakwai
na safe yabi ta sirintacciyar ƙofar da bai zama lallai kowa na gidan ya gansa ba inba wanda suke a
harabar gidan ko aiki ta sashen ba ya fita zuwa office.
Basu gaji ba suka cigaba da zama har kusan sha ɗaya, wasu a cikinsu dai sai ƙunkuni suke a zuciya da
sukar wulaƙancin first lady, waɗan da suke a gidan tun zamanin tsohon shugaban ƙasa na ayyana (ita
kuma da salon wulaƙancin da tazo kenan). Wasu ko masu ɗan hankalin ciki na ayyana maybe ango ya
angwance ne har first lady ɗin kuma amarya ta gagara fitowa. Haka dai sukaita tunani barkatai kowa da
irin nasa hasashen har su aunty Mariya da sukazo kawo akwatinan lefen Raudha suka iso gidan.
Kusan a tare suka iso da su aunty Hannah da sukazo domin amsa. Sai dai halin da suka iske Raudha
a ciki ya sakasu mantawa da wani karɓar lefe ko badawa. Aunty Mariya da tunaninta ya tsaya akan
shugaban ƙasa Ramadhan yayi angwancine amma ya tsallake Raudha ya fita sai faɗa takeyi. Dan duk
wanda ya dubi yanyin Raudha ɗin, da idanunta da suka koɗe saboda kuka dole kai tsaye ransa ya basa
abinda aunty Mariyan ke zargi.
Duk falo suka koma bayan sun mata sannu, aka bar aunty Hannah kawai tare da ita, acewarta zata
taimakawa Raudhan ta gyara jikinta. Dan tasan yaran yanzu da son jiki yanzu haka bata shiga ruwan zafi
ba.
Kalaman aunty Hannah ba ƙaramin ƙona ran Safina ƙanwar shugaban ƙasa dake bi masa a haihuwa
da Aina'u da tazo kallon ƙwaf suke ba. Dan koda akace bara a kimtsa Raudhan Safina ta dubata tunda
likita ce, ca tai bata iya duba patient na gida.
Tsaf aunty Mariya ta fahimceta, dan kaf ƴaƴan gimbiy Su'adah idan ka cire Bilkisu da Basma babu
mai ƙaunar auren Raudha, saboda gimbiya Su'adah ta gama fallashe musu sirrin asalin Raudha ɗin kaf da
cusa musu ƙinta. Su Basma ne kawai basu ɗauki abin da muhimmanci ba. Acewarsu ma ai ba Raudha
ɗince ta aikata karuwancin ba. Talauci kuma ba'a goshi yake ba balle a gane wanda ya fito a cikinsa, su
dai sun son Raudha kodan taimakon kakansu da tayi wanda da yanzu labarin wani ake bashi ba.
Aunty Mariya tasan yanzu Ramadhan zai musu matuƙar wahalar gani musamman a wannan ranar
daya fara shiga office, dan haka tai kiran Anne ta sanar mata suna buƙatar doctor yazo ya duba Raudha
ɗin. Anne da zuciyarta ke mata hashe irin na Aunty Mariya cikin damuwa tace, “Ya cutar musu da yarinya
ko Mariya?!”.
Cikin jin nauyin Annen Aunty Mariya tace, “Anne sai dai haƙuri, ƴaƴan nan namu na yanzu sam basu
da tausayi. Komai yinsa suke da ƙarfin tuwo da tunanin abari ya huce.....”
Ƙwafa Anne tayi cikin takaici ta ballama Shugaban ƙasa Ramadhan da ake kan gaɓar nunawa a
television zaune a office suna gaisawa da vice ɗinsa Alhaji Yaro glass harara. “Kai gaka anan hankali
kwance kabar ƴar mutane a wahale ja'irin kaya”.
Oho baima san tanaiba, hasalima shi har yanzu bai tuna da wata Raudha ba a ransa. Musamman da
tunda yazo office ɗin suna tare ne da vice ɗin nasa, bayan yayi zaman mintuna talatin da wasu manyan
mutane. Yayi ƙyau matuƙa cikin shadda kalar ruwan ƙasa mai ɗan duhu kaɗan sai maiƙo take da ɗaukar
idanu. Ɗinkin babbar rigane daya kara masa kwarjini da girman shekaru ga mai kallonsa. Fuskarsa tayi
fayau saboda ramar da yayi, sai dai wasu kai tsaye suke fassara yanayin cikar haiba da kamalar fuskar
tasa da ya sha angwanci ne kawai. Ga hularsa tangaran dake ta ɗaukar idanu na sake fiddo ainahin
ƙyawunsa kai tsaye.
Anne ta ɗauke kanta daga kallonsa dai-dai sanda aka sake nuno yana musabaha da Alhaji yaro glass,
tsintsiyar hannunsa dake sanye da baƙin agogo da baƙin link mai brown stone suka bayyana. sai zabba
na azurfa biyu dake a yataunsa wanda duk itace ta saya masa su a saudia.
Dattijo Alhaji Hameed Taura ya faɗa lokacin da yake fitowa daga toilet ɗin bedroom ɗin nasa da Anne
ke zaune. Cikin sake ɓata fuska tace, “Da jikanka nake mana”.
Murmushi mai faɗi Alhaji Hameed yayi yana kaiwa zaune kusa da matar tasa ƴar daru. Ya kamo
hanunta cikin nasa idanunsa na yawo a fuskarta. “To amana afuwa dan ALLAH. Insha ALLAH bazamu
sake ba”.
“Ko jikina kunne ne ba yarda zan bazaku sake ba. Amma ina gargaɗinku da ku kiyayeni”.
Tai maganar tana tashi da cire hanunta cikin nashi dan ta ɗakko ɗayar wayarta a ɗaki ta kira Doctor.
Binta yay da kallo yana dariya ƙasa-ƙasa. Banda dai daru irin nata mutum da matarsa sai a hanashi yin
yanda yaso. Shekarar Ramadhan nawa babu aure, kuma shi shaidane Ramadhan baya neman mata tun
yana saurayi balle yanzun. Dole kuwa ya damƙi mace a samu matsala.
Bata daɗe da fitaba ta dawo tana sabuwar mitar ƙin samun Doctor Hauwa'u, dan haka ta sake kiran
Aunty Mariya taji yaya.
Koda aunty Mariya ta ɗaga saita ce tama kwantar da hankalinta an samu doctor da tazo zata dubata.
dan aunty Hannah ta kira wata ƙawarta dake nan kusa da fadar shugaban ƙasar.
Duk da aunty Hannah ta lura zazzaɓi ne kawai da damuwa ke damun Raudha babu wani taɓata da
ango yayi saita zaɓi yi musu ƙarya da zaunar dasu akan hasashensu na cewar ai ta gasa Raudha a ruwan
zafi, dama batayi bane da ƙyau shiyyasa. Shi kuma shugaban ƙasa yana sauri yaje office bai sake taimka
mata ta shiga ba da safen nan.
Kalamanta sun sake baƙanta ran su Safina har Aina'u najan tsaki da hura hanci, zuciyarta kam kamar
ta ɓallo ƙirji ta fito dan takaici. Aunty Hannah najin za'a kira doctor daga Taura house tai ruwa tai tsaki
akan akwai ƙawarta anan kusa zata kirata basai an saka kowa wahala ba. Ilaiko haka akai, Doctor Farhat
tazo ta duba Raudha, ta kuma bata magungunan zazzaɓi harda allura da ledar ruwa ɗaya. Sai suka haɗa
baki koda su aunty Mariya suka shigo nuna musu sukai dai har ciwo shugaban ƙasa Ramadhan ya jima
Raudha, amma basai anyi ɗinki ba zai warke.
Sosai mamaki ya kashe Raudha a kwance, dan kuwa tanajin lokacin da suke ƙulla zancen a toilet da
suka shige, ita kuma ta bisu ta laɓe dan ca take allurar mutuwa zasu mata ma tunda yanzu aunty Hannah
ba'abar yarda bace ba. Sai matuƙar kunya ta hanata iya buɗe ido ta kalli kowa a cikinsu duk da addu'oin
da suke jera mata na samun lafiya da albarka. Ga wani takaicin aunty Hannah da mamakinta. To miye
nayin ƙaryar dan ALLAH anan? Koda ma hakance ta faru sai an fallasata ma duniya da dangin miji.
Har suka bar gidan ran adda Asmah da su Safina a ɓace yake. Aina'u kam ai ba'a magana. Dama can
batazo bikin ba jiya ta iso Bingo saboda bikin rantsar da shugaban ƙasa. Yau ko tazo ne danta gansa duk
da akwai shakkar hakan tare da ita a dalilin wasan ɓuya da sukeyi ita da shi game da wani al'amari daya
faru a america kusan shekara huɗu kenan. Lokacin yana farko-farkon shiga ruɗanin rasa Amnah da
Haseenah.
Bayan wucewar su aunty Mariya, Aunty Hannah da aunty Halima suka buɗe akwatunan lefen suka
gani. Har cikin rai sai da aunty Hannah taji hassada ta soketa, dan ko ita data ɗauka tsahon shekaru tana
kutsetseniya cikin manyan mutane bata taɓa ɗaura wani zanin ba. Kayane masu tsada da ƙyau. Ita kanta
gimbiya Su'adah da wannan takaicin masu kawo lefen suka barota. Aunty Halima dai daɗi taji ta kumayi
addu'a, dan koba komai uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da Asabe. Ballema ita mace ce mai zafi da sauƙi, tana
da kirki kuma da son dangi. Gata ƴar gaskiya da gaskiya. Dan tun bayan auren Asabe itama ta fahimci
aure shine mutuncin ƴa mace ba rayuwar da mahaifiyarsu ta ɗorasu a kaiba. Batai shawara da kowaba ta
nutsu ta tuba, wanda ta tuba dominsa kuma sai ya kawo mata mijin aure cikin sauƙi bisa rahamarsa.
Duk yanda aunty Halima ta hana karsu ɗauki komai aunty Hannah bata saurareta ba. Kowa a
gidansu sai da aka ɗaukar masa wani abu a lefen sannan suka wuce bayan sun damƙa Raudha hannun
Tambaya wai ta kula da ita idan ta tashi a barci. Aunty halima dai ba haka taso ba, taso suyi haƙuri har
Raudha ta farka suji ko tanada buƙatar wani abu, amma babu yanda ta iya tunda aunty Hannah na gaba
da ita.
*_TAURA HOUSE_*
A Taura house kuwa sabuwar fitina su Adda Asmah suka sake kunna gimbiya Su'adah. Wani irin zogi
takeji a ƙirjinta da jin mai rabata da Ramadhan sai ALLAH......
“Wlhy Ramadhan yaban mamaki, banyi zatoba daga garesa, bansan mi yarinyarnan ta mallaka ba da
har ya ruɗesa da kusantar ta....”
A hasale Fulani dake shirye-shiryen komawa masarauta saboda kiran da mai-martaba ya mata tazo
ta tare gidan surukai ta katse Adda Asmah mai maganar a hasale. “Aiko yayi na farko yayi na ƙarshe dan
ubansa. Bandama namiji duk inda yake maye ne (ba ni na faɗaba fulani ce😱) har miye a jikin yarinyarnan
na bibiya. Yayta wani ɗaga kai da izzar banza a waje ashe shashasha ne”.
“Ammy shiyyasa tun jiya nace a fara bata maganin nan na hana ɗaukar ciki ai, shima muyi masa gargaɗin
karya raɓu yarinyarnan dan nidai nasan yanda Ramadhan ya jima babu mace koda bai son yarinyarnan
zaiyi ruwan kashe gobara da ita. Amma sai kukace babu abinda zaiyi da ita. A tunaninku yanda take
ƙyaƙyƙyawa ɗin nan zai iya kauda kansa gareta tunda ma ba tabbacin baya sontane damu ba......”
Gimbiya Su'adah ta haɗiye wasu hawayen baƙin ciki dake neman zubo mata. Cikin kaushin murya da
jin tsananin sakejin sabuwar tsanar Raudha ta katse yayar tata, “Aiko zaiyi aman abinda ya taɓo dan
ubansa. Itako sai na maida rayuwarta abin tausayi a ƙasarnan itada karuwan dangin uwarta da faƙiran
dangin ubanta. Shiko zaiyi nadamar haɗa shimfiɗa da ita da yay, zaizo ya sameni ai”.
Kuka Aina'u ta sake fashewa da shi dan duk suna zaune a falon ita da su Safina. Basma da Bilkisu ne
kawai babu. Lubnah dake bima Safina kam tafi kowa ɗaukar zafi, dan halinta kaf irin na gimbiya Su'adah
ne dama. Rashin son Raudha ya hanata zuwa fadar shugaban ƙasar tun jiya.
Cikin takaici Munirah dake bima Bilkisu ta harari Aina'u. “Wlhy aunty Aina kina bada mata. Miye abin
kuka dan Yaya Ramadhan ya kwanta da waccan wawuyar yarinyar. Nifa kune kuke ganin laifinsa Maa.
Karfa ku manta jinin karuwaice, wama ya sani ko itace taja ra'ayinsa ga hakan tunda iyayenta sun koya
mata. Kuma koba komai ya mora sadakinsa da wahalar da aka sakashi yakeyi na yawon zuwa ƙauye da
kisan kuɗi. Ni dama ya farka shegiya yanda bazata ɗinku ba mtsoww!!”.
Duk da kasancewar Muneera ƙaramar yarinya a cikinsu sai maganarta tai musu daɗi, dan daga
Yusrah sai auta Basma a ɗakin Gimbiya Su'adah, a yanzu hakan shekarun Muneera gaba ɗaya bai wuce
ashirin da ɗaya ba zuwa da biyu. Amma har take iya waɗannan zantukan.
Safina ta ɗanyi dariya, “ALLAH kumafa zancen Muneera haka yake, baima kamata muga laifin
Brother ba. Dan haka kibarma fushi da shi Maah. Yarinyar zamu cima ƙaniya kawai. A kuma ɗorata akan
maganin hana daukar cikin nan da lalata mahaifarta. Sannan tunda Muneera ta kammala karatunta ta
koma can da zama ita da Lubnah, sune zasuci mana ubanta cikin sauƙi kuma suna kawo miki abinda duk
ke faruwa a gidan.”
“Shawararki yayi dai-dai Safina”. Fulani ta faɗa cike da isa da ƙasaita. batare da ta basu damar cewa
wani abuba ta cigaba da faɗin, “Harma da Aina'u. Tsakanin Bilkisu da Basma ma wata taje su haɗu su
zauna”.
Adda Asmah tace, “Eh hakan yayi Ammy. Sai dai kinsan Halin Ramadhan zai iya cewa sunyi yawa.
Kodai su Bilkisun su zauna su”.
“Aiba lokaci ɗaya zasu tafi ba, da daɗɗaya kodan waɗan can tsoffin suma da basa iya gani su ƙyale.
Amma zuwa Basma ko Bilkisu nada nasa amfanin. Su nuna suna sonta suke, zatafi sakin jiki da su har su
san komai nata. Su kuma su Lubnah ta hanyarsu zasu dinga sanin wasu abubuwan ai ko”.
Cikin gamsuwa suke jinjinama Fulani kawunansu. Banda gimbiya Su'adah da har yanzu zuciyarta ke a
matuƙar ƙuntace. Dan ko magana bata iya sakeyi ba.
____________________
A can bangaren su Aunty Hannah ma suna zuwa rabon ganima aka fara, sai dai banda Asabe da
tausayin ɗiyarta ya rufeta game da labarin da aunty Halima ta bata dan itama batasan ba gaskiya bane
tunda aunty Hannah bata sanar mata ba. Taji inama Raudha nada waya yau data kira taji ko muryartane
taji sanyi. Dan rabonta da ita tun randa aka ɗakkota da ga Hutawa. Ita nan gida tayo dama ita da hajiyar
birni. Su aunty Halima ne kawai suka je kai amarya.........✍
*_Hummm🚶🏻_*
________________________
Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama
akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi
anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata
kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu
daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap
yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa
turare ba🤗
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku
hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosaiduk me shakku tayi kokari
tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba
Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge
dukkan dattin jiki
Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu
100%tested nd trusted
Soap price:3k
07046881166
Call 08064532391
Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b
inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏
Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso
yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝
Mg's skincare
_________________________
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_Episode 27_*
*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKK👇🏻_*
https://arewabooks.com/chapter?id=62aa07dd3992cc4a44aaa7a4
________________________
Assalamualaikum lovely brothers and sisters. Please support our YouTube channel *sudais kura* for
Allah sake our channel is all about Qur'an recitation and other Islamic studies 🙏🏼 I am not perfect, but
I'm a mother who love to see kids Recite Qur'an. I'm trying my best with the little I know to install the
love of the holy Qur'an into sudais heart at this young age. Please support our journey by subscribing to
*Sudais kura* YouTube channel 🙏we are planning to start some simple craft and art work too on the same
channel insha Allah. Just subscribe and you will not regret the channel link 👇🏻
https://youtu.be/g6BGEBv-X8Y
________________________
...........*_GOVERNMENT HOUSE_*
Barci sosai tayi har taji babu daɗi. A kowanne motainta Tambaya kan leƙa ta tabbatar tana lafiya.
Bata farkaba sai bayan la'asar. Taji daɗin jikinta sosai dan magunguna masu kyau Dr Farhat ta bata.
Wanka ta farayi mama tambaya ta gyara mata ɗakin tunda dama aikinta ne. Bata tambayeta wacece ita
ba tunda tasan a irin wannan gidan dama dole a samu ma'aikata. Bayan ta gasa jikinta da ƙyau ya sake
warwarewa tayo alwala ta fito. Ɗakin ya sake komawa tsaf sai ƙamshi yake. Batabi takan komai ba ta
gabatar da sallolin dake a kanta sannan ta miƙe ta buɗe akwatinan da aka zube matan. Cikin sa'a ta
samu ɗinkakkun kaya kala kusan biyar da sai daga baya aka amso a wajen tela dan bai kammala mata na
fitar biki ba da a aka kai wancan ranar. Riga ne da skirt na atanfa less Onion color. Sai ratsin milk kaɗan a
jiki da stones da aka kawata ɗinkin da shi. Kayan sun mata ƙyau da fiddo kalar fatarta musamman data
ɗan rame kwana biyun nan.
Duk wanda ya ganta yaga amarya kodan gyaran jikin da tasha na nagartattun kayan *AMARYAR KB
GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* da duk amaryar da akaima gyara da su dole tazama abar kallo.
(Amare dama mata ƴan ƙwalisa dake buƙatar kayan gyaran jiki na musamman, tun daga kan ƙamshi na
turarurrukan gida dana jiki, har zuwa gyaran fata da kayan mata ingantattu ku garzayo ga *AMARYAR KB
GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* domin samun naku kuma. Masu iya magana kance siyen nagari
maida kuɗi gida😘😋🤗), ga lallin ƙafarta da hanunta raɗam tamkar bazai fita ba. Mama tambaya ce tazo ta
sanar mata an shirya mata sabon abinci tunda breakfast ya huce, anma fiddashi tuni. Ta amsa cikin
mutuntawa ga mama Tambaya dan koba komai zata iyama jika da ita.
Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, amma tanajin yunwa. Dan haka tai dauriyar fitowa falon saman
inda mama tambaya ta saka kuku ya shirya abincin. Sosai mamaki ya cikata ganin table ɗin a cike, dan
babu wani zancen ƙauyencin gidan ko tsarin abubuwansu tattare da ita kasancewar an mata lectures na
koma kafin ta shigo. hasalima ta shigo ɗin tun kafin a kawota matsayin matar gidan. “Mama wannan
abinci duk suwaye zasu cisa haka?”.
Kan mama Tambaya dake tsaye a ƙasa tai murmushi. “Ranki ya daɗe ke da shugaban ƙasa ne kawai,
duk da bamu da tabbacin shigiwarsa gida a yanzun”.
Mamaki da takaici ya kume Raudha a rai. dan kai tsaye ta danganta hakan da almazarancine kawai.
Talakawa nawane suke wahala babu ko ruwan kunu da zasu sha a yau, amma an shirya abinci fin kala
huɗu a dining ɗin gidan shugaban ƙasa wai dan shi kawai da matarsa. Tabbas ta sake yarda mulki BAƘAR
INUWA ne kawai. Dan hakkin mutane kawai aka barka da shi ka shiga uku. Ta rumtse idanu da haɗiye
ɓacin ranta, cikin saisaita murya tace, “Mama yayi yawa ai, ya kamata a dinga dafa iya wanda za'a iya ci
kawai ya wadatar. Dan ALLAH daga yanzu a dingayin dai-dai misali. Idan kuma ansan ma shugaban ƙasa
bazai dawo yaci ba adaina girkawa da shi har sai idan shine ya bukaci hakan”.
“Amma ranki ya daɗe haka tsarin yake tun a wancan shugaban kasar mai sauka dana sani nidai.”
“To mama inaso a canja yanzu danni dai bana buƙata sam”.
“Insha ALLAHU za'a gyara ranki ya daɗe, dan dama dai tun ɗazun duk ma'aikatan gidan nan suka
gama taruwa domin gabatar da kansu gareki”.
Duk da gaban Raudha sai da ya tsinke ya faɗi dan fargaba tausayin kanta sai ta dake tace, “Ba
damuwa sai a sanar musu na tashi to”.
Kai kawai Raudha ta iya ɗaga mata, dan babu abinda ƙirjinta keyi sai luguden daka. Ita Raudha,
ɗiyar Mal. Ɗan-azumi da Asabe na Hutawa ce a wannan ajin na ƙaddara. Itace akema wannan
girmamawar duk da ƙarancin shekarunta. Itace matar shugaban ƙasa wadda kowa zai iya kira da first
lady a ƙasar NAYA da ƙetare a yanzun. Itace matar shugaban ƙasa *_Ramadhan B. Hameed Taura_*. Ɗan
ƙwalisar gayen nan maiji da giyar kuɗi da lokaci, ƙyaƙyƙyawa mai girman kai da jan aji wa manyan mata.
Wannan wace irin ƙaddara ce haka mai kama da almara ko hikayoyin marubuta. Badan tayi imani babu
mai iya ja da ikon ALLAH ba da tace kodai ta mutune ko barci take har yanzu komai nazo mata a
mafarkine ba gaske ba. Wannan ƙaddara ta mata nauyi da yawa a zahirin rayuwa da baɗini. Gaskiya
mahaifiyar Ramadhan ɗin ta faɗa ita ba kowan kowa bace, sannan Ramadhan yafi ƙarfin yafi ƙarfin kowa
nata. Sayyadi Abubakar ma da bai kama ko ƙafarsa ba iyayensa suka tabbatar da ya fita balle shugaban
ƙasa.
Waɗan nan tunane-tunanen suka hanata sakin jiki taci abincin kirki har mama Tambaya ta sake
dawowa ta isar mata da saƙon taruwar kowa. Tambayar mizai hana su shigo nan tayi. Cikin girmamawa
mama Tambaya tace, “Ranki ya daɗe basu da wannan hurumin sai mu huɗu kawai. Ni da Chief kuku da
mai gyaran ɗakin shugaban ƙasa sai mai gyaran falon nan kuma.”
Ɗan jimm Raudha tayi tana dubanta, sai dai komai bataceba ta miƙe da ɗaukar milk gyalenta data
fito dashi ta yafa har saman kanta sannan suka fito. Tana gaba mama Tambaya na take mata baya
★Falo ne babba da za'a iya kiransa mafi girma a duk falukan gidan. Komai na cikinsa kalar tutar ƙasar
NAYA ne. Ya ƙawatu matuƙa da kayan more rayuwa. Ma'aikatan da adadinsu zai kai kusan hamsin suka
rissinar da kai domin girmamawa. Gareta suna miƙa gaisuwa. Duk da ba kabilarta bane su duka haka ta
amsa musu cikin mituntawa dan babu wanda bai kere shekarunta ba a cikinsu.
Shugaban ma'aikata na sashen nata ne ya fara gabatar da kansa, sai shugan kuku's da sauran kukus
ɗin, sai Mama Tambaya da mai gyaran ɗakin shugaban ƙasa. Kafin sauran su cigaba ɗaya bayan ɗaya.
Tun ma Raudha na fahimtarsu har da daina tunaninta ya tafi wani wajen da ban. Cikin nutsuwa ta ɗaga
musu kai da fara faɗin,
“Masha ALLAH naji daɗi, ina kuma fatan zaku riƙe amana dan nasan babu wani addini dake goyon
bayan cin amana ko zalunci. Bazance karku cutar damu ba ko a haɗa baki daku wajen cutar damu. Sai dai
zance kuji tsoron ALLAH karku zaluncemu da son zukatanku ko biyewa ruɗin kuɗi. Idan kun kiyaye kuma
ALLAH zai kiyayeku ya ɗaga darajarku zuwa wani matsayi da baku taɓa zato ba. A duk lokacin da bawa ke
tsoron rasa wani abu wani nacan ya samu yayi shi. Idan murna da farin cikin samu kake wani nacan shi
kukan rasawa yayi. Sai musa a ranmu duk zamu iya zama ɗaya daga cikin wannan matsayin. Dan a
duniya babu mai wahala sama da _mai buƙatar abu a lokacin da abun baizo ba. Da kuma mai ƙin abu
bayan ana tsaka da samuwar abun_. ALLAH yasa mu dace, ya bamu ikon sauke nuyin juna bisa bigiren
tsoron ALLAH da cire son zukatanmu ko yanke hukunci akan umarnin zuciya”.
Sosai sunji daɗin kalamnta, wasunsu da zamansu nada alaƙa da kalamnta na son cutar dasu sai jikinsu
ya fara sanyi. Gata dai ƙaramar yarinya amma tanada cikar kamala da kwarjinin manya. Uwa uba iya
sarrafa harshe cikin taka tsantsan da mutunta kowa. Wasu kuwa da yake zuciyar ta bushe ko'a jikinsu, a
ganinsu ma ta cika iyayine da son nuna ita mai addini ce.
Sun shiga mata godiya bayan ta sallamesu. Daga haka ta koma ciki abinta. Zaman ɗaki ta cigaba dayi
har ƙarashen wannan yini babu shugaban ƙasa babu alamarsa. Maganinta da tasha ya sata barci da wuri
ma batare da ta damu da yanda wanda ya aurota ya banzatar da ita ba.
Yau kwankin shugaban ƙasa da amaryarsa biyu kenan a gidan gwamnati, sai dai tunda suka shigo
gidan babu wanda yaga ɗan uwansa. Dama Raudha bata saka a ka ba, sai dai duk sanda za'a nunasa a
television takanji wani iri a ranta tamkar mai ganin laifinsa. A gefe kuma tana yaba iya tsara adonsa da
kyawun haiba da ALLAH ya bashi. Shi mutum ne da ko yaya yasa sutura ko badan kwalliya ba saita nuna
kanta a jikinsa, koda bamai muhimmanci bace da rashin tsada. Abu mafi ɗaukar hankalinta shine ƴar
tsagar kan girarsa dake nuna tamkar irin ta gayun zamani, tunaninta ya tsayane kawai akan ya bada
wanzami yay masa hakane saboda gayu. Bama ita ba, mafi yawan mutane haka suke fassara tsagar dake
kwance da wani salon style tamkar an tsara bisa girarsa ta dama. Da ace tanada dama da saita masa
tambaya akan tsagar.
Ba komai yake mata daɗi ba a gidan, musamman abinci da kaɗaici suna sukar ranta. Sam girkin su
kuku baya mata ɗan ɗanɗano a baki, ga kewar momynsu da ƴan uwanta musamman Yasmin da suka
shaƙu matuƙa. Kai har ƴan hutawa kewarsu takeyi sosai. Sai kwaɗayin karatunta na islamiyya.
A tarewar tasu sau uku tai baƙi manyan mata masu ji da kansu da zasu iya haifarta har jika da ita ma,
wai matan gwamnoni ne sunzo gaisheta. Sai wasu kuma matan manyan ƙasar ne ƴan siyasa. Ita dai nata
gaisuwane a garesu da godiya. Dan duk da ƙarancin shekarun Raudha nasihar sayyadi Abubakar ta jima
da maidata mai halin manya. Tanada nutsuwa da zuciya, ga miskilancin tsiya. shiyyasa takeda
takatsantsan akan abubuwa masu muhimmanci. Ba komai takema garaje da rawar kai ba har saita nutsu
ta fahimcesa. Hirarsu Aunty Hannah na taka rawar gani wajen bude mata ido da sanya ido ga duk wanda
zai raɓeta a yanzun. Dan zuciyarta ta kasa yarda da kowa da komai na gidan. Kullum kuma cikin yin
nazarin ta yaya zata kuɓutar da shugaban ƙasa take.
A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa yayi matukar zama busy ne. Sam baya samun kansa yanda ya
kamata a kwana biyun nan da fara shigarsa office. Wani abu daya faru randa ya fara zuwa office ya
sakashi fara binciken wani abu akan jerin sunayen cabinet ɗinsa da suka tattauna akan zai naɗa. Sai dai
kuma yana gabatar da su ga mashawartan nasa wasu a cikin manyan jam'iyyasa sukayo masa ca akan
akwai tsarin da sukebi wajen naɗa cabinet na shugaban ƙasa. Shi kuma a take zuciyar maza ta motsa
yace bai yarda ya hau kujerar dan ya zama a ƙarƙashin mulkin mallakar wasu ba, dolene a barsa da
zaɓinsa ya samu abokan aikin da zai sauke nauyin talakawan ƙasa. Ja'inja ta ɓarke sosai a tsakaninsa da
su wannan shine ya ƙara ɗauke hankalinsa ga Raudha har ma da su Gimbiya Su'adah data cika tai fam da
tunanin ɗan nata na can na rugurguzar amarci da holewa a gidan gwamnti ya manta da su.
Tayi kiransa har sau uku amma bai daga ba. Daga karshe kuma tama bar samunsa kuma bai biyota ba.
Abun nan ya sake harzuƙa mata zuciya dajin tsanar Raudha. Sai dai UBANGIJI shine kawai masanin gaibu
akan abinda zuciya ke hasashe babu tabbaci. Abinda gimbiya Su'adah bata sani ba shine shugaban ƙasa
baima da lokacin kansa. Dan cikin kwana biyu kawai su Alhaji Yaro glass sun gama hargitsa shi, harya fara
hange da saka inuwar mulki a jerin BAƘAR INUWA ce kawai ga wanda ya tsinci kansa a cikinta. Wayar da
duk family contacts nasa ke ciki a gida yake barinta, hakan yasa taketa kira ba'a ɗaga ba bakuma a bita
ba. Daga karshe ta mutu saboda karancin caji. Shugaban ƙasa bai luraba kuma sai yau da kewar su Anne
ta ishesa yaga ya dace ya kira. A gefe kuma yana buƙatar yin magana da kakansa akan wannan rikicin
nasu na fidda sunayen cabinet ɗin dake faruwa tsakaninsa da ƴan jam'iyya. Dan bai tunkaresa da zancen
bane a tunanin zai iya shi kaɗai, yanzu ko yana buƙatar shawarar sa.
Sai da yay ma wayar caji kafin ya kunnata, da saƙon gimbiya Su'adah ya fara cin karo. Yay ɗan tsamm
kafin ya buɗe ya duba. Tun a layuka ukun farko na saƙon zuciyarsa ta tsarga da abinda ya ta rubuto, ya
ɗan dafe kai yana rumtse idanunsa da cije baki, sai kuma ya buɗe idanun ya ƙarasa karantawa. Missed
calls ɗin nata ya duba, kafin ya ajiye wayar yana jan numfashi da ƙyar. Yasan Maihaifiyarsu mutum ce
mai saurin fushi, sannan tanada yanke hukunci akan abu batare data bincika ba. To amma a wannan
gaɓar maganarta ta tabbatar masa da cewar tana da hujja, dan kuwa ko Anne idan bai manta ba a ranar
ta turo masa wani guntun saƙo itama mai nuni da faɗa akan abinda yay ma yarinyar da shi tunma da aka
kawota gidan bai ko ganta ba. Leɓensa na ƙasa ya tura cikin baki yana ɗan taunarsa kaɗan-kaɗan. Tuni
idanunsa da gaba ɗaya sun koɗe saboda rashin isashen barci da samun hutu suka sake rinewa da takaici.
Mi yarinyarnan ke nufi da abinda tayi? Itace ta faɗa musu ya aikata wani abu da ita kenan? Maganar
mahaifiyarsa ta wancan daren ta shiga dawo masa a cikin kai, sai dai kafin tunanin nasa yakai ko ina kira
ya shigo a wayar. Tun kan ya ɗaga yasan Anne ce, dan ita da Pa da Bappi da Maa duk ya banbanta musu
ringtone. Cikin furzar da fushinsa ya ɗaga yana kaiwa kunne.
Daga can Anne ta ɗan sauke ajiyar zuciya, cikin damuwa tace, “A tunaninmu dawowa ka mulki ƙasar
NAYA zai kusantamu da kai ne? Sai gashi yana sake nisantamu Ramadhan ”.
Murmushi ya ɗanyi mai sauti, cikin tsokana yace, “Ba kune kuka jawo hakan ba Anne.”
Murmushi ya sakeyi mai faɗi, ransa fal ƙaunar tsohuwar. “Am so sorry sweet Anne na, wasa nake miki”.
Itama murmushin tayi da ga can, har yana iya jiyo sautinsa. Ta cigaba da faɗin, “Shike nan ko waya
ma ta gagara muyi da shugaban ƙasar NAYA, sai dai mu gansa a television”.
“Kuyi haƙuri Anne, ni kaina tausayin kaina nakeyi, babu komai a mulkin nan sai baƙar izaya. Wanda ke
nesa damu ne suke hangenmu cikin wata ni'imtacciyar inuwa, amma wlhy Anne mulki BAƘAR INUWA ce
kawai...”
“Asha Ramadhan! Asha. Karna sakejin hakan kaji, komai na rayuwa jarabawace kawai da rubutacciyar
ƙaddara. Ka zama jarumi mai magana ɗaya kawai, sannan jajirtacce wajen tunawa da ɗunbin talakawan
da suka dage rana da dare wajen ganin ka zama shugabansu. Ka kuma zama mai haƙuri da juriya kamar
yanda na sanka kaji”.
Numfashi ya sauke mai nauyi, cikin ƴar nutsuwar da kalamanta suka bashi yace, “Inaha ALLAHU Anne
nagode sosai ”.
“Babu damuwa. Ina Aminatu? Yanda kai wahalar ji itama tayi, har yanzu ban samu damar jin yaya
jikinta ba haɗani da ita”.
Ɗan jimm yayi na alamar ɗaukewar numfashi, sai kuma ya shiga lalubo abinda zaice domin kare
kansa. Sai dai ƙarya ba halinsa bace, dan haka harshemsa ya suɓuce wajen faɗin, “Tana ɗakinta”.
Kamar Anne zatace wani abu sai kuma ta share, sai kawai tace, “Daure ka haɗani da ita naji yaya
take?”.
Baida wani zaɓin daya wuce bin umarninta. Dan haka ya amsa mata da cewar, “To Anne zan kira”.
Komai bata sake cewa ba ta katse kiran. Miƙewa yay cike da nutsuwarsa, ya ɗauka t-shirt mara nauyi
baƙa ya sanya, tare da baƙin 3quarter na wando. Ya shigo gidane da wuri saboda burin yin barci, dan ko
sallar magrib da isha'i ma a massalacin gidan yayi su. Slippers masu taushi baƙaƙe ya saka a ƙafarsa ya
nufi ƙofa, sai kuma ya tsaya cak riƙe da handle ɗin ƙofar, dan haka kawai ya samu kansa da buƙatar
sanya turaren da bai sakama jikin nasa ba, sai dai duk da haka yana ƙamshin sabulan wankansa, suma
kayan suna nasu ƙamshin na kaya da yakan ajiye a Wadrobe, tun yana ƙaraminsa Anne ke masa haka,
koda ya girma abin ya zame masa jiki koda yaushe zaka samu turaren kaya a Wadrobe ɗinsa.
Komawa yay da baya-baya yana ɓata fuska tamkar wanda akaima dole, ya sako turare kala biyu masu
sanyin ƙamshi sannan ya fice. Duk wanda ya kallesa ya kalli yanayinsa dolene ya dangantashi da mutum
mai girman kai, dan ko a tafiya abinda ke gabansa kawai yake kallo, sannan ba kowa bane yake ganin ya
isa ya saka a sabgar rayuwarsa koda ta magana ce. Ko abokai sai ya gadama yake kula wasu. Ba kuma
wai dan baya magana bane ko dariya, dan ko kusa baya kama da miskili. Mutum ne shi mai surutu a inda
yaso ga kuma wanda yaso..........✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke
gani a WhatsApp_*
_Safiyya Huguma_
_Billyn Abdul_
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
1487616276
Access bank
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza
garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka
labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa
zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna
ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan😍😘😍🥰😍😊_.
28